Monday, September 5, 2016

Hattara Da Abokan Facebook Da Baka San su Ba


HATTARA DA ABOKAN FACEBOOK DA BAKA SAN SU BA

Wani abu ya faru a wannan Makon da wani matashi a sanadiyar facebook. Yana da kyau mutane su dinga sanin hakikanin da su wa suke mu'amala a facebook kafin sakin jiki da mutum. Domin kuwa halin da ake ciki yanzu rashin aminci yayi yawa tsakanin wannan al'umma. 

Wani matashi mai suna Salman ya hadu da wani a facebook har ta kai su ga yin magana a Inbox. Suna tattaunawa da wannan mutumin mai suna Micheal amma ba ainihin sunansa Micheal din ya rubuta a facebook ba, ya sa wani suna daban. Suna hira har dai shi Micheal yake tambayar Salman cewar me yake yi na neman kudi a matsayinsa na matashi? Salman yace ba abinda yake yi. Anan ne shi Micheal ya yiwa Salman alkawarin samar masa aiki anan Kano.

Bayan haka, shi Micheal yasha daukar hoton office da gida da mota yana turawa shi Salman yana bashi labarin irin rayuwar da yake ciki ta jin dadi. Wannan ta sanya shi Salman nuna zilama da kwadayi akan abinda Micheal ke nuna masa. Anan ne suka sanya lokacin da shi Salman zai zo Kano tunda yana zaune ne a jihar Adamawa. Salman yazo bisa romon bakan da Michel yayi masa cewar zai sama masa aikin yi a kamfanin da yake aiki.

Ranar Juma'a sai Salman yayi niyyar zuwa Kano, dan haka ya kira Micheal ya sanar masa cewar gashi nan zai Taho.  Shi kuma ya amsa masa da cewar ba matsala Allah ya kawo shi lafiya. Da isowar Salman Kano da yamma ana dab da Magriba, sai ya kira Micheal yake gaya masa cewar gashi ya sauka a Kano. Anan ne shi kuma ya shaida masa cewar baya nan yana wajen aiki, amma zai sanya kan in yazo ya taho da shi zuwa masauki.

Salman na tsaye a tasha wajen karfe 7 na Yamma wani yazo ya same shi bayan da suka yi waya yayi masa kwatancen inda yake a tsaye. Yace masa shi kanin Micheal kuma yazo ne ya kaishi masauki, Salman ya bashi suna tafiya har cikin unguwar Sabon gari a Kano. A lokacin da suka shiga wani layi mara kwalta wanda kuma baya bullewa  (close) sai shi Salman ya lura wasu mutum hudu na biye da su a baya, da ya fahimci lallai wadannan matsa bin su suke yi sai ya tsorata. Yayi nufin ya dawo da baya ya gudu, sai sukai masa ishara da cewar zasu yanka shi idan ya gudu.

Suka nuna masa wani gida suka ce ya shiga, suna shiga gida suka nuna masa wani daki suka ce ya shiga. Ya dan tsaya gardama sai daya ya hankadashi cikin dakin. Bayan da suka tura shi ciki sukai masa mugun duka, suka kwace masa wayoyin sa guda uku, suka kwace masa Agogo da Zobe da kuma kudin sa. Sannan suka tambaye shi Katin cire kudi na ATM yace bai zo da shi ba. Suka caje kayan sa basu ga katin cire kudi ba.

Daga nan suka sanya shi ya tube kayan sa tsirara suka dinga daukar hoton sa, sannan suka ce masa, sai ya sayi wannan hoton Video da suka dauke shi ko kuma su yada video din a Whatsapp da Facebook. Suka ce sai ya saya dubu 70000. Ya amince zai basu kudin, a lokacin da yake yana hannunsu duk abinda suka ce masa baya musantawa. Da suka gama haka, wajen 8:30 na dare sai suka rako shi wai ya hau mota ya koma ya kawo musu kudin video din.

Suka fito da shi suka ce masa idan ya kuskura yayi magana ko yayi wani motsi zasu illata shi, haka ya basu hadin kai.  Suna tafiya da shi suna ce masa bi nan bi can, har dai da Salman yaga sun zo inda Jama'ah suke, kawai sai yayi ta maza ya rumbaci daya daga cikin su suka fadi kasa yana ihun Jama'a ku taimake ni b'arawo ne. Ganin haka sauran suka gudu shi kuma yaci Nasarar damke dayan katamau. Nan ne fa jama’a aka taru ana tambayar me ya faru. Da yake mutanan wajen kabilu ne suna magana da shi yaron da Turanci, sai suka nemi su bawa shi Salman rashin gaskiya. 

Nan ne fa, shi Salman yace wallahi ba zai sake shi ba sai an je wajen 'yan sanda. Suka yi juyin duniya ya cika shi, amma Salman yace sai dai a gaban 'yan sanda sannan zai cika shi. Haka kuwa aka yi, aka kira 'yan sanda suka tafi da su. Ana zuwa caji ofis Salman yayi bayanin abinda ya faru, aka ci Nasarar kama dukkan wadannan matasa a daren, aka tsare su. Da yake a lokacin wajen 11:30 sai 'yan sanda suka ce shi Salman yaje ya dawo da safe. Yace shi bai san kowa ba, suka ce masa ba wani wanda ya sani da zai iya zuwa ya tafi da shi.

Nan ne kawai shi Salman ya tuna cewar ya sanni. Kawai sai naji 'yan sanda sun buga min waya, suka bani labarin abinda ya faru dan haka suke rokon nazo na tafi da Salman. To nima a zahiri ban san Salman din ba sani na hakika, domin a facebook kawai muke gaisuwa, kuma ko a facebook maganar mu bata wuce gaisuwa. Amma da yake naje Adamawa da Azumi Salman yazo har inda nake ya gaishe ni. Anan ya karbi lambar wayata. 

Jin haka, na kira abokaina guda uku na basu labari nace su rakani wajen 'yan sandan. Bayan da muka je na gabatar da kaina a wajen 'yan sanda sannan aka sake yi min bayanin ainihin abinda ya faru. Suka ce na tafi da shi Salman na dawo da shi da safe. Na karbi Salman na kaishi ya kwana. Anan ne nake yi masa fad'a, nace wanne irin hauka ne zai sashi haka kurum ya dauki kafa yaje wajen mutanan da bai san su ba.

Sannan shi kuma yake ce min, ai shi yaudarar sa sukai, domin hoton da suke sakawa a facebook ba nasu bane, sannan sunan da suke amfani da shi shima ba ainihin sunansa bane. Sai daga baya ne ya gane wanda suke magana din ashe sunan sa Micheal. Alhamdulillah mun bi dukkan hanyoyin da suka kamata muka nemawa shi Salman hakkinsa. Kuma har ya koma gida. Dan haka, anan nake amfani da wannan damar wajen kira ga mutane lallai suyi taka tsantsan wajen sanin su waye zasu yi mu'amala da su. Ganganci babba baka san mutane ba, kawai su kira ka kuma ka dauki kafa kaje.

Bayan haka, kuma tilas mutane su rage kwadayi da son banza. Domin a garin kwadayin abin da mutum yake tunanin zai samu zai jefa rayuwarsa cikin garari. Don shi Salman wanda suka yi masa wannan abu zasu iya yin Kidnapping dinsa ko ma su kashe shi, ba abinda ba zai faru ba. Dan haka, mutane ayi hattara. 

Yasir Ramadan Gwale 
04-09-2016

Friday, September 2, 2016

Malam Salihu Sagir Takai Na Iya Zama Mafita A Siyasar Kano A 2019


MALAM SALIHU SAGIR TAKAI NA IYA ZAMA MAFITAR SIYASAR KANO 2019

Zaben Malam Salihu Sagir Takai a 2019 ka iya sanya jihar Kano ta kai bantenta. Malam Salihu bayan bukatar a tallata shi a gayawa al'umma waye shi, duk wani dan Siyasa a jihar Kano da me zabe da wanda ake zabe, babu wanda ke bukatar a sanar da shi Nagarta da Ingancin Malam Salihu Sagir Takai. Domin tuni bayanai suka kara be dukkan wani lungu da sako na jihar Kano suna bayyana kyawawan halayensa wanda ake fatan shugabanninmu su kasance. Malam Salihu na daya daga cikin tsirarun 'yan siyasa a jihar Kano da ya samu kyakkyawar shaida daga kusan Galibin b'angarorin siyasar Jihar Kano.

Maganganunsa da irin kalaman da yake furtawa sun nuna hakikanin irin zaton da ake masa na dattako da kamala da sanin ya kamata wajen jagorantar al'amuran al'umma. Tun Malam Salihu Sagir Takai yana Shugaban karamar hukuma ya samu Yabo da Shaida ta Alkhairi daga Jagoran Gwamnatin Lokacin Alh. Rabi'u Musa Kwankwaso. Duk da sun fito a mabambantan jam'iyyu wannan bata hana Kwankwaso yabawa halayen Malam Salihu a harkar Shugabanci da kiyaye dukiyar al'umma.

Wannan gaskiya tasa da ta bayyana ta sanya Gwamnatin mai girma Malam Ibrahim Shekarau tafiya da shi har kusan Shekaru takwas. Bugu da kari har yayi aikin sa ya gama a matsayin Kwamashina ba a same shi da wani abin Allah wadai wanda ya tabbata cewar yayi abubuwa na rashin gaskiya ba. Wannan ta sanya Malam Shekarau sanya shi a gaba domin zama magajinsa, amma bisa kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala, bai kaddarawa Malam Salihu Sagir Takai zama Gwamnan Kano a lokacin da aka so ba.

