Saturday, June 2, 2012

Al-Adar Sabule Wando Tsakanin Matasa Daga Ina?

AL-Adar Sabule Wando Tsakanin Matasa Daga Ina?

Yana daga cikin munin al'amuran wannan zamanin tsakanin matasa shi ne wannan al'adar ta sabule wando. Sabule wando daga ainihin inda ake daura wandon wato kugu zuwa kan duwaiwai, wannan bakuwar al'adace ga al'ummar Hausawa, kuma wannan mummunan abin koyi ya samo asali ne daga bakaken fata mawaka a kasar Amerika, kuma, wannan mummunar ta'ada abin da zai kara nuna maka cewa ko da a can Amerika 'yan iska da 'yan kwaya suke yinta, don bazaka ga wani mai kima da sanin ya kamata ba yana wannan abu, duk inda kaga mutane zaka gansu da shigarsu ta kamala, sai fa idan kaje sansanin 'yan iska mafiya yawansu bakar fatar Amerika nanne zaka ga irin wannan fitsara da rashin tarbiyya.
A salain wannan fitsara ta sabule wando. Kamar yadda na saurara acikin wani shiri na Murayar Amerika mai suna Sakonmu Na mako, Mallam Sahabo Imam Aliyu Hong ya yi bayani akan asalin wannan fitsara ga abinda y ace " wato ada can a lokacin da ake aikin Bauta a kasar Amerika, idan bakar fata yayi laifi aka kaishi gidan kurkuku, akan bashi kaya irin na nasaru ya saka amma ba tare da mazagi irin na turawa ba, wannan ta sanya, a wancan lokacin, masu cin sarka sukan sanya kayan haka idan akaci sa'a wandon ya yi wa wanda aka baiwa yawa, sai ya rika sabulewa har yazo kan duwaiwai, a lokacin nan su kuma turawa masu kula dasu sai u sanya mutum daukar abu aka kuma ya tallafe da hannayensa guda biyu wannan zata sanya yana tafiya wandon na saukowa kasa, su kuma suna binsa a baya suna ta sheka dariya" a yadda Mallam Sahabo ya fada, wannan itace asalin wannan al'adar ta sabule wando, a lokacin idan turawa suna bada labarin bakaken fata saisu rinka sabule wando da nufin yadda bakin mutum ke tafiya a gidan yari. Wannan shi ne tarihin wannan muguwar dabi'a.
Da yake yanzu matasa kusan a ko ina a duniya zaka samu sun tasirantu da mawakan Amerika. Wadan nan mawaka, bakaken fata wadanda galibinsu ba mutanan kirki bane, kodai 'yan iska 'yan daudu ko 'yan luwadi ko masu neman mata ko kuma 'yan kwaya da 'yan wiwi. Abin mamaki sai kaga duk wani irin hauka da shirme da mawaki ya yi sai ya zama abin ado ga daukacin matasan wannan zamani, ba wai matasanmu na Najeriya ba harda larabawa, harma da turawan suna irin wannan fitsara.
A da can lokacin da wasu shekaru da suka shige ba masu yawa ba, anyi wani mawaki mai suna TuFac (2pac) a kasar Amerika, ya yi sharafinsa kusan zaka samu komai yayi ya zama yayi a wannan lokaci. A lokacin dashi wannan mawaki ke tsiyarsa, zaka samu baya yin wata shiga ta mutunci ko kirki domin sau da yawa zaka ga fitsara kawai sukeyi a cikin wakokinsu, ta yadda zakaga suna rawa da mata tsirara haihuwar uwarsu, shi wannan mawaki shi ne ya koyawa da dama daga cikin matasanmu daura wani yanki aka da yayi kama da kallabi da ake kira "Bandana" sai kaga kowane kucakin idan ya yi wanka so yake a ce ya hadu ta hanyar daura wannan kyalle a kansa, ko kuma, yin aski kwal-kwal tare da barin dan karamin gemu da gashin baki badon koyi da sunnah ba sai kawai domin koyi da wannan mawaki tufac, acikin wakarsa ta Baby Don't cry karara ana koyawa matasa yadda zasu kama 'yan mata ta karfin tsiya ayi lalata dasu ko sun yarda ko basu yarda ba. Shi dai wannan mawaki ya mutu don haka duk tsiyar daya aikata yana can yana ganinta, amma ya barwa matasanmu mummunan gado.
Bayan wannan mawaki, ansamu wasu da yawa daga cikin 'yan wasan kwaikwayon kasashen turai da Amrika inda suke ta koyawa matasanmu sabbin tsiyataku. Misali daura robobi a hannu ko daura tsumma ko sanya manyan sarkoki wanda duk mai hankali idan ya kalla yasan akwai alamar Hauka da tabin hankali, kawai mutum ya sanya sarkoki sun masa yawa a wuya, ko kuma a sanya riga batare da amballe butur ba duk wai don a nuna gayu.
Yanzu kuma wani mawaki da yake tashe ta rashin kunya da fitsara a Amerika shi ne Lil Wayne. Shi dai wannan mawaki da ganinsa babu ko tambaya kasan sunyi hannun riga da mutanan kirki, bayan yasa anyi masa rubutu a kusan ilahirin jikinsa sannan shima yana wannan al'adar ta sabule wando da sanya sarkoki, da bayyana kalamai na batsa. Abin mamaki da ban haushi da yawan matasanmu basu ma san me wadan nan mawaka ke fada a cikin wakokinsu ba, amma kawai sai kaji wai sune abin birgewa, kaga mutane sun cika wayoyinsu da irin wadan nan wakoki wanda galibinsu batsace tsagwaronta.
Sannan kuma, ita wannan dabi'a da matasanmu suke kwaikwayo ta sabule wando sai ka samu suna sanya wani irin wando wanda kasansa ya tsuke sosai ta hanyar kama musu jiki daga mazaunansu, kuma ya dan bude ta yadda ko bakasanya tazuge ba wandon bazai zamo sama da yadda ka sanyashi ba, wato idan ka sanyashi a kasan duwaiwai  a nan zai tsaya saboda kasan ya tsuke, saboda cibayan tunani da rashin fahimtar manufar rayuwa wai wannan shi ne abin birgewa tsakanin matasa, wai komai kauyancinka matukar kayi irin wannan shiga to kai ka-cinye, ka zama wayayye ka zama caburos tunda ka iya tafiya da zamani; wannan ta sanya ko kauyuka ka shiga sai kaga suma ba'a barsu a baya ba ta wannan fannin kowa so yake ace masa shima wayayyene ko kuma gaye.
Abu na gaba, shi ne, yadda kwallon kafa irin ta kasashen turawa ta shiga zukantamu sosai da gaske, ta yadda suma duk wani iskanci da dan kwallo zaiyi abin birgewa ne. yanzu akwai wani irin aski da matasa keyi da ake saisaye gefe da gefe abar gashi a tsakiyar ka, kamar yadda wani dan kwallon kulab din Real Madrid Christiano Ronaldo yake yi, wai duk wannan shi ne babban abin koyi a wajen matasanmu, tur da irin wannan mummunan gado da matasa ke samu daga turai da Amerika.
 Bayan wannan, akwai kuma wasu masu sanya dan kunne guda daya a gefen kunne ko na dama ko na hagu duk wannan shi ma anayinsa da sunan wayewa ko cigaba, ko a sanya kwaftareren takalmi, ko kuma kwaftareren tabarau wanda galibi yanzu mata suka fi sanya irin wannan tabarau.
Wannan babban kalubale ne ga iyaye maza da mata da malamai da kuma hukumomi. Wajibin iyaye ne su baiwa 'ya 'yansu tarbiyyar da tayi dai-dai da koyarwar addinin musulunci, da kuma tsarin zamantakewa irin tamu ta Hausawa. Haka kuma, wajibin hukuma ne ta baiwa mutane kariya ta hanyar tsare musu hankalinsu da tunaninsu da lafiyarsu uwa uba rayukansu da dukiyoyinsu. Sannan suma malamai masu wa'azi tsakani da Allah wannan hakki ya rataya a wuyansu domin cigaba da fadakar da al'umma kamar yadda akeyi, abin mamaki, malamai suna wa'azi amma wannan al'ada kullum dada cigaba ta ke yi kamar wutar daji. Allah ya shirya mana matasanu shirin addini.
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Abokantaka A Sabon Karni!!!


