Matasa
a Jiya da Yau!
Nagartaccen
matashi shi ne ginshikin samar da kyakkyawar al'umma. Hakika dukkan al'ummar da
take da dimbin matasa to tayiwa Allah godiya, domin wannan al'barka ta matasa
itace take nuna cewa lallai za'a jima ana damawa da wannan al'umma a fagen
rayuwa ta nan gaba. Hakika matasa babu
abin da suke da bukata kamar jagoranci da kokarin sanyasu bisa turba ta
gaskiya, wadda zasu gina kansu domin gaba, kuma su sami zarafin gina al'ummar
da suke rayuwa a cikinta.
Manazarta
da masharhanta da dama sun wasa kwakwalwa wajen baje kolin tunani da bincike da
ra'ayin shin wai waye matashi? Kamar yadda larabawa suke da wani Karin Magana inda
suke cewa"ita jarumtaka ga matashi aka santa, idan ya kasance matashi babu
jarumtaka, to sunansa wani abin" wannan Karin Magana ya nuna matukar iya
zance na larabawa, shakka babu kyakkyawan matashi shi ne abin misali da
kwatance, kuma jarumtaka tsakanin matasa wannan abin bukata ne kwarai da gaske.
Hakika dukkan wani mutum da yayi sa'ar samun
kansa a wannan sarari mai fadi da ake kira duniya, kuma yayi katarin dacen
shige wannan yanayi ko lokaci na matashintaka kuma ya yi sa'a ya wuce lafiya to
babu abinda ya kamaceshi illa ya yiwa Allah godiya, da kuma nazarin yadda za'a
gina goben masu zuwa nan gaba.
Bari
mu kalli matashi a shekarun baya: hakika a zamanin dacan matasa su ne
suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen dorewar wannan al'umma, hakika matasan
da suka gabaci wannan al'umma tamu sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin
mun sami ingataccen yanayin wanzuwa; misali ka dauki ganuwar birnin kano da
zariya da kasar karaye da wasu garuruwa a Arewa da suke da ganuwa, ka tambayi
kanka shin su wa suka gina wannan ganuwa? Mala'iku ne, al-janune, mutanan boye
ne, turawan mulkin mallaka ne? shakka babu amsar wannan tambaya itace a'a matasan
wannan al'umma da suka gabacemu su sukayi wannan katafaren aiki mai dumbin
tarihi a lokuta masu tsawo da suka shude; ka zagaya birnin kano tundaga kofar
Danagundi har kazagayo kofar Na'isa kaga yadda akayi gini babu ha'inci babu amaja,
ka kuma lura da yadda ginin yake ka kuma tambayi kanka shin kasar da akayi
wannan gini daga sama aka ringa zubo da ita ko kuwa ya abin yake, hakika wannan
kasa kwakwularta aka ringayi daga kasa anayin bululluka da tubali har akayi
wannan gini, duk wannan fa matasane sukayi, wannan misali kadan ne daga cikin
irin misalign ayyukan da matasa wadan da suka gabaci wannan al'umma sukayi,
kuma idan ana biyansu lada to bai taka kara ya karya ba; nasan watakila wani
yace to ai bayi ne sukayi wannan gina ba 'ya 'ya ba, koma dai su wane sukayi
lallai matasa ne, domin nayi imanin dattawa ko mata bazasu iya irin wannan
namijin kokari ba.
Haka
zalika mu sake komawa baya a tarihi, mu kalli irin yadda akeyin dalar gyada a
kano da hadejiya kaga irin tarin buhunan gyada dubbai kure gani wanda duk
matasa ne suka noma mafi yawanci, kuma a duke da fartanya ba kamar yanzu da ake
da tarakta ba, inda mutum yana zaune akan mota yana bata umarni ba tare day a duka
ba. Kuma suma wadan nan matasa da sukayi wannan noma, sunyi ba tare da samun
wani lada na kuzo mu gani ba.