Duk da rashin samun Nasarar da yayi, hakan bata sanya shi zautuwa ba irin ta gafalallaun 'yan siyasa da kan shiga muguwar damuwa idan sun fadi zabe. Dukkan kalaman sa suna cike da nuna mika lamura ga Allah da nuna cewar shi ne mai bayarwa ga wanda yaso a lokacin da ya so. Malam Salihu yaje kotu domin bin hakkin sa da yake ganin anyi ba daidai ba a zaben 2011 hakan bai nuna rashin tawakkalinsa ba, sai dai bisa tsari na rayuwa idan kana ganin an taka hakkin ka karbi kadu, wanda tsarin siyasar wannan lokaci yayi tanadin hakan.

Gwamnonin Kano da suka gabata Malam Ibrahim Shekarau da Alh. Rabi'u Musa Kwankwaso babu wanda bai bayyana kyawawan halayen Malam Salihu Sagir Takai ba. Haka nan,  shima Gwamna mai ci Alh. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana Malam Salihu Sagir Takai a matsayin mutumin kirki da ya dace da samun shugabanci. Ganduje tunda ya hau Gwamnan Kano bai taba yin wasu kalamai na batanci ga Malam Salihu sai dai yaba masa da yakan yi.

A dan haka, bisa wannan kyakkyawar shaida da Malam Salihu Sagir Takai ya samu, daga dukkan b'angarorin siyasar Kano da suka hada da Shekarau, Kwankwaso da kuma Ganduje ba suda wani sabani da Takai, kuma shima ba shida wani sabani da su a siyasance ko a mu'amala ta rayuwa. A sabida irin wannan kyakkyawan tunanin mu akansa muke ganin cewar shi ne mutumin da zai saita siyasar Kano, tare kawo sulhu da fahimtar juna tsakanin tsaffin Gwamnonin Kano. A duk cikinsu babu wanda yake da tunanin cewar Takai zai wulakanta shi ko tozarta shi, a sabida haka, muke fatan jam'iyyar PDP ta sake baiwa Malam Salihu Sagir Takai dama a 2019, sannan al'ummar jihar Kano su zabe shi domin saita jihar Kano da dora ta akan turba ta zaman lafiya da juna da fahimtar juna da kuma karuwar arziki da bunkasa jihar Kano tare da maida hankalin 2 aje ayyukan da zasu maida jihar Kano ta zarce tsara a Nigeria. 

Muna fatan Malam Salihu Sagir Takai a matsayin Gwamnan Kano a 2019. Idan har ka gamsu da wannan ra'ayin nawa ka bayyana goyon bayan ka ga ga Takai, ta hanyar rubuta, #Takai2019. 

Yasir Ramadan Gwale 
02-08-2016

Friday, August 26, 2016

Jakadan Sa'udiyya A Najeriya Ya Zubda Hawaye Don Tausayin Wata Mata


JAKADAN SA'UDIYYA A NAJERIYA YA ZUBDA HAWAYE DON TAUSAYIN WATA MATA

Mai Girma Jakadan Sa'udiyya a Najeriya, Sheikh Fahad Abdallah Sufyan, ya kadu matukar kaduwa sakamakon wani rahoto da ya karanta wanda Jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar 13 ga watan Agusta 2016. Rahoton an yi masa taken, "Meet Kaduna Lady Who's Raising 5 Abandoned Babies" wato labarin wata mata da ta kula da rayuwar yara biyar tsintattu. Jakadan ya kadu ainun bayan karanta wannan Rahoto, inda ba da bata lokaci ya bukaci Ustaz Abubakr Siddeeq wanda shi ne Limamin Masallacin Abuja da yake Fassara huduba da Turanci, inda ya tambaye shi ko yaga rahoton da Jaridar ta buga. Inda Ustaz Siddeeq yace bai karanta ba. Nan da nan Jakadan ya turawa Ustaz Siddeeq hoton shafin jaridar da ya dauka a wayarsa ta Whatsapp dan ya duba ya gani. Jakadan ya kuma, bukaci Ustaz ya binciko  wannan mata tare da shirya masa yadda zai gana da ita ido da ido.

Labarin dai na wata mata ce mai suna Hajiya Uwani Yusuf Waziri, wadda aka fi sani da Uwar Marayu.  Wannan mata mazauniyar unguwar Kaji ce a jihar Kaduna. Tana da 'ya 'ya goma sha daya, duk da irin halin da take ciki, ta dauki gabarar kula da tarbiyyar yaran da aka tsinta ta rike su a matsayin 'ya 'yan ta. A duk lokacin da aka tsinci jariri a unguwannin Rigachukum ko Barakallahu ko Hayin Na Iya a kasan gada ko cikin Lambatu akan kai su gidan Hakimi, nan take shi kuma Hakimi zai tura da jairin da aka tsinta zuwa gidan Uwar Marayu. 

Ina cikin garin Kaduna a lokacin Jakada Sheikh Fahad Abdallah Sufyan ya bani wannan umarni.  Dan haka abin sai ya zo min da sauki wajen tuntubar yadda zan hadu da wannan mata. Dan haka ne na samu abokina Dr. Mahadi Shehu wanda shi ne Shugaban Kamfanin Dialogue Global Links tare da gudunmawar Maryam Ahamadu - Suka wadda ta hada wannan rahoto da tallafawar Rufa'at Maccido muka kai ga wanna mata.

Bayan da muka yi katarin gamuwa da Hajiya Uwar Marayu, muka sanya ranar Laraba 17 ga watan Agusta 2016, domin ganawar wannan mata da Jakada Sheikh Fahad Abdallah Sufyan da Misalin karfe 11 na safe a Birnin Tarayya Abuja. A lokacin Maryam da Hajiya Uwar Marayu sun zo tare da daya daga cikin marayun da wannan mata take raino mai suna Zainab, wadda take cikin zanin goyo. Mai Girma Jakadan Sa'udiyya Sheikh Fahad, ya yi mana tarba ta musamman a ofishinsa,  ya marabcemu da Shayin Larabawa na Gahwa da Dabino. A lokacin nayi kokarin zubawa kowa da kaina, amma Jakadan yace kar na damu zai zubawa kowa da kansa dan girmama Uwar Marayu. Bayan ya gama zubawa kowa Gahwa, ya kalli Zainab a cikin zanin goyo yace, yanzu wannan jariri bai yiwa kowa laifi ba na zuwan sa duniya amma an yasar da shi. 

A lokacin da Jakada Sheikh Fahad, yake bayani idanunsa sun cika da kwalla, zuciyarsa ta raurawa. Yayi ta kokarin yin magana amma ina kukan da yake a zuciya yaci karfinsa, inda ya kasa hadiye hawayen da suke kwaranya a kumatunsa. Ganin haka,  sai na Mikawa Jakada audugar share Gumi dake kusa da ni, dan ya goge hawayen da suke guda a kuncinsa. Dukkanmu da muke zaune a wannan waje, muka kasa jurewa, zukatanmu suka raurawa hawayen tausayi ya dinga bayyana a fuskokin mu, adaidai lokacin, Zainab dake cikin zanin goyo da bata san meke faruwa ba, ta fa she da kuka, abinda ya kara tsinka mana zukata, nan dai Uwar Marayu ta shayar da ita Madarar da ke tare da ita, wadda ke zube a cikin Bulumboti. 

Haka nan, Sheikh Fahad Abdallah, yayi karfin hali ya fara magana cikin murya mai cike da nuna tausayi da damuwa. Yace, masu Imani sune suke jibantar lamarin 'yan uwansu musamman wadan da suke cikin tsananin bukata. Kamar marayu da mata da aka mutu aka barsu da yara. Wadannan sune suka cancanci a taimaka musu. Ya k'ara da cewar, Manzon Allah Tsira Da Amincin Allah su k'ara Tabbata a gareshi ya ce, Ni da wanda yake jibantar al'amarin Marayu kamar yatsu ne guda biyu, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yana mai nuni da yatsunsa biyu. Ya cigaba da bayani yana cewa; Watarana wani mutum yazo wajen Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam, yake ce masa, Ya Rasulullahi zuciya ta na fama da kunci da damuwa haka kurum, Manzo yace da shi, ka jibinci al'amarin Marayu ka ciyar da su daga abinda kake ci, Allah zai saukaka maka lamarinka, zuciyarka zata samu nutsuwa. 

Jakada Sheikh Fahad, ya cigaba da cewa, Hajiya Uwar Marayu kin cancanci jinjina da Yabo,  kuma kin cancanci ayi koyi da ke, kin zama zak'ak'ura a cikin matan Najeriya. Ya cigaba da bayanin cewar, duk wanda ya yayewa wani damuwa,  Allah zai yaye masa damuwa ranar tashin Alkiyama. Ke uwar marayu ce, ina tunasar dake Hadisin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam da yake cewa zamu shiga Aljannah tare da shi, yayi mata nuni da yatsunsa biyu; duk wanda ya jibanci al'amarin Marayu. 

Bayan da ya gama gajeriyar tunasarwa. Ya mikawa Hajiya Uwani Uwar Marayu wata gagarumar kyautar da ya bukaci kada a bayyanawa duniya kyautar da yayi mata. Sannan ya yiwa Marayun da take raino Goma ta Arziki. A hakikanin gaskiya zan iya cewa wannan kyauta da yayi musu Takai ta kawo duk da ya roki Alfarmar kada na bayyana abinda ya bayar, amma ya yiwa Uwar Marayu kyauta mai girma. "Wanda duk ya taimaki wani, shima Allah zai taimake shi ya jibanci lamarinsa."

