Friday, November 20, 2015

Gwamnoni Na Wadaka Da Kudin Al'umma Suna Kiran Ba Kudi

GWAMNONI NA WADAKA DA KUDIN AL'UMMA SUNA KIRAN BA KUDI 

Abin mamaki ne Gwamnonin Nigeria da suke wadaka su ci su sha a kudin Al'umma, wai ba zasu iya biyan mafi karantar Albashi ba. A cikinsu fa babu wani Gwamna da ya rage irin wadakar da yake da dukiyar al'umma, kowa wane Gwamna idan kaga yadda yake dibar 'yan rakiya a yawace yawacensa bai rage ba, ga shatar jirgi da suke dauka ba kan gado, tafiya Kano zuwa Abuja Gwamna zai dau shatar jirgi ya kwashi mutane  cikin dukiyar al'umma. Ko a satin da ya gabata Gwamnatin Kano Shatar Jirgi sukai aka kwashi mutane zuwa Adamawa daurin auren wani Kwamashina cikin dukiyar al'umma.

Ga wani yawon karya da Gwamnonin suke fita kasashen waje wai kiran masu zuba jari jihohinsu, cikinsu kuwa har da Gwamnan Yobe wai yaje Japan da China yana kiran 'yan Kasuwa su zo Yobe su zuba jari, shin wannan ba wauta bace da barna da dukiyar al'umma, ko tsammanin Gwamna su 'yan kasuwar basu san me ke faruwa a Yobe ba? Shugaban Gwamnonin Najeriya Abdulaziz Yari kullum a tafiye yake yana yawace yawace a jirgin shata, Yaki zama ya yiwa al'ummar sa aiki. Tun daga hawansu mulki babu wani Gwamna da bai je kasar waje ba da sunan ziyarar Bogi wai ta Kiran masu zuba jari? 

Gwamnan Bauchi har wata ziyarar bige yaje Jamhuriyar Czech wai kiran yan Kasuwa,  shin 'yan Kasuwa nawa ne suka zo Bauchi daga Czech? Haka nan fa, Gwamnan Katsina da yake ta korafin ba a yiwa Jihar komai ba, ya kwashi kudi zai gina Hotel a inda baida amfani, shin wannan Hotel din ita ce Bukatar talakawa a Katsina?  Ya kamata Gwamna ya sani yanzu lokacin aiki ne domin amfanin al'umma ba amfanin wasu tsirarun ba.

Gwamnan Kaduna da ya kaddamar da wasu dankara dankaran motocin haya a Kaduna wannan ba barna ce da kudin al'umma ba? Shin wannan motocin al'umma suka fi bukata? Kaduna din da suka ce tayi shekaru 16 babu tituna masu kyau a cikin gari, kuma shi ne za a kawo tsala tsala motocin da aka saya da kudin al'umma dan kawai su lalace a cikin shekara guda? Wadannan Gwamnonin ba su da tausayi idan har suka tabbatar da wannan batu na kin biyan mafi karancin Albashi,  a lokacin da rayuwa take kara tsada.

Farashin komai ya daga, kud'in buhun shinkafa ya haura dubu goma, kayan masarufi duk sunyi tsada, mai yayi karanci kuma yayi tsada, rayuwa ta tsananta ga al'umma, basa neman mafita dan ce to al'umma daga halin kangi da mawuyacin hali sai wadakarsu suke yi? Bama yi musu Hassada su ci kaji su hau zunduma zunduma motoci daga cikin dukiyar al'umma, amma ya dace suji tsoron Allah su tausayawa al'umma, ana rayuwa hannu baka hannu kwarya, komai ya tsananta ga al'umma, ace dan Albashin da bai taka kara ya karya ba, ace wai ba zasu iya biya ba. Haba Nigeria har tayi tsiyacewar haka dan Allah.  Da ace ana yin Mid-term election a Nigeria da Gwamnonin sun sha mamaki.

Ya kamata kowanne Gwamna ya dakatar da duk wasu yawace yawace da suke a Abuja na ba gaira babu dalili suna kwana a Hotel da katuwar tawaga su tsaya su duba abinda ya dace da zai kawowa jihohinsu cigaba da zai amfani rayuwar al'umma da suka fito suka zabe su, haka nan tafiye tafiyen da suke zuwa kasashen waje na rashin lissafi dole su dakatar, a tsara gudanar da rayuwar al'umma cikin ingataccen yanayi da kwanciyar hankali da karuwar arziki. Allah ka fid da mu daga wannan mawuyacin hali.

