Thursday, April 5, 2012

James Ibori: Makaho Baisan Ana Ganinsa ba . . .


James Ibori: Makaho Baisan Ana Ganinsa ba . . .

James Ananebo Ibori kamar yadda aka sanshi, bayanai sunce, yana daga cikin hamshakan attajirai a Najeriya na gani na fada. Shi dai dan siyasa ne, kuma me mai fada aji a tsakanin mutanansa da jam’iyyarsa ta PDP, domin kusan anyi ittifaqin duk kasarnan babu wani mahaluki da ya taimaka da irin kudin da ya baiwa tsohon shugaban kasa Mallam Umaru Musa ‘YarAdua, domin yakin neman zabe kamarsa, bayanai sunce ya taimaka da kazaman kudade da sun shallake hankali da tunani. Wannan ce ma ta sanya aka nada babban yaronsa kuma na hannun damansa Mista Mikel Kaase Aandoakaa a matsayin babban Atoni janar kuma ministan shari’a, na Najeriya, inda ya yi ta cin karensa babu babbaka a gwamnatin YarAdua, bayanai sun tabbatar da cewa, kusan yana daya daga cikin masu juya gwamnatin tarayya daga nesa, inda yaransa ko makusantansu sukayi dumu dumu a harkar gwamnatin tarayya.

Bayanai sun tabbatar da cewa Ibori ya nemi kariya ne da gwamnatin marigayi YarAdua domin boye irin kazamar satar da ya dibga, don haka ne yasa aka tabbatar masa da wannan kariyar da yake nema ta hanyar nada na hannun damansa a matsayin ministan sharia, domin bashi kariya daga gurfana gaban kowane irin kwamitin bincike. Ana zargin Ibori, da yin sama da fadi, da dukiyar al’ummar jihar Delta dake yankin kudu maso kuduncin Najeriya, kuma yankin da yake samar da albarkatun manfetur da dangoginsa.

James Ibori shi ne gwamnan Jihar Delta daga 1999 zuwa 2007, bayanai sunce, ya wawure kudi da suka kai sama da dalar amurka miliyan $250 kwatankwacin kudin kasar ingila Fan miliyan £157 a kudin Najeriya sama da Naira Biliyan 45, saboda kariyar da yake da ita na tsarin mulkin Najeriya na gurfana a gaban kotu a lokacin da yake gwamna, wannan ta sanya tsohon shugaban hukumar EFCC Mallam Nuhu Ribadu, ya baza koma, domin kamo wannan gawurtaccen barawo, anci nasarar kama Mista Ibori a lokacin da wa’adin mulkinsa ya kare kuma yake shirin bajakolinsa a gwamnatin da kusan za’a iya cewa shine jigonta, hakika bayanai sunce Mallam Ribadu ya yi matukar kokari wajen ganin antatse mista Ibori domin maida kudin da ya sata zuwa aljihun gwamnati, inda shi da kansa Iborin ya yi kokarin baiwa Ribadu cin hancin dalar amurka miliyan $15, sai dai, da yawan manazarta suna ganin wannan ce ta sanya akayiwa Mallam Nuhu Ribadu wulakancin da ba’a taba yiwa wani mutum a Najeriya ba kawai don yana kokarin ganin ankame tare da garkame manyan barayi, irinsu Ibori, da farko anfara yiwa Ribadu bitada kulli, ta hanyar cewa, ya koma makaranta ya karo ilimi a kuru dake Jos, aka maye gurbinsa da Madam Farida Waziri, kuma bayanai sun tabbatar da cewa umarnin da aka fara baiwa ita waziri shi ne ta saki Ibori, wannan ta bashi dama inda ya sanya aka dinga yiwa Mallam Nuhu Ribadu wulakanci da bita da kulli na fitar hankali, wannan ta sa Ribadu ya bar kasarnan ba don yana so ba, inda ya tafi gudun hijira zuwa kasar Birtaniya don kare kansa. Kuma saboda karya ake wajen yakar cinhanci da rashawa, wai kotu ta wanke Ibori daga tuhume-tuhumen da EFCC ta ke yi masa.

Kwatsam babu zato babu tsammani, aka kwashi tsohon shugaba YarAdua ranga ranga zuwa kasar Saudiyya domin neman magani. Bayanai sunce halin da shugaban kasa a wancan lokacin yake ciki sun tsananta, Wannan ce ta sanya hantar Ibori da ‘yan kanzaginsa ta kada, kuma cikinsu ya duri ruwa sosai, domin da aka samu tirka-tirkar yiwuwar nada mukaddashin shugaban kasa ministan Sharia Mista Aandoakaa yana sahun gaba wajen adawa da nada Goodluck Jonathan a matsayin mukaddashin shugabansa, da hakarsu ta kasa cimma ruwa Ibori ya gudu kasar Dubai inda shi kuma Aandoakaa ya nufi kasar Amerika domin sunsan bazasu kwashe da dadi da mista Jonathan ba ganin irin cinkashi da wulakancin da sukayi masa, yana matsayin mataimakin shugaban kasa. A gefe guda kuma hukmar ‘yan sandan Birtaniya(Metropolitan Police) suna neman Ibori ruwa a jallo inda akaci nasarar damkeshi a shekarar 2010 a kasar Dubai, tare kuma da tasa keyarsa zuwa kasar Birtaniya domin fuskantar shari’ar zambar kudaden Haram.

