HAR YANZU WASHINGTON DA LONDON BASU TAYA BUHARI MURNA BA
Kamar yadda suka sha nanatawa fadar Gwamnatin Amurka dake Washington cewa suna bibiyar halin da Najeriya take ciki, a sakamakon wannan zabe na 2015. Da kansa Shugaba Barack Obama ya fitar da sanarwa ta musamman ga al'Umar Najeriya akan su tsaya suyi zabe tsakanin da Allah ba tare da tashin hankali ba. Alhamdulillah 'yan Najeriya sun ji wannan kira sunyi zabe cikin tsanaki, amma har yanzu Washington tayi gum game da Nasarar da Muhammadu Buhari ya samu.
Haka nan itama fadar Prime Ministan Burtaniya David Cameron dake Lamba 10 Dorning Street tayi shiru, duk da Kiran da Mista Cameron yayi na ayi zabe na gaskiya da adalci, dan tabbatar da Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa.
Wannan dai zabe ne mai cike da adalci a tarihin Demokaradiyyar Najeriya. Muna cike da masaniyar irin Demokaradiyar da Amurka da Burtaniya suka aiwatar a Algeri da ta kawo Abdulaziz Boutoufiqa. Allah ya kiyaye sabon Shugaban Najeriya daga dukkan masu sharri na gida da na waje.
Idan bamu manta ba Muhammadu Buhari yayi alkawarin daga darajar Naira zuwa matsayin damar Amurka, kamar yadda wasu jaridu suka ruwaito. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
Yasir Ramadan Gwale
01-04-2015
No comments:
Post a Comment