DAGA KALAMAN JOHN DANFULANI
"A cikin al'ummar Najeriya su waye suke da yara sama Miliyan 12 da suke yawo kwararo-kwararo suna bara dan neman abinda zasu Ci? " Tambaya mai nuna kalubale!
Wannan maganar ta tsaya min a Rai. Kuma duk da zagi da cin mutunci da John Danfulani yayi mana, ya manta cewa shima dan Arewa . Idan ya ce mana Almajirai to a wajen mutanan kudu har da shi a cikin Almajiran.
A gefe daya kuma maganganun da ya fadi gaskiya, akan yawan barace barace da muke. Ya kamata mu tambayi kanmu Me yasa bama ganin mutanan Kudancin Kaduna suna yin bara? Shin ko ba su da Nakasassau da talakawa ne? Me yasa sai mu ne kawai muke bara da rokon da ?
Ya kamata, indai mun ji haushin maganganun John Danfulani muma mu kalubalance su ta hanyar mayar da martani da Alkinta rayuwar dukkan Almajirai mu maida su gaban iyaye su. Idan ba haka ba kuwa, to abinda Danfulani ya fada a kanmu haka yake, gaskiya ne; kuma bai kamata mu tada jijiyar wuya ba.
Zance na gaskiya Almajirai sunyi yawa a ko ina, mai makon abin ya ragu kullum sai ka ruwa yake. Almajirai na kwarara cikin birane kamar sun yi kwace, yaushe muke tunanin samun adalci daga na sama a lokacin da muka kasa yiwa na kasa da mu.
Har kullum abin da yake bani mamaki, idan har mutanan da muke kira "Arnan Arewa" zasu killace al'ummar su duk da talaucin su, su hana su Bara, su samar musu da abinci da sana'a, me yasa mu da muke musu tunkaho da Arziki da wadata kullum yaranmu suke yin Bara, wanda har cikin gidajen irinsu John Danfulani yaranmu ke shiga yin ?
Gaskiya dai lokaci yayi da hukumomi da kungiyoyin al'umma da Limamai da masu unguwanni da Sarakuna zasu tashi tsaye haikan a Arewa domin Yaki da yin barace barace. Almajiri ma d'a ne ya kamata yayi karatu a gaban iyayansa kamar 'ya 'yan kowa.
Lallai d'abi'ar Barace barace na daga abinda ke zubar mana da k'ima da mutunci. Ai wannan ya isa abin takaici ace Arnan Arewa ne zai kalubalance mu da cewa mu Almajirai ne. Wallahi ina jin takaicin hakan.
Ya kamata Jami'o'in da muke da su a Arewa su tashi tsaye su yi aiki tukuru wajen yin Nazari da binciken yadda za'a kawo karshen Bara a Arewacin Najeriya da kuma a tsakanin Al'ummar Arewa musamman Hausawa da Fulani da Barebari. Allah ya bamu ikon gyarawa.
Yasir Ramadan Gwale
04-02-2016
No comments:
Post a Comment