Tuesday, September 11, 2012

Madubi (Mirror)



Madubi (Mirror)

Madubi dai kusan duk wanda ka tambaya me ye Madubi? Zai ce maka wani abu ne da ake duba sura da shi wato zati, madubi dai kana duba shi ne yana baka zahirin zatin ka, wato yana kara tabbatar maka da cewar wannan shi ne wane. Kai tsaye zamu iya fassara ma’anar haruffan madubi kamar haka, wato MA tana nufin “Ma’auni” haruffan DUBI kuma suna nufin “Rayuwa” wannan fassara ce bisa abinda muka fahimta.

Menene Madubi? Madubi dai zamu iya cewa wani irin sinadari ne wanda ake sarrafa shi ta hanyar wasu abubuwa da ake samu misali akwai mudubin da ake kira  Plane glass wanda bai da zane wato mai ruwan Garau Garau, sannan akwai madubi wanda ake kira Curves glass wato mai zane ko wanda aka yabe bayansa da wani abu, madubi an samoshi sama da shekaru miliyan daya da dari biyar da suka gabata.

Madubi dai yana baka hoton rayuwarka ne ta zahiri wadda kake acikinta. Lallai idan ka tsaya ka nutsu zaka samu cewa madubi yana baka hoton irin yadda rayuwarka ta ke, kuma madubi yana gaya maka waye kai, misali Baki, fari, gajere, dogo, kyakykyawa, mummuna da sauransu wannan shi ne kai tsaye abinda madubi yake gaya maka game da kanka.

Madubi yana tarkato Dukkan abinda yake iya kaiwa gareshi. Wato a fakaice yana gaya maka waye kai? Ina zaka? Me zaka yi? Hakika Madubi yana yin isharori da yawa izuwa gareka, amma mai hankali da lura ne kadai yake ganewa. Idan ka dauki misali madubin gefen mota, yana yi maka ishara ne da abinda yake wajen wato ina zaka je, ka kusa zuwa ko ka wuce, ko zaka fada wani wajen da bai kamata ba. Ka dauki kuma madubin mota da yake a gaba wato saman kurar mai tuka mota, yana dauko hoton abinda yake baya ne yake isar da shi zuwa ga matukin motar nan. To shakka babu haka madubi yake a cikin rayuwa, ba wai kawai yana nuna maka cewa kai wane ka yi kyau ko baka yi kyau ba a’a yana baka labarin rayuwar da ta gabata a gareka da kuma wadda zata zo nan gaba, domin idan ka tsaya tsaf ka kalli kanka sai kaga da fa ba haka nake ba, amma yanzu gashi nayi kaza da kaza.

Idan ka yi sa’a kai kadai ne a cikin daki, kuma ka dauki madubi ka duba fuskarka me ne yake fara zuwa ranka? Wani ya yi murmushi, wani ya yi sigina wa kansa, wani watakila har gwalo yake yiwa kansa, duk saboda ya samu damar ganin aininhin zatinsa a zahiri. A lokacin da ka kalli Madubi ka tambayi kanka da babu madubi duk wannan abubuwan da ke jikinka da madubi kan sada su da idanuwanka baza ka samu damar ganinsu ba. Madubi wani jakada ne a gareka da yake baka sakon izna zuwa gareka cewa lallai fa ka shiryawa mai aukuwa a gareka, domin kai matafiyi ne ba mazauni ba, kamar yadda wata mawakiya ta ke cewa “rayuwa tana faruwa wucewa take kamar ba’a yiba” shakka babu wannan haka yake, domin da za’a dauki Madubi a haska sai a hango ga wane can ya tafi, haka nan za’a yi ta wucewa kamar ba’a rayu a wannan duniyar ba.

Lallai mu tsaya tsaf mu lura da irin abinda madubi yake nusar da mu izuwa gareshi. Lallai ka duba rayuwarka ta baya ka ga me ye abinda ka aikata na kuskure ka gyara sannan kuma, ka duba abinda ya kamata ka yi a gaba. Kukan kurciya . . .

Wannan bayani ne wanda dan uwana Auwalu Adamu Tahir Sabon Gida ya taba gabatarwa, ni kuma naga dacewar na yi masa ta’alika na kawo muku.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Sunday, September 9, 2012

Fim Din Umar!



Fim  Din Umar!

Umar: wani shiri ne na wasan kwaikwayo da gidan Talabijin na MBC 1 suka gabatar a watan Azumin Ramadhan da ya gabata na wannan shekara ta 1433. Wannan fim na Umar kusan ya dauko hoton rayuwar khalifa na biyu bayan Manzon Allah salallahu Alaihi wasallam ne a takaice, inda aka bayar da tarihinta, ta wata irin siga wadda mutane zasu yi saurin fahimtar wanene Khalifa Umar? A cikin wannan shiri anyi bayanin irin Yana yin gwamnatinsa (Umar), da Gaskiyarsa da Adalcinsa a matsayinsa na Amirul mu’uminina, sannan wannan shiri ya yi karin haske akan rayuwar Khalifa  Umar ta kashin kansa, wato rayuwa wadda yake gudanarwa zatiyyan shi da iyalinsa.

Idan ba mu manta ba, a wasu ‘yan shekaru da suka gabata shi wannan gidan Talabijin na MBC1 a cikin watan Azumi ya taba gabatar da wani shirin wasan kwaikwayo irin na tarihin Musulunci mai suna HURUN EIN, wanda malamai da dama a cikin kasashen Larabawa suka soki wannan fim din da kakkausar Murya, dole ta sanya Gidan talabijin na MBC suka janye wannan fim din.

Wannan shiri na Umar kusan ankwashe kwanakin Azumi gabaki daya ana kawoshi sau biyu a kowace rana a tashar MBC 1. Ana  yin sabon shirin da karfe 8:00 na dare a gogon Najeriya, sannan a sake maimaitashi da karfe 8:00 na safe a agogon Najeriya. Shi dai wannan fim kusan na hadin gwiwa ne da gidan Talabijin na Qatar TV, su suka yi hadin gwiwa wajen watsa shi ga daukacin kasashen Larabawa, da kuma wasu daga cikin kasashen Afurka, musamman wadan da suke iya kama tashar MBC din a Nile da Arab Sat. Haka kuma, an watsa wannan shiri a kasar Indonesia kai tsaye daga tashar MBC zuwa gidajen talabijin da ke kasar ta Indonesia inda kuma aka fassara shi da yaren kasar.

Wani katafaren kamfanin shirya fina-finai ne da ke kasar Turkiyya mai suna 03 Production tare da hadin gwiwar ATV Network suka dauki nauyin shirya wannan fim din, a wani waje na musamman da aka tanadar domin shirya wannan fim, da ake kira da sunan Film Village a turance. Akalla ana zaton sama da mutum Miliyan 190 ne suka kalli wannan fim a dukkan kasashen da aka haska shi ko kuma wadan da suke da damar kama tashar MBC ko kuma Qatar TV da kuma mutanan gabas me nisa na Indonesia.

Kusan, daga farkon wannan fim, an nuna irin yadda Khalifa Umar Bin Khattab ya yi rayuwa ta jahiliyya da kuma rayuwa irin ta Musulunci, da kuma irin yadda ya rayu tare da manzon Allah salallahu Alaihi wasallam. Sannan an nuna zamantakewarsa da mu’amalarsa da sauran abokansa sahabbai kamar su Abubakar Bin Abu-Kuhafa da Usman Bin Affan da Aliyu Bin Abi-Talib da sauran Sahabbai. Sannan wannan fim ya yi karin haske akan irin yakukuwan da Umar ya halatta tare da Annabi da kuamirin bajintar da ya nuna.

