WAKAR GASKIYA TA SA'ADU ZUNGUR
In za Ka faďi, faďi gaskiya,
Kome taka ja maka ka biya! "
Sai mu gode Allah shi ďaya,
Don Shi ne sarkin gaskiya.
Ya mallaki dukkan talikai,
Na kwari da tudu da samaniya.
Da mutun, aljan damala'ika,
Dabbar sarari Da ta Malaya.
Mulki, iko, daula duka,
Na ga Sarki Allah shi ďaya.
Shi ya ke ba wanda ya so duka,
Ya sarautu a lardin duniya.
Shi ya ke karbe ta ga talikai,
Don ya ďanďani wahalan duniya.
Shi ka girmama Wanda ya so duka,
shi ka sanya waďansu su sha wuya.
Shi ka cusa dare a cikin wuni,
Kuma ya zaro hasken dariya.
Shi ka rayawar mamaci,
Shi ke kashe mai rai, shi ďaya.
Ikonsa a kan kome ya ke,
A ruwa Da tudu da samaniya.
Alwakilu, mu dogara duk garai,
Zahirinmmu Da boye a zuciya.
Mu amince, zai mana taimako,
Na hakika inda majaziya.
-(Mohammadu, 1972) KA KOYI KARATU 4)
Yasir Ramadan Gwale
21-06-2015
Don Shi ne sarkin gaskiya.
Ya mallaki dukkan talikai,
Na kwari da tudu da samaniya.
Da mutun, aljan damala'ika,
Dabbar sarari Da ta Malaya.
Mulki, iko, daula duka,
Na ga Sarki Allah shi ďaya.
Shi ya ke ba wanda ya so duka,
Ya sarautu a lardin duniya.
Shi ya ke karbe ta ga talikai,
Don ya ďanďani wahalan duniya.
Shi ka girmama Wanda ya so duka,
shi ka sanya waďansu su sha wuya.
Shi ka cusa dare a cikin wuni,
Kuma ya zaro hasken dariya.
Shi ka rayawar mamaci,
Shi ke kashe mai rai, shi ďaya.
Ikonsa a kan kome ya ke,
A ruwa Da tudu da samaniya.
Alwakilu, mu dogara duk garai,
Zahirinmmu Da boye a zuciya.
Mu amince, zai mana taimako,
Na hakika inda majaziya.
-(Mohammadu, 1972) KA KOYI KARATU 4)
Yasir Ramadan Gwale
21-06-2015
Gaskiya yasir abun nan ya birgeni Allah yasa kaci gaba da wannan aiki me kyau. Alhamdulillah
ReplyDeleteEnter your commentAllah ya saka da alkhairi
ReplyDeletetun sanda na baro Sec. Sch nake neman wannan wakar complete sai yanzu na samu.
ReplyDeletezan cofa a nawa blog mai suna Daular Usmaniyya.
www.usmaniyya.com.ng
Dalhatu Abubakar Sokoto.
Nagade.
Allah yajiqan Mazan jIYA
ReplyDeleteAllah ya jilan Alhaji sa'adu Zungur
ReplyDeleteAllah ya biya
ReplyDeleteAllah ya saka da Alkhairi, amma akwai dan gyara kadan kamar haka:
ReplyDelete1. Kuma ya zaro hasken SAFIYA, ba dariya ba.
2. Shika rayawar mamaci DUKA,