Sunday, June 21, 2015

Tsokaci Kan Azumi #Ramadan 2015


TSOKACI KAN AZUMI #RAMADAN 2015

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, Yace duk wanda ya ciyar da mai Azumi yana da kwatankwacin ladansa. Da yawan al'umma da sun fahimci wannan magana ta Manzon Allah SallLlahu Alaihi Wasallam, da kowa ya kasance mai kokarin ciyarwa, ba wanda ake ciyarwa ba. Haka kuma, Manzon Allah tsira da Amincin Allah su kara tabbata a gareshi yana cewa, ku fanshi kanku daga wuta ko da kuwa da tsagin dabino ne.

Babu shakka wadannan maganganu guda biyu suna nuna mana tsananin kwadaitarwa da ciyarwa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yayi mana umarni da su. Sai dai kadan ne daga cikin al'ummarmu suka fahimci wadannan maganganu biyu masu matukar muhimman. Allah ka bamu ikn ciyarwa da dan abinda muka mallaka.

Yasir Ramadan Gwale
21-06-2015

Wakar Gaskiya Ta Marigayi Sa'adu Zungur



WAKAR GASKIYA TA SA'ADU ZUNGUR

In za Ka faďi, faďi gaskiya,
Kome taka ja maka ka biya! "
Sai mu gode Allah shi ďaya,
Don Shi ne sarkin gaskiya.

Ya mallaki dukkan talikai,
Na kwari da tudu da samaniya.

Da mutun, aljan damala'ika,
Dabbar sarari Da ta Malaya.

Mulki, iko, daula duka,
Na ga Sarki Allah shi ďaya.

Shi ya ke ba wanda ya so duka,
Ya sarautu a lardin duniya.

Shi ya ke karbe ta ga talikai,
Don ya ďanďani wahalan duniya.

Shi ka girmama Wanda ya so duka,
shi ka sanya waďansu su sha wuya.
Shi ka cusa dare a cikin wuni,
Kuma ya zaro hasken dariya.

Shi ka rayawar mamaci,
Shi ke kashe mai rai, shi ďaya.

Ikonsa a kan kome ya ke,
A ruwa Da tudu da samaniya.

Alwakilu, mu dogara duk garai,
Zahirinmmu Da boye a zuciya.

Mu amince, zai mana taimako,
Na hakika inda majaziya.
-(Mohammadu, 1972) KA KOYI KARATU 4)

Yasir Ramadan Gwale
21-06-2015

Tuesday, June 16, 2015

Albashi Da Alawus Din 'Yan Majalisu


ALBASHI DA ALAWUS DIN 'YAN MAJALISU 

Indai da gaske wannan canji an same shi domin al'ummar kasa, da  sake gina kasa da hidimtawa al'umma, to ya kamata a zaftare wannan mahaukacin Albashi da alawus na 'yan majalisu. Kai jama’a! Ana maganar wasu jihohi ba su da kudin da zasu yi Albashi,  amma ace kudade masu tarin yawa suna shiga aljihun 'yan majalisu ba tare da sun yi wani aiki mai yawa ba da suka cancanci wannan kudi. Wannan abin yayi kama da yiwa 'yan Najeriya fashi, ace wadannan mahaukatan kudade zasu dinga shiga aljifan 'yan majalisu duk Shekara. Gaskiya da sake.

YASIR RAMADAN GWALE​
16-06-2015

Sunday, June 14, 2015

Su Waye Ke K'ok'arin Ganin Bayan Dr. Ahmad BUK?


SU WAYE KE K'OK'ARIN GANIN BAYAN DR. AHMAD BUK?

Kamar yadda labari ya bazu cewar Khalifan Tijaniya Isyaku Rabi'u da sauran jagorancin  dari'kar sun shigar da Babban Malamin Hadisi na Tudun Yola Dr. Ahmad Ibrahim BUK k'ara wajen Shugaban shiyya ta d'aya ta rundunar 'yan Sanda ta k'asa dake Kano, Tambari Yabo Mohammed akan zargin sa da suke ya aibata Shehunsu Inyass Kaulaha! 

Babu shakka wannan abu da ya faru, mun ji dad'i kuma mun yiwa Allah godiya domin ya tabbatar da cewar Dr. Ahmad ba k'arya yayi ba da yayi rantsuwa da Allah  yace "wallahi yadda suke girmama Shehunsu basa ganin Girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam haka" hakika a wannan marra, Allah ya kubutar da Malamin Hadisi Dr. Ahmad ga masu ganin baiken kalaman sa. 

Haka kuma, a cikin raddin da Dr. Ahmad d'in yayi bayan waccan tab'argaza da kafurci da Abul Inyass yayi da sunan Tijaniya, Malamin Hadisin Dr. Ahmad ya kalubalanci 'yan Tijaniya akan su zo a zauna a gidan Radio a yiwa al'umma bayani, yace Darul Hadith zata biya kudin a ji shin sharri ne ko karya ake yiwa Inyass Kaulaha, amma suka k'i amsa wannan gayyata suka b'ige da bita da k'ulli.