Wannan abinda Jakadan Sa'udiyya ya yiwa wannan mata Hajiya Uwani Uwar Marayu ya kamata ya zabarurar da al'ummar mu wajen tausayawa Marayu musamman jariran da ake haifa kuma a yasar da su akan titi ko cikin Lambatu. Mu yawaita kyauta da sadaka domin bamu san Me Allah ya yi mana tanadi na alheri ba. Allah Ta'ala ya fada a cikin Sura Ta Biyu Aya Ta 268, Shaid'an yana tsoratar da ku da talauci da fatara, yana kuma yi muku bushara da rayuwa mai tsawo. Allah kuma yayi muku alkawarin Rahama da sakamako mai gwabi. Allah shi ne Masani mai hikima".

Hanzari: Wannan bayani Ustaz Abubakr Siddeeq ne yayi a shafinsa na Facebook da Blogspot. Ni kuma na fassara shi zuwa Hausa. Allah yasa mu dace.

Yasir Ramadan Gwale 
26-08-2016

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari


SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI 

Muhammadu Buhari Shugaban kasa ne kuma Shugaban mu ne, muna so masa Alkhairi kamar yadda muke so wa kanmu. Bama fatan Allah ya azabtar da shi a dalilin hidima da ya yiwa wannan kasa, muna fatan Allah ya sauka ka masa lamura ya bashi lafiya da ikon sauke nauyin da yake kansa. Bama aibata shi ko yi wasa mummunan fata, ko samun sakamako mai muni a karshen Gwamnatinsa, a ko da yaushe fatanmu shi ne, Allah ya saukaka masa lamura, ya aiwatar da ayyukan alkhairi ga wannan kasa tamu. Samun Nasarar sa shi ne cigaban mu, idan yayi Nasara kasarmu ce ta cigaba, idan kasarmu ta cigaba mune muka cigaba.

Bamu gushe ba, muna masa uzuri muna masa kyakkyawar fata. A kullum burin duk wani dan kasa na gari ne a ce kasar mu Nigeria ta samu cigaba fiye da dukkan kasashen Afurka. Ba muda wata kasa da za mu yi alfahari da ita da ta wuce Nigeria, dan haka duk wanda yake rike da ragamar jagorancin ta tilas ai masa biyayya da fatan ya samu Nasara wajen cimma manufofin sa na Alkhairi da yayi nufin wanzar da su a tsakanin wannan al'umma tamu.

Muna da masaniyar cewar babu wani shugaba da yake da hankali da kuma yasan me yake, da zai yiwa al'ummar sa mugunta da yi musu fatan shiga mawuyacin halin ni 'ya su. Kullum Shugabanni na gari buri suke da fatan saukakawa al'umma da kawo musu cigaba mai dorewa. Muna da masaniyar halin da tattalin arzikin kasarmu ya shiga na koma baya, wanda muke fatan ya zama Rahama a gare mu nan ga. Muna kuma fatan shugabanni na yanzu da masu zuwa nan gaba su himmatu wajen Alkinta dukiyar kasa domin amfanin jama'a. 

Amma duk da wannan buri da fata da muke yiwa Shugaban kasa, tilas ne mu fito mu nuna damuwar mu akan irin wannan mawuyacin hali da muke ciki. Ba laifi bane, dan wasu ko wani yayi korafin halin da yake ciki na tsanani, dukkan dan kasa yana da 'yanci daidai da kowa wajen bayyana gamsuwa ko rashin ta kan kowace irin Gwamnati. A dan haka muke kira ga Shugaban Kasarmu da yayi duba na tsanaki akan irin mawuyacin halin da al'umma suke ciki, a aiwatar da sauye sauyen da zasu kawo sauki a rayuwar al'umma ba tare da tsanantawa ba.

Hakkin Gwamnati ne kare muradun kasa da na al'umma. Amma kula da Al'umma shi ne akan gaba. Mutane suna cikin hali na yunwa, Masallatai da Majwmi'u sun zama tamkar wajen bara da roko, haka duk wata matattara ta jama'a, ta zama wajen roko. Mutane a cikin galabaita suke rokon abinda zasu ci dan su samu rayuwa. Khalifan Musulunci na biyu Umar Bin Khaddab Allah ya kara yadda a gare shi, yakan zama cikin zullumi da damuwa, akan kada Akuya tayi tuntube ko ta rasa abinda zata ci karkashin jagorancin sa Allah ya tambaye shi. Akuya fa tsoro yake kada Allah ya tambaye shi hakkin ta, sabida tsananin tsoron Allah.

Misalin irin zullumin da Umar Bin Khaddab ya kamata shugabannin su dinga kasancewa, domin samun kubuta a ranar gobe kiyama. Yanzu kai kadai a gidan ka, a tara maka iyalanka su yi maka tambaya akan hakkin su, sai ka shiga cikin tashin hankali da damuwa dan baka san me zasu ce ba. To ina ga tambayar ranar Alkiyama ace al'ummar Nigeria na batun hakkin su kan Shugabanni?  Ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaji tsoron Allah wajen tafiyar da Gwamnatinsa. A saukakawa al'umma mawuyacin hali. Allah ya bamu dacewa.

Yasir Ramadan Gwale 
26-08-2016

Thursday, August 25, 2016

Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu Ya Tsage Gaskiya Akan Gwamnatin Buhari


SHIGA LAFIYA ALFANDA: MAI MARTABA SARKI MUHAMMADU SUNUSI II YA TSAGE TA

Ba shakka Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na Biyu ya tsage gaskiya mai mugun daci  game da kudurorin wannan Gwamnati kan batun tattalin arzikin Kasa. Lokaci yayi da wannan Gwamnati zata bi shawarwarin kwararru domin ceto tattalin arzikin kasarmu daga halin tangal tangal din da yake. Idan ba haka ba kuma, labarai marasa dadi ne zasu ci gaba da faruwa. Abin kam akwai ban tsoro matuka idan aka cigaba da tafiya a haka. 

Ga kadan daga abinda mai martaba Sarki yace,  "misali a lokacin da Babban Bankin kasa CBN yake sayar da Dollar akan farashin hukuma na 197 amma mutane na saya 300 a kasuwar bayan fage, idan na zauna a gidana na dauki sailula ta ina da adadin mutanan da zan kira da zasu samo min zunzurutun kudi har Dollar Miliyan Goma a farashin hukuma na 197 ni kuma na sayar a farashin kasuwar bayan fage na 300, kunga kenan zan ci kazamar riba a wannan harka, domin na samu riba sama da Naira Biliyan Daya. Haka na nuna cewar idan na samu Dollar Miliyan goma sau hudu na ci ribar sama da Naira Biliyan hudu, Bugu da kari zan yi haka ne fa ina dakina ba tare da naje ko ina ba.

To a irin wannan yanayi ne fa ake cewar an shirya tattalin arzikin Æ™asa domin ya amfani talaka. Ku gaya min ta ina Talaka yake amfana, idan ba masu kudi bane suke sake kudancewa? Ya zama tilas Gwamnati tayi abinda ya dace domin ceto tattalin arziki daga lalacewa. Idan ba haka ba kuwa, Talaka zai sake shiga matsanancin talauci masu arziki kuma na kara kudancewa." 

Wadannan sune kadan daga cikin kalaman Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi wanda Galibin jaridun yau suka wallafa. Don haka ya zama tilas Gwamnati tabi shawarar kwararru domin fitar da kasar nan daga halin da take ciki.

Allah ya taimaki Sarki ya kara masa lafiya da karfin fadar gaskiya komai dacinta. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-08-2016

Tuesday, July 26, 2016

Zamani Riga


ZAMANI RIGA 

A lokacin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau, Gwamnati ta kuduri aniyar gina katafaren Hotel a Lamba One Ibrahim Taiwo Road, inda yanzu aka mayar makarantar Sakandare. Gwamnati tayi la'akari da yanayin Jihar Kano a matsayin ta na cibiyar Kasuwanci a Arewacin Najeriya dama Yammacin Afurka da kasashen dake kudu da Sahara, amma duk da wannan bunkasa da buwayar da Kano tayi a harkar kasuwancin saye da sayarwa, Kano din babu masauki wadatattu domin saukar baki. Wannan na daya daga dalilin da Gwamnatin Kano ta bayar a wani tsari da suka yi da aka kira Kano Economic Road Map.

Anyi wannan kuduri ne da kyakkyawar niyya dan habakar kasuwancin Kano. Kasancewar gari kamar Kano babu wani katafaren Hotel dan saukar baki irin na Alfarma. Dan haka ne aka sanya wannan damba ta samar da Five Star Hotel Lamba one Ibrahim Taiwo Road. Amma sai wannan abin ya samu mummunar fahimta daga kungiyoyin al'umma da wasu daga cikin shugabannin al'umma a jihar Kano. Inda aka dinga sukar lamirin gina wannan hotel, ana cewa Gwamnati zata gina wajen badala a kusa da cikin birnin Kano.

A haka wasu mutane suka je fadar mai martaba Sarkin Kano Marigayi Alh.  Ado Bayero suka gaya masa karya da gaskiya akan wannan yunkuri na Gwamnati. Daga ciki dalilin a da suka baiwa Sarki Allah ya jikansa, har da cewar wai za'a gina Hotel mai tsawo da baki zasu dinga zuwa suna gane sirrin Kano. Da wasu zantuka marasa tushenmu masu kama da abin dariya. A haka suka gamsar da Sarki Marigayi, dan haka ya ja Hankalin Gwamnati karkashin Malam Ibrahim Shekarau da ta jingina wannan shiri na samar da wannan hotel.

Meye Hotel? Hotel fa ba wani abu bane illa masauki. Kuma akan haka ake gina dukkan wani Hotel, masauki ne domin amfanin baki da zasu shigo su yi wani uzuri, ko kuma samar da wajen yin taruka da sauransu. Amma sai muka yiwa Hotel guguwar Fahimta. Wasu da dama da an ambaci Hotel kawai sai suce wajen fasikanci ne da aikata badala. Hotel masauki ne da mutum zai biya kudi ya kwana. Wanda duk ya kama ya aikata fasadi ko barna ba zai zama adalci a hukunta Hotel da aikin da wani yayi a cikinsa ba.