Haka kuma, an nuna jarumtaka irin ta Umar Bin Khattab da kuma nuna tausayawarsa ga al’ummarsa, da kuma irin tsoron Allah da yake da shi da kankan da kai da tawali’unsa ga Allah subhanahu wata’ala. Kusan duk wani lungu da sako na rayuwar khalifa Umar wannan fim ya tabo ta a takaice.

Sai dai wani fitaccen Malamin Jami’ah da ke a kasar Saudiyya, mai suna Prof. Khalid Al-Muleh da ke a jami’ar nan ta Al-Qassam University ya soki lamirin wannan fim sosai, inda ya bayyana shi da cewa cin-fuska ne ga Amirul-muminina Umar Bin Khattab Allah ya yarda da shi. Shehun malamin a lokacin da yake zantawa da jaridar  Al-Hayat ta kasar Saudiyya ya ce bai kamata a ringa nuna sahabban manzon Allah ta irin wannan siga da aka yi amfani da ita a wannan shiri ba, ya kara da cewa babu nuna girmamawa ko ladabi ga Sahabbai a ringa sanya wasu mutane da sunan cewa wannan shine Umar ko Abubakar da sauransu.

Haka kuma, malamin ya kara da cewar wannan fim din yana iya bayarda da dama ga masu zagin Khalifa Umar Bin Khattab su zageshi, musamman inda ya ce akwai wajejen da bai kamata a ce an nuna su ba, yana ganin miyagu azzalumai masu zagin sahabbai zasu iya fakewa da wannan wajen cin-kasuwarsu wajen zagin sahabban manzon Allah.

Bayan wanna malamin Jami’ah malamai da yawa daga kasar Saudiyya da Bahrain sun soki wannan fim. Inda da yawa suke ganin kamar yadda bai halatta a nuna wani hoto da sunan cewa Manzon Allah  ba ne, haka ba kamata a ringa sanya wasu mutane da sunan cewa wadan nan sune sahabban manzon Allah Salallahu Alaihi wasallam, suka kara da cewar wani zubin akan sanya mutanan da ba Musulmi ba wajen gudanar da irin wadan nan fina-finai, kamar yadda ya faru a fim din tarihin fitaccen dangwagwarmayar nan na kasar Libya wato Umar Mukhtar, suka nuna cewar wajibi ne a kiyaye al-farmar sahabbai ta wannan janibi.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Kaunar Manzon Allah Salallahu Alahi Wasallam



Kaunar Manzon Allah Salallahu Alahi Wasallam


Sheikh Jafar Mahmoud Adam

Bayan haka, Ya ‘Yan uwa, Hadisi ya tabbata daga Nana A'isha bint Abi Bakr (R.A), tana hakaito wani yini da Manzon Allah (s.a.w) ya tsaya a tsakanin sahabbansa yana mai basu labarin wani abu daga cikin abubuwan mamaki daga cikin abubuwa na gaibu, wanda Allah (M) ya nuna masa daga cikin abin da zai zo a gaba har abinda yake cikin Aljannah da wuta. Yana cewa :

"Babu wani abu wanda ban taba ganinsa ba, face yanzu dinnan ina ganinsa har ma abin da yake cikin wuta da Aljannah".

Wannan daya ne daga ukun manyan dalilai da hujjoji da suke tabbatar da Manzancinsa da kasancewarsa badadi na Allah, ta yanda Allah (M) ya kebance shi da sanar da shi, da sanar da shi wani ilmi na gaibu irin wanda ba a saninsa sai ta fuskar wahayi ga wani wanda Allah (M) ya kebance shi ya zabe shi. Allah (M) ya nuna masa Aljannah da wuta ya kuma nuna masa dangin ni'imomin da ke a cikin ita Aljannah din, sannan kuma ya nuna masa irin dangogi na azabobi da wahalhalu da ke a cikin wuta. Duka wannan an nuna masa ne alhali yana a farke ba a cikin barci ba wato (mafarki).

Hakika wannan mu'ujiza ce cikin mu'ujizozin da Allah ya yi masa. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: 

" Hakika an yi mani wahayi cewa lalle, ku, za a fitine ku a cikin kaburburanku, irin, ko kusa da fitinar masihul Dajjal".

Abin da ake nufi da fitinar kabari a nan ita ce tambayoyin da za a yi wa kowane daya daga cikinmu (mazanmu da matanmu). Ita kuwa fitinar Dajjal ba karamar fitina ba ce domin irin yadda tasa da yawa daga cikin mutane suka halaka; ta hanyar nuna musu irin abubuwan da ido bai saba da ganinsa ba; ko kuma bai taba jinsa ba. Misali kamar ya tashi idon makaho ya warke, ko ya tayar da matacce daga kabarinsa, da sanya abubuwa su faru, sannan ya yi da'awar Allantaka, wasu mutane kuma su bishi. Kuma ya zagaye duniyan nan a cikin kwanakin da ba su wuce arba'in ba, ya shiga ko wane gari in ban da Makka da Madina, wadanda Allah (M) zai kiyaye su da Mala'iku wanda suka zagaye su ( Makka da Madina). Sai dai wanda duk zai bi Dujjal zai fito wajensu domin ya bishi.

Daga Hadisin za mu iya fahimtar cewa Manzon Allah (s.a.w) yana buga misalin yawan wakanda za su fitinu a kaburbura cewa sun kai kwatankwacin yawan wadanda za su bi Dujal. Ya ci gaba da cewa za a tayar da mutum a tambaye shi cewar : Me ka sani game da wannan mutumin (Watau Manzon Allah (s.a.w) ). Amma mumini sai ya ce shi ne Muhammadu Manzon Allah (s.a.w) ya zo mana da hujjoji da shiriya, sai muka amsa, muka yi imani da shi, kuma muka yi masa biyayya". A cikin duka abin da shi mumini zai ambata akwai imani da biyayya, ko da kuwa bai taba yin kasida ko guda daya ba ga Manzon Allah (s.a.w). Abin da kawai aka bukata shi ne cika zuciya da kaunarsa ta hanyar yi masa biyayya, da ganin mutumcinsa, da girmansa fiye da dukkan wani dan Adam da aka yi a da ko za a yi a nan gaba. Saboda haka ba ya bin wasu tafarki, hanyoyi ko dariku da dokokin da basu da asali, face tafarkin shiriya ta Manzon Allah (s.a.w) a nan za mu iya fahimtar cewa imani kadai ba ya wadatarwa sai da aka yi masa biyayya. Biyayya a cikin akida, ibada, dabi'u da ma'amalolinka duka su kasance yadda ya koyar ne a cikin hadisansa ingantattu, ba irin wanda aka kirkira ba, hadisai raunana, da maudu'ai ko Isra'iliyyat ba. Dukkan nau'ukan ibadarka kamar sallah, zakkah, zikiri, istigfari su kasance irin wanda Manzon Allah (s.a.w) ya yi ne ko ya yi umarni a yi, ba irin wadanda wasu mutane suka kirkiro ba ne bayan mutuwarsa (s.a.w). Ya kasance dukkan dabi'unka, halayenka, cin abincinka, kwanciyarka, tafiya, magana da sauransu kana kwaikwayon irin na Manzon Allah ne (s.a.w). wanda duk ya kasance ya yiwa Manzon Allah (s.a.w) irin wannan son, biyayya, da imanin sai mala'iku su ce da shi:

"Kwanta (ka huta) kana salihi muna da masaniya (ta fuskar takardunka dake a wurinmu) cewa dama kai mai yakini ne da Manzon Allah (s.a.w).
Manzon Allah (s.a.w) ya ce :

"Amma munafiki ko mai shakka (mai raba kafa) sai ya ce: Ban sani ba, na ji kawai mutane suna cewa kaza sai na ce" .

