Thursday, March 5, 2015

BOKO HARAM: Makaircin Kasar Tchadi karkashin Kulawar Faransa


BOKO HARAM: MAKIRCIN KASAR TCHADI KARKASHIN KULAWAR FARANSA

Manyan kasashen duniya da ke da kujerarar din-din-din a kwamatin tsaro na majalisar dinkin duniya, kusa sune kanwa uwar gami akan duk wani rikici da ke faruwa a galibin kasashen duniya. Suna amfani da wadannan yake yake da suke faruwa a kasashen duniya, tare da kirkirar kungiyoyi na ta'addanci da daure musu gindi da mara musu baya, sannan a gefe guda kuma su cika duniya da surutun yaki da ta'addnaci,ta hanyar samun cin kasuwar makamai. 

Abu mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne karfi ta fuskar kafafen watsa labarai. Domin da su ne ake yakar tunanin mutanan duniya, a sauya karya ta zama gaskiya, gaskiya kuma ta zama karya. Misalai akan haka shi ne, abinda ke faruwa a kasar Suriya! Har yau manyan kasashen duniya basu kira Bashar Assad da sunan dan ta'adda ba, domin yana yin abinda ake cin moriyarsa. Makamansu na kara samun kasuwa a kasashen da ke kewaye da Suriya, sabida tsoron kwararowar 'yan ta'addan Suriya zuwa kasashensu, sannan a gefe guda bashar Assad ba shida wata damuwa idan kasashen Yamma sun rushe Suriya gaba dayanta inda zai tabbata a matsayin Shugaba, tare da samun kariyar wadannan kasashe.

Da farko anyi wasa da hankulan mutane ainun a Suriya. Aka yi amfani da guguwar sauyi, aka kauda hankulan kasashe da dama daga abinda ya kamata su maida hankali kansa zuwa kare kai daga barazanar guguwar sauyi dake gauraye da 'yan ta'adda. Da farko akwai FREE SYRIAN ARMY suna yakin kwatar 'yancinsu bilhakki da gaskiya, da nufin kawo sauyi da kuma 'yanto Suriyawa daga bakin mulkin zalinci irin na Zurriyar Assad.

Lokacin da tafiya tayi Nisa FSA sun kama hanyar kifar da gwamnatin Assad sai aka yi kutsen kungiyar NUSRA da nufin taimakawa FSA dan yakar Assad, alhali kuwa Sharewa su Albaghadadi hanya akai dan shigowa Suriya su lalata batun yakin da ake yi da Assad, da kuam sanya tsoro a daukacin kasashen gabas ta tsakiya da kuma kasashen Arewaci da gabashin Afrika. Yanzu dai sunci nasarar kassarawa wannan gwagwarmaya a Suriya, ta yadda yanzu duk wasu masu yakar Assad sun narke sun zama ISIS, kuma kaikayi ya koma kan mashekiya, duk mai yakar Assad yanzu kai tsaye za'a kirashi dan ta'adda. 

ISIS kuma na cigaba da sanya tsoro da firgici a zukatan kasashe da yawa musamman wadan da suke da burbushin yake a tattare da su, yanzu dai LIBYA, SURIYA, YEMEN duk sun gama yawo. Wannan wani al'amari ne mai tsayi mai kuma rudani.

A Afrika kasar Faransa ita ce kasar da tayi fice wajen yakar 'yan Ta'addan kudu da Sahara. babu ko tantama cewa Duk wasu kungiyoyin ta'addaanci a Arewacin Afurka da yammaci akwai hannun Faransa a ciki, domin Faransa ita ta san, yadda ta tsuguna ta haifi 'yan ta'adda a MALI kuma ita ta murkushe su. Haka zalika duk wasu kungiyoyin hayaniya da karyar Addini da Shari'ah suna da alaka da Faransa ta kusa ko ta nesa, domin miliyoyin tantan da Allah ya huwacewa kasashen Arewacin Afurka sune ke haskaka fitulun Birnin Paris da gudanar da fadar Champs-Elyees.

Maganar da Shugaban Tchadi, Idriss Devi Ittono yayi na cewar ko dai Shekau ya fito daga inda yake a Boye ko kuma su bayyanawa duniya inda yake. Wannan kai tsaye ya nuna mana cewa duk wannan lokacin da aka dauka, ashe Tchadi na daurewa Boko Haram gindi. Domin shi dai wannan mutum Shekau, tuni Amerika ta bayar da sanarwar Ladar Dalar Amurka 50,000 ga duk wanda ya bayar da bayanan da suka kai ga kama Shekau. Har yau Amerika bata janye wannan sanarwa ba.

Ba shakka, kasar Tchadi ba tada karfi na iya daurewa Boko Haram gindi face ta samu cikakken goyon bayan kasar Faransa tare da samun tallafi da kuma dabaru. ya isa misaali yadda Faransa tayiwa Kasar Afurka Ta Tsakiya da Mali da Nijar da kuma Aljeriya, inda faransa take yiwa wadannan kasashe katsalandan a sha'anin tsaronsu.

Kasar Tchadi da faransa sunyi amfani da sakarci da tsoro irin na Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan​ sukai wakaci ka tashi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Yanzu kuma a halin da ake ciki Faransa da Tchadi sun fahimci cewa matsin lamba ta sanya Shugaban Najeriya daukar tsauraran matakai dan yakar Boko Haram kuma Asiri na gab da tonuwa, shi ne Devi yayi farat da garajen cewar ko Shekau ya fito ko su tona masa Asiri. Daman Ashe sun san inda yake sukai Shakulatun Bangaro suna shigoNajeriya da sojojinsu da nufin yakar Boko Haram suna yiwa Najeriya leken asiri?

Koma ya ake ciki bama fatan gwamnatin najeriya ta ragawa kasar Tchadi akan duk wata maniksa da kutunguila da ta shirya dan daurewa ta'addancin Boko Haram gindi. Faransa kuwa daman taci dubu sai Allah . . . Mun san Allah Fa'alun Lima Yurid ne, zai maganta mana su ta inda basu zata ba. Allah ka taimaki musulunci da musulmi ka rusa kafurci da kafirai. makiyanamu na fili da na boye Allah ka sansu Allah kayi mana ganinsu. Allahumma Rudda Kaiduhum Alaiihim.

YASIR RAMADAN GWALE​
05-03-2015

No comments:

Post a Comment