Yanzu a jiha Kamar Kano, idan ka cire Hotel din Tahir Guest Palace babu wani Hotel da yake biye da shi a daraja. Sauran duk basu wuce alallaba ba. Wannan mutum fa me Tahir ba dan kasarnan bane, amma mu kalli irin mahaukatan kudin da yake samu a Harkar Hotel. Shin yaushe ne zamu yi kishin kanmu wajen bunkasa tattalin arzikin kasarmu da jihar mu? Duk wanda yake matafiyi yasan muhimmancin Hotel, amma duk da haka muna yiwa Hotel Kallon wajen aikata fasadi da barna.

A irin haka muke yiwa komai fassara. Yana da kyau al'ummarmu mu fadada tunani, mu wanke zuciyar mu ta hanyar duba duk wani abu na zamani da yake da Maslaha a rayuwar yau da gobe. Amma kuskure ne mu dinga kafewa akan abinda ba muda cikakkiyar fahimta akansa. Allah ya sakawa Malaminmu Sheikh Dr. Sani Umar Rijiyar Lemo da alheri, domin a lokacin da ya bayar da fatawa akan daukar hoto ba laifi bane, na san wasu da dama da suka kafa akan Hoto Haramun ne suka sauka daga kan wannan ra'ayin.

Lallai wannan gari namu mai albarka da muke fatan Allah ya tsare mana shi ya yaukaka arzikin sa,  yana bukatar Malamai masu zurfin Ilimi irinsu Dr. Sani da Dr. Bashir da zasu dinga haskawa al'umma abubuwa musamman wadan da zamani yazo da su kuma ake da gajeran tunani akansu, domin shi zamani riga ne, idan yazo dauka ake a saka ba mayar da kai baya ba. Allah ka haskaka zukatanmu wajen karbar gaskiya da kuma aiki da ita.

Yasir Ramadan Gwale 
26-07-2016

Sunday, July 24, 2016

Meye Ake Nufi Da Film Village?


MEYE AKE NUFIN DA FILM  VILLAGE? 

Wannan tambaya ce da dan uwa Malam Misbahu Saminu Madabo yayi a Shafin sa na Facebook. Sakamakon tattaunawar da naga ana yi a karkashin posting din nasa yasa na bashi amsa kamar haka:
Alkali Misbahu Saminu MadaboMadabo sannu da kokari. Daga wannan tambaya da kuma maganganun da masu koment ke yi ya nuna da dama kawai sunan suka sani amma sam basu fahimci meye ake nufi da film Village ba.

Amma a zance na hakika Film Village da Gwamnati zata gina, wani waje ne da zaka kirashi ma'aikata da za a tanadar masa abubuwan bukata irin na abinda aka yi domin sa.  Misali, idan Gwamnati ta gina Film Village zai zama tamkar garin aiki ne. Wato duk wanda zai shirya film zai je wannan waje ya biya Gwamnati kudin amfani da wajen sannan a bashi iznin shiga, wajen zai kunshi lambu da dakunan daukar hoto da wajen tace sauti ko Studio, da kuma nau'I na Kyamarori da suturu da abubuwan da masu film zasu bukata, za tanadar da komai, amma fa duk abinda mutum zai yi amfani zai zama sai an biya kafin fara amfani da shi.

Bayan haka kuma, Gwamnati fa ba wai kawai wajen zata gina ta dankawa masu shirya film sai yadda suka ga dama ba, ba haka bane, wajen zai kasance akwai jami'an tsaro da zasu dinga sanya ido akan masu shiga da fita, dan tabbatar ba sace ko lalata kayan da aka sanya dan amfanin wajen ba. Jami'an tsaro anan ba ina nufin zata zuba sojoji ko 'yan sanda ba, za a samarwa wajen Security ne da ya dace da kuma wanda aka ga yayi daidai.

Sannan kuma, a cikin wajen dai za a bayar da damar bude kantuna na sai da abinci da kayan ciye ciye. Wanda wannan gwamnati na da zabi ko dai kantuna su zama nata ma'ana abinda ake sayarwa ko kuma a baiwa mutane shaguna su kuma su zuba kaya a ciki.

Gwamnatoci na samar da irin wannan waje ne, dan kebe masu yin a abin da kuma samar masa da tsarin da zai bawa hukuma damar samun cikakken kudin shiga. Amma fa mutane su sani, duk wannan abinda za ai tilas Gwamnati zatai ne bisa la'akari da yanayi da kuma al'adunmu da suka dace da addini. 

Misali idan Gwamnati ta gina, zata ce dokokin jihar Kano sun haramta sha da sayar da giya. Dan haka zai zama doka a wannan waje ba za a sayar da giya ko shanta ba, dan haka wanda duk aka kama ya karya dokar shan giya ko sayar da ita a wajen zai fuskanci hukuncin da aka tanadar wa hakan. Wannan ya hada da sauran abubuwan da Musulunci ya hana, kuma dokokin Jihar Kano suka tabbatar da haninsu kamar Zina, Luwadi, Sata, Sane, kwace fada da sauransu.

Bugu da kari, akwai wajen shakatawa na Gwamnati dake Yankari a Bauchi, a wannan waje akwai dakunan kwana da wajen ganin na mun daji da kuma wajen linkaya. Kaga ai Gwamnati ce ta samar amma dokokin wajen sun dace da mutanan Bauchi da Arewacin Najeriya. Sannan kuma akwai irin wannan wajen shakatawa a Cross Rivers da ake kira Obudu, a wannan waje sha da sayar da giya ba laifi bane, sabida a jihar shan giya da sayar da ita ba laifi bane. Amma kuma abinda zamu gane shi ne dukkan su da wannan film Village Gwamnati tayi ne dan samun kudin shiga, ba wai dan kawai bukatun wasu tsiraru bane.

Bayan haka kuma, Gwamnati ba wai kawai zata zura ido ayi duk abinda aka ga dama ba, tilas akwai dokokin da za ai domin wajen. Dan ita Gwamnati zai zamar mata wajen samun kudin shiga. Tunda kasashe irinsu India da Turkiyya da Masar suna da irin wannan waje, kuma yana daga cikin abubuwan samar musu da kudin shiga.

A dan haka, mutane su sani, wannan waje zai zama ne kamar gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Gwamnati ce ta gina, amma ana zuwa a kama hanyar dakuna a kwana, sannan kuma akwai dakunan taro wanda za a biya a gudanar da wani sha'ani.

A Takaice wannan shi ne Film Village kuma shi ne abinda Gwamnati zata gina a Kano. Duk wanda yace ba haka bane, to bai fahimci meye Film Village ba. 

Dan gane da batun lalacewar tarbiyya kuwa. Duk wanda misali ya karbi wannan waje dan gudanar da wani sha'ani kuma ya karya doka to akwai tsari na hukunci. Sai dai kuma wanda zai yi ba a sani ba, amma wannan ba zai sanya a hukunta wajen da aikin wasu tsiraru ba tunda ba manufarsa batawa ba.

Kamar Musulmi ne yaje ya aikata ta'addanci yasa Bom ya kashe mutane. Wannan ba zai zama dalilin da zai sanya a hukunta Musulunci da cewar shi ya horar da shi wannan aikin ba. Duk kuwa da cewar wanda yasa Bom din ya kashe Mutane Musulmi ne. Dan haka, ba zaka hukunta Film da aikin da kaga wani yayi da bai dace ba. Allah shi ne mafi sani.

Yasir Ramadan Gwale 
24-07-2016

Thursday, July 21, 2016

Meye Illa Ko Amfanin Samar Da Film Village?


MEYE ILLA DA KUMA AMFANIN SAMAR DA FILM VILLAGE A KANO?

Naga mutane da yawa na magana kan batun kaddamar da Film Village da akai a Kano kwanaki. To gaskiya ni kam ban fahimci wace irin Illa mutane suke magana da wannan abu zai yi ba. Misali ada can da babu wannan film Village din an fasa shirya tare da gudanar da Fina-finai a Kano? Ina Jama'ah suke lokacin da masu sana'ar shirya film suka fitar da Clip na Video suna kiran magoya bayan su da su zabi APC da 'yan takarar ta a 2015! Bana kare sana'ar Fina-finai, amma meye laifin Gwamnati dan ta samar musu da muhalli na shirya film? Kamar yadda nace ni a karan kaina ban fahimci Illar da mutane suke magana ba, amma ina fatan wanda suka sani su fahimtar da ni.

A ganina a yadda mutane suke ta korafin lalacewar al'amura a harkar Fina-finai, shin samar musu da wannan matsuguni ba zai bada damar samar da sauye sauye wadan da zasu bada sararin kawo gyara a harkar ba? Wannan fahimtata ce, gani nake hakan zai baiwa Hukumomi damar fahimtar hakikanin inda matsala take da kuma kawo gyara a harkar, tunda a zamanin yanzu babu wani dan siyasa da baya fatan samun goyon masu shirya film. Wanda suna amfani da wakoki da suke tsuma zukatan magoya bayan dukkan jam'iyyun siyasa.

Harkar filming din nan fa sabida muna kallo ne shi yasa har muke shaida kurakurai da abubuwan da basu dace ba a ciki. To ina ganin ba Condemnation ya kamata ayi ba, kamata yayi a duba hanyoyi na kawo gyara a harkar. Kamar yadda tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau ya kawo sauye sauyen da suka tsabtace harkar film a zamanin mulkinsa. Kowa ya shaida yadda Shugaban hukumar tace film ta Kano Malam Rabo Abdulkarim ya sha Gwagwarmaya wajen kawo sauyi da gyararraki a harkar shirya film a Kano. To misali, idan akace suna killace a muhalli guda daya kuma akwai tsayayyen shugaba a harkar ai tilas a kawo gyara. Amma wannan tunani na ba mamaki ina kan kuskure, a fahimtar da ni.

