YASIR YA TAYA TAKAI, RIBADU, EL-RUFAI, DANKWAMBO MURNAR ZABE
Dazu muka yi waya da Malam Muhammad Salihu Sagir Takai dan takarar Gwamnan mu na PDP a Kano. Na taya shi murnar wannan zabe tare da yi masa godiya bisa kyawawan halayen da ya nuna a yayin wannan zabe. Na shaida wa Malam Salihu cewar mu da muka ce mun ji mun gani akan wannan al'amari na sa, hakika munyi Nasara a wannan zabe, domin mun ji kuma mun gani yadda al'mma ta nuna kauna da soyayya dan Allah ga wannan tafiya, kuma ko kadan bama yin nadama ko da-nasani akan abinda muka kudurce muna yi da gaske, domin cigaban al'umma da addini a jihar Kano ba.
Malam Salihu cikin farin ciki da annashuwa ya shaida min cewa wallahi yana gani kuma yana jin labarin dukkan irin kokarin da muke, ya kuma kara da cewa, shi al'amarin nema irin wannan daman dole daya ne zai samu a cikin masu nema, sannan yace, a duk abinda Allah ya hukunta babu kuskure a ciki. Daga karshe na sake tabbatar masa cewa wannan Nasara domin bamu dauke ta faduwa ba, babu abinda zata sanya mana sai karin tabbata akan manufa tare da kyautatawa Allah zato!
Sannan kuma, ina taya Malam Nuhu Ribadu murnar Nasarar wannan zabe. Hakikanin gaskiya, tunda Ribadu ya shiga wannan takara ban taba jin an zarge shi da rashin cancanta ko dacewa da zama Gwamna ba, illa kawai abinda wasu ke ganin Malam Nuhu Ribadu ya fito a jam'iyyar PDP shi ne dalilin faduwarsa, wanda wannan tunanin kuskure ne, Mulki Allah ke bayar wa, kuma shi ke hukunta wanda ya so dan ya zama Shugaba a lokacin da ya so.
Hakan nan a Jigawa, ina taya Malam Aminu Ibrahim Ringim murnar Nasarar wannan zabe. Na so ace Malam Aminu ya Dora daga inda Gwamna Sule Lamido zai tsaya, amma Allah bai hukunta hakan ba. Ina masa fatan alheri.
A wannan zabe ina mai cike da farin cikin Nasarar da Malam Nasiru el-Rufai ya samu a Kaduna, ina fatan Malam Nasiru zai baiwa al'umma mamaki wajen kawo ayyuka na cigaba wadan ba Kaduna kadai zasu amfana ba har da Arewacin Najeriya.
Haka nan, ina jinjinawa mutanan Gombe, da suka fito suka tsaya wajen tabbatar da zab'in da suke ganin shi ne daidai domin cigaban jiharsu, duk da jafa'I da mugun baki da su Danjima Goje sukaiwa PDP wannan bai hana ta cin zabe a Gombe ba, wannan kuma na kara tabbatar mana da yadda al'umma suka duba cancanta ba inna rududu ba.
Ina fatan alheri ga duk wadan da suka ci zabe ko aka ce sunci zabe, ina fatan alheri ga Gwamnan Kano Gonduje, ina fatan Allah ya basu ikon sauke nauyin alkawarin da aka daukarwa al'umma. Ko da Alkawari ko babu Mulki / Shugabanci amana ne akan duk wanda yake kansa. Idan yayi gaskiya zai tsira kuma zai rabauta har a wajen Allah, wanda duk ya kaucewa gaskiya yabi san zuciya, yabi hanyar zalince to ba shakka shi ne wanda zai Fi kowa takaici a ranar da mulki ba zai amfana masa da komai ba sai nadama mara amfani.
Allah ka bamu alherin da ke cikin wadannan Shekaru hudu da zamu shiga na mulkin Demokaradiyya, ka kare mu daga dukkan wani sharri, musamman na asarar rayuka da dukiya. Allah karaba mu da Boko Haram ka raba mu da barayi, ka raba mu da masu magudin zabe. Allah ka taimaki Najeriya.
Yasir Ramadan Gwale
15-04-2015
No comments:
Post a Comment