Yasir Ramadan Gwale 
20-11-2015

Thursday, November 19, 2015

Jan Hankali Ga Masu Yada Munanan Hotunan Tashin Hankali


JAN HANKALI GA MASU YADA MUNANAN HOTUNAN TASHIN HANKALI 

Naga mutane da yawa da suke ta yin kira ga Jama'a akan su dena yada hotuna masu tayar da hankali, musamman wadan da aka dauka a yayin tashin Bom.  A ganina yana daga cikin rashin ladabi mutum Musulmi ya tsaya daukan hoton gawa a lokacin da aka zare mata Rai!  Musulmi yana da Alfarma ta tsare masa mutunci da tsiraici a yayin da yake raye ko yake mace, sam bai dace ba mutane a lokacin in da gawa ta Musulmi tafi bukatar addu'ah sama da komai, amma mutane su manta da cewar wanda ya mutu addu'ah yake bukata,  su shagaltu da daukan hotuna suna yadawa, abin mamakin wasu da aka dauki hotunan gawarwakinsu ba wai addu'ah ake musu ba, illa addu'ah ga wanda suka kashe su, to ina amfanin ka dauki hoton mutane kana yiwa wasu addu'ah?  Abin bakinciki wata gawar cikin tsiraici ake daukar hoton ta ba tare da nuna martabar ta ba ake yadawa. Kayi tunani shin gawar da aka dauki hoton  tsiraicinta a Bude, idan da yana raye zai bari a dauki hoton? To haka zalika idan ya mutu yana da hakkin a tsare masa mutuncinsa.

Ya 'yan uwa a hakikanin gaskiya babu wani abun burgewa mu dinga yada hotunan Hannu ko kafa ko rabin jikin mutum ko wani abu mai tayar da hankali musamman gawar da tayi daga-daga dan kawai muna son nuna irin girman tashin hankalin da ya auku. Wanda duk ya mutu kwanan sa ya kare, kowa da hanyar da Allah yake Kaddara masa hanyar mutuwa,  muyi kokarin suturta gawarwakin wadan da suka rasu a tashin Bam tare da nema musu gafara, shi ne abin yafi dacewa ba tozarta tsiraicin su ba. Allah yasa mu cika da Imani mu tashi da Imani,  Allah ka yaye mana wannan masifa da bala'i.

Yasir Ramadan Gwale 
18-11-2015

Wednesday, November 18, 2015

Sa'udiyya: Babu Wanda Yafi Karfin Doka Hatta Sarki Salman


SA'UDIYYA: BABU WANDA YAFI KARFIN DOKA HATTA SARKI SALMAN 

Gidan Talabajin na Al-Arabiyya ya ruwaito Sarkin Sa'udiyya Salman Bin Abdulaziz yana shaidawa manyan jami'an Gwamnatinsa cewar kaf fadin Kasar Sa'udiyya babu wanda yafi karfin doka hatta shi kansa (Sarki Salman) bai fi karfin doka ba. Sarkin ya kara da cewar duk wani dan kasar ta Sa'udiyya na da 'yanci ya kalubalanci kowa a Kotu matukar anci zarafin sa ko an take masa Hakki ko da shi da kansa ne za a iya gurfanar da shi a kotu.

Sarkin ya fadi haka ne, a ranar Laraba a yayin da yake gabatar da jawabi ga manyan jami'an Gwamnati dake Yaki da cin hanci da rashawa. Sarki Salman ya shaidawa al'ummar Sa'udiyya cewar kofar sa da kunnen sa a Bude suke dan sauraron korafin duk wanda aka takawa Hakki, yace za a biyawa kowa hakki ba tare da nuna bambanci tsakanin dan Sarauta da wanda ba shi ba. Sarkin yace, yafi damuwa da hakkin al'ummar kasar sama da hakkin sa a matsayinsa na Salman Bin Abdulaziz. 

Haka kuma, Sarkin ya gargadi jami'an hukumar Yaki da cin hanci da karbar rashawa cewar su sani Allah da ManzonSa sune suka fara Yaki da cin hanci da rashawa, dan haka su yi aiki da gaskiya da amana. Jama'a  Wannan fa shi ne, Sarkin Sa'udiyya Salmanu Dan Abdulaziz wanda Iran da Shiah da 'yan kanzaginsu a Nigeria  kullum suke yiwa jafa'i da fatan masifa da bala'i su auka musu, kullum bakin cikinsu Alsaud. Ya Allah ka yiwa bawanka Sarki Salman jagoranci, Allah ka taimake shi ka kunyata makiyansa na sarari da na b'oye. Allah ka taimaki adalan Shugabanni a duk inda suke, Allah ka taimaki kasarmu Nigeria. 