Aboki wani mutum ne majibincin rayuwar dan uwansa. wato aboki shi ne wani mutum da zuciyarka da tunaninka ya zo daya da nasa, kamar yadda Hausawa kance sai hali ya zo daya sannan ake abokantaka. Haka kuma, malamai masana nazariyyar dan adam sun ta yin binciken shin wane aboki. kamar yadda Allen 1996 yake cewa " dole ne kayi wa kanka tambaya kafin ka zabi aboki" yace dole ne mutum ya yiwa kansa tambayoyi kamar haka: Shin wane ni? wa nake bukata ya zama abokina? Me yasa nake son wane ya kasance tare da ni? da wasu tambayoyin daban. ta hanyar samun amsoshin wadan nan tambayoyi ne zaka gane mutanan da kake bukata a rayuwarka da kuma mutanan da suke bukatarka a rayuwa.
Hakika acikin wannan rayuwa, zaiyi wahala ka samu wanda yake rayuwa shi kadai ba tare da taimakon abokansa ba, wato abin da ake kira (Recleus Life), abokanai suna da matukar muhimmanci tare kuma da tasiri a rayuwa, domin sune sukan taimakamaka wajen yanke hukuncin tunaninka, da kuma tayaka hangen abinda ya kamace ka. lallai duk wanda yake rayuwa ba tare da samun goyon bayan abokansa ba to yana da babban gibi a cikin rayuwa, domin akwai al'amura da yawan gaske wadan da bazaka iya yin maganarsu da iyayanka ko matarka ko kanneka ba dole sai da abokai. Shakka babu yanayinka yanayin abokanka, kamar yadda Allen ya fada, idan kayi sa'a kai mutumin kirki ne to da wahala ka samu abokanka mutanan banza, don haka zasu taimaka maka da muhimman shawarwari wajen yanke hukunci a rayuwa.
Sauda yawa abokai sukanyi tasiri sosai azukatan abokansu sama da iyaye. wannan yana faruwane musamman a wannan zamanin ta yadda ake kara samun gibi mai yawa tsakanin iyaye da 'ya 'yansu, wasu iyayan tsakaninsu da 'ya 'yansu maganganu ne takaitattu, basu ko san halin da 'ya 'yansu suke ciki ba, basa shawara da su, don haka dole ne su kuma 'ya 'ya su cike wannan gurbi da abokansu, wadanda sau da yawa sune suke dauke musu kewar rayuwa. Musamman 'yan uwanmu mata sunfi fadawa cikin wannan yanayi ta yadda zakaga mace a gidansu ba'a damu da ita ba, ba'a neman shawararta, kaga yarinya ta balaga, amma ubanta baisan ya takeyi da kayan amfani na yau da kullum ba, kamar audugar mata, kayan kwalliya, sau da yawa iyaye maza, zaka samu wani uban baitaba sayawa 'yarsa kayan kwalliya ba kuma bai taba bata kudi ta saya ba, ita kuma uwarta sai ka samu tana kunyar tayi magana da ita akan musamman abin da ya shafi al'ada, yarinya sai ta fara al'ada har ta gama babu wanda ya sani tsakanin iyayanta tana ta kunzugu da tsummokara, sai dai idan ta hadu da kawayanta su tattauna.
Ta ya ya ake  iya samun abokai? Hakika wannan tambaya tana da matukar muhimmanci kwarai, domin kamar yadda mukayi bayani a sama cewa aboki majibincin lamarin abokinsa ne, kuma rayuwa bata yiwuwa sai da abokai. Kamar yadda muka sani a da can kakanninmu da kakannin kakanninmu rayuwarsu batyi fadiba kamar tamu. Hakika a wancan lokacin abokai basu da yawa domin galibi idan ka duba rayuwarsu zaka samu, galibi mutanan kauye daya ko gari daya kai koma unguwa daya ne ke abokantaka. Saboda karancin rashin sadarwa ko kuma "wayewa" irin ta zamani. A wancan lokacin hanyoyin da ake bi wajen samun abokai sun hada da Dandali, wato samari maza da mata kan hadu a dandali domin tattaunawa da sada zumunci tsakaninsu da kuma nishadi, ananne ake haduwa tsakanin 'yan waccan unguwar da wannan unguwar don kulla zumunci; Daga nan kuma sai makarantar Allo inda zaka samu mafiya yawanci yaran unguwa daya kanyi karatu a hannun malamai guda, hana rantsuwa sai yaran da ake dauka ake kaisu wasu garuruwan domin neman ilimin al-qurani, wannan ta baiwa wasu da yawa dama wajen samun abokai wadan da suke da al'adu da suka sha bamban da nasu, misali, a makarantar allo daya zaka iske yara daga kasar sokoto ko daga kasar Gongola ko kano ko zariya da sauransu duk suna karatun allo tare a wancan lokaci.
Har ila yau, wata hanya ta samun abokai cikin sauki, itace matarantar boko. Hakika, wannan tana daga cikin damarmaki na farko-farko na samun abokai da suka sha bamban da wanda akeyi tsakanin al-majirai, domin zaka samu wannan yara ne kowa ya sa kayansa fes-fes sabanin makarantar allo da yare ke zama da datti, haka abin kan ci gaba har zuwa makarantun gaba da firamare wato sakandare, wanda wannan abokantaka itace tafi kowacce dorewa a wannan zamani, domin zaka samu galibin abokai na sakandare basu cika sakaci da wannan abokantaka tasu ba ko da kuwa sun kammala makaranta, musamman wadan da sukayi makarantun kwana, shi yasa, yanzu zakaji kungiyoyin tsaffin dalibai kamar Barewa Kwalej Zariya da sauransu .
Akwai aboki daya amsa sunan aboki, wanda idan baka ganshi ba kwana biyu zaka ji dalili; sannan akwai wanda ake kira da turanci (Acquaintance) wato shima abokine amma bana kusa ba, misali wanda kuke haduwa dashi a makaranta, idan ka ganshi kukan gaisa, idan kuma baka ganshiba bazaka damuba haka shima bazai damuba. Akwai bambanci mai yawa tsakanin Aboki na kusa da na nesa (Friends da Acquaintance).
Baya ga wadancan hanyoyi na makaranta da ake iya samun abokai, ana iya samun abokai ta hanyar kasuwa, ko wajen aiki. Itama wannan wata muhimmiyar hanya ce ta samun abokai majibinta sashe, suma sukan taka muhimmiyar rawa sosai a rayuwar mutum, ta yadda zakaga ana samun karuwar alaka da dangantaka sosai tsakanin abokan kasuwa dana wajen aiki.
Wata hanya mafi Sauki da zamani yazo da ita ta samun abokai itace ta hanyar Sadarwa. Hakika wannan hanya ta sadarwa (Social Network) ta zo da abubuwa masu saukin gaske, kusan itace hanya mafi sauki da zaka fahimci kanka da kuma abokan mu'amalarka, Kana dakinka a zaune zaka iya Magana da mutumin da yake a can wata kasa mai nisan gaske, kuma ya zama abokinka sosai kamar kun tashi tun yarinta, bayan kuma watakila bai taba ganinka ba kaima baka taba ganinsa ba, wannan hanya itace ta zaurukan tattaunawa da musayar ra'ayi kamarsu Fesbuk da Twitter da Friends Reunited da Classmate da sauransu. Bayan wannan kuma akwai wata hanyar ta amfani da wayar hannu, musamman wadanda suke amfani da wayoyin Blackberry, da dangoginta, da kuma damar da kamfanonin sadarwa suke bayarwa ta amfani da tsarin tura gajeren sakon SMS da kuma tura sakonnin hotuna daskararru da masu motsi, da kuma tsarin shiga dakin hira da abokanai wato Chart Room. Akwai hanyoyi da daman gaske kusan kullum ana kara samun wasu sabbin hanyoyi na kulla alaka da zumunta tsakanin abokanai a Internet.
Muhimmancin abokantaka ta Internet: Wannan hanya ba karamin saukakewa mutane abubuwa da dama tayi ba, domin mutumin da kake ganinsa daga nesa ya yi maka nisa sosai, amma sai kaga cikin arha gashi kana Magana dashi yana mayarmaka, misali wannan hanya ta sadarda shugabanni da talakawa, ta yadda zakaga Gwamna ko shugaban kasa yana musayar kalamai da talakawa wanda ko kusa a zahiri hakan zata zama da kamar wuya. Wannan hanya tana da muhimmanci sosai, zata bata damar sanin al'adun wasu mutanan, misali zaka samu Bakano da Bazazzage da Bahadeje da Baktsine an hadu anata barkwanci, wannan yakan baka damar fahimtar wasu abubuwa da dama da baka sansu ba. Wannan tsari na abokantaka yana kaiwa harga abokantaka ta zahiri, inda ake haduwa a wasu kebantattun lokuta domin ganin juna da kara dankon zumunci
Abokankatar Internet Gaskiya ce kuwa? Shakka babu wannan abokantaka akwai yaudara a cikinta sosai da gaske, domin idan ka shiga bayanan wasu da suke sanyawa sai ka kasa fahimtar su waye su? Wani lokacinma kakan kasa bambance tsakanin mace da namiji, sai kaji wani ya yi amfani da wasu irin sunaye wadan da ba ma'arufai ba. Sannan wannan abokantaka takan zama gaskiya ya yin da ka hadu da mutumin da kake abokantaka dashi a zahiri, kuma akan samu shakuwa ta karu sosai, fiye da abokanka na kuruciya, Misali akwai abokina da muka jima tare dashi a wannan kafa ta sadarwa, wata rana kwatsam na niki gari nace zan kawo masa ziyara, inda na taka har inda yake a cikin Jami'ar Ahmadu Bello dake zariya, wannan ya kara karfin alaka sosai tsakanina dashi, haka nima nakan samu mutane da yawa wadan da suke zuwa takanas ta kano domin kawomin ziyara kasancewar mundade da sanin juna ta wannan hanya, hakika wannan wata muhimmiyar kaface da mutum zai samu mutane daga gurare daban daban a wannan duniya.
Matsalar Abokantaka: Mutane sukan kaunaceka saboda kabiyo hanyar da zasu kaunaceka. Yana da kyau mutane su sani gaskiyarka itace babbar damarka ta samun masoya na hakika, wasu da yawa sukan yi karya mara misaltuwa a wannan hanya, misali, wani zai ringa nuna maka shi mai arziki ne, alhali kuma ba haka abin yake ba, ko kuma wani ya nuna maka shifa a Abuja yake rayuwa inda yake kashe kudi masu yawa, kaga duk wadan nan matsaloli ne da idan ta bayyana ga yadda zahirin mutum yake sai kaga anji kunya, a har kullum abin da nayi imani dashi shi ne duk wanda zanso ina soshi ne don Allah haka kuma, duk wanda zanki zanki shi ne saboda Allah, bawai saboda wani abin duniya ba. Mallam Sa'adu Zungur acikin wakarsa ta Arewa Jamhuriyya ko Mulukiyya yana cewa "inzaka fadi fadi gaskiya komai taka jamaka . . .! Ina fatan Alheri ga 'yan uwa abokai na hakika, kuma ina fatan saduwa da dukkan abokaina wadan da muke soyayya don Allah. Allah ya sadamu da alherinsa

Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com


Saturday, May 19, 2012

Saudi-Bahrain: Karyar Iran ta kare!

Saudi-Bahrain: Karyar Iran ta kare!

A ranar sha hudu ga watan mayun wannan shekara ne (14th May, 2012) kungiyar kasashen Gulf Cooperation Council (GCC) wadan da suka hada da kasar Saudiyya da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait da Oman da kuma kasar Qatar, suka bada shelar da ta ke nuna hadewar kasar Saudiyya da Bahrain, a matsayin kasa guda mai bin tafarkin mulkin Sarauta karkashin Larabawa sunni. Hakika wannan hadewa muhimmin al'amari ne ga samun zaman lafiyar kasashen yankin Gulf. Hadewar dai tazo ne a yayin da aka samu akalla shekara guda 'yan shi'ah masu samun goyon baya daga Iran da Hizbolla ke ta kokarin yin juyin juya halin da zai kai ga kifar da gwamnatin Sheikh Hamad Bin Issa Alkhalifa a kasar ta Bahrain. Da farko dai sun fara ne da neman kawo sauyi a bisa yadda ake tafiyar da mulkin kasar, inda masarautar kasar ta bayyana gudanar da wasu sauye sauye da zasu baiyawa majalisar kasar dama mai yawa a cikin kundin tsarin mulkin kasar.

Ita dai kasar Bahrain, kusan za a iya cewa wani tsibiri ne da ya ware kadan daga cikin kasashen larabawa, kasar tana gab da kasar Saudiyya. ita dai wannan kasa ta Bahraina ta samu ne a shekarar 1783, lokacin da musulmi Ahlussunnah karkashin Gidan sarautar Alkhalifa suka fatattaki 'yan shi'ar Farisa. inda suka kafa daula mai bin tafarkin Sunni. Tun wancan lokacin ne kasar Farisa wadda ake kira Iran a yanzu take ta hakilon ganin cewar kasar Bahrain ta komo karkashin Daular Shi'ah, kasan cewar Bahrain ita ce kadai daga cikin kasashen larabawa da ta ke da mabiya addinin Shi'ah masu yawa. Kamar yadda muka sani kasar Iran kusan itace kasar da tafi kowacce kasa kusanci da kasashen larabawa bayan kuma ita ba kasar Larabawa bace, don haka kullin tunaninsu shi ne ya zasuyi su kwato kasar bahrain daga hannun gidan Sarautar Alkhalifa. Da kuma kokarin kawo tarzoma a daukacin kasashen larabawa, wanda suke gani wata dama ce a garesu ta su shiga su yada addinin Shi'a ga larabawa musulmi.

Tun bayan bore tare da zanga-zangar kasashen larabawa da ta samo asali daga Tunisiya, inda talakawa sukaci nasarar hambarar da gwamnatin zalunci ta Zainul Abedeen Ben Ali, abin ya rika yaduwa tare da goyon bayan munafukar kasar Iran da kuma 'yan Shi'ar Lebanon. haka abin ya ci gaba da yaduwa har ya isa kasar Masar wadda ita ce mafi kusanci da kasashen Turai da Amerika, inda suma talakawa sukaci nasarar hambarar da Shugaba Hony Mubarack duk kuwa da barazanar da ya ringayi musu, haka dai wannan guguwa ta yi ta kadawa a tsakanin kasashen larabawa, kuma itace tayi sanadiyar tafiyar Shugaba Ali Abdallah Saleh na Yemen da kuma kisan da akayiwa Shugaba Mu'ammar Ghaddafi na libya.

Haka dai wannan zanga-zanga ta cigaba da ruruwa har ta isa kasar Siriya, inda anan ne tafi yin muni ainun sama da kowacce kasa da akayi wannan zanga-zanga. Hakika gwamnatin Shugaba Bashar Assad ta yi amfani da wannan dama inda tayi ta kisan musulmi mabiya sunnah wadan da su ne suke da rinjaye a wannan kasa ta Siriya, anruwaito sosjoin gwamnatin Assad suna kai muna nan hare-hare akan garuruwan musulmi mabiya sunnah wadan da suka hada da Homs da Dar'a da Hama da Idlib da Aleppo da sauransu bayan kuma an yanke musu wutar lantarki da ruwan famfo, harkokin kasuwanci sun durkushe gabikidaya a wadan nan yankuna, duk kuwa wannan na faruwa ne da goyon bayan da Assad yake samu a fakaice daga kasar Iran da kuma kungiyar Hezbollah dake kasar Lebanon, kasancewarsa Dan Shi'a Alawiyyi, a gefe guda kuma shi Assad din yana kara samun goyon baya daga kasashen Turai da Amerika da Chana da kuma Rasha, duk wannan saboda suna tsoron kada su bari Assad ya sullube a sami wani shugaba daga cikin musulmi Sunni wanda zai kasance mai kishin addinin musulunci, wanda hakan zai kai ga tayar da maganar tuddan Golan da kasar Israela ta mamaye wanda shi shi Bashar Assad da Mahaifinsa Hafeez Assad suka kauda kai wa Israela. Sai kayi mamakin duk irin kurarin da kasashen turai sukeyi akan hakkin dan Adam, Bashar Assad yana kashe mutanansa amma suna rarrashinsa.

Duk da cewa kasashen larabawa sun goyi bayan wakilin majalisar dinkin duniya Mista Kofi Anan akan ya je kasar Siriya ya tattauna yadda za'a sasanta rikicin siyasar kasar. Amma wannan babu abinda akeyi illah yawan shakatawa da taron shan shayi, domin duk irin manufofin da Kofi Anan ya je da su Assad ya sa kafa ya yi fatali da su amma kuma ana tausarsa da cewa ya yi hakuri, a zauna akan tebur a sulhunta. shakka babu abin nan ne da ake kira Interest ya yi yawa akan kasar Siriya shi ya sanya kasashen Turai da Amerika suke ta jan-kafa akan Assad duk wannan yana kara bayyana karara irin yadda sakatariyar harkokin wajen Amerika Hilary Hoadharm Clinton da kuma jakadiyar Amerika a majalisar dinkin duniya Suzan Rice suke ta yin amai suna lashewa akan wannan batu na kasar siriya, da kuma 'yancin dan Adam.

Idan har da gaske suke akan yadda suke lallabar Assad, me yasa basuyiwa marigayi Saddam Hussein Allah yajikansa irin wannan ba? ko kuwa kawai domin shi musulmi ne sunni, shakka babu wannan a bayyane take cewa Amerika da NATO sun afkawa Saddam Hussein saboda kasancewarsa Musulmi sunni, domin dukkan irin bayanan da mista Hatz Blick ya bayar sun nuna cewar Saddam ba shida wasu makamai masu hadari ko guba. A gefe guda kuma ana ta kokarin nunawa duniya cewa akwai baraka tsakanin Amerika da Iran, sanin kowane cewar da hadin bakin kasar Iran dari bisa dari aka yaki Saddam, kuma 'yan shi'a su Muktada Al-sadar da suke samun goyon baya daga Iran suka ci karensu babu babbaka duk da ana nuna cewa akwai tsamin alaka tsakaninsu da Amerika, koma dai meye Hausawa sunce shi munafurci dodo ne mai shi yake ci, don haka komai tsawon lokaci zai bayyana.