Yasir Ramadan Gwale 
21-07-2015 

Gaskiya Da Rikon Amana Da Aiki Tukuru Suka Janyowa Malam Nuhu Ribadu Martaba Da Daukaka


GASKIYA DA RIKON AMANA DA AIKI TUKURU SUKA JANYOWA MALAM NUHU RIBADU MARTABA DA DAUKAKA 

Malam Nuhu Ribadu mutum mai gaskiya kamar Littafi. Ka duba yadda gaskiya da rikon Amana da aiki tukuru suka janyowa Malam Nuhu Ribadu martaba da daukaka. A kakar zaben 2015 Malam Nuhu Ribadu ya shiga tsaka mai wuya, wadda ta janyo dukkan jam'iyyun APC da PDP suka yi ta kokarin ganin shi ne zai zamar musu dan takarar Gwamnan Jihar Adamawa. Cikin ikon Allah mai aukuwa ta auku, Allah ya kaddari Malam Nuhu da samun tikitin tsayawa takara karkashin jam'iyyar PDP. 

Yanzu kuma bayan dan wani lokaci jam'iyyar APC ta fahimci irin wawar asarar da ta yi ta Malam Nuhu Ribadu, dan haka suka yi ta aika masa da wasiku na fatan alheri da fatan ganin ya koma APC. Mu muna da masaniyar dukkan abubuwan da suka wakana wanda suka janyo ficewar irinsu Malam Nuhu Ribadu da Sardaunan Kano Malam Ibrahim Shekarau fi cewa daga APC jam'iyyar da suka kafa ta da hannunsu,  suka koma PDP. 

Malam Nuhu Ribadu na da damar zab'in abin da yaga yafi masa daidai kuma zai fi zama Maslaha a gareshi da al'ummarsa da kuma mu da muke tare da shi. Ni a nawa ra'ayin bana fatan Malam Nuhu Ribadu ya fita daga PDP ya tsallaka APC. Ina fatan ya cigaba da zama a PDP domin ko ina muna bukatar wakilcin mutane na gari. Amma idan ya yanke shawarar komawa APC wannan yayi hukunci ba wanda raina zai so ba, amma  ina masa fatan alheri. 

Na gamsu dari bisa dari akan nagartarsa da kishin sa da son sa da gaskiya. Allah ka taimake shi kayi riko da hannunsa, ka tabbatar da shi akan gaskiya komai rintsi.  

Yasir Ramadan Gwale 
21-07-2015

Monday, July 18, 2016


MEYE AIBU NA SALON DAUKA HOTON DAB? 

A satin da ya shige naga kusan hankalin mutanen Social Media gaba daya ya karkata kan wannan salon daukar hoto. Naga da yawa daga cikin bayanan da akai tayi na sukar abin da cewa 'WAI' bautar Iblis ne. Amma a zahirin gaskiya babu wani wanda na gamsu da hujjojinsa akan cewa hakan bautar shedan ne. Yana da kyau mutane su sani a rayuwa fa komai Halal ne, sai abinda Shari'ah tayi togaciya akansa, kamar sata, sane, bizi, zara da sauran kaba'ira. Allahumma sai kuma abinda ya shafi koyi da Wanda ba Musulmi ba a abinda ya shafi Ibada. 

A wannan zamanin na yayi, kusan komai ana kwaikwayo ne daga ko dai masu shirya Fina-finai ko 'yan kwallon kafa ko mawakan disko da sauransu wadan da ake kira da Celebrities. Tun daga yanayin dinkin da sanya sutura da yin aski da gyaran fuska da sauran kwalliyar gayu ta kece raini duk ana kwaikwayo ne a wajen su. To meye yasa sai akan salon daukar hoton DAB mutane suke ta magana basu yi kan sauran ba? Watakila sabida ance bautar shedan ne. To abin tambaya shi ne, meye bautar Iblis ko shedan? Shin yanzu ne a 2016 Iblis ya nuna yadda za a dinga yi masa Bauta? Da can walawa mabiyansa yayi?

Yana da kyau mutane su dinga lura da yanayin rayuwa da kuma sassauyawar zamanin da yadda ake samun canji daga lokaci zuwa lokaci. Kowane zamani kan zo da nasa salon, a da can a tara gashi him da sanya fankacecen wando da katuwar Radiyo shi ne cinyewa. A wannan lokacin idan ka baiwa gaye tsukakken wando ta kasa ba zai saka ba, amma kuma yanzu shi ne gayu sabida ana yayinsa. To haka zamani kan zo da salo iri iri.

A ganina dan masu Sha'awa sunyi irin wannan daukar hoto ba wani abin kausasa harshe bane. Yayi ne kuma zai wuce kamar yadda komai kan zo ya wuce. Yanzu irin yadda 'yan mata kan yi kwalliya a Shekara 20 da suka wuce idan mace tayi ba zata iya fita ba, sabida zata zama abin tsokana da zolaya. Amma yanzu gayu ne sai mace ta zambada hoda tai ta yawonta tana tunkahon tayi gayu na kece raini.

Sai dai kuma, yana da kyau mu sani muna da kyawawan dabiu da halaye da suka wadace mu wajen yin kwalliya. Amma wannan ba zai zamu aibu ba dan mutane sun dinga tafiya da zamani matukar ba a kaucewa Shari'ah ba. 

Yana da kyau mutane su zama masu saukakawa kansu ba masu tsanantawa ba. Abinda ba sabon Allah ba amma mutane suyi zafi akansa.

Yasir Ramadan Gwale 
18-07-2016

Saturday, July 2, 2016

OZONE LAYER : WANI Bargo Da Allah Ya Sanya Tsakanin Rana da Wannan Duniya Yayi Wagegiyar Hujewa


OZONE LAYER: WANI BARGO DA ALLAH YA SANYA TSAKANIN RANA DA WANNAN DUNIYA YA YI WAGEGIYAR HUJEWA

Jaridar The Guardina ta kasar Burtaniya ta wallafa Wani binciken masana 'yan kasashen Amurka da Burtaniya kwararru akan sanin kimiyyar sararin samaniya. Shi dai wannan bincike da aka buga a babbar mujallar kimiyya dake taskance binciken kwararru ta bayyana cewar wannan bargon da ake kira ozone layer da Allah ya sanya shi a matsayin kariya tsakanin wannan duniya tamu da kuma rana ya fara hujewa tun kusan shekarun 1980 inda bular ta dinga fadada tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu, inda a wannan lokaci aka gano wagegiyar  hujewa a jikin ozone layer din.  Shi dai wannan bargo da ake kira ozone layer, Allah ya sanya shi ne a sararin samaniyar wannan duniya domin ya zama kariya ga halittun kasa daga sinadaran da suke zubowa daga zafin rana wanda zasu cutar da Bil-Adama ta hanyar sanyawa mutane cututtukan da ke da alaka da fata da kuma sankara. 

Allah Buwayi gagara Misali, ya sanya wannan abu tamkar bargo a sararin saman wannan duniya domin ya zama kariya gareta da kuma Bani-Adam. Wannan wagegiyar hujewa da ozone layer tayi, babbar barazana ce ga Bil-Adama. Ita dai wannan ozone layer masana sun fadi cewar samun sauyin da duniya take yi na d'umamar yanayi ne kan sabbaba hujewar ta. D'umamar duniya da ake kira da global warming ya taimaka matuka wajen cigaba da hujewar ozone layer. Dan haka ne a kusan ko da yaushe Majalisar Dinkin Duniya kan shirya manya manyan tarukan karawa juna sani domin a fadakar akan irin hadarin da wannan duniya take ciki a kuma tattauna yadda za a kaucewa d'umamar duniya da kuma sauye sauyen da ake samu na yanayi. Ta hanyar rage yawan hayakin masana'antu da manyan kasashen masu karfin tattalin arziki ke samarwa. 

Bayan haka kuma, majalisar dinkin duniya tayi ta bijiro da shirye shirye na daddasa bishiyu wadan da suke taimakawa wajen samar da yanayin da zai taimaka wajen rage wannan barazana da duniya ke fuskanta ta hanyar d'umamar yanayi. Sare dazuka da Bankawa tsirrai wuta na daga cikin abubuwan da suke sabbaba d'umamar yanayi da kuma cigaba da karuwar hujewar ozone layer, wanda hakan kan haifar da kafewar manya da kananan koguna ta hanyar gurgusowar hamada da kuma narkewa tare da zaftarewar daskararriyar kankarar da ke makare kudancin wannan duniya, yayin da a hannu guda hakan ke kara yawan ruwan da ke cikin manyan kogunan wannan duniya, abinda ke haifar da ambaliyar ruwa da kan haifar da asarar muhalli me girman gaske.

Binciken na kwararru ya nuna cewar samun karuwar d'umamar duniya da ake yi shi ne yake haifar da karin bulewar ozone layer, hakan kuma karin barazana ce ga lafiyar Bil-Adama dake rayuwa a wannan duniya musamman sassan duniyar dake fama da yanayin zafin rana. Domin ana samun karin sabbin cututtukan da suke da alaka da fata da kuma sankara fata mai wuya sha'ani. Sabida a dalilin wannan hujewa sinadarin Nitrogen na sulalowa ya gauraya da yanayin wannan duniya, wanda barazana ce mai girman gaske.

