Wednesday, July 30, 2014

Abokanka Makasanka

ABOKANKA MAKASANKA


Wani abokina ya bani labari mai daure kai, yace ya gayyaci wasu abokansa su je gidansu dan su ci abincin Sallah, su goma ya gayyata, dukkansu abokansa ne babu wanda ba shi ya gayyata ba. Da suka zo gidan ya kawo abinci kala-kala aka ci akai warisa aka kunna Talabijin aka kalla, kawai Bawan Allah da ya shiga dakinsa sai yaga babu wayarsa kuma babu kudinsa Naira 20000. Ya kira daya daga cikinsu ya sanar masa abinda ya faru, yace tabbas shigowarku na shiga daki na aje wayar da kudin kuma idan banda ku babu wanda ya shigo, kuma gashi ku duka kuna nan. Ya tambayeshi yanzu ya zamu yi, kawai abokin ya fusata yace Wallahi sai anyi caje na rashin mutunci har under wear sai an duba. Anyi cajen kuwa an duba ko ina ajikin kowa amma ba'a ga kudin ba kuma ba'aga waya ba. Sai daga baya aka ga Sim din wayar a cikin Ban-daki, wanda ya dauka da yaga ba zasu satu ba sai ya zuba kudin da wayar cikin Shadda, amma da yake bandaki ne mai ruwa an tsamo wayar kudin kuwa ruwa ya tafi da wasu. Da aka bincika su goma kowa ya shiga ban-dakin.

Wadannan fa wai sune mutanan da ka kyautatawa. Allah ka karemu da mutuwar zuciya.

Yasir Ramadan Gwale 
30-07-2014

Tuesday, July 29, 2014

Hare-Haren Da Aka Kai Kano

HARE-HAREN DA AKA KAI A KANO

"Allah ya sa ba 'yan matan Chibok ba ne aka yi amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake a Kano"

Wannan maganar naga mutane da dama suna fadinta tun bayan da aka kai hare-hare a Kano. Wannan maganar sai ta sanya na fara tunin ko jama'a sun fara gamsuwa cewa BH ne ke kai wadannan hare-haren? Allah masani.

Indai tunani na gaskiya ne, to mun kama hanyar magance matsalar da ta addabemu. Babu yadda mutum zai zauna idonsa na ciwo amma yana cewa laifin kafa ne, ya zama dole a sha maganin ciwon ido dan ido ya samu lafiya, idan kuwa za'a bige da neman maganin ciwon kafa to a sannu idon zai mamaye fuska. Allah ya jikan wadan da suka rasu a wadannan hare-haren da 'yan Ta'adda suka kawo Kano, masu raunukan cikinsu Allah ya basu lafiya. Dole mu cigaba da yin addu'o'in Alkunuti da muka saba yi a Ramadan kuma mu yi riko da sababi na neman Allah ya fitar da mu daga wannan halin da muke ciki.

Amma lallai mu sani ba kawai addu'ah zamu yi a wayi gari komai ya lafa ba, harkoki sun koma kamar yadda aka saba, dole ta inda aka hau tanan ake sauka. Zamu zama gidadawa idan har wanda ba Dan Arewa ba watakila ma ba Musulmi ba ya fimu fahimatar yadda za'a shawo kan wannan Bala'i da muke ciki. Tilas a duba hanyoyi na gaskiya dan kawo karshen wannan al'amari. Batun siyasa dole a ajiye shi gefe a yi magana ta gaskiya, rayukan al'umma ne suke salwanta babu ji babu gani.

Matar da ta je saro kalanzir dan ta kasa ta sayar, meye laifinta? Yara kanana da basu balaga ba, meye laifinsu? Wasu da dama Allah yana yi musu talala mai kamar sake a cewar Bahaushe, suna tsammanin akan dai-dai suke saboda suna samun Nasara akan ayyukan barna da suke yi, da sannu irin wadannan mutane ajali zai riskesu sun shirya ko basu shirya, a tashe suna masu nadamar da bazata amfanesu ba, suna kaskantattu wulakantattu.

YASIR RAMADAN GWALE
29-07-2014

Baki Biyu

BAKI BIYU: Abinda yake faruwa Ghazza na aikin Ta'addanci da zalinci da tauye 'yancin Bil-Adama da Israela ta ke yi, Amerika ta goyi bayansa tare da cewa Israela na da ikon kare kanta daga 'yan "ta'adda" a cewarsu. Amma kuma Amerikar da kanta na cewa Russia na taka 'yancin Bil-Adama yayin da ta ke nuna goyan baya ga 'yan ta 'bare a Crimea na kasar Ukrain. Indai abinda Russia ta yi ba daidai bane ko sunansa tauye 'yanci,to na tabbata abinda Israela ke yi a Ghazza shi yafi zama rashin daidai da tauye 'yanci.