Idan kuma muka dawo batun kasar Bahrain, dole ne mu yabawa sarkin Qatar Sheikh Hamad Bin Jassim Althani da kuma shi kansa sarkin Bahrain Shiekh Hamad Bin Issa Alkhalifa da kuma Sarki Abdallah Bin Abdulazeez Ali-Saud na Saudiyya, hakika wannan namijin kokari ne sukayi na kokarin dinke barakar wannan yanki. kuma muna fatar watan wata rana a samu yanayin da zai kai ga kafa kasar larabawa kwaya daya (United State of Arabia), wadda muna sa ran ita zata kai ga kafa shugabancin musulmi guda daya a duniya, kuma muna nan muna fatan ganin kasar Iran ta komo karkashin Musulmi sunni, a kusa ko a nesa. domin sanin kowa ne cewa babu wata kasa a yanzu da take mafi hadari a duniya sama da kasar Iran, domin duk wani munafurci da fadi tashi da su akeyi, ya Allah ka wargaza aniyarsu ka rusa lamarinsu, ka hansu sakat.

kaicon tsufa, hakika Tsufa wata cuta ce da batada magani, kuma babu yadda dan Adam zai yi da rayuwa sai tsufa ya riskeshi, tsufa ya zowa Sarki Abdallah Bin AbdulAzeez Al-Sa'oud na Saudiyya a lokacin da duniyar Larabawa da ta musulmi suke da bukatar shawarwari da tunaninsa, da hange irin nasa, muna addu'a ga Khadumul Haramainissharifain, Allah ya kara masa lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya sanya albarka acikin rauwarsa, hakika ya yi hidima ga dakin Allah mai alfarma da masallacin manzon Allah dake madina, Allah ya cika a mizaninsa, Allah ya jakwanansa. Muna kuma Addu'ar Allah ya yafe masa laifukansa wanda ya aikata bisa kuskure da wanda ya aikata bisa sani ko ajizanci. Allah ya taimaki Masarautar Sadiyya da Addinin Musulunci baki daya. ya Allah ka nuna mana ranar da za'a kawo karshen shi'ah a wannan duniyar.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com  

Saturday, May 12, 2012

Matasa a Jiya da Yau!


Matasa a Jiya da Yau!
Nagartaccen matashi shi ne ginshikin samar da kyakkyawar al'umma. Hakika dukkan al'ummar da take da dimbin matasa to tayiwa Allah godiya, domin wannan al'barka ta matasa itace take nuna cewa lallai za'a jima ana damawa da wannan al'umma a fagen rayuwa ta  nan gaba. Hakika matasa babu abin da suke da bukata kamar jagoranci da kokarin sanyasu bisa turba ta gaskiya, wadda zasu gina kansu domin gaba, kuma su sami zarafin gina al'ummar da suke rayuwa a cikinta.

Manazarta da masharhanta da dama sun wasa kwakwalwa wajen baje kolin tunani da bincike da ra'ayin shin wai waye matashi? Kamar yadda larabawa suke da wani Karin Magana inda suke cewa"ita jarumtaka ga matashi aka santa, idan ya kasance matashi babu jarumtaka, to sunansa wani abin" wannan Karin Magana ya nuna matukar iya zance na larabawa, shakka babu kyakkyawan matashi shi ne abin misali da kwatance, kuma jarumtaka tsakanin matasa wannan abin bukata ne kwarai da gaske.

 Hakika dukkan wani mutum da yayi sa'ar samun kansa a wannan sarari mai fadi da ake kira duniya, kuma yayi katarin dacen shige wannan yanayi ko lokaci na matashintaka kuma ya yi sa'a ya wuce lafiya to babu abinda ya kamaceshi illa ya yiwa Allah godiya, da kuma nazarin yadda za'a gina goben masu zuwa nan gaba.

Bari mu kalli matashi a shekarun baya: hakika a zamanin dacan matasa su ne suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen dorewar wannan al'umma, hakika matasan da suka gabaci wannan al'umma tamu sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin mun sami ingataccen yanayin wanzuwa; misali ka dauki ganuwar birnin kano da zariya da kasar karaye da wasu garuruwa a Arewa da suke da ganuwa, ka tambayi kanka shin su wa suka gina wannan ganuwa? Mala'iku ne, al-janune, mutanan boye ne, turawan mulkin mallaka ne? shakka babu amsar wannan tambaya itace a'a matasan wannan al'umma da suka gabacemu su sukayi wannan katafaren aiki mai dumbin tarihi a lokuta masu tsawo da suka shude; ka zagaya birnin kano tundaga kofar Danagundi har kazagayo kofar Na'isa kaga yadda akayi gini babu ha'inci babu amaja, ka kuma lura da yadda ginin yake ka kuma tambayi kanka shin kasar da akayi wannan gini daga sama aka ringa zubo da ita ko kuwa ya abin yake, hakika wannan kasa kwakwularta aka ringayi daga kasa anayin bululluka da tubali har akayi wannan gini, duk wannan fa matasane sukayi, wannan misali kadan ne daga cikin irin misalign ayyukan da matasa wadan da suka gabaci wannan al'umma sukayi, kuma idan ana biyansu lada to bai taka kara ya karya ba; nasan watakila wani yace to ai bayi ne sukayi wannan gina ba 'ya 'ya ba, koma dai su wane sukayi lallai matasa ne, domin nayi imanin dattawa ko mata bazasu iya irin wannan namijin kokari ba.

Haka zalika mu sake komawa baya a tarihi, mu kalli irin yadda akeyin dalar gyada a kano da hadejiya kaga irin tarin buhunan gyada dubbai kure gani wanda duk matasa ne suka noma mafi yawanci, kuma a duke da fartanya ba kamar yanzu da ake da tarakta ba, inda mutum yana zaune akan mota yana bata umarni ba tare day a duka ba. Kuma suma wadan nan matasa da sukayi wannan noma, sunyi ba tare da samun wani lada na kuzo mu gani ba.
Hakika matasa a lokutan baya ba malalata bane idan mutum ya kalli wadan nan misalai guda biyu da muka bayar, matashi ne zakaji ance ya nome gonarsa da ta mahaifinsa da kuma ta surikinsa duk a damina daya ba tare da anbashi ladan ko sisi ba da sunan ladan hidima. Shakka babu tarihin wannan kasa bazai taba mancewa da irin gagarumar gudunmawar da matasa suka baiwa wannan kasaba a lokutan da suka gabata.

Sannan mu kalli matasa a wannan lokaci: shakka babu bazanyi kuskure ba idan nace matasan wannan al'umma a yanzu malalata ne na kin karawa, kowa ya nade hannun riga jira yake yaci ko ya samu ba tare da yasha wahalar ko kwabo ba, ka duba irin yadda Allah ya hore mana dimbin matasa ninkin ba nikin wadan da suka gabata, amma amfanuwar da akeyi dasu ko kusa bata kai amfanuwar da akayi da matasan da suka gabata ba; tambaya shin me ya jawo haka? Shin tarbiyya ce wadan nan matasa na yanzu basu samu ba daga magabatansu ba ko kuwa ya abin yake? Ka shiga cikin lungunanmu da sako da kwararo-kwararo kaga dimbin matasa 'yan bana bakwai majiya karfi suna zaune babu aikin fari balle na baki kawai suna zaune suna hira marar amfani a duniyance ko a lahirance, daga rana ta tarar da inuwa a sake daukar benci a maidashi inuwa, a cigaba da hira maras kan-gado.

Allah ya hore mana kasa mai fadi ba mai kwazazzabo da yawa ba, kuma bamai tuddai da yawa ba, kasar noma iya ganinka tundaga Kauran Namoda har katagum ka zarce har zuwa Nguru kasace mai fadi da za'a iya noma abinda zai iya cida kasarnan da makwabtanta, uwa uba kuma ga albarkar kasa da Allah ya bamu, mangwaro zaka sha ka yarda kwallon insha Allah idan ruwan damina ya dakeshi sai kaga yayi tsiro idan akayi sa'a babu abinda ya tabashi akwana a tashi sai kaga ya zama bishiya, duk wannan kadan ne daga cikin irin al'barkar da Allah ya yiwa wannan kasa.

Babu shakka kamar yadda na fada a farko, matasa sune kashin bayan kowace al'umma! Amma idan ya kasance matasan ba cima zaune bane kamar yadda muke a yanzu; abin mamaki kaga katon gardi yakai shekara 30 ko 35 amma wai har yanzu a gidansu ana bashi kudin batarwa, ba'a yi masa wani tanada da zai dogara da kansa ba, ballantana ya yi tunanin gina rayuwar manyan gobe.