Hakika
matasa a lokutan baya ba malalata bane idan mutum ya kalli wadan nan misalai
guda biyu da muka bayar, matashi ne zakaji ance ya nome gonarsa da ta
mahaifinsa da kuma ta surikinsa duk a damina daya ba tare da anbashi ladan ko
sisi ba da sunan ladan hidima. Shakka babu tarihin wannan kasa bazai taba
mancewa da irin gagarumar gudunmawar da matasa suka baiwa wannan kasaba a
lokutan da suka gabata.
Sannan mu
kalli matasa a wannan lokaci: shakka babu bazanyi kuskure ba idan nace matasan
wannan al'umma a yanzu malalata ne na kin karawa, kowa ya nade hannun riga jira
yake yaci ko ya samu ba tare da yasha wahalar ko kwabo ba, ka duba irin yadda
Allah ya hore mana dimbin matasa ninkin ba nikin wadan da suka gabata, amma
amfanuwar da akeyi dasu ko kusa bata kai amfanuwar da akayi da matasan da suka
gabata ba; tambaya shin me ya jawo haka? Shin tarbiyya ce wadan nan matasa na
yanzu basu samu ba daga magabatansu ba ko kuwa ya abin yake? Ka shiga cikin
lungunanmu da sako da kwararo-kwararo kaga dimbin matasa 'yan bana bakwai
majiya karfi suna zaune babu aikin fari balle na baki kawai suna zaune suna
hira marar amfani a duniyance ko a lahirance, daga rana ta tarar da inuwa a
sake daukar benci a maidashi inuwa, a cigaba da hira maras kan-gado.
Allah ya hore
mana kasa mai fadi ba mai kwazazzabo da yawa ba, kuma bamai tuddai da yawa ba,
kasar noma iya ganinka tundaga Kauran Namoda har katagum ka zarce har zuwa
Nguru kasace mai fadi da za'a iya noma abinda zai iya cida kasarnan da
makwabtanta, uwa uba kuma ga albarkar kasa da Allah ya bamu, mangwaro zaka sha
ka yarda kwallon insha Allah idan ruwan damina ya dakeshi sai kaga yayi tsiro
idan akayi sa'a babu abinda ya tabashi akwana a tashi sai kaga ya zama bishiya,
duk wannan kadan ne daga cikin irin al'barkar da Allah ya yiwa wannan kasa.
Babu shakka
kamar yadda na fada a farko, matasa sune kashin bayan kowace al'umma! Amma idan
ya kasance matasan ba cima zaune bane kamar yadda muke a yanzu; abin mamaki
kaga katon gardi yakai shekara 30 ko 35 amma wai har yanzu a gidansu ana bashi
kudin batarwa, ba'a yi masa wani tanada da zai dogara da kansa ba, ballantana
ya yi tunanin gina rayuwar manyan gobe.
Tun
Ran Gini Tun Ran Zane: Allah ya albarkaci Bahaushe da iya Magana. A
ganina dalilan da suke janyo matasa su zama masu mutuwar zuciya sune kamar
haka:
Iyaye:
Hakika, iya ye a wannan zamanin sun taka muhimmiyar rawa wajen ragwantar da 'ya
'yansu, domin zaka samu, musamman tsakanin iyaye maza da 'ya 'yansu babu wata
alaka mai karfi, uba baya zama da 'ya 'yansa yana nuna musu yadda rayuwa take,
ballantana ya basu irin tarihin gwagwarmayar da yasha a rayuwa ba, kalilan ne
daga cikin iyaye suke zama da 'ya 'yansu suke nusar da su irin yadda rayuwa
take. Tabbas da iyaye sun tsaya sun kula da tarbiyyar 'ya 'yansu maza da mata
wajen nusantar dasu akan yadda zasu gina rayuwarsu a nan gaba da abin ba haka yake ba.