Watau a nan duk abinda ya ji mutane suna yi ko cewa sai ya yi misali idan sun yi kida, ko waka, da sauransu sai ya yi ba tare da ya tsaya ya yi bincike ba ya samu wayewar kai daga Ayar Alkur'ani ko Hadisi ingantacce a kan yadda zai bi tafarki na gaskiya na Manzon Allah (s.a.w) ba. Shi dai kawai "mukalladi" ne watau mabiyi ne kawai ga malamai da shehun nai ba a kan hujja ko gaskiya ba, saboda haka ya kamata ‘yan uwa mu fahimci cewa Alkur'ani da hadisai ingantattu su ne ma'auni da ake gane akida ta gaskiya, da ibadoji, halaye da dabi'u na gari. Abin da duk ya yi daidai da su wannan shi ne shiriya, abin da duk kuwa ya saba masu shi ne bata, kuma shirme, komai girman ilmin wadanda suka yi riko da shi suna kiran mutane a kan su wajibi ne mu nisance shi.

Ya ‘yan uwa lallai Allah (M) ya zabi Manzon Allah (s.a.w) ya sanya shi ya zama shi ne karshen Annabawa, kuma karshen Manzanni. Babu wata shiriya sai wadda ya zo da ita, haka kuma babu wani alkhairi sai ga wanda ya yi riko da abin da ya zo da shi. Kuma Ubangiji ya lamuncewa wadanda suke yi masa biyayya cewa:

" Idan har ku ka yi masa da'a to za ku shiryu".

Ya ‘yan uwa! Da yawa daga cikin mutane suna tsammanin cewa tsira tana samuwa ne ga wanda kawai ya furta yana son Manzon Allah (s.a.w) wasu kuma suna tsammanin cewa za a samu matsayi da martaba a Aljannah gwargwadon baitoci na wake da mutum ya shiryawa Manzon Allah (s.a.w) da kida ko babu kida, a tsammaninsu ko da kuwa mutum bai yi riko da sunnarsa ba, ko da mutumin ya saba masa a addini, watau a ibada, dabi'u, aiki da mu'amaloli da sauransu. Alhali ita soyayya bata tabbata ta hanyar kudurtawa a zuci kawai face an gauraya ta da wasu abubuwa masu muhummanci, wadanda idan babu su to, soyayyar za ta zamo ba ta gaskiya ba ce, kuma ta shirme ce kawai. Wadannan abubuwa kuwa su ne :

1- Imani da shi (Manzon Allah (s.a.w)) da imani da manzancinsa

2- Aiki da sunnarsa tare da koyi da shi

3- Gabatar da zancensa a kan na kowa, komai girmansa, waliyantakarsa, ko malantakarsa.

4- Takaituwa ga hujjarsa. Ba zai taba yiwuwa mutum ya ce yana sunnarsa, kuma yana darikar wani shaihi ko waliyi ba. Domin duk wani wanda ya samu shi ne gwargwadon yadda ya yi riko da sunnar Manzon Allah (s.a.w) ; ba tare da garwayata da shirkoki, bidi'o'i ko al'adu ba.

5- Riko da wasiyyarsa (s.a.w) inda yake cewa : " Ku bi tafarkina da tafarkin sahabbaina". Saboda haka dole ne mu yi ko yi da abin da suka aikata, ko suka ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w). Amma duk abin da ba su yi ba, mu kuma muka kawo shi muna kokarin sai mun mayar da shi addini, to ba komai muke yi ba, face kokarin cin gyaran ko tuhumar Annabi (s.a.w) da sahabbansa cewar ga wani abin alheri a addini wanda su suka ki yi, ko suka manta ba su yi ba.

6- Biyayya gare shi (s.a.w) da sallamawa cikakkiya ga duk wani abu, ko kaso shi ko da kuwa kana kinsa. Ya kasance hujjarka kawai ita ce shin ya inganta daga gare shi ko kuwa? Ba tare da cewar kuma wane ai yace kaza (daga shaihinnai ko waliyyai ba) domin idan ana maganar Manzon Allah (s.a.w) wane ne kuma za a yi maganarsa?

7- Sannan ya kasance kuma mutum bai samu wani kaikayi ba a zuciyarsa a yayin da ya yi da'a ko biyayya ga Manzon Allah (s.a.w). Domin fadarsa Madaukakin Sarki :

" Na rantse da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, har sai sun sanyaka mai yin hukumci a cikinsu ga abubuwa da suka gudana tsakaninsu na sabani, sannan basu samu wani kaikayi ba ga abin da ka yanke (na hukumci) kuma su mika wuya, iyakar mika wuya".

Ya kamata mu sani cewa a duk duniya babu wanda yake da adadin masoya irin Manzon Allah (s.a.w), domin in dai so ne kawai ba tare da da'a ko biyayya ba, hatta da yawa daga cikin kafirai na duniya a yanzu da kuma a da sun so Annabi (s.a.w). Na nesa da na kusa, wanda ya ganshi da wanda bai ganshi ba. Mu sani cewa da a ce ita soyayya kadai tana wadatarwa ga shiga Aljannah (ba tare da da'a da biyayya ba) lalle da Abu Talib yana cikin wanda suke cikin wanda za su zama na farkon a shiga Aljannah, domin a tarihi da wuya ka samu wanda ya nunawa Manzon Allah (s.a.w) soyayya irinsa, har ma tare da ba shi kariya.

Hakanan da yawa daga cikin kafiran kuraishawa, wadanda domin tsananin soyayyarsu gare shi har suka sanya masa suna " Al Amin" wataun amintacce. Saboda haka ba su tabSa shakkar gaskiyarsa ba. Allah Madaukaki Sarki ya ce:

" Lalle su ba su karyataka, sai dai su, azzalumai da ayar Allah ce suke musu". Wannan ya sanya soyayyarsu kawai ta zuci ce wacce ba za ta amfanar da su ba, domin ba su garwayata da yi masa da'a da biyayya a cikin addinin ba.

Haka kuma idan muka duba cikin Alkur'ani za mu ga cewa ayoyin da suke umarni kan yin da'a ga Manzo (s.a.w) kamar :

"Kuma ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga ManzonSa".

"Wanda duk ya yi da'a ga Manzo (s.a.w) hakika ya yi da'a ga Allah".

" Ku yi da'a ga Allah, kuma ku yi da'a ga Manzo (s.a.w) kar ku yi jayayya".

" Wanda duk ya yi da'a ga Allah da ManzonSa, to wadannan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a gare su, daga cikin Annabawa da masu gaskatawa, da shahidai...".

Wadannan ayoyin da kuma wadanda suka yi magana a kan yin imani da bin Manzon Allah (s.a.w) misali:

" Ku bi abin da aka saukar zuwa gareku".