Tun Ran Gini Tun Ran Zane: Allah ya albarkaci Bahaushe da iya Magana. A ganina dalilan da suke janyo matasa su zama masu mutuwar zuciya sune kamar haka:

Iyaye: Hakika, iya ye a wannan zamanin sun taka muhimmiyar rawa wajen ragwantar da 'ya 'yansu, domin zaka samu, musamman tsakanin iyaye maza da 'ya 'yansu babu wata alaka mai karfi, uba baya zama da 'ya 'yansa yana nuna musu yadda rayuwa take, ballantana ya basu irin tarihin gwagwarmayar da yasha a rayuwa ba, kalilan ne daga cikin iyaye suke zama da 'ya 'yansu suke nusar da su irin yadda rayuwa take. Tabbas da iyaye sun tsaya sun kula da tarbiyyar 'ya 'yansu maza da mata wajen nusantar dasu akan yadda zasu gina rayuwarsu a nan gaba da abin ba     haka yake ba.

Tsananin son 'ya 'ya: Hakika a wannan lokacin Allah ya jarrabi iyaye da yawa da tsananin son 'ya 'ya zakaga kowane uba baya son yaronsa ya sha wahala ko da kuwa wahalar alkhairi ce anan gaba, misali zakaga yaro tun yana karami irin yadda ake tarairayarsa da irin yadda duk sadda ya nemi abin batarwa a dauka a bashi ba tare da nuna masa cewa wannan abinda ake bashi sai ansha wahala ake samu ba, kai wasu iyayenma har kudi sukeyi canji wadan da zasu rika baiwa 'ya 'yansu duk safiya kafin su fita, idan kuwa akayi sa'a wani uban yana da dan abin hawa sai kaji wai kullum sai ya dana yaransa kafin ya fita, duk wannan yana daya daga abinda ya janyowa matasan wannan al'umma lalaci.

Halin ko inkula daga makwabta: A bayyane yake cewa yanzu makotaka ta dauki wani irin mummunan salo, ta yadda zakaga makwabci babu ruwansa da ladabtar da dan makwabcinsa don gudun kada ran mahaifin yaron ko mahaifiyarsa su baci, abin mamaki idan makwabci ya daki dan makwabcinsa sai kaji uwar yaron ta aiko "wai me wane ya yi aka dake shi" da yawan wannan takan sanya da yawa daga cikin makwabta ko inkula da duk wani abu da yaro zaiyi matukar ba dansu bane; ada yadda muka sani mutum daya zai iya yiwa yaran unguwa ladabi kuma kaji iyayensu suna godiya, ba tare da bin bahasin abinda yaro ya yi aka dokeshi ba.

'Yan Siyasa: Ina fatar kana biye da ni sau da kafa ya dan uwa mai karatu, kamar yadda nace 'yansiyasa sun samu galibin matasa suna da son jiki da rashin son wahala da kuma tsananin son kudi da son hutu, shi yasa yanzu zakaga kansiloli da 'yan majalisu na jiha dana tarayya da shugabannin kananan hukumomi suna yawan kafa rumfuna a mazabunsu da kuma yin odar sabbin bencina domin duk a cigaba da kashewa matasa zuciya da sage musu gwiwar amfanar lokacinsu na kuruciya, ba karatu ba sallah, sai yawan zagi da gulma da kinibibi, idan wani ya wuce da sabuwar riga ace ya cika girman kai, idan kuwa akaga mai sabuwar mota ace masa barawon gwamnati suna zaune babu abinda suke har maraice ya riskesu. Kaga 'yan siyasa sunyi amfani da lalacin da iyaye suka sanyawa 'ya 'yansu suka sake lafkarda su.
A ganina wadan nan da ma wasu suna daga cikin dalilan da suka sanya matasan wannan al'umma suke cikin halin da suke ciki na lalaci da son jiki da mutuwar zuciya. Lallai ne idan muna son gyara sai mun koma baya munga me ya gyara al'ummar farko har ta kasance abin misali yanzu a garemu sannan zamu sami hanyar da zamu gyara halin da muke ciki, duk kuwa da dimbin ilimin da ake dashi wanda ya ninka na dacan ninkin banikim.

Lallai lokaci ya yi da zamuyi tunanin fitar da kawunanmu daga cikin wannan mummunan kangi na lalaci da mutuwar zuciya da ko inkula da tsananin son 'ya 'ya da baya amfana musu da komai sai da na sani a gaba, kuma wannan hali shi ne ya haifarmana da karuwar mugun talauci, ta yadda munaji muna kallo sana'o'inmu da muka gada iyaye da kakanni wasu sukazo daga nisan duniya suka kwace mana sakamakon fatali da mukayi das u. Nawane wadan da suke zuwa garuruwanmu babu ko sisi kuma su kayi sana'ar da mukaki koya su koma garuruwansu suna masu arziki! Idan kunne yaji . . .!


Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com

Saturday, April 7, 2012

Hattara Dai Sardaunan Kano!!!



Mallam (Dr) Ibrahim Haruna Shekarau Sardaunan Kano wazirin Raya kasar Nufe, kuma tsohon gwamnan kano, basarake, jigo a siyasar jihar kano da Najeriya. Hakika mallam shekaru bashida bukatar fassara a siyasar Najeriya, tun daga Patakwal har Jibiya, haka kuma, tundaga Badagary har zuwa Nguru, sunan Sardauna ya kewaya tun lokacin yana gwamna, ballana tana kuma, mutumin da ya yi takarar shugaban kasa, a babbar jam’iyyar adawa.

Ya maigirma Sardauna! Hakika kana daga cikin mutane kalilan da Allah ya yiwa wata irin baiwa marar misaltuwa a tarihin siyasar Kano da Najeriya. Allah ya baka zalakar harshe da iya magana da bayani wanda duk mai sauraronka da budaddiya kuma kyakkyawar zuciya dole ya gamsu da kalaman bakinka, hakika wannan, wata baiwa ce da Allah ya yiwa mutane kalilan, sannan kuma, Allah ya kimsa maka nautsuwa da takatsantsan a tsakanin jama’a, domin a irin yadda Allah ya yi maka ni’ima ta kasancewa mai mulki ba kowa ne za’a taba mutuntakarsa ya yafe ba.

Ya mai girma Sardauna, kamar yadda tarihinka ya nuna, ka shiga siyasa ba tare da kana da wasu kudade na kuzo mu gani ba, duk da cewa a zamanin da muke ciki, tsarin jari hujja shike tafiyar da siyasa; haka ka fito takarar gwamna baka da kowa sai Allah kamar yadda kake cewa, kuma cikin ikonsa ya yi maka jagora, kana matsayin tsohon malamin makaranta kayi takara da gwamna mai-ci, da yake Allah shi ne malikul mulki ya kwace daga hannunsa ya damka maka, wannan ma wata baiwace da duk kasar nan babu wanda Allah ya yiwa irin wannan gamdakatar din, ya mai girma Sardauna, ka zama gwamna a wani lokaci da ya zowa da wasu da bazata, wadan da suke ganin cewa kai din ba kowa bane, kuma ba komai bane, sannan, wasu kuma ya zo musu suna masu kyautata zato zuwa ga mamallakin mulki.

Ya maigirma Sardauna, hakika Allah ya haskaka jihar kano da mulkinka. Jihar kano kamar yadda kowa ya sani kusan itace jagorar sauran jihohin Arewacin Najeriya, kuma jihace ta malamai musamman bangarori uku, wato ‘yan darikar Kadiriyya da darikar Tijjaniyya da kuma ‘yan Ahlussunnah ko Izala kamar yadda sunan yafi shahara, haka kuma kano, jiha ce ta ‘yan kasuwa tun usuli, jihar kano tayi fice a fannoni daban daban, sannan kuma Allah ya azurtata da salihin mutum irin Sardauna, hakika mun shaida cewa lokacin da kake gwamna kayi kokarin kamanta adalci ga musamman bangarorin dariku da muke dasu, wannan kuma, bazai hana wasu su fahimci akasin haka ba. Ka taba kusan dukkan bangarori, domin hattana nakasassu wadan da ba’aciki lura dasu a cikin al’umma ba ka jawo su ajiki inda ka nuna suma mutanene kamar kowa, wanda yafi wani shine wanda ya fi tsoron Allah, sannan kuma, a lokacinka ne mutane masu addini suka sami gata a harkar tafiyar da gwamnati, haka kuma ayyukan da ake ganin babu ruwan hukuma da su ka nuna lallai hukuma tana da ruwa da tsaki da su, kamar harkar makarantun allo da alarammomi, sanna kuma, idan ana batun ayyukan raya kasa nanma babu mai ganin baikenka, tabbas kano ta haskaka kuma ta tserewa saura ta bangarori da dama.