Ni ina ganin abinda ya kamata su Khalifa Isyaku Rabi'u suyi kenan, na amsa waccan gayyata da shi Malam yayi ya kuma ce zasu biya kudin ko awa nawa za a yi a Freedom Radio da Rahama da Radio Kano, domin bayyanawa al'ummar da suke ganin abin ba haka yake ba. Ko kuma su 'yan Tijaniya su kare abin da hujja su ce ba haka bane.

A dan haka, wannan abu, babu abinda zai k'ara illa k'ara tsiraita Tijaniya da kuma d'aukaka darajar Malamin Hadisi Dr. Ahmad Ibrahim BUK. Idan kuma sun gayawa Tambari Yabo cewar Malamin Hadisin ba d'an Najeriya bane, sai muce ai Shima Inyass Kaulaha  din ba dan Najeriya bane, mutumin kasar Senegal ne.

A sabida haka, muna kara jaddada cewar wallahi summa tallahi Martaba da Darajar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam tafi ta uban kowa, kuma tafi ta ko wanne irin Shehu na da da na yanzu. Kuma Alhamdulillah wannan lokaci ne da al'umma zata fahimci hak'ik'anin abubuwan da suke cikin Tijaniya da littattafan Inyass Kaulaha. 

Malaminmu Dr. Ahmad Ibrahim muna tare da shi kuma muna goyon bayan dukkan maganganun da yayi na rushe wannan kafurci da yake cikin Tijaniya. Wanda duk ya kuduri aniyar ganin bayan Malamin Sunnah ko waye Ya Allah ka nuna mana karshensa, Ya Allah ka bakanta musu ciki da samun d'aukakar Sunnah, Allah ka dirkake Bid'ah da dukkan dangoginta. 

Daga karshe kuma, muna kira ga Babban Kwamandan Hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa, kamar yadda ya bada sanarwa cewar hukumarsa ta karbi gabarar wannan Shari'ah da aka kai wannan zindiki Batijane da ya zagi Manzon Allah Sallallahu was Alaihi  Wa Sallwm cewar muna nan muna bin bahasinsu. 

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam na dukkan Musulmi ne dan haka ne al'umma a ciki da wajen jihar Kano hankalin su ya tashi akan wannan batu. A bisa jagoranci da Hukumar Hisbar Kano suka ce sunyi na wannan Shari'ah zamu dinga matsa muku lamba har sai an hukunta wannan zindikin, idan ba haka ba kuma kun yaudari jama'a kuma Allah ba zai kyale ku ba.

Ya Allah ka tozarta duk wanda ya tozarta ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam akan Shehunsa. Ya Allah ka la'anci duk wadan da suka fifita wani Shehunsu akan ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah kayi dadin tsira a gareshi da Alayensa da Sahabbansa da wadan da suka biyo Tafarkin su da kyautatawa har  ya zuwa ranar sakamako. 

Yasir Ramadan Gwale
14-06-2015

Friday, June 12, 2015

Mutuwa Rigar Kowa


MUTUWA RIGAR KOWA

A 'yan kwanakin nan naga mutane da yawa suna ta bayar da labarin rasuwa nan da can, wasu iyayansu wasu 'yan uwansu, wasu 'ya 'yansu wasu dangi wasu Abokai da sauransu da dama Allah ya jikan Musulmi.

Hakika nima a Makon jiya da wannan satin anyi rasuwa uku da ta girgizani ainun. Abokinmu Muzammil Ahamad Jihar yaro matashi da kuma wasu Abokanmu su biyu da suka rasu sakamakon kad'e su da mota tayi a Makon da ya wuce, rasuwar da ta girgiza mutane da yawa a Khartoum.

Haka kuma a wannan satin na samu labarin rasuwar Shamsiyya Lawal Gwale, Alal hakika naji wannan rasuwa sosai, tare aka sanyamu a Gwale Primary da Shamsiyya, muna mutunci da zumunci har zuwa lokacin da tayi aure. Ina yiwa mijinta Basiru Miller Gwale ta'aziyar rasuwar ta, da kuma 'yan uwa da dangi musamman Babban yayanmu Pharm. Ibrahim Lawal​ Allah ya jikanta ya gafarta mata.

Yadda muke karanta labarin rasuwar wasu haka muma watarana za'a karanta labarin rasuwar mu. Zato zo mana ko mun shirya ko bamu shirya ba, Malamai suka ce babu wani wa'azi ko nasiha ko Jan hankali da ya kai mutuwa, domin ita ce, mai yanke komai, wanda duk ya Rasu to shi kenan haihata haihata tasa ta riga ta kare.

Dan haka irin wadannan labari da muke samu na rasuwa nan da can, tabbas, wata rana muma zata zo kanmu, muna sane ko mun gafala. Dan haka muji tsoron Allah mu sauya halayenmu daga munana zuwa kyawawa, daga masu zafin zuciya zuwa masu saukin rai,  daga masu tsanani zuwa masu hakuri. 