Wadannan ayoyi sune suka fi yawa a cikin Alkur'ani fiye da wadanda suke nuna soyayya gareshi. Dalilai kuma, idan ance da'a, biyayya da imani wasu abubuwa ne da so baya tabbata sai da su, shi ya sanya aka maida hankali wajen yin bayaninsu. Haka kuma, da an ce so ne tsuransa, sai ya kasance musulmi ya yi tarayya da kafirai ne na da da na yanzu a cikinsu, domin kuwa har yanzu akwai kafirai na duniya da suke jinjinawa Manzon (s.a.w). Misali akwai "Micheal Hart" wanda ya rubuta littafin mutane dari (100) da suka ci nasara a duniya, ya sanya Manzon Allah (s.a.w) cewar shi ne na daya, wannan ba zai sa shi ya samu aljannah ba, domin bai yi imani da shi ba ta hanyar yi masa da'a da biyayya.

Wannan abu shi ne da yawa daga cikin mutane a yau suke da bukatar a wayar musu da kai. Lalle mu fahimci cewar ko yake akwai ayoyi da hadisai da suka yi umarni da soyayya ga Manzon Allah (s.a.w) za mu iya fahimtar cewar ayoyi da hadisai wadanda suka yi umarni da yi masa da'a da biyayya a (cikin addini) sun ninninka na soyayyar sau tarin yawa. Saboda haka samun tsira yana tattare da imani biyayayya da da'a a gare shi, bayan tabbatar da kaunarsa (s.a.w). Allah ya sa mu da ce.

Wannan khuduba ce da Babban Malaminmu Sheikh Jafar Adam Kano ya gabatar a lokacin Rayuwarsa, a masallacin Juma’a na Dorayi. Allah ya jikan Mallam ya gafarta masa ya sanya al-jannar firdausi ta zama makoma a gareshi.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale



Saturday, September 8, 2012

Illolin Da Suke Tattare Da Auren Dole



Illolin Da Suke Tattare Da Auren Dole
Auren dole akasar Hausa, aure ne da akeyiwa yarinya(budurwa) ba tare da tana so ba, wato atursasa mata auren wani wanda ba shi ne zabinta ba, kuma a mafi yawancin lokuta iyaye suna yiwa diyarsu auren dole ne ga wani mutum wanda shekarunsa suka jaa, kuma sau da yawa, auren dole haka yake kasancewa a tsakanin Hausawa. haka kuma, akan baiwa mutum karamar yarinya ya aura, kodai saboda mai hannu da shuni ne, ko kuma saboda wani mukami da yake dashi, ko kuma saboda wani dalili na samin abin duniya, wasu kuma suna yiwa diyarsu auren dole ne ta hanyar hadin zumunci ko kuma kulla alaka tsakanin iyaye ko kuma abokai.
Ko shakka babu iyaye sunada rawar takawa mai yawan gaske wajen fitarwa da diyarsu mijin da zata aura, domin sun fita hange da sanin yakamata, kuma addini ya basu dama, kamar yadda addini ya nuna cewa biyayya ga iyaye wajibine, don haka nema Allah yace aljannar ‘ya ‘ya tana karkashin iyayensu.
 A lokacin Manzon Allah anyi wani mutun da ake kira da suna Mughir wanda Allah ya jarrabe shi da tsananin son wata mata da ake kira da suna Barira, amma kuma cikin ikon Allah ita kuma duk duniya babu wanda bataso irinsa (Mugheer), har saida takai yana bin ta a hanya, yana kuka, yana rokonta, da ta soshi, amma ita kuma ta kekasa kasa. Wata  rana sahabbai suka ga irin halin da mughir ke ciki, suka cewa manzon Allah shin baza kashiga cikin al’amarin Mughir da Barira ba, Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam, da kansa yace hakika anjarrabi Mughir da soyayyar Barira. Manzon Allah ya taka da kafarsa mai daraja, yaje wajen Barira da kansa Salallahu Alaihi Wasallam, ya ce yanzu Barira baza kiso Mughir ba! Ta ce ya Manzon Allah! kana bani umarni ne, ko kuma kana bani shawara, yace ina baki shawara ne salallahu Alaihi Wasallam, ta ce ya Manzon Allah bana sonsa, haka Manzon Allah ya taso yana mamakin irin yadda zuciyar Barira bata nutsu da Mughir ba duk kuwa da irin yadda yake nuna soyayya a gareta. Ya  ‘yan uwana da auren dole yana da muhalli a musulunci da Manzon Allah ya umarci Barira ta auri Mughir sai dai baiyi hakan ba. Wannan shi ya nuna mana cewa addinin Musulunci bai yarda da auren dole ba, domin da ana yi, da saboda yadda Manzon Allah ya tausayawa Mughir da ya umarce ta da ta aureshi amma haka ya bata cikakken ‘yancin ta salallahu alaihi wasallam.
Yaka mata iyaye su sani cewa ‘ya ‘ya suna da kimar da shariah tabasu wajen zabar mijin da zasu aura, kuma auren dole babu abin da yake haifarwa sai bacin tafarki, da kuma, dana sanin da batada amfani. Galibi auren dole ke sanya karuwanci da yawon banza, harma da wasan kwaikwayo da kananan yara mata suka tsunduma cikin harkar gadan gadan, wanda da zaka ji tabakinsu sai kaji dalilin auren dole da kuma mutuwar zuciya yasa su wannan harkar.
Ko shakka babu illolin da suke tattare da auren dole sun bayyana karara kamar wata daren sha biyar a wannan zamanin, kuma yaka mata iyaye ayi hattara. Sannan akwai wani al’amari muhimmi, shi ne tarbiyya, galibin iyaye musamman maza sunyi sakaci da al’amarin tarbiyyar ‘ya ‘yansu mata inda suka barta a hannun iyayensu mata, haka suma mazan ina ganin matukar iyaye sun baiwa diyarsu tarbiyya mai kyau babu yadda za’ayi su bata zabi ta kauce masa. Kuma sannan iyaye maza babban laifin yana kanmu domin galibi bamu fiya nunawa ‘ya ‘yanmu mata soyayya ba kamar yadda muke nunawa maza, wannan ce ta ke sanyawa da yawan ‘yan mata basu da kwarin gwiwa akan iyayensu maza, saboda suna ganin kamar babu su a cikin yadda ake dama al’amura, ba’a neman shawararsu ko jin ta bakinsu.
Zaka ga uba baitaba sayawa diyarsa kayan kwalliya ba, bai san ya ta ke da wannan janibi na larura ba, domin mata tamkar kayan Karau ne, dole sai ana kula da su kuma ana bibiyarsu, kai hattana ma irin audugar da mata ke anfani da ita wani uban bai sani ba yaya diyarsa take yi, ba’a neman shawararsu anmaidasu tamkar bayi ba ‘ya ‘ya ba. Don Allah amatsayinka na mahaifi taya ‘yarka zata fahimci kana kaunarta bayan baka kulawa da duk wani al-amari da ya shafeta ba. Amma matukar zaka kula da ita ka saya mata kayan kwalliya akai-akai, da audugar mata da janyo ta ajiki, da nuna mata muhimmancin da ta ke da shi a rayuwa, dole idan ka nuna mata hanya tabi ko da kuwa ya ci karo da muradinta, amma muddin ana samun akasin haka dole shegu suyi yawa acikin gari, da masu yawon ta zubar, da ‘yan daudu, da ‘yan gud ebini kai harma da barayi da kasha-kashe; kamar yadda wani mawakin Nijar ya ke cewa “ashe mata mu bayinsu ne, komai dansu muke”. Kuma wannan maganar tasa haka take, kusan duk wani fadi tashi da muke a rayuwa karshe wajen mata ya ke komawa, idan kuwa haka ne to bai kamata mu yi sakaci da wannan janibi ba.
Haka Kuma, suma a nasu bangaren, iya ye mata suna da tasu gudunmawar da suke badawa wajen sagewa ‘ya ‘yansu mata gwiwa, domin suma basu cika tattaunawa da ‘ya ‘yansu mata ba, suna jin matsalolinsu na rayuwa da kuma na zamantakewa, tare da basu shawarwari akan irin tunanins da kuma irin hukuncin da suke kokarin yankewa rayuwarsu, an maidasu kawai tamkar ‘yan aiki, ba su da wani amfani illa su yi wanke-wanke da shara da dora sanwa da yiwa yara wanka, dole iyaye mata su janyo su ajiki da nusar dasu yadda raywa take da nuna musu suna da muhimmanci a rayuwa, kamar yadda suma Iyaye maza wannan wajabci bai saraya akansu ba; da iyaye suna haka, da babu wasu da zakaji sun fito suna babatun ‘yancin mata wai andanne masu hakki. Kaji wai matan da suka kasa zaman aure, su ke son samowa na cikin gida ‘yanci da walwala da jin dadi, duk kuwa da cewar ana danne hakkokin mata da yawa a gidajen aure.
Sanin kowanne magidancine yanzu musamman wanda yake da mota yadda ‘yan mata ke rububinsa daga ka tsaya abakin titi sayan wani abu, sai kaga yarinya tazo ta dauka ko dan ita ka tsaya, anan ya kamata duk wani magidanci yayi karatun ta natsu shin wadan nan ‘yan mata wane dalili ya sanya su wannan harkar, shin da ‘yar kace ta ke wannan hali ya zakaji abin a ranka, akwai takaici kwarai da gaske ganin wadan nan yara mata da zaka ji ta bakinsu sai kaji auren dole za’a yimusu shi ne suka gudo, ko kuma ma anyi auren ta gudo. Allah ya shirya mana ‘ya ‘yanmu, kuma yabamu ikon yimasu adalci gwargwadon iko, sukuma Allah ya sanya tsoron sa azukatansu su fahimci cewa iyaye suna da matukar muhimmanci arayuwa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Friday, September 7, 2012