YASIR RAMADAN GWALE
29-07-2014

Sunday, July 27, 2014

Sakon Barka Da Sallah Cikin Alhini

SAKON BARKA DA SALLAH CIKIN ALHINI

Amadadin ni YASIR RAMADAN GWALE da Zainab da su Utman, da dukkan 'yan uwa da dangi da abokan arziki muna mika sakon taya murnar Barka Da Sallah na wannan Shekara ga dumbin al'ummar Musulmi musamman a Najeriya da suka Sallahci wannan rana ta yau a matsayin Ranar idin karamar Sallah wanda hakan yake tabbatar da karewar kwanaki 29 masu albarka na watan Ramadan, Allah ya sa ibadun da muka gabatar a wannan wata karbabbu ne, laifukan da muka yi a wannan wata wadan da muke sane da wadan da bama sane Ya Allah kai mai afuwa ne kana son Afuwa, Allah ka yi mana afuwar laifukanmu.

Babu shakka lokacin Sallah lokaci ne na murna da farinciki da kuma ambaton Allah. Ina amfani da wannan damar wajen yiwa kaina Nasiha da jin tsoron Allah da kiyaye dokokin Shari'ah a yayin gudanar da Shagulgulan Sallah. Allah ya maimaita mana ta badin badada lafiya.

Babu shakka dole mu yi alhinin halin da kasarmu ta ke a ciki na zaman zullumi da razani da wadansu makiya Allah makiya zaman lafiya makiya addinin Allah suka sanyamu a ciki, Ya Allah kasansu kasan duk inda suke a labe, kasan irin makircin da suke kulla mana Allumma rudda kaiduhum Alaihim! Al'ummar Musulmi da yawa a yankin Ghazza na Palastine zasu yi Sallah a gobe cikin tashin hankali da fargaba da razanai sakamakon hare-haren zalinci da Israela ke kai musu, Allah ka amintar da su ka sanya wadan da suka rasu su tashi a matsayin Shahidai, yan uwanmu da aka karkashe a Borno da Yobe da Adamawa da Kano da Kaduna da sauran jihohinmu Allah ka jikansu ka gafarta musu.

Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya a duk inda muke. Yana da kyau idan mun hadu da juna mu yiwa juna addu'ah tare da fatan karbuwar ibadunmu. Wata Shekara a BUK Sheikh Abubakar Jibrin ya ce a Rungume juna a yi murna. Barka Da Sallah.

Yasir Ramadan Gwale
27-07-2014

Saturday, July 26, 2014

Abin Al-Ajabi Mai Ban Tausayi

ABIN AL'AJABI MAI BAN TAUSAYI

Da yawa daga cikin jaridun kasashen larabawa na yau Asabar sun ruwaito labarin wata jaririya mai cike da ban tausayi da kuma ban al'ajabi. Ita dai wannan jarirya an haifeta ne bayan da mahaifiyar ta da ke dauke da cikinta ta rasu. Mahaifiyar wannan jaririya mai suna Sheima tana kwance kan gadonta a dakinta a birnin Ghazza a daidai lokacin da sojojin Israela suka harbo wani makamin roka da ya sauka akan gidansu, nan take gidan ya rushe gaba daya, mahaifiyar wannan jaririya ta yi kokarin kubutar da ranta da na d'an cikinta, amma ina! Sheima ta rasu a sakamakon munanan raunuka da ta samu sakamakon manyan duwatsun da suka rufto akanta, cikin gaggawa matasan Palasdinawa masu taimako suka tono Sheima daga cikin barguzan ginin da ya rushe akanta aka garzaya da ita Mustashfa.

Bayan da aka garzaya asibiti da wannan baiwar Allah ne aka tarar tuni Allah ya yi mata cikawa. Ba tare da wani bata lokaci ba likitoci suka shiga kokarin ceton abinda ke cikin matar, cikin taimakon Allah aka yi sa'ar farka cikin matar aka ciro jaririya da ranta. Ita dai wannan jaririya yanzu haka tana asibiti ana kula da ita, likitan da ya yi aikin ceton wannan jaririya Dr. Fadi ya yiwa Allah godiya da ya basu ikon ceton ran wannan jaririya, sannan ya kuma yi bayanin cewa hakika ya tausayawa wannan jaririya domin ta zo duniya a wani irin yanayi na tashin hankali da ya mamaye yankin Ghazza, gashi an kashe mahaifiyarta an kuma kashe mahaifinta.

Yanzu dai tuni dangin wannan jaririya suka bayyanawa duniya cewar sun mayarwa da jaririyar sunan Mahaifiyarta. Allah ya jikan mahaifiyar wannan jaririya ya gafarta mata. Allah ya taimakin Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafurci da kafurai. Mutanan Ghazza Allah ya taimake su akan abokan gaba.

