ALBASHI DA ALAWUS DIN 'YAN MAJALISU
Indai da gaske wannan canji an same shi domin al'ummar kasa, da sake gina kasa da hidimtawa al'umma, to ya kamata a zaftare wannan mahaukacin Albashi da alawus na 'yan majalisu. Kai jama’a! Ana maganar wasu jihohi ba su da kudin da zasu yi Albashi, amma ace kudade masu tarin yawa suna shiga aljihun 'yan majalisu ba tare da sun yi wani aiki mai yawa ba da suka cancanci wannan kudi. Wannan abin yayi kama da yiwa 'yan Najeriya fashi, ace wadannan mahaukatan kudade zasu dinga shiga aljifan 'yan majalisu duk Shekara. Gaskiya da sake.
YASIR RAMADAN GWALE
16-06-2015
No comments:
Post a Comment