Hukuncin Wanda Ya Yi Kisan Kai Bisa Ganganci: tare da Sheikh Jafar Adam



Hukuncin Wanda Ya Yi Kisan Kai Bisa Ganganci
Tare da
Shiekh Ja'far Mahmoud Adam

Ya yan uwa musulmi, yana daga cikin manufofin shari'ar musulunci tsare rayukan bil'adama tsare jinin su, don haka ne nassoshi suka zo acikin alkurani mai girma da abin da ya inganta na hadisan manzon Allah salallahu alaihi wasallam, wadan da suke nuna haramcin jinin bil'adama mu samman dan adam musulmi.

Ubangiji ta'ala ya yi wannan bayani ta hanyar salon zance da ban da ban, ta hanyar nau'ikan magana da ban da ban, Salon zan ce na farko. Ubangiji ta'ala ya wajabta kisasi (ramuwar gayya) ga dukkan wanda ya kashe musulmi da ganganci, hukuncin sa shi ne a kashe shi, dukkan wani mutum da ya kashe musulmi da ganganci ya yi amfani da wani abu wanda ya iya zare rai, ya nufi dan uwan sa musulmi ya aiwatar da wannan makamin akan sa har ya kashe shi, to shi ma akamashi a kashe shi ko shi kadai ne, ko su da yawa ne, sai dai fa idan dangin wanda aka kashe musu dan uwan su suka ce sun yafe, zasu karbi diyya, to sai a basu diyya.
To amma idan ba hakaba hukuncin su da Ubangiji Ta'ala ya nassanta shi ne kisasi, ko da mutum daya ne, ko biyu, ko uku, ko sama da haka, sukayi taron dangi suka kashe mutum daya, kuma hakan ya tabbata, ta hanyara tabbatar da laifi a addinance, a musulunce, hukuncin su shi ne akamasu a kashe su gaba dayan su; Kamar yadda aikin Umar bin Khaddab ya nuna lokacin da wani adadi na wasu mutane suka yi taron dangi suka kashe wani mutum daya su kadai, Umar ya ce a kashesu su duka, wadansu suka yi masa inkari da cewa ya ya za a yi ace a kashe rayuka da dama bayan rai daya suka kashe, Umar ya ce wallahi inda mutanan birnin san'a za su hadu su kashe rai daya to wallahi da na kashe su gaba daya.

Hikimar hakan cikin shari'ar musulunci, shi ne in da ace ana yin kisasi ne kadai idan mutum ya kashe mutum daya za'a kashe shi, sai wanda zai yi kisan ya raba goran gayyata ga abokansa, ko yan uwansa, su je, su kashe wane, don sun san insunyi baza a kashe suba, gobe kai ma idan kana jin hashin wani sai karaba goran gayyata ga wadan da zasu taya ka fada domin kuje ku kashe wane. Wannan sai ya bayu zuwa ga hasarar rayuka, amma idan mutum biyu ko uku ko sama da haka sukayi haka aka kashe su,wannan zai sa dukkan wani da da wani ya rabawa goron gayyata cewa zaka rakani in kashe wane to bazai je ba saboda yasan idan ya aikata hakan to zai bayu zuwaga akashe shi, don haka sai rayukan mutane su zauna cikin aminci. Allah ta'ala yana cewa "lallai kuna da tabbatacciyar rayuwa a cikin kisasi matukar an tabbatar da kisasi a bankasa, wanda duk ya kashe wani da ganganci da kowanne irin dalili cikin dalilai to shi ma za'a kama shi a kashe shi"  to wannan sai ya bayu zuwa ga tsare rayukan mutane, kisa ba zai yaduba a bankasa da kowanne irin dalili cikin dalilai. wannan salon magan na farko kenan.

     Salon magana na biyu, Ubangiji Ta'ala ya saukar da narkon azaba da firgitarwa da rudarwa da kidimarwa ga dukkan mutumin da ya kashe mumini da ganganci yana ji yana gani sakamakon sa wutar jahannama, zai dawwama a cikin ta ubangiji ta'ala ya yi fushi da shi, ya tsine mashi, sannan yayi masa tanadin azaba maigirma. kaji irin wannan firgici, ka ji irin wannan razani, ka ji irin wannan tsawa, da ya sauka cikin suratul Nisa'i domin aja hankalinka aja hankalina kada kayi dukkan wani yunkuri na zubar da jinin dan uwanka musulmi bisa ganganci.

    Salon magana na uku, Ubangiji Ta'ala ya nuna cewa duk wanda ya kashe mumini da ganganci, to baya cikin siffofin muminai nagari, wadan da ubangiji ta'ala ya jero siffofin su a cikin suratul furqan a inda Allah ta'ala yace "sune wadan da basa kiran wani tare da Allah, suna kiran Allah ne kadai dan jawo amfani ko dan ko dan dauke musu wata cuta, sannan ba sa kashe wata rai da Allah ya haramta kisan ta sai ta hanyar gaskiya da adalci”.  Sannan  kuma cewa mumini baya kisan kai, wannan dalili ne da yake nuna cewa idan kuna son kalmar adalci ta tabbata a kanku to kuyi iyakar kokarinku na tsare jinin yan uwan ku musulmi.