Yasir Ramadan Gwale 
19-11-2015

Saturday, November 14, 2015

SUWA ZA A ZARGA DA KAI HARIN BIRNIN PARIS NA FARANSA?



SUWA ZA A ZARGA DA KAI HARIN BIRNIN PARIS NA FARANSA? 

A tsakar daren jiya wayewar garin yau Asabar kafafen yada labarai na kasar Faransa suka bayar da labarin wasu hare hare da aka kai birnin Paris shalkwatar Gwamnatin kasar Faransa, inda mutane fiye da 100 rahotanni suka nuna cewar sun mutu. Bayanai sun tabbatar da cewar gurare biyar aka nufa da wannan hari,  inda hare hare ya rutsa da su sun hada da:

1- Harin Bom a Harabar wani filin wasa mai suna Stade De France, inda aka ce Shugaban kasar Faransa, Farnciou Hollande yana wajen inda yake kallon kwallo tsakanin Faransa da kasar Jamus. Bayanai sunce a gigice a aka fice da Shugaban kasar daga filin wasan, inda hankalin mutane ya tashi, kowa ke gudun yada-kanin-wani.

2- Anyi Garkuwa da mutane kusan 100 dari a wani gidan disco da ake kira Bataclan concert hall, inda daga bisa ni aka ce an kashe gaba dayan mutanan da ke cikin gidan disco din.

3- Waje na uku da aka kai wannan hari shi ne wani katafaren gidan cin abinci da ake kira  Le Carillon, inda aka dinga harbin kan-me-uwa-da-wabi. Rahotanni sun ce kimanin mutane 11 suka hallaka a yayin wannan bude wutar.

4 - Waje na hudu da aka kai wannan hari ita ce wata karamar mashaya da ake kira LA Belle Equipe inda aka budewa mashaya wuta bayan sunyi mankas, bayanai sunce ba a samu asarar rayuwaka da yawa a mashaya ba, amma dai an samu jikkata da yawa.

5- Waje na biyar kuma na karshe da aka kai wannan hari shi ne wani gidan cin abinci da ke sayar da kayan kwalama da ake kira Le Petit Cambodge, anan ma maharan sun bude wuta kan masu ciye ciye da lashe lashe babu ji babu gani.

A Jumlace bayanai sun ce an kashe mutane sama da 120 a daren jiya a Birnin Paris. Wannan harin yayi matukar girgiza  Faranasawa ma zauna birnin Paris, tuni bayanai suka ce Shugaban kasar Hollande ya soke halartar taron kasashe masu karfin Tattalin arziki da ake kira G-20 da zai fara gudana yau Asabar a kasar Turkiyya. 

Idan ba a manta ba, Jaridar nan ta Charlie Hebdo mai zanen hotunan batanci, tayi wani zanen batanci akan wani jirgin kasar Russia da yayi hatsari a Birnin Sinai na kasar Masar ya kashe duk mutanen da ke cikinsa, zanen dai ance yayi matukar bakantawa Gwamnatin Kasar Russia rai, inda aka ce Shugaban kasar VV Putin ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan cin mutunci da Charlie Hebdo ta yiwa kasar, ba tare da girmama rayukan wadan da suka rasu ba.

Tuni dai kasashen duniya ciki har da kasar ta Russia suka taya Faransa jimamin ab inda ya faru. A ganina wannan harin ba shida wata alaka da Musulunci balle a dora laifin ga Musulunci. Amma dai al'adar kasashen Turai ce na dora laifin irin wannan hari akan kungiyoyin 'yan tayar da kayar baya da ke jingina kansu da Musulunci, tun ba a kai ga yin binciken gano hakikanin su waye suka kai harin ba. Allah masani.