Yasir Ramadan Gwale
26-07-2014

Thursday, July 24, 2014

Gaskiya Daya Ce

GASKIYA DAYA CE

Mu 'yan Arewa muna addu'ar Allah ya yi mana maganin abubuwan da suke faruwa na tashe-tashen Bama-bamai, amma a gefe guda kuma mun kauda kai daga ainihin masu laifi muna jingina laifi ga Goodluck Jonathan da cewa shi ne yake kashe 'yan Arewa, su kuma 'yan Kudu suna ganin duk dan Arewa dan BH ne, a gefe guda kuma su 'yan Boko Haram da na yi Imani sune suke aikata wannan ta'addancin mun kauda kai daga garesu suna ta cin karensu babu babbaka.

Wallahi matukar muka cigaba da juya baya ga gaskiya haka zamu wayi gari sun mamaye ko ina da hare-harensu, tunda muna kauda kai a garesu. Indai da gaske muke fatan karbuwar addu'armu akan abubuwan da suke faruwa dole mu nemi inda gaskiya ta ke dan ayi amaganin wannan al'amari. Ta yaya ido yana ciwo ana cewa laifin kafa ce sannan a yi zaton samun waraka? Ya zama dole mu gayawa kanmu gaskiya, ga inda laifi yake, ga inda matsala ta ke muna ji muna gani amma muna yin buris da cewa ba hakan bane.

Yakamata mu ajiye duk wani batu na Siyasa mu fuskanci gaskiyar abubuwan da suke faruwa, rayukan al'ummarmu suke salwanta dare da rana. Duk wanda ya kalli Video da Sahara Reporters suka sanya na sojan Air Force mai suna Umar Abubakar da su 'yan BH suka kama suka yanka, zai tabbatar da cewa abinda ke faruwa sune suke aikatawa, domin su basu yarda cewa Muluncin da muke yi gaskiya ba ne, a wajensu duk wanda ya saba da aqidarsu dagutu ne jininsa ya halatta. Tayaya mutanan da suke da irin wannan ra'ayi da tunani da suka yi imani su mutu akansa, zasu tausayawa al'umma?

Indai gaskiya muke nema dole mu nemi inda ta ke, idan kuma zamu cigaba da kauda kai ga masu laifi, to babu shakka har jikokinmu zasu bamu labari ko bayan ranmu na irin abinda ke faruwa. Wasu da yawa kanyi tambayar wai a ina su 'yan BH suke samun makamai da kudade. Wannan tambaya ce mai kyau, amma kuma an manta cewa duk kumgiyoyin 'yan Ta'adda irinsu Al-Qaida da Alshabab da Hizbola da sauransu duk jirgi daya ya kwaso su da BH inda suke hanyarsu duk iri daya ce. Shi Shedan ai danginsa yawa garesu kuma sashinsu na taimakon sashi.

Yasir Ramadan Gwale
24-07-2014

Kano

KANO: Jiya muka yi alhinin abinda ya faru a Kaduna na tashin bom da ya yi sanadiyar halakar mutane da dama, kwatsam kuma yau muma sai gashi an gaishemu da shi a Kano. Babu shakka Allah Buwayi Gagara Misali Assami'u Ne kuma Albasiru! Idan wadannan masu tayar da hankali sun faku a garemu babu shakka ba zasu iya kaucewa ganin Ubangiji ba. Muna tunawa wadannan miyagu azzalumai cewa tunda Allah ya halicci duniya ya halicci lokaci, da sannu suma lokacinsu zai riskesu, zasu su mutu suna wulakantattu abin wualakntawa. In Sha Allahu azzalaumai ba zaku ci nasara ba, ku koma ku karanta tarihi babu wani wanda ya shuka zalinci kuma rayuwarsa ta dore, duk wani dan iska da yace muku wannan hanya ce ta shiga Al-jannah ya cuceku, da ku da shi zaku dandana kudarku a wajen Allah ba zamu gushe ba muna yi muka fatan Narko na azabar Allah. Miyagu azzalumai 'yan ta'adda marasa tsoron Allah munafukai.

Ya Allah ba dan halinmu ba, Ya Allah ba dan laifukan da muka aikata ba, Ya Allah mun tuba ka yafe mana laifukanmu. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya, Ya Allah kada ka baiwa mmiyagu azzalumai 'yan Ta'adda Nasara akan al'ummarmu. Allah duk wadan da suke shirya wannan mummnan tashin hankali Allah ka sansu kasan a duk inda suke Allah ka wargaza sha'aninsu, Allah ka rusa su, Allah ka dammara su, Allah karka basu alherin duniya da lahira. Allah ka azabtarda su azaba mai radadi.

Allah ka amintar da mu. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya. Wadan da suka rasa rayukansu a tsakanin jiya a Kaduna da yau a Kano Allah ya jikansu ya gafarta musu, wadan da suka jikkata kuma Allah ka basu lafiya, Allah ka sanya abinda ya samesu ya zama kaffara a garesu. Allahumma Taqabbal Minna Du'a'ana Ya Rabbal Alameen.

YASIR RAMADAN GWALE
24-07-2014