A GABAN KHADIMUL ISLAM AKE BARNA DA KUDI?
Jiya Gwamnatin Kano karkashin Jagorancin Gwamna Abdullahi Ganduje ta shirya bakin sabuwar shekara inda mawaka suka sha ruwan Nerori. A irin wannan lokacin da ake cewa tattalin arzikin kasa ya shiga mawuyacin hali, Gwamnatin tarayya da na jihohi na ta batun tsuke bakin aljihu, amma abin mamaki a gaban Gwamna wasu mutane suka dinga yiwa mawaka da makada ruwan kudi, wannan abin takaici ne kwarai da gaske. Domin bayan tozarta ita kanta dukiya sam bai kamata a ce a gaban Gwamna ana irin wannan dabdalar yana gani bai tsawatar ba.
Yana da kyau mutanan da Allah ya baiwa arziki su nuna godiya ga Allah ta hanyar taimakawa mabukata da yin Zakkah akan kari domin ragewa al'umma radadin talauci. Zan ce na gaskiya naji takaici matuka ace har yanzu irin wannan cibayan ta'ada tana tare da al'ummar mu har yanzu ta yin liki da kudi a bainar Jama'ah. Yana da kyau Gwamnan da ake kira da Hadimi ga Addinin Islama a same shi da kwatanta bin addini a lamuransa, hakkin Gwamna ne ya tsawatar a lokacin da mutane suka tozarta dukiya irin haka. Allah ya kyauta.
Yasir Ramadan Gwale
01-01-2016
No comments:
Post a Comment