Tsananin
son 'ya 'ya: Hakika a wannan lokacin Allah ya jarrabi
iyaye da yawa da tsananin son 'ya 'ya zakaga kowane uba baya son yaronsa ya sha
wahala ko da kuwa wahalar alkhairi ce anan gaba, misali zakaga yaro tun yana
karami irin yadda ake tarairayarsa da irin yadda duk sadda ya nemi abin batarwa
a dauka a bashi ba tare da nuna masa cewa wannan abinda ake bashi sai ansha
wahala ake samu ba, kai wasu iyayenma har kudi sukeyi canji wadan da zasu rika
baiwa 'ya 'yansu duk safiya kafin su fita, idan kuwa akayi sa'a wani uban yana da
dan abin hawa sai kaji wai kullum sai ya dana yaransa kafin ya fita, duk wannan
yana daya daga abinda ya janyowa matasan wannan al'umma lalaci.
Halin
ko inkula daga makwabta: A bayyane yake cewa yanzu makotaka
ta dauki wani irin mummunan salo, ta yadda zakaga makwabci babu ruwansa da
ladabtar da dan makwabcinsa don gudun kada ran mahaifin yaron ko mahaifiyarsa
su baci, abin mamaki idan makwabci ya daki dan makwabcinsa sai kaji uwar yaron
ta aiko "wai me wane ya yi aka dake shi" da yawan wannan takan sanya
da yawa daga cikin makwabta ko inkula da duk wani abu da yaro zaiyi matukar ba
dansu bane; ada yadda muka sani mutum daya zai iya yiwa yaran unguwa ladabi kuma
kaji iyayensu suna godiya, ba tare da bin bahasin abinda yaro ya yi aka dokeshi
ba.
'Yan
Siyasa: Ina fatar kana biye da ni sau da kafa ya dan uwa mai karatu,
kamar yadda nace 'yansiyasa sun samu galibin matasa suna da son jiki da rashin
son wahala da kuma tsananin son kudi da son hutu, shi yasa yanzu zakaga
kansiloli da 'yan majalisu na jiha dana tarayya da shugabannin kananan hukumomi
suna yawan kafa rumfuna a mazabunsu da kuma yin odar sabbin bencina domin duk a
cigaba da kashewa matasa zuciya da sage musu gwiwar amfanar lokacinsu na
kuruciya, ba karatu ba sallah, sai yawan zagi da gulma da kinibibi, idan wani
ya wuce da sabuwar riga ace ya cika girman kai, idan kuwa akaga mai sabuwar
mota ace masa barawon gwamnati suna zaune babu abinda suke har maraice ya
riskesu. Kaga 'yan siyasa sunyi amfani da lalacin da iyaye suka sanyawa 'ya
'yansu suka sake lafkarda su.
A ganina
wadan nan da ma wasu suna daga cikin dalilan da suka sanya matasan wannan
al'umma suke cikin halin da suke ciki na lalaci da son jiki da mutuwar zuciya.
Lallai ne idan muna son gyara sai mun koma baya munga me ya gyara al'ummar
farko har ta kasance abin misali yanzu a garemu sannan zamu sami hanyar da zamu
gyara halin da muke ciki, duk kuwa da dimbin ilimin da ake dashi wanda ya ninka
na dacan ninkin banikim.
Lallai lokaci ya yi da zamuyi tunanin fitar da
kawunanmu daga cikin wannan mummunan kangi na lalaci da mutuwar zuciya da ko
inkula da tsananin son 'ya 'ya da baya amfana musu da komai sai da na sani a
gaba, kuma wannan hali shi ne ya haifarmana da karuwar mugun talauci, ta yadda
munaji muna kallo sana'o'inmu da muka gada iyaye da kakanni wasu sukazo daga
nisan duniya suka kwace mana sakamakon fatali da mukayi das u. Nawane wadan da
suke zuwa garuruwanmu babu ko sisi kuma su kayi sana'ar da mukaki koya su koma
garuruwansu suna masu arziki! Idan kunne yaji . . .!
Yasir Ramadan Gwale
yasirramadangwale@gmail.com
http://yasirramadangwale.blogspot.com
hakika wannan nazari naka yaburge kwarai da aniya ni duk da cewa ba a kasar najeriya nake ba. allah ya saka da alkhairi.
ReplyDeleteallah yabada lada
ReplyDelete