Ya mai girma Sardauna, lokacin da wa’adin mulkin ka na biyu ya zo karshe, jama’a da dama ciki da wajen jihar kano sunata yimaka kiraye kiraye akan ka fito takara, wasu na ganin ka fito takarar sanata wanda shine mukamin da tsaffin gwamnoni suka fiya tsayawa bayan gama wa’adinsu, wasu kuma, suna ganin ka fito takarar Shugaban kasa bisa irin yadda suke kyautata zato a gareka cewa zakayi adalci ga al’ummar Najeriya kamar yadda ka nuna a jihar kano, domin ansamu fahimtar juna da sauran kabilun kudancin kasarnan da al’ummar jihar kano a lokacinka, da kuma mabiya addinin kirista, inda har ka nada mutane wadanda ba ‘yan kanoba a cikin gwamnatinka, sannan kuma ga zaman afiya da aka samu a kusan tsawon wa’adin mulkinka. Wannan kira da al’umma suka ringa yi maka ya yi tasiri kwarai da gaske baga kai kadaiba harda sauran magoya bayanka, hardai daga karshe ka yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasar Najeriya.

Tabbas, ya mai girma Sardauna, kayi takarar Shugaban kasa. Kuma Allah shi ne masanin abinda bamu sani ba, wasu suna cewa, boyayyar alakace tsakaninka da gwamnatin PDP domin ka kawo cikas ga kuri’un Arewa, wanda ga duk mai hankali yasan da cewa tsarin mulkin Najeriya ne ya baka wannan dama ta tsayawa ko wane irin mukami, kuma babu wani laifi da kayi da ka tsaya wannan takara, wanda kuma yace kudi aka baka ka tsaya takara wannan tsakaninka ne da shi dakuma Allah, domin Allah shi ne masani kuma mai hikima, yasan abinda yake boye da sarari. Bayan ka kewaya kusan jihohin kasarnan domin yakin neman zabe, nasan wannan wani babban aiki ne da zaibaka damar ganin halinda yankunan kasarnan mabambanta suke ciki. Bayan da akayi zabe kuma sakamako ya fito, ance kaine kazo na uku a ‘yan takarar da suka fito daga yankin Arewa, wato na hudu kenan a kasa baki daya, Goodluck Jonathan shine wanda akace ya sami nasarar wannan zabe, sai Gen. Muhammadu Buhari a matsayin na biyu da Mallam Nuhu Ribadu a matsayin na uku da kuma kai maigirma Sardauna a matsayin na hudu. Wasu na cewa daman nasan za’a rina wai ansaci zanin mahaukaciya, wasu kuma na fadin maganganun da basuda hakikanin masaniya akansu, haka dai jama’a sukayi ta fashin baki akan wannan takara da ka tsaya, Allah dai shine masanin abinda yake fake.

Ya maigirma Sardauna, kamar yadda ka sani, tsarin siyasarmu tsari ne na jari hujja, kamar yadda ake yi a Amerika. Da yawan kananan magoya baya a yanzu suna ganin lokaci na gaba mai zuwa ka sake gwada sa’a a wannan takara ko Allah zaisa a dace; a wannan gabace nake so nayi kira ga Sardauna da cewa lallai yayi hattara da masu yi masa wannan kiran, domin shakka babu maganar takarar Shugaban kasa magance babba kuma mai bukatar abubuwa da yawa, musamman abin da akafi sani a siyasance da kayan aiki, nasan da cewa lokacin da katsaya takara ka samu gudunmawa daga ‘yan uwa da abokan arziki da magoya baya da yawa, saboda kana kan kujerar gwamna a lokacin da kake neman wannan takara. Ya maigirma Sardauna lallai yanzu kai ba mutum bane da za’a baiwa shawara akan harkar takarar shugaban kasa, saidai ka baiwa wani, duk da haka, zamuyi karambanin isar da namu sakon gareka.

Ya maigirma Sardauna a lokacin da Bashir Tofa ya tsaya takarar Shugaban kasa, a zaben 12 ga watan yuni da akafi sani da june 12, kusan yana da goyon bayan gwamnatin soja ta General Babangida a wannan lokaci amma duk da haka bai kai ga nasara ba, ko shakka babu, bama gafala da cewa wannan wani hukunci ne na ubangiji, a wancan lokaci Bashir Tofa yana da goyon baya a jihohi da dama na kasarna, sannan duk da haka Bashir Tofa ya cigaba da gwada sa’arsa domin neman wannan takara, amma Allah bai bashi nasaraba ko da kuwa tsallake matakin farko na jam’iyya, haka abin yazo har lokacin da kukayi takara tare da shi ka kuma samu galaba akansa, akaikaice wannan yana nuna cewa lallai farin jinin Alhaji Bashir Tofa ya ja baya ainun daga yadda aka sanshi a 1993. Kuma wannan yake nuna cewa kusan yanzu a siyasar Najeriya musamman ta shugaban kasa duk mutumin da ya yi takarar farko bai samu nasaraba to idan ya sake nema farin jininsa na dusashewa idan aka auna farkon fitowarsa, idan muka kalli Gen Muhammadu Buhari zamu tabbatar da haka, domin farin jinin Buhari a 2007 ya ragu kafin 2011, wannan kuma yana nuna irin yadda siyasar kasarnan ta dauki wannan salon.

Ya maigirma Sardauna, yanzu kai ka zama uban kasa, kuma uban al’umma. Hakika Najeriya tana bukatar mutum irinka, domin Allah ya baka daukaka a tsakanin sauran takwarorinka tsaffin gwamnoni, don babu wani da ake cin-cirondo dominsa sai kai, wannan kuma yake nuna cewa lokaci zaizo, kana gidanka a mundubawa Najeriya zata nemi agajinka, domin sanin kowa ne, idan al’amura suka rincabe dole a bukaci mutane wadan da zasu iya magana a sauraresu, wadanda kuma suke da zalakar harshe, wanda kuma maganarka tanada matukar tasiri a tsakanin magoya bayanka da kuma sauran al’ummomin kasarnan.

Maganar takarar shugaban kasa a nan gaba, ya mai girma Sardauna tana bukatar a tsaya ayi mata duba na tsanaki. Shakka babu kamar yadda na fada kai ba mutum bane da za’a baka shawara akan wannan batu saidai ka bayar, kuma nasan yanzu kana iya rubuta babban littafi mai sufulai da yawa idan ambaka maudu’i akan hakan, don haka ga masu yin kira cewa ka fito takara a 2015, lallai a duba wannan batu, kai tsaye bazance kada maigirma sardauna ya sake yin takara ba, haka kuma bazan ce kada yaki tsayawa takaraba, amma dai abinda masu iya magana ke cewa kana kallon tarihin rayuwar wasu domin samun yadda zaka inganta taka, hakika wadanda suka gabaceka zasu zama ishara a gareka, da sauran al’umma.

Daga karshe, ina mai yin fatan alheri a gareka, kuma ina rokon Allah yacigaba da yi maka jagoranci, ya shiga tsakaninka da makiyanka da kuma mahassada, Allah ya zaba maka abinda ya ke shine mafi a’ala a gareka da kuma al’ummar jihar kano da Najeriya baki daya, wassalam ka huta lafiya.

Yasir Ramadan gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Friday, April 6, 2012

Hukumar Hizba Ta Jihar Kano Kada Wankin Hula Ya Kaiku Dare



Umarni da kyakkyawa da Hani ga mummuna, kusan shi ne jigo ko kashin bayana aikin Hukumar Hizaba ta jihar kano. Kamar yadda muka sani, wannan jigo na aikin Hizba, kusan Hadisi ne na manzo salallahu alaihi wasallam, aka fassarashi, kuma ya kasance hadafin hukumar tun lokacin da aka samu matasa masu kishin addini ‘yan sa kai suka assasata, da nufin motsa zukatan masu kishin addini, da kuma neman gwamnati ta aiwatar da shari’ar Musulunci a jihar kano a shekara ta 2000 kamar yadda akayi a zamfara; aikin hukumar Hizba kamar yadda muka sani ba sabon abu bane a musulinci.

A wancan lokaci, matasan da suke aikin Hizba a jihar Kano, suna yi ne na sa kai, wato babu wanda ake biya ko anini, hasalima sune suke yin karo-karo domin samar da kudin gudanarwa a unguwanni da kananan Hukumomi, anga mutane irinsu marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam sanye da kayan Hizba a wajen wa’azozin neman kafa shari’a a wurare irinsu Majalasin Triumph da Masallacin Umar Bin Khattab da sauran gurare a fadin Jihar kano.