    Sannan salon magana na gaba, Ubangiji ta'ala ya danka amana ko ya bayara da iko a hannu wadan da aka kashe wa dan uwa da ganganci, dangin duk wanda aka kashe bisa ganganci. Haka ya ce ya basu iko duk wanda aka kashe bisa ganganci ya bada dama ga yan uwan sa, a hannun dangin sa ko makusantan sa, wannan iko kodai su nemi a basu diyya, ko su nemi a kashe wanda da ya kashe musu dan uwansu, Allah ya basu kowacce daya daga cikin biyun nan a matsayin zabi in suka zabi na farko ya yi in suka zabi na biyu ya yi.

     Bayan haka ubangiji subahanahu wata'ala, ya nuna tsare jinin mumini, tsare jinin musulmi, kare jinin dan uwanka musulmi, wannan daya ne daga cikin wasiyyoyi guda goma da Allah ya kebanci al-ummar manzon Allah dasu, wadan da suka zo a jere cikin "suratul An'am" Ya ‘yan uwa musulmi! Manzon  Allah sallalahu alaihi wasallam, ya labarta mana cewa dukkan wani mutum da ya kashe dan uwansa da ganganci, to za a zo dasu, ranar alkiyama sai wanda aka kashe ya rike wanda ya kashe shi, hannun sa yana kan zankonsa ya ja shi sutafi gaban Ubangiji Ta'ala ya ce ya ubangiji tambayi wane, me nayi ya kasheni? Alokacin  da zai fadi haka jijiyoyin wuyan sa suna furzar da jini domin a halartowa da makshin munin hotan abin da ya akata a gidan duniya, yace tambayi wane me nayi ya kashe ni akan wanne dalili? banbancin siyasa, ko addini, ko manufa, zai ce ya ubnagiji tambayi shi me nayi ya kashe ni. Haka hadisi ya tabbata acikin Sinanu Nisa'i wanda ya ke hadisi ne sahihi.

   Ya yan uwa musulmi, addinin musulunci a lokacin  da yake haramta kisan kai, ba wai yana haramta zubar da jinin muminai ba kadai! a a hatta daga cikin kafirai wanda shariar musulunci ta kare masu jinin su da dukiyoyinsu, to in ya zamto dokokin Allah da ya saukar ta haramta zubar da jinin wanda bai furta kalmar shahada ba, jinin wanda ya ce Allah uku ne, wanda ya ce Uzairu Binullah! To  ya ya kima da daraja da tsada ga jinin wanda ya ce ya shaida babu abin bautawa bisa cancanta da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad Manzan Allah ne.
Haka kuma, kafiri wanda kuka yi yarjejeniyar zaman lafiya tsahon wasu shekaru kan cewa ba za ku yaki juna ba a iya wannan sheakarun na yarjejeniya, to haramunne ka kashe daya daga cikin su ko ka kwace dukiyar sa, sai wadan da kuka yi yarjejeniyar basu rushe ko wanne irin sharadi ba na yarjejeniyar, kuma  baku tallafawa wasu ko wani akan ya yake su ba. To,  irin wannan, ku tsare masu alkawarin su na tsahon lokacin da kuka yi alkawarin da su, alokacin inda zaku kashe wani kafiri to wanda yayi kisan, Manzan Allah ya ce tsakanin sa da Al-jannah tshon tafiyar shekara dari biyar, haka ya bayyana acikin hadisi sahihi, ga shi kuma arne ka kashe ba musulmi ba, to ina ga dan uwanka musulmi! Ka  dauki bindiga da kowanne irin dalili cikin dalilai ka rabashi da rayuwar sa, to kai kuma kayi me a bankasa? kuma mu duba muga "Al-mu'utamalun" wadan da yaki tsakanin ku da kasar su wanda akace inda daya da ga cikin su ya nemi izinin zuwa kasar ku, kuma ku ka bashi dama ya zo yayi iya ka kwanakin da zai yi, to wajibine ku tsare masa jinin sa da dukiyar sa har ya gama iyakar kwanakin da zaiyi, kuma ku yi masa rakiya har sai kunje inda zai ji ya amintu daga gare ku. Wannan ya na nuna kulawar shari’ar musulunci da dokokin Allah dangane da tsadar rayuwar biladama, ko da ya ki da aka shar’anta mana ba wai an halarta mana shi ne kawai don malalar da jinin kafirai ba, manufar shar’anta yaki ne idan kafirai suka furta kalmar shahada bisa ga zabin su sai a kyale musu jinin su, wannan tasa idan kafirai sukaki su furta kalmar shahada amma zasu shiga cikin "amman dinku" wato karkashin gwamnatinku, ku kyale su akan addinin su, baza ku kashe su ba. Ashe da manufar itace kisa to da idan amfito sai an kashe mutum koda ya yi kalmar shahada, sai ace ai anriga anfito lokaci ya kure me yasa yaki yi kafin a fito, da manufar itace kisa to da babu yadda za'a ce an samu wasu kafiran amana wadan da zasu zauna karkashin daular musulunci, kuma a tsare musu jinin su da dukiyar su ba tare da anribace su ba.

 To wannan ya nuna cewa addainin musulunci addini ne da yake kare rayuwa, ba na salwantar  da rayuwa bane, duk wanda dokokin addini suka ce a salwantar da rayuwarsa, to idan ka duba zaka ga babu abin da yafi dacewa sama da a salwantar da ratuwar sa, shi yasa kafirai duk kafircin su duk barnar da sukayi a bankasa, Allah ya ce idan sun tuba ta hanyar furta kalmar shahada sun bayar da zakkah, kar a kashe masu rayukansu kar a ribace su, to ina ga dan uwanka musulmi wanda ba tuba ya yi ba, dama can shi musulmi ne, bawai tuba yayi ba, yana sallah, yana zakkah, yana karatun al-qurani, da salati da istigfari gwargwadon iko, yana yi, tare da haka kace zaka rabashi da rayuwar sa da wanne dalili cikin dalilai.

Ya yan uwa dalilan da suke sanya mutane kisan kai suna da yawa, amma ga misali, yan fashi da makami wanda zasu kashe mutum don su kwace dukiyar sa sawa'un a cikin gidan sa ko akan hanya lokacin da yake tafiya a kashe shi don a kwaci dukiyar sa, to wadannan Allah ya fadi sakamakon su acikin Al-qurani hukuncin su shi ne akashe su ko a tsire su ko a yan ke musu kafar dama da hannun hagu ko kuma akore su daga kasar musulmi.  

Haka kuma, ‘yan ta’adda wadan da su ba dukiyarka suke da bukata ba, rayuwarka kawai suke son dauka, saboda kawai wata manufa ta duniya da suke fatan samu, sannan da tunanin watakila kana iya zamar musu barazana wajen samun abinda suke son samu.

Wannan dai Khudba ce da Marigayi Shiekh Jafar Adam ya gabatar a masallacin Juma’a na Dorayi a lokacin da yake raye. Muna addu’ar Allah ya kai rahama gareshi, ya kyauta makwancinsa.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale
    

Wednesday, September 5, 2012

Wa’azin Sheikh Jafar Mahmoud Adam Na Karshe a Duniya Kuma Ga Matasa Da ‘Yan Siyasa



Wa’azin Sheikh Jafar Mahmoud Adam Na Karshe a Duniya Kuma Ga Matasa Da ‘Yan Siyasa

Wannan Nasihar Marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam Rahimahullah  ya gabatar da ita ne a ranar Alhamis 25/Rabi’ul Auwal,1428. wato dai-dai da 12th April, 2007. Ya gabatar da wannan Nasihar a daren Juma’ar da aka kashe shi, a wajen muhadarar da aka shirya a masallacin Juma’a na Usman Bin Affan dake kofar Gadon kaya. Bayan dawowar sa daga garin Bauchi.

