Sunday, January 31, 2016

Ya Kamata Gwamnatin Nigeria Da Jihohi Suyi Doka Kan Amfani Da Amsa Kuwwa


YA KAMATA GWAMNATIN NIGERIA DA JIHOHI SU YI DOKAR AMFANI DA LASIFIKA (AMSA KUWWA)

A gaskiya d'armu yayi yawa matuk'a ta yadda muke amfani da sunan Addini Sana'a domin cutar da al'. Zance na gaskiya yadda mutane ke amfani da Amsa Kuwwa barkatai babu wata doka abin ba tsari. A tsari na zamantakewa da Addinin Musulunci ya koya mana, bai ce muyi amfani da addini ko hanyar neman abinci wajen cutar da abokan zaman mu ba.

Haka kurum da sunan neman Abinci mutum ya mak'alawa motarsa k'atuwar Amsa Kuwwa ya shigo cikin aunguwa yana tallar magani. Wani abin damuwa shi ne, galibi tallan da ake na maganin gargajiya da Amsa Kuwwa batsa ce tsagwaron ta, masu tallar ke yi. Ba shakka akwai bambancin tarbiyyar magana tsakanin garuruwanmu, maganganun mu sun bambanta, wata maganar da Bakatsine zai fad'a a garinsu ba wanda zai kalle shi, a Kano idan ya fada sai ta zama abin takaici.

Haka nan, wata maganar da Basakkwace zai fad'a a garinsu a jinjina masa, idan yazo Kano ya fad' sai kaji magana ce me nauyin gaske da bata kamata mutum mai hankali ya fad'a ba. Duk da haka yana da kyau, idan mutumin Katsina ko Sokoto zai yi talla a Kano to ya kamata ya kiyaye da Kalmomi irin na mutan Kano. Wannan na daga cikin neman ilimin yin sana'a kafin yinta.

Zaka ji takaici matuk'a a lokacin da kake zaune da iyalanka da safe ko da daddare wani mai tallar magani daga Katsina ko Sokoto yazo unguwar ku ya tsmotarsa watakila kusa da gidan, yana ta bayanin maganin karfin mazakuta. Suna maganganu gatsal babu sayawa babu sakaye, a sanya mutum jin kunya cikin yaransa.

Lallai ya kamata hukumomi su yi doka kan irin wad'annan masu tallar maganin masu yawo da katuwar Amsa Kuwwa cikin unguwanni da sunan Sana'a. Ba daidai bane dan mutum na saida magani sai ya dinga fad'a yana kwatanta yadda Al'aurar Namiji take idan yasha maganinsa, abin sam babu dad'in ji wallahi. Kuma ya kamata duk wani bako da zai shigo wa mutane unguwa yana irin wannan tallar a taka masa birki.

Ita kuma hukuma wajibi ne ta samar da dokokin da zasu baiwa mutane ikon walwala a gidajensu tare da iyalansu ba tare da wani ya cutar da jin su ba, da sunan sana'a yasa su ji abinda zai kunyata su cikin 'ya 'yansu, ko damun su a lokacin da suke bukatar hutawa cikin iyalansu.

In sha Allah, a gaba zan yi magana kan yadda ake amfani da Amsa Kuwwa da sunan Addini ana cutar da mutane. Allah ya bamu ikon kiyayewa ya bamu ikon gyarawa.

Yasir Ramadan Gwale
31-01-2016

1 comment:

  1. Wallahi wannan maganar ka gaskiya ne. Da farko za su fara ne da ambaton sunan Allah sai ka dauka tamkar wasu masu wa'azi ne. Bayan yan mintoci sai su fara tallar tsiyar su. Allah ya sa mahukunta su dubi wannan al'amari da idon rahama.

    ReplyDelete