Yasir Ramadan Gwale 
02-07-2016

Thursday, June 30, 2016

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari A Yau


GWAMNATIN SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI A YAU 

Wani lokaci kan da ya shude bayan da wannan Gwamnati ta gama tattabata a matsayin na cikakkiyar Gwamnati. Naji wani mai kira yana kira da kakkarfar muryar yana ta b'urari yana mai Yabo da jinjina akan abinda akai yayi masa dadi na wasu da ake kamawa da ake zargin sun zambaci wannan kasa a zamanin Gwamnatin tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan da ta shude, a lokacin da ake tsaka da wannan kame da daurin a gefe guda kuma farashin kudin musanye na hauhawa a kasuwannin canji. Anan ne naji wannan mai kira yana cewar su ba suda wata damuwa, Dollar Amurka daka fi amfani da ita a kudin musanye ta tashi ta kai Naira dubu su kam bukatar su ta biya, babu ruwansu da wani abu tashin dollar. 

Ba mamaki wannan mai kira a lokacin da yake wancan batu na Dollar tayi ta tashin gwauron zabi tana kanshin tura re dan goma a kasuwar musanye, bai san hakikanin yadda hauhawar farashin dollar yake shafar tsarin tattalin arziki ba, shi sa a zaton sa Dollar zata yi ta tashi shi kuma rayuwarsa ta cigaba da gudana yadda yake so. Kwatsam bayan wani lokaci sai na sake jin wannan me kira yana korafi yana fadin rayuwa ta tsananta ya kamata Gwamnatin da suka zaba ta yi wani abu akan halin da ake ciki na tattalin arziki da kusan farashin komai ya linka sakamakon tashin dollar da wancan mai kira yayi ta mata fatan tashi babu kakkautawa. 

Na saurari wani bayani na wani fitaccen Malamin masanin kimiyya da hamayya dan Adam, yana fadin cewar. Idan mutum yayi burin auren mace kakkyawa to ya tabbata ya same ta kuma ya aura,  haka nan kuma, idan ya aureta kada daga baya yayi korafin ba tada tarbiyya ko bata iya girki ba, domin asali ba hakan ya nema ba, kyau yake so kuma ya samu. Kamar me wancan kira ne akan wannan gwamnati, asali shi ne, yaso kuma yayi fatan Muhammadu Buhari ya zama Shugaban kasa kuma ya zama, to ba shakka shi bukatar sa ta biya tunda abinda yayi ta fata kenan.

Mafiya yawancin mutane sun so zuwan wannan gwamnati ne kai tsaye ba wai ainihin saukin lamari ake nema a wajen Allah ba. Misali a baya kafin zabe yana zama laifi babba akan wasu suyi addu'ah suce Allah yayi mana zabi mafi alheri, kawai an tafi akancewar tilas kowa ya goyi bayan Buhari watakila sabida k'abilanci da kuma Addini. Allah Buwayi ne gagara Misali,  a tsarin Mulkin Dimokaradiyya da babu ruwansa da addini, mulki ne da ke tafiya da manufofin jam'iyyun siyasa da kuma wanda aka zaba. 

A dan haka, akan samu wasu shugabannin suyi Gwamnatin adalci a tsarin Demokaradiyya sama da gwamnatin da ba ita ba da ta fi kusa da addini. Misali tsarin Gwamnatocin kasashen turai da Amurka ya sha bamban wajen tafiyar da gaskiya akan mafi yawancin tsarin mulkin da ba shi ba, a gani na zahiri sai kaga wadannan kasashen da suka cigaba suna kwatanta adalci a tsakanin Al'ummar da suke shugabanta. Sabbin sauran da ba su ba.

A dan haka game da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ina ganin da yawa kawai fatan su zuwa ta ba wai sun kyautata zato ne ga Allah ba, illa shi wanda sukai masa fatan zuwa suke marari zai yi abinda suke so. To a ganina duk mutumin da yayi fatan zuwan wannan gwamnati ya fito ya zabe ta kuma aka tabbatar da ita, to bukatar sa ta biya, zancen korafi ba nasa bane, kamar dai Misalin wanda yake san mace mai kyau.

Yasir Ramadan Gwale 
30-06-2016

Sunday, June 5, 2016

Kyakkyawar Shaida Da Mohammed Ali Ya Samu Abin Alfahari Ce


KYAKKYAWAR SHAIDAR DA MOHAMMED ALI YA SAMU ABINDA ALFAHARI CE

A jiya Asabar na jima ina kallon video tare da karatun maganganun mutane akan rasuwar Mohammed Ali zakaran damben duniya mai girma. Ba ko tantama rasuwarsa ta girgiza mutane da yawa tun daga kan shugabanni a Amerika da sauran shugabannin al'umma dama gama garin mutane irina, anyi ta yin jawabi da tariyar irin kalaman sa da yayi akan addini da rayuwa. Mutane sun fadi Alkhairi mai yawa akan Mohammed Ali, anyi masa addu'o'i masu yawa. Musulmi da kirista duk fatan alheri suke yi masa.

Alal hakika samun irin wannan shaida a wajen mutane ba karamin alkhairi bane. Domin Hadisi ya tabbata daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam cewar Shaidar duniya ita ce Shaidar Lahira; duk mutumin da ya samu kyakkyawar shaida a duniya ana sa masa ran samun sakamako mai kyau a duniya. Mu aikata alkhairi mai yawa mu kaunaci Allah da ManzonSa muyi gaskiya muyi sadaka muyi kyauta muji tsoron Allah mu kyautata niyya tare da Ilkhlasi Allah zai bamu me kyau a duniya me kyau a Lahira. 

Mohammed Ali ba wani shahararren Malamin Addini bane da ya koya da ilimin addini ba. Ba komai bane face dan dambe da ake kutufarsa shima ya kutufa. Amma sabida yaso Allah yaso Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ga yadda duniya ta nuna kaduwa da rashinsa, duk kuwa da cewar an jima ba'a ganshi ko jin kalaman sa ba, amma wannan bai sanya jama'a sun manta da shi ba. An fadi Alkhairi mai yawa akansa. Lallai wannan darasi ne babba a garemu da muke raye mu sani,  ba sai lallai ka zama Babban Malamin addini zaka yi umarni da kyakkyawar ko hand ga mummuna ba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam yace kyakkyawar magana ma sadaka ce. Irin kyawawan maganganun Mohammed Ali akan addini da rayuwa kadai abin alfahari ne. Kuma wannan yake nuna mana cewar addini shine gatan mu, shi ne silar samun Nasarar mu a rayuwa. Mu rike Allah mu bi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam Mubi addinin Musulunci sau da kafa In sha Allah zamu hadu da Ubangiji lami lafiya. Allah ka dauka ki Musulunci da Musulmi. Allah ka jikan zakaran damben duniya Mohammed Ali ka haskaka kabarinsa. 

Yasir Ramadan Gwale 
05-05-2016 

Wednesday, May 25, 2016

MALAM SALIHU SAGIR TAKAI : GASKIYA MATAKIN NASARA


MALAM SALIHU SAGIR TAKAI: GASKIYA MATAKIN NASARA 

Kwanakin baya wani bawan Allah ya samu Malam Ibrahim Shekarau Sardaunan Kano yake shaida masa cewar; indai ana son aci zabe to ya kamata a sauya Malam Salihu Sagir Takai a matsayin dan takararmu. Domin a cewar sa Kano ba irin Takai take bukata ba, ya cigaba da cewar, Jihar Kano na bukatar mutum marar kunya wanda zai iya taka kowa kuma yayi rashin mutunci ba wanda zai tanka masa, ya buda misali da wanda suka gabata wai a samo mutum mutakabbiri Mai Takalmin Karfe. 

Gama bayanin sa ke da wuya, Sai Sardaunan Kano, yayi Hamdala ya godewa Allah. Ya kada baki yace masa, Alal hakika wad'annan bayanai naka akan Malam Salihu sun sake tabbatar min da abinda na sani kuma nake da yak'ini akansa. Duk abin da ka fad'a, ya kara tabbatar min da cewar ba ko Shakka Malam Salihu Sagir Takai mutumin kirki ne mai gaskiya da rikon Amana, mai girmama mutane da sanin ya kamata. Kuma wad'annan bayanai naka sun k'ara nuna mana cewar Lallai Malam Salihu shi ne mutumin da ya cancanci mu saka a gaba domin samun Nasara.

Bahaushe yace wai a san mutum a san cinikinsa. Ko da yaushe ana san mutumin kirki ya kasance yana nan yadda aka sanshi, rud'i da bukata ba zasu tab'a sanya shi ya canza daga mutumin kirki yayi sako-sako ba dan neman biyan wata bukata. Alal hakika wannan hali na Malam Salihu Sagir Takai ya sanya muka ce mun ji mun gani har gobe har jibi muna yinsa a matsayin dan takarar Gwamnan Kano. Muna da yakini, kuma mun kyautata zato ga Allah cewar alkhairai da mukewa Malam Salihu zato akansu suna nan.

Nayi matukar farinciki lokacin da naga Farfesa Salisu Shehu BUK yayi kalamai na Yabo akan Malam Salihu bisa wannan Waki'a da ta same shi. Ya k'ara tabbatar min da abinda na jima ina ji ana fad'a akan Malam Salihu Sagir Takai. Ya ya be shi, kuma yayi masa shaida ta gari, ya kuma tabbatar da cewar tun da can haka ya sanshi mutumin kirki mai amana. Daman kuma, shaidar duniya ita ce Shaidar Lahira inji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam. 

Mutanan Alkhairi, masu mutunci da daraja su baka shaida cewar kai mutumin kirki ne mai mutunci da karamci da amana. Wannan kadai Nasara ce a rayuwa. Ina taya Malam Salihu Sagir Takai murnar wannan shaida da ya samu daga bakin mutumin kirki, Farfesa Salisu Shehu BUK. Muna maka  fatan alheri da fatan cigaba da dorewa akan yadda muka sanka kuma muke jin labarin ka da kuma yadda jama’a sukai maka shaida ta alkhairi. Ina addu'ah ta musamman ga wannan bawan Allah Malam Salihu Sagir Takai. 

