SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI
Muhammadu Buhari Shugaban kasa ne kuma Shugaban mu ne, muna so masa Alkhairi kamar yadda muke so wa kanmu. Bama fatan Allah ya azabtar da shi a dalilin hidima da ya yiwa wannan kasa, muna fatan Allah ya sauka ka masa lamura ya bashi lafiya da ikon sauke nauyin da yake kansa. Bama aibata shi ko yi wasa mummunan fata, ko samun sakamako mai muni a karshen Gwamnatinsa, a ko da yaushe fatanmu shi ne, Allah ya saukaka masa lamura, ya aiwatar da ayyukan alkhairi ga wannan kasa tamu. Samun Nasarar sa shi ne cigaban mu, idan yayi Nasara kasarmu ce ta cigaba, idan kasarmu ta cigaba mune muka cigaba.
Bamu gushe ba, muna masa uzuri muna masa kyakkyawar fata. A kullum burin duk wani dan kasa na gari ne a ce kasar mu Nigeria ta samu cigaba fiye da dukkan kasashen Afurka. Ba muda wata kasa da za mu yi alfahari da ita da ta wuce Nigeria, dan haka duk wanda yake rike da ragamar jagorancin ta tilas ai masa biyayya da fatan ya samu Nasara wajen cimma manufofin sa na Alkhairi da yayi nufin wanzar da su a tsakanin wannan al'umma tamu.
Muna da masaniyar cewar babu wani shugaba da yake da hankali da kuma yasan me yake, da zai yiwa al'ummar sa mugunta da yi musu fatan shiga mawuyacin halin ni 'ya su. Kullum Shugabanni na gari buri suke da fatan saukakawa al'umma da kawo musu cigaba mai dorewa. Muna da masaniyar halin da tattalin arzikin kasarmu ya shiga na koma baya, wanda muke fatan ya zama Rahama a gare mu nan ga. Muna kuma fatan shugabanni na yanzu da masu zuwa nan gaba su himmatu wajen Alkinta dukiyar kasa domin amfanin jama'a.
Amma duk da wannan buri da fata da muke yiwa Shugaban kasa, tilas ne mu fito mu nuna damuwar mu akan irin wannan mawuyacin hali da muke ciki. Ba laifi bane, dan wasu ko wani yayi korafin halin da yake ciki na tsanani, dukkan dan kasa yana da 'yanci daidai da kowa wajen bayyana gamsuwa ko rashin ta kan kowace irin Gwamnati. A dan haka muke kira ga Shugaban Kasarmu da yayi duba na tsanaki akan irin mawuyacin halin da al'umma suke ciki, a aiwatar da sauye sauyen da zasu kawo sauki a rayuwar al'umma ba tare da tsanantawa ba.
Hakkin Gwamnati ne kare muradun kasa da na al'umma. Amma kula da Al'umma shi ne akan gaba. Mutane suna cikin hali na yunwa, Masallatai da Majwmi'u sun zama tamkar wajen bara da roko, haka duk wata matattara ta jama'a, ta zama wajen roko. Mutane a cikin galabaita suke rokon abinda zasu ci dan su samu rayuwa. Khalifan Musulunci na biyu Umar Bin Khaddab Allah ya kara yadda a gare shi, yakan zama cikin zullumi da damuwa, akan kada Akuya tayi tuntube ko ta rasa abinda zata ci karkashin jagorancin sa Allah ya tambaye shi. Akuya fa tsoro yake kada Allah ya tambaye shi hakkin ta, sabida tsananin tsoron Allah.
Misalin irin zullumin da Umar Bin Khaddab ya kamata shugabannin su dinga kasancewa, domin samun kubuta a ranar gobe kiyama. Yanzu kai kadai a gidan ka, a tara maka iyalanka su yi maka tambaya akan hakkin su, sai ka shiga cikin tashin hankali da damuwa dan baka san me zasu ce ba. To ina ga tambayar ranar Alkiyama ace al'ummar Nigeria na batun hakkin su kan Shugabanni? Ya kamata Shugaban kasa Muhammadu Buhari yaji tsoron Allah wajen tafiyar da Gwamnatinsa. A saukakawa al'umma mawuyacin hali. Allah ya bamu dacewa.
Yasir Ramadan Gwale
26-08-2016
No comments:
Post a Comment