YI WA YUNUSA YELLOW SHARI'A SHI NE ADALCI
Sau da dama rashin sani da ad'ifar k'abilanci kan hana mutane ganin gaskiya. Mutane da yawa basu fahimci hakikanin abinda ake tuhumar Yunusa Yellow akai ba, dangane da batun Ese Oruru (A'isha). Kawai abinda mafiya yawa suke kallo shi ne batun addini, da kuma shi wanda abin ya faru da shi, wato Musulmi, kuma Bahaushe 'dan Kano ko Arewa. Yawancin mutane a tunaninsu idan Bahaushe Musulmi ya aikata wani laifi, komai muninsa, tilas kafatanin Musulmi su goyi bayansa, musamman ma ace abin ya had'a da wanda ba Musulmi ba. Amma abinda muke kira a koda yaushe shi ne: ayi Adalci, don Musulunci shi ke kira ga yin adalci fiye da komai.
Tunanin wasunmu da yawa, gani suke idan mutanan kudu ko wad'anda ba Musulmi ba sun yi mana rashin adalci, tilas ne mu ma idan mun samu dama mu yi musu rashin adalci. Sun manta cewar addinin Musulunci da muke 'kafafa ko tutiya da shi ya horemu da yin adalci. Saboda Adalci Allah ya azabtar da Bil Adama a dalilin ya cutar da dabba. Annabi (SAW) ya gaya mana cewar, Allah ya azabtar da wata mata a dalilin kyanwa, sabida ta cutar da dabbar!
Wannan batun na Ese Oruru (Aisha) yayi matukar daukan hankalin mutane fiye da batun Abdul Nyass lokacin da yayi kalaman ridda, har wasu tsiraru suna maganganu na rashin kyautawa, a tunaninsu hakan zai nuna cewar su masu kishin Musulunci ne ko kishin Arewa. Wannan ba daidai bane, mutum ya tafka kuskure kawai saboda namu ne Musulmi d'an Arewa mu goyi bayan abinda ya aikata ba tare da tuntubar me addini yace ba kafin ya aikata.
Ga dukkan alamu wannan matashi bai nemi sanin meye addinin Musulunci yace ba akan abinda ya aikata, kafin ya aikata din, wanda a hakan kuma wasu ke ganin tilas kowane Musulmi ya goyi bayansa, haka kuma, bai nemi sanin tanadin dokar kasar nan mai al'ummar da ke da ma'abuta addinai daban daban ba. Abu na farko dai, a tuhumar da ake yiwa wannan matashi, babu batun addini. A cikin jerin tuhumar da akai masa babu inda aka ambaci ana tuhumar sa da cewar ya Musuluntar da wannan yarinya da yardarta ko babu. Batu na addini kam, yarinya ta Musulunta, muna fatan Allah Ya tabbatar da duga-duganta akan turba ta Musulunci, Ya kare ta da dukkan kariyar Sa, Yayi mata garkuwa da dukkan garkuwar Sa.
Bayan haka, wannan matashi, ya tabbatar da cewar shi ya kawo ta Kano daga Bayelsa, kuma ya amince cewar yana tarawa da ita tun a garin su Bayelsa, wannan yasa yarinya ta samu juna biyu mai kimanin watanni biyar. To anan, kawai sai mu goyi bayan barna? Yaro ya dauko yarinya daga garinsu bayan yayi mata ciki, sannan kuma yanzu sai a zo da batun addini a fake don a nemar masa kariya?
Abin mamaki ne, ka ji mutane masu hankali da ilimi suna fadin kalamai marassa kan gado, kamar cewa: wai Mu Musulmi mun ji kunya! Kuma mutanan da aka fi zargin sune Malamai da Sarakuna da Shugabanni wai suna gani anzo an tafi da dan uwanmu za a je wulakanta Musulmi da sauran ire-iren wadannan kalamai masu cike da wauta da rashin sani da tunzura al'umma.
Hakika wadancan kalaman shiririta ne da zafin kai na babu gaira babu dalili. Batun da yake gaban Shari'ah me kuma mutum yake fatan a yi? Ko kuwa, muna so Malamai da Sarakuna su hana a yi masa Shari'ah saboda shi Bahaushe ne dan Kano Musulmi? Dole dai dayan biyu za a yi, ko dai a same shi da laifi ai masa hukunci daidai da abinda ya aikata bisa tanadin dokar kasa, ko kuma a ce ba shi da laifi. Dole dayan biyu ya faru. To me kuma, muke son ayi?
Wasu ma saboda tsabar rudani da rashin sanin makama, cewa suke wai akwai wani Pastor daga kudu da yazo Arewa ya saci 'yayan Musulmi ya kai su kudu zai maida su kiristoci. Abubuwan tambaya ga masu wannan shirbici, sune :
Shin sai yanzu ne kuka samu labarin satar yaran?
Idan ka kwana biyu da masaniya akai, shin a bayan wani mataki ka dauka?
Me ya hana ku kai shi Pastor din zuwa kotu indai batun gaskiya ne?
Kuma ma, shin yaran nan da muka bari a tituna suna watangarirya suna gararambar neman abinda zasu ci, cikin tsummokarai da datti da kazanta da rashin nagartacciyar koyarwar addini, wai sune muke nuna kishin riya akan su? A tsakanin mu ne fa mu Mutanan Arewa Musulmi ake maganar akwai Almajirai sama da Miliyan goma sha biyu (12,000,000), me mu kayi na taimaka musu fita daga halin kunci da suke ciki?
Bamu iya mu taimakawa wanda ke cikin halin bukata ba, sai wanda ya aikata laifin da ya hada da dan kudu, wanda ba Musulmi ba, sannan ne kishi da son al'ummar mu zai motsa? Ya kamata mu daina yaudarar kawukan mu, mu gayawa juna gaskiya. Wannan matashi, Yunusa Yellow dan uwanmu ne, yayi kuskure ya aikata ba daidai ba, ya kamata a nuna masa kuskurensa, don hakan ya zama izna ga na baya.
Haka kuma, yana da kyau mutane su fahimta, a cikin Shari'ah da kuma jerin tuhumar da aka yi wa wannan matashi, babu inda aka zarge shi da cewar ya tursasawa yarinya bin addinin Musulunci. Balle wasu su rud'a mutane da cewar, ai don ya Musuluntar da ita ne akai masa haka. Wannan Sam ba gaskiya bane, ai a kasar Bayelsa akwai Musulmi 'yan asalin yankin kuma suna rayuwa cikin 'yanci kamar kowane d'a, ballantana kuma batun Musuluntar wannan yarinya, batu ne da kungiyar kare hakkokin Musulmi kamar MURIC tana sane da shi (wanda tunin ma ta fidda matsayan ta akan matashin yayi ba daidai ba) da masu ayyukan da'awa da kula da sabbin Musulunta suna sane. Allah ka nuna mana gaskiya ka bamu ikon binta, ka nuna mana karya ka bamu ikon kauce mata.
Yasir Ramadan Gwale
09-03-2016
No comments:
Post a Comment