Yasir Ramadan Gwale 
14-11-2015

Sunday, November 8, 2015

Raddi Akan Fatawar Aminu Gamawa Kan Zaben Mace


RADDI AKAN FATAWAR MALAM AMINU GAMAWA KAN ZABEN MACE

Addinin Musulunci shi ne addini a wajen Allah, duk wani addinin da ba shi ba b'ata ne kuma tab'ewa ce. Babu wani abu da Musulunci ya bari bai yi bayani ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam kafin yabar duniya yayi bayanin komai da ya shafi al'amarin Musulmi, musamman Al'amari na shugabanci da Amanw da adalci da zamantakewa da kasuwancin da sauransu. Haka zalika Manzon Allah ya fada cewar "Halal a bayyane take haka ma Haram a bayyane take", Allahumma sai dai abinda Shari'ah tayi shiru akansa kuma malamai sukai sabani akai. Amma duk lokacin da sabani mai girma ya bayyana game da hukuncin wani lamari, abinda Musulunci yayi umurni da shi shine a koma ga Alqur’ani da Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa sallam don samun mafita.

Jiya naga wata sabuwar fatawa da Malam Aminu Gamawa ya fitar, inda ya bayyana cewar "Munafuki shi ne wanda ya taya Matar Taraba murna ta samu zabe, sannan idan mace ta tsaya zabe a jihar sa ba zai zab'eta ba" Haka Aminu Gamawa ya bada wannan fatawa mai cike da hatsari, domin fatawa ce da kai tsaye ta ke kunshe da kafirta musulmi. A hakikanin gaskiya wannan ba karamin kuskure bane sauyawa abu fassara domin ta dace da son ran mutum akan abinda yake son ya zargi wasu. Haka kuma, irin wannan fatawa ta 'yan boko, tana daga cikin manya manyan sabubban da suke haifar da fikrar khawarijanci, domin tana kara k'aimi ga masu wuce gona da iri a addini, su samu abin fakewa da cewa 'yan boko suna 'bata addini da fikrar yahudawa ko yammacin duniya. 

Kai bama batun Musulunci ba, hatta a Demokaradiyya Aminu Gamawa ya tafka babban kuskure, wanda girmansa ya kai ayi Allah wadai ga duk wanda ya furta wannan magana. Domin a tsari na Demokaradiyya, dama ce  da aka baiwa duk wanda ya isa jefa kuri'a, ya zab'i wanda yaga dama ko kuma yafi gamsuwa da manufofinsa domin ya Shugaban ce shi ko ya wakilci shi. Ta ina mutum zai zama Munafuki a Demokaradiyyance idan yace shi ba zai zabi mace ba? Shin akwai wata ayar doka a kundin Demokaradiyya da ta ce duk wanda Ya'ki zab'en mace ya zama Munafuki, kamar yadda Aminu Gamawa ya kawo? Bana zaton ko shi kansa Malam Gamawa zai iya kare kansa da hujja me karfi akan wannan ikirari da yayi na cewa wanda duk Ya'ki zab'ar mace a matsayin Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki?

Haka kuma, kalmar MUNAFUKI hukunci/kalma ce da Musulunci yayi bayanin ta filla-filla. Baya ga Ayoyi masu tarin yawa da suka yi bayani akan ta, akwai sanannen Hadisi sukutum da gudu, wanda ga duk wanda ya halarci makarantar Islamiyya ya san shi, wanda nayi Imani a matsayin Aminu Gamawa na tsohon Dalibin Sheikh Ibrahim Gomari ya san wannan hadisi? Shin ya akai Aminu Gamawa ya sauyawa wannan hadisi fassara ko ma'ana kawai dan ta dace da abinda yake son yin suka akai? Ta yaya akan Demokaradiyya zaka kifa Musulmi har abada a cikin wutar Jahannama can kasan ta?  Idan Malam  Aminu Gamawa ya gafala ne to lallai ya sani, abinda kalamin sa ke nufi kenan fa da fassarar da ya kawo kan zaben matar Taraba: wanda Yaki zaben Mace Gwamna a jihar sa ya zama Munafuki kai tsaye ba tare da wani kwane kwane ba, wannan shine zahirin abinda maganar ke nufi.

Lallai ina amfani da wannan damar, in jawo hankalin Malam  Aminu Gamawa da ya janye wannan magana tasa, kuma ya nemi gafarar Allah akan abinda ya aikata na kuskure, Allah mai afuwa ne yana son Afuwa, amma cigaba da tafiya ko kafewa  kan wannan magana/mahangar kuskure ne babba, ba a Musulunci ba kadai, hatta a ita kanta Demokaradiyya din da Malam Aminu Gamawa yayi wannan magana akanta. Domin duk mai zab'e yana da ikon zab'ar abinda yaga dama a Demokaradiyyance bai aikata wani laifi ba, tunda doka ce ta bashi dama. Ya Allah ka nesanta mu daga sharrin kawukanmu, ka yafe mana kurakuranmu wad'anda mukai muna sane da wad'an da mukai bisa ganganci. 