Ita wannan muhadarar malamai uku ne suka gabatar da ita daga cikin su akwai sheikh Dr Muhammad Sani Umar R/lemu da Malam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa da sheikh Muhammad Nazeefi Inuwa. Wadannan sune malaman da suka gabatar da wannan muhadar, amma kasan cewar sheikh Jafar ya dawo daga tafiya ne sai aka bashi minti goma yayi ta’aliki. Ga kuma yadda ta’alikin nasa ya kasance :

Bayan Mallam ya yi godiya ga Allah, tare da yin salati ga manzon Allah salallahu alaihi wasallam,  sannan ya yace “ya yan uwa musulmi abin da zan fada a nasiha ta ta karshe ’’ Allahu akbar wato wannan jumla ita Mallam ya fara bude maganarsa da ita, kamar  yasan cewa washe gari juma’a zai riga mu gidan gaskiya, sai yaci gaba da cewa “Muji tsoran Allah,  mu duka, muda zamuyi zabe’’ wato ya yi wannan Nasihar ne ana jajiberin tsamiya na zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jihohi,  Sannan ya ci gaba da cewa “ muda zamuyi zabe  da kuma wadan da za’a zaba.

Asalin zaben nan malamai sunyi bayanin sa. Dukkan mutumin da zaka zaba, to ya zama cewa zaka zabe shi ne ba don maslahar ka ba kai kadai, sai don maslahar al’umma gaba daya. Akwai mutanen da suke fama da kuncin tunani, wadan da su tunanin su me zasu samu a karkashin dan takara, sannan su ce a zabe shi; ko kuma me suka rasa suce kada a zabe shi. Inda dan takara zai zo yabani naira miliyan goma ni kadai a matsayi na na Ja’afar amma ya ha’inci alummar da yake wa mulki ta hanyar sauran bukatunsu, wadan da a asusun gwamnati akwai kudaden da za’a iya wadan nan bukatu amma yaki yi, Ni kuma in kalli miliyan goman nan ince ku zabe shi. To hakika na ci amanar kaina, kuma na ci amanar ku talakawa bayin Allah, shi kuma shugaba na haince shi. Inda shugaba zai hana ni ko kwabo, amma ya zanto kudaden daya karba daga asusun gwamnatin tarayya ya aiwatar da su ta hanyar da ta dace. To wajibi na ne, in kiraye ku cewa ku zabe shi. Ba a dauki ma’aunin na ni me na samu ko me na rasa ba, masu irin wannan sune wadan da suka jahilci Addini kuma suka jahilci rayuwa. Domin wannan shi ne yakai Nigeria cikin halin ka-ka-ni-ka-yi. Ganin in amfana ni kadai ko kuma a bude mana wata kafa mu yan tsiraru shi ke nan sai muyi shiru alhali mun san abin da shugaba yake yi ha’inci ne,amma sai mu daure masa gindi,hasali ma mu dinga kuruta jama’a cewa dole ne su zabe shi, ba don komai ba sai don  abin da bai taka kara ya karya ba.

 To wannan kuntataccen tunani ne, kuma rashin hangen nesa ne rashin sanin ya kamata ne. Kullum zaka kalli me muka samu na ci gaba,  ba me ni kadai na samu ba ’’ Allahu akbar sai malam ya kara da cewa “ ina kira ga ku matasa ku lura da yadda ake amfani da ku ’’malam ya buga wani misalin abin da ya gani yayin da yake dawowa daga tafiya sai yace “ Da zu na shigo kano dab da lokacin sallar maghriba kafin zuwana nan sai naga wadan da suke kanfen (campaign) wato da alamu anyi yawo da su cikin garine za su koma gida. Naga yara matasa an ciko su akan akorukura su kusan hamsin acikin motar nan kai da ganin su babu wanda ya yi sallar azahar ballan tana la’asa kuma galibin su da alamun sun bugu mota tana ta layi dasu suna ihu suna dauke da hotuna suna sai wane sai wane kuma su wadan da suke bada kudi ayi hakan ciki babu ‘ya ‘yan su, nasu suna can, sun kai ‘ya ‘yan su mayan makarantu na cikin gida ko na waje. Wannan shi ne hakikanin cin amanar al-umma, kai wannan shi ne kakikanin rashin mutunci, ka haukata ya yan talakawa bayan ka yinwatar da su ka kuma ka jahiltar da su babu ilmin addini babu na rayuwa su kashe lokaci mai tsaho suna dauke da hotunan ka kan kana son ka tsaya zabe a wani mataki na zabe. Akan abin da za’a basu wanda bai gaza Naira dari uku ko da hamsin ba.

Sannan mallam ya cigaba da nanata maganar sa ta farko inda yace “Hakika wannan ya kamata ayi hattara, duk wanda zamu zaba, kada mu kalli me ya bamu, mu kalli dacewar sa da cancantar sa. Duk wanda zamu zaba ya kasance ya cancanta ko yabamu kudi ko bai bamu ba. Duk wanda bai cancanta ba to ko yabamu fan taba sama to mu kadashi wannan shi ne gaskiyar lamari, amma idan ku ka tsaya da jahilci da kuntatacciyar kwakwalwa ta ni an bani kaza ni naci kaza. To wannan tunani na ci bayane ba tunani ne na wanda yasan abin daya kamata ba’’.

Sai malam ya kara da cewa “Abin haushi da takaici hatta wadan su masu Magana da yawun Addini akwai masu irin wannan kuntataccen tunani ubangiji ta’ala ya yi mana gamdakatar’’.

Allahu akbar wannan it ace Nasihar da malam ya yi ta karshe ga matasa kai dama dukkan wani mutum mai hankali. Bayan an kammala wannan muhadarar da niyyar washe gari juma’a malam zai yi khudba akan zabe. Ranar juma’a da asubahi malam yana cikin sallah, ya karanta suratul Ma’arij aka samu wasu mutane miyagu azzalumai makiya Allah makiya san cigaban Addini, suka yi masa harbi da bindiga ba sau daya ba, ba sau biyu ba, kisan gilla inda suka harbe shi a kirjinsa na gefen hagu.

Anan muna rokon Allah ta’ala ya sa malam ya yi mutuwar shahada kuma ya karbi shahadar sa, Allah ya kyautata bayansa, ya sanya Albarka a cikin iyalansa da zurriyarsa. wadanda suka aikata wannan aiki na ta'addanci a’ansa, su sani wannan tafarki da Mallam Jafar ya mutu akansa, kamar wata bishiya ce da bata tsiro bata tofo har sai mun shayar da ita da jinin jikinmu, wannan abu ko kadan bazai sanyamu mu yi rauni ba akan wannan tafarki. Allah ya daukaka Musulunci da Musulmai, ya Allah kada ka baiwa azzalumai dama domin su cutar da al’umma.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale

Tuesday, September 4, 2012

Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki!



Mallam Nasiru el-Rufai: Dangajere Kusar Yaki!

