OZONE LAYER: WANI BARGO DA ALLAH YA SANYA TSAKANIN RANA DA WANNAN DUNIYA YA YI WAGEGIYAR HUJEWA
Jaridar The Guardina ta kasar Burtaniya ta wallafa Wani binciken masana 'yan kasashen Amurka da Burtaniya kwararru akan sanin kimiyyar sararin samaniya. Shi dai wannan bincike da aka buga a babbar mujallar kimiyya dake taskance binciken kwararru ta bayyana cewar wannan bargon da ake kira ozone layer da Allah ya sanya shi a matsayin kariya tsakanin wannan duniya tamu da kuma rana ya fara hujewa tun kusan shekarun 1980 inda bular ta dinga fadada tun daga wancan lokaci har zuwa yanzu, inda a wannan lokaci aka gano wagegiyar hujewa a jikin ozone layer din. Shi dai wannan bargo da ake kira ozone layer, Allah ya sanya shi ne a sararin samaniyar wannan duniya domin ya zama kariya ga halittun kasa daga sinadaran da suke zubowa daga zafin rana wanda zasu cutar da Bil-Adama ta hanyar sanyawa mutane cututtukan da ke da alaka da fata da kuma sankara.
Allah Buwayi gagara Misali, ya sanya wannan abu tamkar bargo a sararin saman wannan duniya domin ya zama kariya gareta da kuma Bani-Adam. Wannan wagegiyar hujewa da ozone layer tayi, babbar barazana ce ga Bil-Adama. Ita dai wannan ozone layer masana sun fadi cewar samun sauyin da duniya take yi na d'umamar yanayi ne kan sabbaba hujewar ta. D'umamar duniya da ake kira da global warming ya taimaka matuka wajen cigaba da hujewar ozone layer. Dan haka ne a kusan ko da yaushe Majalisar Dinkin Duniya kan shirya manya manyan tarukan karawa juna sani domin a fadakar akan irin hadarin da wannan duniya take ciki a kuma tattauna yadda za a kaucewa d'umamar duniya da kuma sauye sauyen da ake samu na yanayi. Ta hanyar rage yawan hayakin masana'antu da manyan kasashen masu karfin tattalin arziki ke samarwa.
Bayan haka kuma, majalisar dinkin duniya tayi ta bijiro da shirye shirye na daddasa bishiyu wadan da suke taimakawa wajen samar da yanayin da zai taimaka wajen rage wannan barazana da duniya ke fuskanta ta hanyar d'umamar yanayi. Sare dazuka da Bankawa tsirrai wuta na daga cikin abubuwan da suke sabbaba d'umamar yanayi da kuma cigaba da karuwar hujewar ozone layer, wanda hakan kan haifar da kafewar manya da kananan koguna ta hanyar gurgusowar hamada da kuma narkewa tare da zaftarewar daskararriyar kankarar da ke makare kudancin wannan duniya, yayin da a hannu guda hakan ke kara yawan ruwan da ke cikin manyan kogunan wannan duniya, abinda ke haifar da ambaliyar ruwa da kan haifar da asarar muhalli me girman gaske.
Binciken na kwararru ya nuna cewar samun karuwar d'umamar duniya da ake yi shi ne yake haifar da karin bulewar ozone layer, hakan kuma karin barazana ce ga lafiyar Bil-Adama dake rayuwa a wannan duniya musamman sassan duniyar dake fama da yanayin zafin rana. Domin ana samun karin sabbin cututtukan da suke da alaka da fata da kuma sankara fata mai wuya sha'ani. Sabida a dalilin wannan hujewa sinadarin Nitrogen na sulalowa ya gauraya da yanayin wannan duniya, wanda barazana ce mai girman gaske.
Yasir Ramadan Gwale
02-07-2016
No comments:
Post a Comment