Ya Allah ka tsare shi ka tsare masa Imaninsa, Allah ka yi masa jagoranci a dukkan lamuran sa na rayuwa, Ya Allah Kada ka jarrabe shi da abinda ba zai iya ba. Allah ka azurta Kano da samun Malam Salihu Sagir Takai a matsayin Gwamna. Allah ka shige masa gaba kayi riko da hannunsa, Allah Kada ka barshi da iyawarsa. Allah ka baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano a 2019. Amin Summa Amin. 

Yasir Ramadan Gwale 
25-05-2016

Sunday, March 13, 2016

Ta'addancin Da Shiah Sukaiwa Mai Martaba Sarkin Hadejia


TA'ADDANCIN 'YAN SHIAH GA MAI MARTABA SARKIN HADEJIA

A ranar Juma'ar wannan makon mai karewa ne, 'yan Shiah suka yiwa fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia tsinke, inda suka aikata Ta'addqnci ga Mai Martaba Sarki. Rahotanni sun nuna cewsr 'yan Shiah sun shiga harabar Fadar sarki da nufin zanga zanga dauke da kwalaye da takardun bango da suke nuni da a saki Shugabansu da ke tsare hannun sojoji.

Wannan dalili yasa 'Yan Shiah sukaiwa Mai Martaba sarki ihu da jifan ayarin Dogaransa da duwarwatdu da kwalaye. Wannan kadan ne daga cikin irin ayyukan Ta'addanci da Shiah suka jima suna aikatawa a Duniya. Su din daman wasu mutane ne da basa kaunar zaman lafiya a ko da yaushe.

Dan haka muna kira ga mahukunta da su dauki mataki na hana yin duk wata zanga zangar 'Yan Shiah a ko ina a kuma ko da yaushe. Ba daidai bane, hukumomi su zubawa wasu mutane ido suna daukar doka a hannunsu suna yiwa mutane abinda suka ga dama ba tare da an taka musu birki ba.

Muna kara yin Adduah ta musamman ga Mai Martaba Sarkin Hadejia, Allah ya kara masa lafiya. Ya kare shi daga dukkan sharrin masu sharri. Ya yi masa garkuwa da garkuwarsa. Allah ya daukaka darajarsa da masarautarsa. Allah ya karawa Sarki Lafiya. Wadannan Shedanun mutane Allah kai mana maganinsu a duk inda suke.

Yasir Ramadan Gwale
13-03-2016

Wednesday, March 9, 2016

Yiwa Yunusa Yellow Shari'ah Shi Ne Adalci


YI WA YUNUSA YELLOW SHARI'A SHI NE ADALCI 

Sau da dama rashin sani da ad'ifar k'abilanci kan hana mutane ganin gaskiya. Mutane da yawa basu fahimci hakikanin abinda ake tuhumar Yunusa Yellow akai ba, dangane da batun Ese Oruru (A'isha). Kawai abinda mafiya yawa suke kallo shi ne batun addini, da kuma shi wanda abin ya faru da shi, wato Musulmi, kuma Bahaushe 'dan Kano ko Arewa. Yawancin mutane a tunaninsu idan Bahaushe Musulmi ya aikata wani laifi, komai muninsa, tilas kafatanin Musulmi su goyi bayansa, musamman ma ace abin ya had'a da wanda ba Musulmi ba. Amma abinda muke kira a koda yaushe shi ne: ayi Adalci, don Musulunci shi ke kira ga yin adalci fiye da komai.

Tunanin wasunmu da yawa, gani suke idan mutanan kudu ko wad'anda ba Musulmi ba sun yi mana rashin adalci, tilas ne mu ma idan mun samu dama mu yi musu rashin adalci. Sun manta cewar addinin Musulunci da muke 'kafafa ko tutiya  da shi ya horemu da yin adalci. Saboda Adalci Allah ya azabtar da Bil Adama a dalilin ya cutar da dabba. Annabi (SAW) ya gaya mana cewar, Allah ya azabtar da wata mata a dalilin kyanwa, sabida ta cutar da dabbar!

Wannan batun na Ese Oruru (Aisha) yayi matukar daukan hankalin mutane fiye da batun Abdul Nyass lokacin da yayi kalaman ridda, har wasu tsiraru suna maganganu na rashin kyautawa, a tunaninsu hakan zai nuna cewar su masu kishin Musulunci ne ko kishin Arewa. Wannan ba daidai bane, mutum ya tafka kuskure kawai saboda namu ne Musulmi d'an Arewa mu goyi bayan abinda ya aikata ba tare da tuntubar me addini yace ba kafin ya aikata. 

Ga dukkan alamu wannan matashi bai nemi sanin meye addinin Musulunci yace ba akan abinda ya aikata, kafin ya aikata din,  wanda a hakan kuma wasu ke ganin tilas kowane Musulmi ya goyi bayansa, haka kuma, bai nemi sanin tanadin dokar kasar nan mai al'ummar da ke da ma'abuta addinai daban daban ba. Abu na farko dai, a tuhumar da ake yiwa wannan matashi, babu batun addini. A cikin jerin tuhumar da akai masa babu inda aka ambaci ana tuhumar sa da cewar ya Musuluntar da wannan yarinya da yardarta ko babu. Batu na addini kam, yarinya ta Musulunta, muna fatan Allah Ya tabbatar da duga-duganta akan turba ta Musulunci, Ya kare ta da dukkan kariyar Sa, Yayi mata garkuwa da dukkan garkuwar Sa. 

Bayan haka, wannan matashi, ya tabbatar da cewar shi ya kawo ta Kano daga Bayelsa, kuma ya amince cewar yana tarawa da ita tun a garin su Bayelsa, wannan yasa yarinya ta samu juna biyu mai kimanin watanni biyar. To anan, kawai sai mu goyi bayan barna? Yaro ya dauko yarinya daga garinsu bayan yayi mata ciki, sannan kuma yanzu sai a zo da batun addini a fake don a nemar masa kariya?

Abin mamaki ne, ka ji mutane masu hankali da ilimi suna fadin kalamai marassa kan gado, kamar cewa: wai Mu Musulmi mun ji kunya! Kuma mutanan da aka fi zargin sune Malamai da Sarakuna da Shugabanni wai suna gani anzo an tafi da dan uwanmu za a je wulakanta Musulmi da sauran ire-iren wadannan kalamai masu cike da wauta da rashin sani da tunzura al'umma. 

Hakika wadancan kalaman shiririta ne da zafin kai na babu gaira babu dalili. Batun da yake gaban Shari'ah me kuma mutum yake fatan a yi? Ko kuwa, muna so Malamai da Sarakuna su hana a yi masa Shari'ah saboda shi Bahaushe ne dan Kano Musulmi? Dole dai dayan biyu za a yi, ko dai a same shi da laifi ai masa hukunci daidai da abinda ya aikata bisa tanadin dokar kasa, ko kuma a ce ba shi da laifi. Dole dayan biyu ya faru. To me kuma, muke son ayi?

Wasu ma saboda tsabar rudani da rashin sanin makama, cewa suke wai akwai wani Pastor daga kudu da yazo Arewa ya saci 'yayan Musulmi ya kai su kudu zai maida su kiristoci. Abubuwan tambaya ga masu wannan shirbici, sune : 
Shin sai yanzu ne kuka samu labarin satar  yaran? 
Idan ka kwana biyu da masaniya akai, shin a bayan wani mataki ka dauka? 
Me ya hana ku kai shi Pastor din zuwa kotu indai batun gaskiya ne?
Kuma ma, shin yaran nan da muka bari a tituna suna watangarirya suna gararambar neman abinda zasu ci, cikin tsummokarai da datti da kazanta da rashin nagartacciyar koyarwar addini, wai sune muke nuna kishin riya akan su? A tsakanin mu ne fa mu Mutanan Arewa Musulmi ake maganar akwai Almajirai sama da Miliyan goma sha biyu (12,000,000), me mu kayi na taimaka musu fita daga halin kunci da suke ciki? 

Bamu iya mu taimakawa wanda ke cikin halin bukata ba, sai wanda ya aikata laifin da ya hada da dan kudu, wanda ba Musulmi ba, sannan ne kishi da son al'ummar mu zai motsa? Ya kamata mu daina yaudarar  kawukan mu, mu gayawa juna  gaskiya. Wannan matashi, Yunusa Yellow dan uwanmu ne, yayi kuskure ya aikata ba daidai ba, ya kamata a nuna masa kuskurensa, don hakan ya zama izna ga na baya.

Haka kuma, yana da kyau mutane su fahimta, a cikin Shari'ah da kuma jerin tuhumar da aka yi wa wannan matashi, babu inda aka zarge shi da cewar ya tursasawa yarinya bin addinin Musulunci. Balle wasu su rud'a mutane da cewar, ai don ya Musuluntar da ita ne akai masa haka. Wannan Sam ba gaskiya bane, ai a kasar Bayelsa akwai Musulmi 'yan asalin yankin kuma suna rayuwa cikin 'yanci kamar kowane d'a, ballantana kuma batun Musuluntar wannan yarinya, batu ne da kungiyar kare hakkokin Musulmi kamar MURIC tana sane da shi (wanda tunin ma ta fidda matsayan ta akan matashin yayi ba daidai ba) da masu ayyukan da'awa da kula da sabbin Musulunta suna sane. Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.

