Wednesday, March 18, 2015

Wanda Ya Dogara Ga Allah Ya Rabauta

WANDA YA DOGARA GA ALLAH YA RABAUTA

Wata rana, a Masallaci aka daukewa Alhaji Isyaku Mota yaje Sallar Juma'a. Da ya dawo inda ya aje motar bai ganta ba, aka dudduba ko ina ba'a ganta ba, da ka kalli fuskar Alhaji Isyaku zaka ga alamun sauyi da ke nuna Alamun wani abu ya dan dameshi amma ba me tsanani ba, a lokacin aka fara yi masa adduar ALLAH YA MAIDA ALHERI, kana tunkararsa Murmushi zai yi maka har da dariya yana cewa ba komai tare da cewa Amin ga adduar da kayi masa. A lokacin har wasu suke cewa haba Alhaji Isyaku kamar ba wanda aka daukewa mota ba kai ta dariya, yace to ai a matsayina na Musulmi dole na yadda da kaddara! Kaji magana mai cike da tauhidi.

Daga nan wajen, yaje ya sanarwa da caji-ofis na 'yan sanda dake kusa, ko da za'a kama barawon Motar. Kana taka, Allah na tasa, Shi Allah buwayi ne gagara Misali, mai yin komai a lokacin da yaga dama. A wannan ranar Juma'ar da aka sacewa Alhaji Isyaku Mota, bayan ya koma gida da daddare sai ya tarar da wani abokinsa Dan Majalisa ya aiko masa da kyautar sabuwar Mota. Ya Salam, Al'amarin Ubangiji sai shi. Wallahi Allah maji rokon bawansa ne.

Duk wanda ya dogara ga Allah ya rabauta duniya da lahira. Duk halin da ka shiga na wuya da tsanani kada ka taba yankewa daga samun taimakon Ubangiji, ka shagaltu da kaskantar da kai ga Ubangiji kuma ka kyautatawa Allah zato.

Wannan hali da ake ciki na tsanani da rudani, mafita tana wajen Allah, mu kyautata masa zato, mu nemi taimakonsa da agajinsa, Allah ne yace shi mai ji ne, kuma mai gani ne, tare da haka yace, ku rokeni zan amsa muku. Ya Allah ka bamu mai kyau a duniya ka bamu mai kyau a lahira.

Yasir Ramadan Gwale
17-03-2015

No comments:

Post a Comment