ZARATAN CANJI NA HAKIKA
Zanyi amfani da wannan dama wajen kara mika sakon taya murnar Nasarar Gen. Muhammadu Buhari ga mutanan da na kira zaratan canji na hakika, wadan da tun da aka faro wannan tafiya sun tabbata akan manufar su basu yi rani ba kullum kara samun yakini suke akan abinda sukai Imani zai faru. Ba shakka wannan Gwagwarmaya da mu aka farota tun a Shekarar 2003 munyi kuka mun zubar da hawaye a baya sabida rashin Nasara, ashe bamu sani ba hawayen da muka zubar na farin ciki ne, jiya Allah ya tabbatar mana da cewa Mulki da iko nasa ne.
Haka kuma, jiya Allah ya nuna mana cewar komaI na da lokaci, babu wani abu da yake zuwa lokacin sa bai yi ba, wannan tafiya an farota tare da 'yan uwa da yawa, wasu sun sare, wasu sun gajiya, wasu sun fidda tsammani, wasu sun saduda, wasu sun mika wuya, amma zaratan canji sun tabbata akan manufa tare da kyautatawa Allah zato! Alhamdulillah.
Sakon fatan alheri ga zaratan canji irinsu Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi da Kwamared Baban Shareek Gumel da Affan Buba Abuya da Garba Tela Hadejia da Sagir Musbahu Daura Dole da Hamza Ibrahim Baba da Yakubu Muhammad Rigasa da Hamisu Gumel da Hisham Habib da sauransu da dama da suka tabbata akan manufa tare da yakinin cewar hakarsu zata cimma ruwa, Alhamdulillah!
Mutanan da sukai rawa ko suka sare da wadan da sukai ungulu da kan kaza irinsu Jaafar Jaafar da Ibrahim Musa da Fatuhu Mustapha da kuma abokina Sheriff Muhammad Ibrahim Almuhajir wanda kusan kullum ina cike da takaicin sa baya mana kara baya daga kafa amma daga jiya duk na huce. Yayyanmu irinsu Aunty Saratu G. Abdul duk da irin cakulkuli da ake mana amma ya zuwa yanzu munyi tarayya wajen nuna farin ciki da murnar mu.
Abokai da 'yan uwa da muke wannan tafiya tare suma ina taya su murna, Ahmad Abubakar-Dr, Shamsu Abbaty, haka nan irinsu Mansur Manu Soro da Abdulrashid Ahmad da Baba Bala Katsina da Muhammad Aliyu Dutsin-Ma da kullum ake mana gatsune da cakulkuli duk mun taya juna murna da fatan alheri. Ba zan manta da abokan Gwagwarmaya guda biyu da suka riga mu gidan gaskiya ba akan wannan tafiya kamar Dalhatu Mai Chemist Makarfi da Bilyaminu Adanji Abdullahi Allah ya kai Rahama garesu, ina musu bushara da samun sauyin da sukai ta fatan ganin faruwarsa suna raye, cikin Kaddarawarsa Subhanahu Wata'ala ya tabbatar mana bayan sun rigayemu.
Haka nan ina kira ga sabon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya rungumi kowa a tafi tare dan samun Nasarar da aka jima ana tsammani da wadan da suka ji haushi suka daina da wadan da suka fusata suka bar tafiyar da wadan da aka fusata da gangan a yafi kowa a tafi tare dan samar da sabuwar Nigeria. Allah ya yiwa sabon Shugaban kasa jagoranci yayi riko da hannunsa wajen aikata dai dai.
Yasir Ramadan Gwale
01-04-2015
No comments:
Post a Comment