Bayan duk abin da ya faru ya faru na gwagwarmayar tabbatar da shari’ah a kano, kuma akaci nasarar kafata, gwamnatin Injiniya Rabiu Musa kwankwaso a wancan lokacin, batayi nisan kwana ba, wannan ce ta bada kofa ga gwamnatin Mallam Ibrahim Shekarau, da daukin jama’a na ganin aiwatar da sharia a kano. Da mallam Shekarau ya zo ya nemi majalisar dokoki ta jihar kano tayi dokar da zata kai ga kafa Hizba a Hukumance ta yadda babu wani da zai iya yi mata barazana ko katsalandan, gwamnatin tayi kokari wajen gyara tare da tsarkake Hukumar hizba tare kuma da mayar da ita tayi dai-dai da zamani, wannan ta sanya akayiwa dakaru kusan 9000 a mazabu da kananan hukumomi da kuma jiha rejista tare da sama musu albashi na kusan Naira 15000 a kowane wata, tare da babban kwamanda guda daya, a mtsayin jagora. Kusan aikin Hizba yana tafiya kafada da kafada ne da Hukumar Shari’ah ta Jihar Kano. Kusan duka aikinsu mai taimakon sashe ne, wajen ganin al’amuran shari’a sun inganta, tare kuma da dawo da tsoron Allah a zukatan jama’a. Madallah da wannan aiki na Hukumar Hizba mai dumbin lada.

Yanzu kamar yadda kowa ya sani, babban aikin da Hukumar Hizba ta sanya a gaba shi ne na aurar da zawarawa kusan 1000 a jihar kano. Mallam Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa, shi ne babban kwamandan Hizba na jihar kano, tare kuma da manyan mataimakansa guda uku da kuma takwararsa ta bangaren mata da sauran masu taimaka musu, da kuma kwamandoji na kananan hukumomi 44 na jihar Kano. A wani lokaci a can baya a lokacin da Gwamnan jihar Gombe Muhammad Danjuma Goje ya gayyaci Mallam Aminu Daurawa zuwa buda baki da Azumi a gidan gwamnati, ya yi wasu kalamai na gugar zana ga ita hukumar Hizba ta jihar kano, sannan kuma a wasu wa’azozi nasa ya zargi hukumar da gazawa wajen iya tafiyar da aikinsu.

Hukumar Hizba tayi wannan tanadi ne, na rage adadi na yawan zawarawa dake lungu da sako na jihar Kano. Hukumar tayi tanadi, na baiwa duk wanda zaiyi wannan aure sadaki da kuma kayan daki da wasu kayayyaki na koya sana’o’i ga matan da za’a aurar, Kamar yadda aka ce hukumar, tana kokarin tantance zawarawa mata da kuma maza wadanda za’a daura wannan aure da su. Kusan rahotanni sun nuna cewa da yawan matan da za’a aurar basu san wanda za’a aura musuba; kamar yadda wakilin BBC na jihar kano ya zanta da wasu da suke jiran tantancewa ya fada. Tambaya ga hukumar Hizba, shin tayaya ake tsammanin dorewar auren da mata da mijin basu gama fahimtar juna ba? Ganin cewa ba ‘yan mata bane balle a ari bakinsu a ci masu albasa, sannan kuma, shin idan andaura wannan aure wane tabbaci suke da shi na cewa auren bazai sake mutuwa ba? Menene matsayin mutumin da hukumar ta yiwa auren kuma daga baya ya saki matar? Ina matsayin kudadan da aka kashe domin hidimar wannan aure? Misali ka dauka cewa duk wanda zaiyi auren hukumar zata taimaka masa da 10,000 a matsayin sadaki, kaga kenan zata kashe kusan Miliyan 10, a sadaki kawai, sannan sukuma bangaren matan, da kayan daki da na sana’a ka dauka cewa za’a kashewa kowacce 50,000, kaza za’a kashe akalla miliyan 50, sannan kuma da kudin da hukumar zata kashe wajen aiwatar da wannan aure.

Duk wadan nan kudade zasu fito ne daga asusun gwamnatin jihar kano, wanda ya nuna cewa lallai kudin al’umma ne! Shawarata anan ga hukumar Hizba shi ne da wadanan kudade da za’a kashe, da mutum 200 farko aka inganta aurensu tare da baiwa mazajen jari ko kayan sana’a wadan da zasu iya daukan dawainiyar wannan aure, domin idan hukumar Hizba batayi hankali ba garin neman gira sai ta rasa idanu, kamar yadda sukace shi mijin za’a taimaka masa da sadaki, ita kuma matar za’a taimaka mata da kayan sana’a, shin me wannan yake nunawa? Ita matar ita zata rike kanta kenan? Zata dauki dawainiyar kanta da mijinta kenan? Idan har banyi kuskureba haka batun yake, cewa matan za’a taimakawa da kayan sana’o’i tabbas sunan wannan aure sakakke domin babu yadda aure zaiyi karko a irin wannan yanayi na mace ita ke da gida. Lallai hukumar hizba ya kamata tayi duba na tsanaki a kan wannan batu.

Sannan, wannan batu na auren da hukumar zatayi, idan basubi a hankali ba shi ne zai dauke hankalin hukumar kusan tsawon wa’adinsu. Domin tabbas su shirya jin koke da korafe-korafe ga wadan da aka aurar, domin a irin yanayi na mallam Bahaushe, duk abinda ya samu a bagas kamar yadda turawa ke cewa at aplata gold bai cika bashi muhimmanci da kimar da ta dace da shi ba, kaga kenan, angama da wannan kaso na mutu 200 ana shirin na wasu 200, sannan ga na farko sun fara zuwa da korafi, ina sake jaddadawa tabbas sai hukumar ta sami korafi musamman daga matan da aka aurar, domin duk matar da ta sami matsala ba gidan ubanta zata nufaba, hukumar zata nufa, kaga kenan ana yunkurin daura wani daga gefe guda kuma ana kokarin sasanta na baya don gudun sakwarkwacewa, Allah ya kiyaye.

Idan kuma muka shiga cikin hukumara Hizbar, zamuga irin yadda korafi ya yi yawa na korar da yawa daga cikin ‘yan Hizbar da wannan gwamnatin ta gada daga gwamnatin baya ta Mallam Ibrahim Shekarau. Daman kuma an zargi gwamnatin PDP ta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso tun farkon hawanta cewa za ta kori ’yan Hisba bisa zargin sun taka rawa wajen goya wa gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau baya a lokacin zaben da ya gabata, tare da kokarin ganin wannan gwamnati ba ta kai ga nasara ba. Domin yanzu haka rahotannin da suke fitowa daga hukumar suna nuna cewa ansauke dukkan kwamadoji na kananan hukumomi 44 da wannan gwamnati ta gada, sai dai kuma, kamar yadda mataimakin kwamanda ya kare wannan batu da cewa tunda ansamu sabon kwamanda a jiha ya zama tilas, a kananan hukumomima a samu sabbin kwamandoji, yace wannan al’adace ta sauyin kowace irin gwaamnati.

Sannan kuma, hukumar ta bullo da wani shiri na tantance dakarunta inda ta ce ta yi hakan ne don tsabtace hukumar, amma sai wadansu daga cikin ’yan Hisbar suka ki a tantance su bisa zargin an shirya haka ne da boyayyiyar manufa ta a ci musu mutunci suna zargin cewa akwai shugabannin Jam’iyyar PDP na kananan hukumomi a cikin aikin. Hakika mun kyautata zato ga sabon babban kwamanda Mallam Aminu Daurawa, amma kuma kada wannan ya tabbata cewa suma suna siyasa in da rahotanni suka nuna kamar anayin bita da kulli ga ‘yan Hizbar, domin yanzu zancen da akeyi ance ankori kusan mutum 2,357 daga aiki a kananan hukumomi 23 da suka hada da Makoda da Madobi da Warawa da Fagge da Albasu da Tsanyawa da Sumaila da karaye da Rogo da sauransu. Sannan ba’a bayar da bayanin cewa su wadan nan da aka kora ma’aikatan bogi bane, idan har wannan ba bita da kulli bane me ye dalilin da zaisanya a kori wadan nan mutane daga aiki? alhali da yawa daga cikinsu sun dogara da wannan aiki da sukeyi kasancewar suna da iyalai.

Kamar yadda suka ce, an zargi da yawada daga cikin ‘yan Hizbar da sanya baki a siyasa. Musamman kwamandoji na kananan Hukumomi da ake musu kallon sun dafawa gwamnatin da ta gabata ta mallam Ibrahim Shekarau, amma kuma kamar yadda Mataimakain babban kwamanda na jiha Dr Maigida Kacako yace hukumar bata hana kowa yabi ra’ayinda yake so a siyasa ba, amma kada ya yi amfani da aikin Hizba a siyasa, idan har da gaske hukumar take, suke akan wannan batu, to da alama suna tufaka suna warwara. Allah shi ne maSani mai hikima.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

Thursday, April 5, 2012

James Ibori: Makaho Baisan Ana Ganinsa ba . . .


James Ibori: Makaho Baisan Ana Ganinsa ba . . .

