Sunday, June 14, 2015

Su Waye Ke K'ok'arin Ganin Bayan Dr. Ahmad BUK?


SU WAYE KE K'OK'ARIN GANIN BAYAN DR. AHMAD BUK?

Kamar yadda labari ya bazu cewar Khalifan Tijaniya Isyaku Rabi'u da sauran jagorancin  dari'kar sun shigar da Babban Malamin Hadisi na Tudun Yola Dr. Ahmad Ibrahim BUK k'ara wajen Shugaban shiyya ta d'aya ta rundunar 'yan Sanda ta k'asa dake Kano, Tambari Yabo Mohammed akan zargin sa da suke ya aibata Shehunsu Inyass Kaulaha! 

Babu shakka wannan abu da ya faru, mun ji dad'i kuma mun yiwa Allah godiya domin ya tabbatar da cewar Dr. Ahmad ba k'arya yayi ba da yayi rantsuwa da Allah  yace "wallahi yadda suke girmama Shehunsu basa ganin Girman Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam haka" hakika a wannan marra, Allah ya kubutar da Malamin Hadisi Dr. Ahmad ga masu ganin baiken kalaman sa. 

Haka kuma, a cikin raddin da Dr. Ahmad d'in yayi bayan waccan tab'argaza da kafurci da Abul Inyass yayi da sunan Tijaniya, Malamin Hadisin Dr. Ahmad ya kalubalanci 'yan Tijaniya akan su zo a zauna a gidan Radio a yiwa al'umma bayani, yace Darul Hadith zata biya kudin a ji shin sharri ne ko karya ake yiwa Inyass Kaulaha, amma suka k'i amsa wannan gayyata suka b'ige da bita da k'ulli.

Ni ina ganin abinda ya kamata su Khalifa Isyaku Rabi'u suyi kenan, na amsa waccan gayyata da shi Malam yayi ya kuma ce zasu biya kudin ko awa nawa za a yi a Freedom Radio da Rahama da Radio Kano, domin bayyanawa al'ummar da suke ganin abin ba haka yake ba. Ko kuma su 'yan Tijaniya su kare abin da hujja su ce ba haka bane.

A dan haka, wannan abu, babu abinda zai k'ara illa k'ara tsiraita Tijaniya da kuma d'aukaka darajar Malamin Hadisi Dr. Ahmad Ibrahim BUK. Idan kuma sun gayawa Tambari Yabo cewar Malamin Hadisin ba d'an Najeriya bane, sai muce ai Shima Inyass Kaulaha  din ba dan Najeriya bane, mutumin kasar Senegal ne.

A sabida haka, muna kara jaddada cewar wallahi summa tallahi Martaba da Darajar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam tafi ta uban kowa, kuma tafi ta ko wanne irin Shehu na da da na yanzu. Kuma Alhamdulillah wannan lokaci ne da al'umma zata fahimci hak'ik'anin abubuwan da suke cikin Tijaniya da littattafan Inyass Kaulaha. 

Malaminmu Dr. Ahmad Ibrahim muna tare da shi kuma muna goyon bayan dukkan maganganun da yayi na rushe wannan kafurci da yake cikin Tijaniya. Wanda duk ya kuduri aniyar ganin bayan Malamin Sunnah ko waye Ya Allah ka nuna mana karshensa, Ya Allah ka bakanta musu ciki da samun d'aukakar Sunnah, Allah ka dirkake Bid'ah da dukkan dangoginta. 

Daga karshe kuma, muna kira ga Babban Kwamandan Hisbah na Kano Mal.Aminu Ibrahim Daurawa, kamar yadda ya bada sanarwa cewar hukumarsa ta karbi gabarar wannan Shari'ah da aka kai wannan zindiki Batijane da ya zagi Manzon Allah Sallallahu was Alaihi  Wa Sallwm cewar muna nan muna bin bahasinsu. 

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam na dukkan Musulmi ne dan haka ne al'umma a ciki da wajen jihar Kano hankalin su ya tashi akan wannan batu. A bisa jagoranci da Hukumar Hisbar Kano suka ce sunyi na wannan Shari'ah zamu dinga matsa muku lamba har sai an hukunta wannan zindikin, idan ba haka ba kuma kun yaudari jama'a kuma Allah ba zai kyale ku ba.

Ya Allah ka tozarta duk wanda ya tozarta ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam akan Shehunsa. Ya Allah ka la'anci duk wadan da suka fifita wani Shehunsu akan ManzonKa Sallallahu Alaihi Wa Sallam. Allah kayi dadin tsira a gareshi da Alayensa da Sahabbansa da wadan da suka biyo Tafarkin su da kyautatawa har  ya zuwa ranar sakamako. 

Yasir Ramadan Gwale
14-06-2015

No comments:

Post a Comment