Tuesday, February 2, 2016

Hattara Dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari


HATTARA DAI SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI

Sama da mutane 86 rahotanni suka tabbatar da cewa sun rasa rayukan su a garin Dolari dake kusa da birnin Maiduguri kwana biyu da suka gabata. Wannan rasa rayuka ya faruwa ne bayan gida je sama da 300 da aka kone kurmus a garin da kuma daruruwan dabbobi da suka halaka. Wannan abu yakai a jallin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tsaida duk abinda yake gabànsa dan zuwa da kansa ya ganewa idan sa irin mummunar asarar da akai, tare da jajantawa al'ummar garin wannan masifa da ake fama da ita, daidai lokacin da ake cewar anci galabar 'yan ta'adda.

A wannan halin da mutanan garin Dolari suke ciki na juyayin da alhinin rashin da sukai, a lokacin da Shugaban kasa ke karakaina tsakanin kasashen Afurka. Kwastam sai muka ji ance Shugaban kasa ya sake daukan jakarsa zuwa kasashen Turai. Na tabbata duk muhimmancin wannan taro da Shugaban kasa zai halarta a Faransa bai kai muhimmancin Taron G20 da akai a kasar Turkiyya ba a watan nuwanba Shekarar bara, ana tsaka da fara wannan muhimmin taro wanda kasar Faransa jigo ce a cikin kasashen G20, a 13 ga watan nuwamban ranar fara wannan taro aka kai wani Hari a Faransa, wannan tasa shugaba Hollande ya bayar da sanarwar soke halartar taron G20, duk kuwa da irin muhimmancin da taron yake da shi a wajensa.

A Takaice dai Rayuwar al'ummar da Shugaban Faransa Hollande yake Shugabanta tafi duk wani taro a duniyar nan muhimmanci a wajensa. Alal hakika wannan shi ne irin Misalin shugabanci na adalci da kaunar al'umma da kishin kasa. Wannan shi ne nauyi da kuma amanar da ya kamata duk wani shugaba ya kula da ita, martabar rayukan al'umma yafi duk wani taro da za ai muhimmanci. Shugaban kasar Faransa da bai san Allah ba, bai san tsananin AzabarSa akan wadan da suka ci amanar shugabanci, bai kuma san tanadin da Allah ya yiwa shugabanni Adalci ba, yayi haka! Ina ga Shugaban da yasan Allah yasan girman AzabarSa da kuma tanadin ga shugaba Ajali?!

Amma dai mu anan gida Nigeria abin ba haka yake ba. Shugabannin mu basu cika baiwa rayuwar al'ummar su muhimmanci ba. Halartar taruka da harkokin gabansu yafi muhimmanci a wajensu. Abin mamaki hatta nan makotanmu Jamhuriyar Nijar, shugabannin kasar sun fi mutunta al'ummar su akan namu shugabannin. Misali a turmutsutsun da ya faru a hajjin da ya gabata Alhazan Nijar 34 ne kacal suka rasu a wannan ibtila'i. Duk da haka, sai da Shugaban kasar yaje har Filin Jirgin saman kasar a lokacin da Alhazan kasar zasu fara dawowa, yayi musu ta'aziyar rasuwar 'yan Nijar da suka rasu a wannan turmutsutsu. Sannan kuma a al'adar Gwamnatoci na nuna juyayin ta hanyar sassauto da tuta dan girmama rayuwar wani ko wasu da aka rasa, Shugaban kasar ya bada hutun kwana uku a duk fadin Nijar dan Jajantawa iyalan wadan da suka rasu. Sannan aka sassauto da tutar kasar kasa dan girmama wadan da suka rasu a hukumance.

A ta bangaren Nigeria kuwa, Shugaban da ake gani shi ne mafi soyuwa a zukatan al'ummatai sam bai yi haka ba. Duba da cewar sama da mutun 100 ne 'yan Nigeria suka rasa rayukansu a wannan turmutsutsu babu wani abu mai kama da nuna jajantawa a hukumance. Haka kuma, duk da irin asarar rayuka da akai a Borno da Yobe da Adamawa tun daga hawansa Mulki har ya zuwa yau Shugaban kasa bai taka da kafarsa yaje musamman domin ganewa idansa da kuma Jajantawa wadan da suka rasa yan uwansu da dukiyoyinsu ba.

Yana da kyau Shugaban kasa ya sani, alhaki duk al'ummar kasarnan na wuyan sa, wajibin sa ne, ya kare mana abubuwa guda hudu. Rayuka, Dukiya, Hankali da kuma Addini. Lallai ya zama wajibi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi hattara kuma ya maida hankali wajen yin abinda ya kamata dan kula tare da Jajantawa mutanan dan suke cikin bala'i irin wannan. Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance abin tambaya ranar gobe kiyama akan irin wannan mummunar kisan gilla da akewa al'umma babu gaira babu dalili.

Akwai takaici kwarai akan yadda shugabanninmu basu cika damuwa da abubuwa na wajibin su ba, su gwammace shiga duniya ana ta ruwa ana hirarraki. Ya Allah ka bamu ikon cin wannan jarabawa da kai mana, ka jarrabemu da shugabanninmu, ka jarrabi shugabanninmu da mu. Allah ka bamu mai kyau a duniya ka bamu mai kyau a Lahira.

Yasir Ramadan Gwale
02-02-2016

1 comment:

  1. Excellent Sir, Allah ya sa wanda aka yi don shi ya ji kuma ya gyara.

    ReplyDelete