MARTANI: BOKO HARAM DA GOODLUCK JONATHAN
Daga Ibrahim Abu Mufidat
A rubutun da Malam Yasir Ramadan Gwale yayi jiya Laraba 3 ga watan Yuni, naga mutane da yawa sun kasa fahimtar abun kamar yadda Yasir ya haska mana, da yawa suna maganar an janye sojoji kafin harin da 'yan ta'add a suka kai a kauyen Buni-Yadi dake jihar Yobe, abinda ya kamata masu zargi su sani shin shi Jonathan ne yake kwamandin din su sojojin a wajen? Ba jagororin kusa dasu za a zarga ba? Duk da cewar Shugaban kasa shi ne, shugaban kwamandan askarawan Najeriya baki daya, amma kowa yasan a matsayinsa na shugaba yana magana ne da shugabannin sojoji ba daidaikun kwamandoji ba, haka kuma, muna gani har korar irin wadannan sojojin akeyi a yanzu bayan anyi bincike an gano cewar haka kawai suka dinga guduwa?
Haka Kuma, bari na gayawa muku wani abu da baku sani ba, tun usli sojojin Buni-Yadi tsorata suka yi suka gudu, bayan da suka ga baza su iya tunkarar mayakan Boko Haram ba, saboda karfinsu, sannan anan zan bijiro da wata tambaya, bayan an kai harin Buni-yadi an kai sojoji garin da dama, wata rana Boko Haram suka zo sukai musu kawanya suka kashe su su da 'yan sanda kusan hamsin har kwamandan su bai tsiraba hadda DPO na 'yan sanda gaba daya duk aka kashe su, to shima kenan Jonathan ne yasa akashe sojojin kasarsa?
A Pakistan kungiyar Taliban sun shiga makaranta sun kashe matasa kusan dari biyu (200) su mai yasa ba'a cewa Gwamnati ce take sa a kashe su sai mu a Najeriya? Idan fa kukayi tunani Jonathan yazo ya tarar da Boko Haram ne fa ba wai sai da yazo suka zo ba, mai yasa ba a zargin tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa 'YarAduwa da aka fara abin lokacin sa? Yakamata mu sani babu abin da ya zamto sanadin rashin tazarcen Jonathan kamar Boko Haram, shima a bangarensa na kudancin kasarnan zargi suke cewa 'yan Arewa ne suka kirkiri Boko Haram don a dagula masa lissafin Gwamnatin sa, shi wanne irin mutum ne zayyi sanadin faduwar mulkinsa da kansa? Da sunan Boko Haram!
Duk kishinka da son Buhari, an sha tambayarsa bai taba cewa yana zargin Jonathan da hannun ba, sai dai yace akwai sakaci na daukar matakin da ya dace daga Gwamnati, kuma duk masu irin wannan tunanin abu biyu ke damunsu, (1) Rashin adalci da kuma (2) Jahilci. Na farko, basu san su waye Boko Haram ba, saboda duk duniya tana fama da irin wadannan yan ta'adda, misali ga shi nan a kasar Mali, sai da suka kwace fiye da rabin kasar suka kafa abin da suke kira "daularsu", kuma lokacin har Boko Haram sunje sun tayasu yakin tsawon wata shida sukayi suna rike da fiye da rabin kasar, kuma abin sha'awa cikin sojojin da suka yi kokarin fatattakarsu karkashin jagorancin Faransa, har da sojojin Najeriya, to abin tambya shine, ya za'ayi su yan jihadin Mali su yarda Boko Haram su shiga cikinsu suna fada tare, bayan sun san cewa Jonathan ne yake daukar nauyinsu, kuma ahannun guda ga sojojin da Jonathan ya turo suna kashe su a Mali?
Kuma wani rashin adalci mafi girma da akewa Jonathan shine, idan sojojin Najeriya suka samu nasara kan Boko Haram ko suka hanasu shiga gari, ba a jingina wa Jonatan nasarar, amma idan sun gudu ko an samu nasara akansu sai ace Jonathan ne yace su gudu, kai sai ka dauka kamar sojojin da suke kokari bana Najeriya bane, sai wadan da suke guduwa sune na Najeriya.
Misali 'yan Boko Haram bayan sun kwace garin Goza suka kwashi makaman da basu taba mallaka ba, hankali ya tashi sosai, suka tunkaro Maiduguri gadan gadan, suka fara zuwa bama ko awa biyu basu yi ba suka fatattaki sojojin Bama, saura gari daya ne ya rage musu tsakanin su da Maiduguri, shine Konduga, amma da yake sojojin konduga sun tsaya sun bayar da rayuwarsu, sai da suka yiwa Boko Haram kofar raggo sukai musu barna mai yawan gaske, saboda haushi da fusata da Boko haram suka yi suna ganin gari daya ne ya rage su shiga maiduguri, sukayita zuwa sojojin kondiga na kashesu, arana daya tak, sai da suka je sau biyar, an kashe su sunfi dubu aranar, har aka kama mataimakin shekau wanda hotonsa ya shahara ana cewa shekau din ne, anan kuma aka kashe mai daukar musu video, kuma aka kwace dukkan makaman da suka kwato daga Bama da Goza, amma baza ka taba jin ana jingina irin wannan nasarar ga Jonathan ba, sai ake cewa wai Goza cewa akai sojojin su fita, to shin Konduga fa, yace su fita sunki kenan?
Abinda da yawa daga mutane suka kasa fahimta shi ne, idan akazo ana lissafin nasara wallahi sojojin Najeriya sunfi samun nasara kan Boko Haram, sama da yadda Boko Haram ke samu akansu, don har yanzu Boko Haram burinsu shine su dawo Maiduguri su kwaci Markazin su, abin da yasa suka haukace suke kashe kowa da kowa kenan, haushin rashin nasarar da suke samu shi ne, sai suke bi suna kashe mata da yara da kauyawa, kuma ko kai yanzu akace duk inda kaga mutum wanda ba kai ba ka kashe shi, to kafin a kama ka za a dade, saboda Allah yayiwa dan Adam yawa abayan kasa, da yawa daga wasu kauyuka ma Gwamnati bata san da su ba, mu Najeriya duk inda kaga hanya cikin daji komai duhun dajin to idan kabita sai ka samu mutane suna rayuwa a wajen, to irin wadannan nefa Boko Haram suke gwada nasararsu akansu.
Don haka ni anawa ra'ayin, yadda naga Jonathan ya shirya zabe mafi tsabta kuma ya miqa mulki cikin ruwansanyi, yakamata koda kana masa zargi abaya na rashin son zaman lafiya, to kagane ayanzu haka da yayi shi mai son zaman lafiyane da dorewar Najeriya kasa daya al'umma daya.
Yasir Ramadan Gwale
04-06-2015