Yasir Ramadan Gwale 
08-11-2015

Thursday, November 5, 2015

Hannunka Mai Sanda Ga Gwamnatin Shugaba Buhari


HANNUNKA MAI SANDA GA GWAMNATIN SHUGABA BUHARI

A kwanakin baya, bayan da sabon shugaban kasa na goma sha shida Muhammadu Buhari​ ya sha rantsuwar kama aiki, nayi wani rubutu tare da bayar da Misali da Shudaddiyar Gwamnatin Mursi ta Masar. Mutane da yawa suka kasa fahimtar abinda nake nufi, masu zafin soyayyar Buhari da makauniyar biyayya suka dinga fadin cewar ina yiwa Gwamnatin ta Buhari mummunan fata da fatan tsiya. Haka naga mutane da yawa suna fadi, amma sam ban damu ba, sabida na san, da yawa tsananin soyayyarsu da Buhari yasa suke ganin komai aka fada a kansa laifi ne, kuma duk abinda ya aikata daidai ne.

Jiya cikin Ikon Allah, sai ga daya daga cikin fitattun Marubuta masani kuma mutafannini Dr. Aliyu U. Tilde​ yayi hannunka mai sanda ga Gwamnatin Ta Buhari da irin kalaman da nayi a baya lokacin da aka kasa fahimta ta. A rubutun da Dakta Tilde yayi jiya mai take "Manufacturing Another Mursi in Nigeria" A takaice a gajarce Dakta Tilde ya bada misalin abinda ya faru ga Gwamnatin Mursi tsakaninsa da masu bore da kuma abinda su Abdulfattah Alsisi suka yi.

Haka kuma, Dakta Tilden yayi tsokaci kan tuntsurarriyar Gwamnatin Buhari ta 1983, ya buga Misali kan abinda ya faru na halin da al'umma take ciki, sannan ya kwatantan da irin halin da aka shiga a wannan sabuwar Gwamnatin ta Buhari a 2015. A karshe Daktan yayiwa Gwamnati hannunka mai sanda akan irin mawuyacin halin ha'u'la'i da al'umma suke ciki.

A dan haka ya zama tilas a yi ta kiraye kirayega wannan Gwamnati ta san irin halin da al'umma suke ciki. Lokaci ya wuce da za ai ta zarge zargen gwamnatocin baya. Domin Obasanjo da ya zo a 1999 ya zargi Gwamnatin Abdulsalam da bar masa "empty treasury" haka nan YarAdua ya zargi Obasanjo da bar masa Gwamnati a murgude, to yanzu ana ta maganar PDP ta ruguza Nigeria. Wannan ba zai zama Uzuri ba a ko da yaushe. Lallai ya kamata Gwamnati ta himmatu wajen samar da canjin da aka zabe ta dominsa.

Yasir Ramadan Gwale
05-11-2015

Sakon Taya Murna Ga Mai Daraja Sardaunan Kano


SAKON TAYA MURNA GA MAI DARAJA SARDAUNA KANO

Ina amfani da wannan dama, a wannan rana, a madadin Ni Yasir Ramadan Gwale da mai daki da dangi baki daya, wajen taya Jagoranmu Mai Daraja Sardaunan Kano Malam (Dr.) Malam Ibrahim Shekarau​ bisa wannan ni'ima da Allah  yayi masa, na cika Shekaru 60 cikin koshin lafiya.

Ba shakka, duk wanda rayuwarsa ta tsawaita zai ga al'amura masu yawa, mabambanta. Da yawa an haifesu kuma sun rayuwa, amma mutuwa ta yanke musu hanzari basu iya kaiwa ko cika shekaru 60 a duniya ba, wasu kuma na nan cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai. Muna yiwa Allah Subhanahu Wata'ala godiya da ya baiwa ubanmu kuma Jagoranmu Malam Ibrahim Shekarau aron lokaci har ya riski wannan muhimmin taqi a rayuwarsa.

Mai Daraja Sardauna Kano, Allah ya bashi dama wajen hidimtawa al'umma a cikin wadannan shekaru, wanda kuma har yanzu akan wannan bigire yake na yin hidima ga wannan al'umma tamu. Allah ya yi masa jagora, ya sanya masa alheri a Shekarunsa da zasu zo nan gaba. Kurakuransa na baya Allah ya yafe masa, muma ya yafe mana namu baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
05-10-2015