James Ananebo Ibori kamar yadda aka sanshi, bayanai sunce, yana daga cikin hamshakan attajirai a Najeriya na gani na fada. Shi dai dan siyasa ne, kuma me mai fada aji a tsakanin mutanansa da jam’iyyarsa ta PDP, domin kusan anyi ittifaqin duk kasarnan babu wani mahaluki da ya taimaka da irin kudin da ya baiwa tsohon shugaban kasa Mallam Umaru Musa ‘YarAdua, domin yakin neman zabe kamarsa, bayanai sunce ya taimaka da kazaman kudade da sun shallake hankali da tunani. Wannan ce ma ta sanya aka nada babban yaronsa kuma na hannun damansa Mista Mikel Kaase Aandoakaa a matsayin babban Atoni janar kuma ministan shari’a, na Najeriya, inda ya yi ta cin karensa babu babbaka a gwamnatin YarAdua, bayanai sun tabbatar da cewa, kusan yana daya daga cikin masu juya gwamnatin tarayya daga nesa, inda yaransa ko makusantansu sukayi dumu dumu a harkar gwamnatin tarayya.

Bayanai sun tabbatar da cewa Ibori ya nemi kariya ne da gwamnatin marigayi YarAdua domin boye irin kazamar satar da ya dibga, don haka ne yasa aka tabbatar masa da wannan kariyar da yake nema ta hanyar nada na hannun damansa a matsayin ministan sharia, domin bashi kariya daga gurfana gaban kowane irin kwamitin bincike. Ana zargin Ibori, da yin sama da fadi, da dukiyar al’ummar jihar Delta dake yankin kudu maso kuduncin Najeriya, kuma yankin da yake samar da albarkatun manfetur da dangoginsa.

James Ibori shi ne gwamnan Jihar Delta daga 1999 zuwa 2007, bayanai sunce, ya wawure kudi da suka kai sama da dalar amurka miliyan $250 kwatankwacin kudin kasar ingila Fan miliyan £157 a kudin Najeriya sama da Naira Biliyan 45, saboda kariyar da yake da ita na tsarin mulkin Najeriya na gurfana a gaban kotu a lokacin da yake gwamna, wannan ta sanya tsohon shugaban hukumar EFCC Mallam Nuhu Ribadu, ya baza koma, domin kamo wannan gawurtaccen barawo, anci nasarar kama Mista Ibori a lokacin da wa’adin mulkinsa ya kare kuma yake shirin bajakolinsa a gwamnatin da kusan za’a iya cewa shine jigonta, hakika bayanai sunce Mallam Ribadu ya yi matukar kokari wajen ganin antatse mista Ibori domin maida kudin da ya sata zuwa aljihun gwamnati, inda shi da kansa Iborin ya yi kokarin baiwa Ribadu cin hancin dalar amurka miliyan $15, sai dai, da yawan manazarta suna ganin wannan ce ta sanya akayiwa Mallam Nuhu Ribadu wulakancin da ba’a taba yiwa wani mutum a Najeriya ba kawai don yana kokarin ganin ankame tare da garkame manyan barayi, irinsu Ibori, da farko anfara yiwa Ribadu bitada kulli, ta hanyar cewa, ya koma makaranta ya karo ilimi a kuru dake Jos, aka maye gurbinsa da Madam Farida Waziri, kuma bayanai sun tabbatar da cewa umarnin da aka fara baiwa ita waziri shi ne ta saki Ibori, wannan ta bashi dama inda ya sanya aka dinga yiwa Mallam Nuhu Ribadu wulakanci da bita da kulli na fitar hankali, wannan ta sa Ribadu ya bar kasarnan ba don yana so ba, inda ya tafi gudun hijira zuwa kasar Birtaniya don kare kansa. Kuma saboda karya ake wajen yakar cinhanci da rashawa, wai kotu ta wanke Ibori daga tuhume-tuhumen da EFCC ta ke yi masa.

Kwatsam babu zato babu tsammani, aka kwashi tsohon shugaba YarAdua ranga ranga zuwa kasar Saudiyya domin neman magani. Bayanai sunce halin da shugaban kasa a wancan lokacin yake ciki sun tsananta, Wannan ce ta sanya hantar Ibori da ‘yan kanzaginsa ta kada, kuma cikinsu ya duri ruwa sosai, domin da aka samu tirka-tirkar yiwuwar nada mukaddashin shugaban kasa ministan Sharia Mista Aandoakaa yana sahun gaba wajen adawa da nada Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin shugabansa, da hakarsu ta kasa cimma ruwa Ibori ya gudu kasar Dubai inda shi kuma Aandoakaa ya nufi kasar Amerika domin sunsan bazasu kwashe da dadi da mista Jonathan ba ganin irin cinkashi da wulakancin da sukayi masa, yana matsayin mataimakin shugaban kasa. A gefe guda kuma hukmar ‘yan sandan Birtaniya(Metropolitan Police) suna neman Ibori ruwa a jallo inda akaci nasarar damkeshi a shekarar 2010 a kasar Dubai, tare kuma da tasa keyarsa zuwa kasar Birtaniya domin fuskantar shari’ar zambar kudaden Haram.

A lokacin da Mallam Nuhu Ribadu yake binkitar almundahanar da Ibori ya tafka, ya hada kai da hukumar ‘yan sandan duniya ta INTERPOL domin taso keyarsa duk inda ya shiga, haka kuwa akayi anci nasarar kama Ibori inda aka tasa keyarsa zuwa kasar Birtaniya domin yi masa shari’a akan zarginsa da hallata kudaden haram da suka shallake hankali, alokacin da ya gurfana ya amsa laiffufuka 10 acikin 22 da ake zarginsa da aikatawa, wannan kuma ta tabbatar da ya karyata kansa kamar yadda a baya yaki amsa wadan nan laifuka, ya yarda cewa yayi almundahana da dukiyar jihar Delta kuma ya halatta dukiyar Haram; mai gabatar da kara Sasha Wass ta shaidawa kotun lardi ta Southwark crown court dake birnin landan cewa James Ibori ya amsa laifi 10 daga cikin 22 da ake tuhumarsa da aikatawa na almundahana da dukiyar jihar Delta a lokacin da yake Gwamna.

Wass taci gaba da shaidawa kotu cewa Ibori ya yi amfani da takardun haihuwa na karya, domin boye laifin da ya aikata a baya, da ya hana masa rike kowanne irin mukami na gwamnati, a lokacin da yake neman takarar gwamnan jihar Delta, ta kara da cewa muna murna da wannan amsa laifi da Ibori ya yi domin wannan shi ne zai kawo saukin shari’ar da ake yi masa, kuma tace za a kwace tare da mika kadarorin da ya mallaka a kasar Birtaniya, zuwa jiharsa ta Delta kamar yadda dansandan da ya gabatar da kara Paul Whatmore na hukumar ‘yan sandan birnin landa wato Metropolitan police ya nema, dan sandan yace zasu ci gaba da sanya ido akan kadarorin da Ibori ya mallaka a kasar ta Birtaniya.

James Ibori dai kafin zamansa gwamna, a shekarar 1999 yana zaune ne a Primrose Hill a Arewacin Landan a Birtaniya, kuma yana aikin akawu ne a DIY store in Ruislip, Middlesex, bayanai sun tabbatar da cewa ibori ya mallaki katin fitar da kudi na Credit Card, da yakai kimanin dalar Amurka $200,000 a wata, kuma ya mallaki wasu irin dirka dirkan motoci masu dankaren tsada da ake kira Range Rover, kuma wani karin abin mamaki a lokacin da Ibori yake a tsare a Landan yayi yunkurin sayan wani karamin jirgi mai cike da kayan alatu da yakai kimanin fan na ingila miliyan 20.

Saboda irin facakar da yake tafkawa a kasar Birtaniya, da kasashen turai hukumar ‘yan sandan birtaniya karkashin sashin proceeds of corruption unit (POCU) suka fara bincikarsa tun a shekara ta 2005 tare da hadin gwiwar hukumar EFCC ta Najeriya wadda Mallam Nuhu Ribadu ya jagoranta a wancan lokacin. Haka itama a nata bangaren kungiyar nan ta DFID tace ta sanya ido akan James Ibori musamman ganin irin yadda yake ta jibge makudan kudade a kasashen Turai da Amurka da Dubai.

Irinsu james Ibori yanzu suna nan jibge a Najeriya. Sun dibga mahaukaciyar sata kuma suna shiga siyasa da nufin samun kariya domin boye irin mummunar satar da suka dibga. Don haka duk wani shugaba na gari da ake fatan samu a Najeriya matukar ba wanda zai iya yakar cin hanci da rashawa bane, to, ya zama aikin banza, domin haka irinsu Ibori zasu cigaba da cin karensu babu babbaka a karkashin gwamnatin da suka taimakawa da dukiyar sata. Allah ya bamu shugabanni na gari, masu kishin kasa kuma wadan da zasu iya yakar cin hanci da rashawa, Allah ya kawo mana Su.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com