Kamar yadda tsohon mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya taba fada a wata hira da ya yi da Jaridar This Day, cewar tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo ya buka ce shi da ya zabo masa mutum mai jini a jika kuma wanda ba shi da tsoro, wanda idan ma ta kama zai iya yin akuya ga mahaifiyar obasanjon don ya bashi mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja saboda ya dai-daitawa mutane sahu daga karkacewar da ya yi. Atiku ya shaidawa Obsanjo cewar Nasan wasu mutane guda biyu abokai da Allah bai sanya sun taba hada hanya da tsoron wani mahaluki ba a fadin tarayyar kasar nan, daya daga cikinsu kuwa shi ne Nasiru el-Rufai, wanda a lokacin shine shugaban hukumar sayar da kadarorin gwamnati ta kasa (Director General  Bureau of Public Enterprises (BPE) and the Secretary of the National Council of Privatisation).

Tabbas Mallam Nasiru el-Rufai ya nuna cewar shi ba matsoraci bane, lokacin da majalisa ta zo tantance shi a matsayin mutumin da za’a nada minister. Domin idan zamu iya tunawa anyi dauki babu dadi da el-Rufai kafin a nada shi minister, inda aka nemi ya bayar da cin-hanci shi kuma ya yi kememe ya ki bayarwa, wanda wannan ta sanya wasu da yawa daga cikin shugabannin majalisa a wancan lokacin jin kunya ciki kuwa harda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Nasir Ibrahim Mantu, inda el-Rufai ya bayyana a majalisa dauke da al-qur’ani a hannunsa ya yi rantsuwa cewar an nemi hanci daga wajensa, kuma shi Mantu ya karyata, inda el-Rufai ya bukaci Mantu shima da ya rantse da Al-qur’ani amma hakan ta gagara inda ya ce shifa bashi da tsarki duk kuwa da cewar akwai makewayi a majalisar, kusan zamu iya cewa tun a wannan lokacin el-Rufai ya nuna jarumtaka da tabbatarwa da duniya cewar shifa ba mutumin banza bane. Wannan namijin kokari da bajinta da el-Rufai ya nuna, shi ya sa jihar Georgia da ke kasar Amerika ta bashi izinin zama dan wannan jihar, wanda yanzu haka el-Rufai yana daga cikin ‘yan Najeriya da suke zuwa kasar Amerika ba tare da anyi musu binciken kwakwaf ba.

Lokacin da Mallam Nasiru el-Rufai ya zama babban ministan babban birnin tarayya ya nuna babu sani babu sabo. Domin ya kau-da duk wasu gine gine da akayi ba bisa ka’ida ba, ciki kuwa harda gidan matar shugaban kasa marigayiya Stella Obasanjo da gidan shugaban PDP na wannan lokacin Sanata Amadu Ali da wasu manya manyan kusoshin gwamnati a wancan lokacin. Haka dai el-Rufai ya ringa sanya gireda yana ma-ke duk wani gini da aka gina shi ba bisa kai’da ba a Habuja. Mallam Nasiru el-Rufai kusan shine ministan Abuja mafi dadewa a tarihin wannan birni tun daga 1999 har zuwa 2007, kuma ya yi aiki dai-dai nasa.

Tun da Marigayi Mallam Umaru Yar’Adua ya zama shugaban kasa el-Rufai ya tsallake yabar kasar nan inda ya tafi kasar Amerika ya koma makaranta, ya halarci kwasa kwasai da dama a fannoni daban daban, ciki kuwa harda katafariyar Jami’arnan ta Harvard, kadan daga Makarantun da el-Rufai ya halarta sun hada da Jami’ar Ahmadu Bello University, Zaria, Najeryia, Jami’ar London ko University of London a Burtaniya da Harvard Business School,  Arthur D. Little School of Management a birnin Massachusetts da Georgetown University da School of Foreign Services a birnin Washington dukkaninisu a kasar Amerika da kuma D.C. da John F. Kennedy School of Government da Harvard University duk dai a can Amerika. Sannan el-Rufai yana da babbar Lambar yabo ta kasa wadda ake kira  OFR (Officer of the Order of the Federal Republic of Nigeria) wadda aka bashi tun yana BFE, kuma yana da digirin girmamawa wanda Jami'ar Abuja ta Bashi a 2005 wato Doctorate Degree.

Bayan da el-Rufai ya dawo gida Najeriya, ya fada Jam’iyyar adawa ta CPC inda ya mara baya ga takarar tsohon shugaban kasa Gen. Muhammadu Buhari duk kuwa da ana kallon zai goya baya ne ga takarar babban abokinsa wato Mallam Nuhu Ribadu. A halin yanzu dai Mallam Nasiru el-Rufai shi ne babban bakaniken jam’iyyar ta CPC wadda Buharin ya dora masa wannan nauyi na dai-daita sahun jam’iyyar kamar yadda a yiwa birnin tarayya Abuja, saboda fama da matsaloli da jam’iyyar ta ke yi a kusan daukacin jihohin kasarnan.

Bayan haka kuma, el-Rufai shi ne kusan mutum daya tilo wanda tauraruwarsa ke haskawa wajen adawa da gwamnati mai ci ta Goodluck Jonathan da kuma Jam’iyyar PDP. Mallam Nasir el-Rufai ya dauki lokaci yana sharhi akan kasafin kudi na wannan shekarar ta 2012 inda ya yi kaca-kaca da wannan gwamnatin ya nuna ma basu san me suke yi ba. Hakan ta sanya el-Rufai ya dinga daukan hankalin jama’a a ciki da wajen kasarnan wajen yadda yake fashin baki a harkar tafiyar da wannan gwamnatin musamman a harkar da ta shafi tattalin arziki, wannan ta sanya jami’an SSS suka ringa sanya masa tarko suna kamashi a kusan duk lokacin da zai yi wata tafiya zuwa kasashen waje, haka nan yake tsallake irin wannan turaku da ake sanya masa.

Bahaushe ya ce al-kalami ya fi Takobi, lallai wannan magana haka ta ke, domin shakka babu wannan gwamnati mai ci babu wani alkalami da ta ke jin tsoro a kullum kamar na el-Rufai, domin sun san cewar mai ilimin gaske ne kuma masani ta fannoni da daman gaske. Mallam Nasiru el-Rufai dai idan ka ganshi irin mutanan nan ne da zaka gansu ‘yan tsirit wato ba shi da wani cika ido, wannan ce ma ta sanya abokansa suke masa lakabi da sunan GIANT wato wani babban mutum kamar dai yadda Bahaushe yake ce wa gajere malam dogo. Lallai kam ya zuwa yanzu babu wani daga cikin ‘yan Adawa wanda tauraruwarsa take haskawa kamar el-Rufai ba, kuma duk wannan ya faru ne ta sanadiyar al-kalaminsa da yake caccakar wannan gwamnati da shi. Tabbas maganar Bahaushe gaskiya ce da ya ce Alkamai ya fi takobi, domin idan da fada za’a iya da takobi watakila da farat daya za’a gama da el-Rufai amma da yake fadan na alkalami ne, babu yadda aka iya da shi sai dai a kayar da shi da hujja idan ana da ita.

Lallai Najeriya tana bukatar mutane masu gaskiya wadan da zasu iya yakar cin-hanci da rashawa da gaskiya kuma hazikai irinsu Mallam Nasiru el-Rufai.

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
www.facebook.com/yasirramadan.gwale