Yasir Ramadan Gwale 
09-03-2016

Thursday, March 3, 2016

Mayar Da Ese Oruru Gaban Iyayanta Shi Ne Abinda Ya Dace


MAYAR DA ESE ORURU GABAN IYAYANTA SHI NE ABINDA YA DACE

Ni kam banga wani abin tashin hankali dan an mayar da wannan yarinyar gaban iyayanta ba. Iyayan ta mahaifa suna da hakki akanta, dan haka ba wani abin tayar da jijiyar wuya bane dan an mika musu ita. Rayuwar Musulmi cike take da abin koyi, ga duk wanda ya fahimci darussan da ke cikin SULHUL HUDAIBIYYA da mayar da sahabi Abu Jandal Ibn Suhailu Ibn Amri r.a da Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam yayi ga iyayen sa mushrikai a tsakiyar sulhun, na meye nasa zai tayar da hankali dan an ce yarinya ta koma ga iyayanta? 

Addinin Musulunci na Allah ne, kuma da kaddarawarsa ne Subhanahu Wata'ala, komai yake tabbata. Wannan yarinya da ta Musulunta, indai ta Musulunta don Allah da neman yardarsa, Allah zai bata kariya a duk inda take. Haka kuma, a Musulunci komai yana da ka'ida da kuma sharadi. Babu yadda za a ce mutum ya dauko 'yar mutane ya aureta ba tare da sanin iyayanta ko da amincewar shuwagabanni ba kuma ace auren ingantacce ne. 

Ni ina ganin indai ba tsananin zafin kai da kafiya ba, ai wannan lamari mai sauki ne. Tunda yarinya ta koma gaban iyayanta, sai shi yaron yabi hanya sahihiya dan neman aurenta a wajen waliyyanta. Ba yau aka fara yin aure tsakanin mutanan kudu da Arewa ba, ba kuma yau ne Musulmi suka fara auren wanda ba Musulmi ba su musuluntar da su. Jiya naji Malam Aminu Daurawa yayi bayani gamsasshe akan wannan batun. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya. Ya Allah ka cigaba da baiwa addininka kariya.

Yasir Ramadan Gwale 
03-03-2016

Tuesday, March 1, 2016

Ana Fakewa Da Guzuma . . .


ANA FAKEWA DA GUZUMA . . .
Bayan da asirin su Malam Ibrahim Zakzaky ya tonu, kuma Allah ya kama su ta hanyar turo musu da Sayyid Ayatollah Buratai Yusuf ya darkake su darkakewa. Muna fatan abinda ya samesu na wannan jarabawa ya sa masu hankali da fahimta daga cikinsu su fahimci gaskiya su karbeta, su gane turba ta gaskiya su kama Sunnar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam su daina Shiah domin b'ata ce mabayyaniya. Muna fatan abinda ya same su ya zama ukuba anan duniya ga duk masu zagi da aibata Iyalai da abokan Ma'aiki Sallallahu Alaihi Wasallam.
Da yake macizai ne basa gina rami da kansu, sukan fake da guzuma su sari karsana. Su dai sun san karyarsu ta sha karya ba zasu iya fitowa fili su zagi ko Aibata Sayyadi Ayatollah Burtai Yusuf ba, a dan haka sai suka fake da siyasa suna zagin Shugaban kasa sabida da d'an siyasa ne.
Shugaba ko wane iri ne yana da kima da daraja a Musulunci, haka kuma zaginsa fasikanci ne. To amma su dama suje nema dan su yiwa shugaban kasa tatas, su amayar da miyagun maganganun akansa. Dan haka daga zarar wani yayi maganganu na suka ko hamayya da Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari sai su fake da wannan suyi ta zagi da cin mutunci. Alhali kuma su din turbar siyasa Dagutanci ne a wajensu balle muce su shigo fagen siyasa a buga da su.
Hamayya ko kalubalanta a siyasar Demokaradiyyar da Shiah suka kafirta Halal ne. Mun gamsu, mun kuma Amincewa da haka, cewar a kalubalanci Gwamnati kuma ai mata hamayya. Amma su 'yan Shiah abinda suke yi ba haka bane. Suna amfani da damar 'yan hamayya suna cin zarafi da mutuncin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimceta kuma ka bamu ikon binta. Ka nuna mana karya kamar yadda ka nuna Mana Shaianci mu gane karya ne ka bamu ikon kauce mata, kamar yadda muka kaucewa Shiah kuma muke neman tsari da ita. Allah ka taimaki kasarmu ka bamu lafiya da zaman lafiya.
Ya Allah kasa wannan abun da Sayyid Ayatollah Buratai Yusuf yayi shi ne silar kawo karshen duk wani makirci da makida ta 'Yan Shiah gurbatattu lalatattu. Allah ka kare kasarmu daga maguanci da kafircin Shiah.
01-03-2016

Thursday, February 4, 2016

Ziyarar Da Na Kai Cibiyar Addinin Musulunci Ta Al'umma Dake Garin Baltimore


ZIYARAR DA NA KAI CIBIYAR ADDININ MUSULUNCI TA GARIN BALTIMORE

Daga Barack Obama

A yau, cikin ikon Allah na samu zarafin kai ziyara ga katafariyar cibiyar addinin Musulunci ta al'umma dake garin Baltimore. Naga Masallaci inda dubban Musulmi Amerikawa ke haduwa da juna da iyalai dan gudanar da Ibada kamar ko wane irin Masallaci a Amurka, cibiyar waje ne inda dangi da makwabta kan hadu tare da juna suna gudanar da ayyukan Ibada na addini, ga makaranta da yara kan koyi Ilimin addini da zamantakewa, sannan ga sashin bayar da agajin gaggawa, naga mutane da dama da suka bayar da lokacin su kyauta domin aikin hidimtawa al'umma.

Wannan ziyara tawa, wata muhimmiyar dama ce a wajena da zan ganewa ido na yadda Musulmi ke aiwatar da alamuransu na addini, sannan na karfafa musu guiwa wajen taimako da ayyukan sa-kai, sannan kuma na tuna musu cewar Musulmi da yawa sun bayar da gudunmawa mai dumbin yawa a baya domin ciyar da wannan kasar tamu gaba. Kuma wannan ne Babban dalilin da yasa kasarmu abin alfaharinmu ta daukaka a duniya, domin kowanne dan Adam yana da 'yanci da kuma ikon yin addinin sa.

Al'ummatai da dama na Musulmi musamman daga cikin Manoma da 'yan Kasuwa da masu sana'o'i da dama suka taimaka wajen gina tare da bunkasa habakar wannan kasa tamu. Su ne suka taimaka wajen ilmantar mana da 'ya 'yanmu, da yawansu daga masu aikin jiyya da likitoci sun hidimtawa al'umma a wannan kasa ta Amurka. Wasunsu da dama sun samu lambobin Yabo bisa wasu ayyuka da suka na bajinta, ciki kuwa har da karbar lambar Yabo ta zaman lafiya wato Nobel Peace Prize.

Haka kuma, dumbin matasan Musulmi Amurkawa sunyi abubuwa na bajinta da suka Shafi fasaha da kimiyya da kirkire kirkire. Wannan ce ta sanya a koda yaushe mukan hadu domin nuna jinjina da godiya ga irin wadannan matasa, daga cikinsu kuwa, akwai irinsu Mohammed Ali da Kareem Abdul-Jabbar, wanda suka sanya farin ciki da annashuwa da dama a zukatan al'ummarmu. Daga cikin Musulmi a Amurka akwai, 'yan kwana-kwana wanda suke sadaukar da rayuwarsu dan kashe duk wata gobara. Sannan ga kuma 'yan sanda mata da maza wanda suke aiki tukuru dan kasarmu.

Yanzu haka, Musulmi da dama anan Amurka na cikin zullumi da damuwar taka musu hakki ko cin zarafinsu. Iyaye da 'ya 'ya na ta karakaina cikin tsoron taka musu martaba da mutunci, to ya ku ina mai tabbatarwa da duk wani Musulmi a Amurka ba Baltimore kadai ba cewar mu duka Amurkawa ne, kuma mu al'umma daya ne, dan haka duk wanda zai kaiwa Musulmi hari anan to ya sani mu duka gaba dayanmu ya kaiwa hari.
Dan haka, duk wani tsagera ko mara kunya da zai ci zarafin Musulmi akan addinin sa to ya sani ya shirya fada da mu ne baki daya, kuma zamu tsaya kai da fata wajen ganin bamu bari anci zarafin Musulmi a Amurka ba, kawai dan sunce su Musulunci zasu yi. Haka nan kuma, zamu yi fatali da duk wani tsarin siyasa da zai cuzgunawa Musulmi, zamu yi magana da murya daya, ba tare da mun cutar da wani ko wasu al'umma ba akan addinin su. Kuma yana da kyau duknamu mu sani cewar gaba dayanmu daga Allah muke kuma gareshi zamu koma.

A saboda haka, ina amfani da wannan dama na tabbatarwa da dukkan Musulmin Amurka maza da mata cewar, kowannenmu yana da iko da 'yancin da doka ta bashi a matsayinsa na dan kasa. Ku din nan ba wai kawai Musulmi bane ko Amerikawa a'a ku Musulmin Amerika ne, kuna da cikakken 'yancin yin walwal karkashin koyarwar addinin Musulunci. Na gamsu kuma na yadda, al'ummar Musulmi a Amurka mutane ne masu zaman lafiya da fatan Adalci ga kowa.

Wannan shi ne dalilin kawo muku wannan ziyara domin na karfafa muku guiwa, ku sami yakini akan abinda kuka yi Imani da shi, babu mai cin zarafinku sabida addini mu zuba masa ido. Dan haka, idan muka cigaba da kasancewa al'umma daya, zamu sami karfi kuma rauni ba zai riskemu ba. Dole ne kuma mu mutunta bukatun juna. Na gobe, shukran.

Yasir Ramadan Gwale
04-02-2016