Ya Allah ka jikan mamatanmu,  ka yafe musu laifukan su da dukkan kurakuransu, Allah ka sadar da su da RahamarKa, mu kuma da muka Rage Ya Allah ka sa mu cika da Imani, Allah kasanmu kasan halayenmu, Allah ka yafe mana laifuka da kurakuran da mukai maka muna sane ko mun gafala, Allah kai mai afuwa ne kana son Afuwa, Allah kai mana afuwar laifukanmu,  Allah ka lullubemu da RahamarKa. 

Yasir Ramadan Gwale​
12-06-2015

Tuesday, June 9, 2015

Shugabancin Majalisa: Lissafi Ya Kwacewa Shugabancin APC


ZAB'EN SHUGABANCIN MAJALISA: LISSAFI YA K'WACEWA SHUGABANCIN APC

Abin mamaki ne a wannan lokacin uwar Jam'iyyar APC ta kasa ta nuna fushi ko damuwa akan zaben da akaiwa Sen. Abubakar Bukola Saraki​ da Dogara Yakubu a matsayin sabbin shugabannin majalisar Dattawa da ta wakilai. Sune fa Shugabannin APC suka dinga bin su Bukola da Gwamnonin PDP biyar da sukai mata tawaye gida gida suna rokonsu Allah su shigo APC, suka amsa wannan kira suka shiga aka nuna musu babu wani bambanci kowa daya ne.

Wadan da suka sha wahalar kafa APC akai fatali da su, aka nuna su ba komai bane, aka fusatasu da gangan suka d'an su fice, aka nuna su Bukola sune mutanan kirki. Sai yanzu da aka kafa Gwamnati ake neman kwashe musu kafa, su Bukola suka had'a kansu suka samarwa da kansu makoma, sannan ne shugabancin APC na kasa suka fahimci cewar wadannan shigogo ne a cikin jam'iyyar? 

Ba shakka wannan zabe da akaiwa Bukola Saraki da Yakubu Dogara ya dace, domin ko babu komai ya nuna tsantsar Demokaradiyya, domin hakan ya tabbatarwa duk wani wanda yake jin cewar shi ne ya mallaki APC sai abinda yake so shi za ai, to zai gane cewa kan mage ya waye, ba kowa bane Bayerbe. Idan ana batun Demokaradiyya to tilas a bar kowa da ra'ayinsa. 

Wannan Zabe da akaiwa Bukola Saraki da Dogara Yakubu yana bisa doron Demokaradiyya, hakan kuma ya dace. Ai idan ba lissafi ne ya kwacewa shugabancin APC ba, jagororinta a baya sune suka zuga 'yan majalisun ACN da ANPP da CPC da wasu daga cikin mambobin PDP akan su bijirewa 'yan takarar da PDP ta tsayar su zabi  Aminu Waziri Tambuwal, kuma akai hakan. Shin tsammaninsu PDP bata dauki darasi akan abinda ya faru ba?

A ganina wannan shi ne tsantsar Demokaradiyya,  domin samun wannan shugabanci zai taimakawa shi kansa Shugaban kasa Muhammadu Buhari​ wajen aiwatar da aikin sa ba tare da tunanin cewar wani mutum shi kadai ra'ayi sa ya rinjaye na kowa ba, kuma abinda yake so shi za ayi. 

A dan haka wannan babu abinda yake nufi zai tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mutum daya ba zai iya saka al'ummar Najeriya a aljihunsa shi kadai ba, ya zama ba abinda zai faru a Najeriya sai abinda yake so. Ina amfani da wannan damar wajen taya sabon Shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ikweremadu murnar wannan zabe da akai musu, haka shima Dogara muna taya shi murna.

Yasir Ramadan Gwale​ 
06-06-2015 

Ashe Dogara Ma Ya Kada Femi Babanjamila


ASHE DOGARA MA YA KADA FEMI BABANJAMILA??
Yanzu dai babu ko tantama cewar, Shugabannin Jam'iyyar APC ba su da wani iko akan 'yan majalisun da suka ci zabe karkashinsu, dazu a majalisar Dattawa an Kada wanda jam'iyar ta nuna inda aka zabi Abubakar Bukola Saraki tsohon dan PDP wanda ya shigo APC daga baya, bayan ta gama nuna.
Ya zu ma gashi a majalisar wakilai an zabi sabon Kakakin Majalisar Hon. Dogara Yakubu, wanda shima tsohon dan PDP daga jihar Bauchi, ya shiga APC ne bayan D ta gama nuna. Wannan yake nuna cewar 'yan majalisun guda biyu sun kawo karshen fad'a a jin da Jagoran APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake da shi a jam'iyar. Zamu jira muga irin yadda itama majalisar karkashin Dogara zata yi nata rabon mukamai din.
Ko za'a samu jituwa tsakanin Bangaren Majalisar wakilai karkashin Jagorancin Saraki da Dogara da kuma Majalisar Zartarwa karkashin sabon Shugaban kasa. A baya dai mu ga yadda akai zaman do ya da man ja tsakanin Goodluck Jonathan Da majalisar wakilai.
Yasir Ramadan Gwale 
09-06-2015