A lokacin da Mallam Nuhu Ribadu yake binkitar almundahanar da Ibori ya tafka, ya hada kai da hukumar ‘yan sandan duniya ta INTERPOL domin taso keyarsa duk inda ya shiga, haka kuwa akayi anci nasarar kama Ibori inda aka tasa keyarsa zuwa kasar Birtaniya domin yi masa shari’a akan zarginsa da hallata kudaden haram da suka shallake hankali, alokacin da ya gurfana ya amsa laiffufuka 10 acikin 22 da ake zarginsa da aikatawa, wannan kuma ta tabbatar da ya karyata kansa kamar yadda a baya yaki amsa wadan nan laifuka, ya yarda cewa yayi almundahana da dukiyar jihar Delta kuma ya halatta dukiyar Haram; mai gabatar da kara Sasha Wass ta shaidawa kotun lardi ta Southwark crown court dake birnin landan cewa James Ibori ya amsa laifi 10 daga cikin 22 da ake tuhumarsa da aikatawa na almundahana da dukiyar jihar Delta a lokacin da yake Gwamna.

Wass taci gaba da shaidawa kotu cewa Ibori ya yi amfani da takardun haihuwa na karya, domin boye laifin da ya aikata a baya, da ya hana masa rike kowanne irin mukami na gwamnati, a lokacin da yake neman takarar gwamnan jihar Delta, ta kara da cewa muna murna da wannan amsa laifi da Ibori ya yi domin wannan shi ne zai kawo saukin shari’ar da ake yi masa, kuma tace za a kwace tare da mika kadarorin da ya mallaka a kasar Birtaniya, zuwa jiharsa ta Delta kamar yadda dansandan da ya gabatar da kara Paul Whatmore na hukumar ‘yan sandan birnin landa wato Metropolitan police ya nema, dan sandan yace zasu ci gaba da sanya ido akan kadarorin da Ibori ya mallaka a kasar ta Birtaniya.

James Ibori dai kafin zamansa gwamna, a shekarar 1999 yana zaune ne a Primrose Hill a Arewacin Landan a Birtaniya, kuma yana aikin akawu ne a DIY store in Ruislip, Middlesex, bayanai sun tabbatar da cewa ibori ya mallaki katin fitar da kudi na Credit Card, da yakai kimanin dalar Amurka $200,000 a wata, kuma ya mallaki wasu irin dirka dirkan motoci masu dankaren tsada da ake kira Range Rover, kuma wani karin abin mamaki a lokacin da Ibori yake a tsare a Landan yayi yunkurin sayan wani karamin jirgi mai cike da kayan alatu da yakai kimanin fan na ingila miliyan 20.

Saboda irin facakar da yake tafkawa a kasar Birtaniya, da kasashen turai hukumar ‘yan sandan birtaniya karkashin sashin proceeds of corruption unit (POCU) suka fara bincikarsa tun a shekara ta 2005 tare da hadin gwiwar hukumar EFCC ta Najeriya wadda Mallam Nuhu Ribadu ya jagoranta a wancan lokacin. Haka itama a nata bangaren kungiyar nan ta DFID tace ta sanya ido akan James Ibori musamman ganin irin yadda yake ta jibge makudan kudade a kasashen Turai da Amurka da Dubai.

Irinsu james Ibori yanzu suna nan jibge a Najeriya. Sun dibga mahaukaciyar sata kuma suna shiga siyasa da nufin samun kariya domin boye irin mummunar satar da suka dibga. Don haka duk wani shugaba na gari da ake fatan samu a Najeriya matukar ba wanda zai iya yakar cin hanci da rashawa bane, to, ya zama aikin banza, domin haka irinsu Ibori zasu cigaba da cin karensu babu babbaka a karkashin gwamnatin da suka taimakawa da dukiyar sata. Allah ya bamu shugabanni na gari, masu kishin kasa kuma wadan da zasu iya yakar cin hanci da rashawa, Allah ya kawo mana Su.

Yasir Ramadan Gwale

yasirramadangwale@yahoo.com

http://yasirramadangwale.blogspot.com

No comments:

Post a Comment