Wednesday, March 25, 2015

Tsakanin SAK Da CANCANTA


TSAKANIN KALMAR SAK DA CANCANTA

Ya zuwa 'yanzu babu wani dan Najeriya da yake bukatar ayi masa tallar wani dan takara dan ya zabe shi, kowa yasan wanda zai zaba a cikin zuciyarsa (illa kalilan da ana iya sauya musu ra'ayi a lokacin zabe, dan koni ma a zaben da ya gabata 'yan dakikoki kafin Zainab ta jefa kuri'ah na sauya mata ra'ayi, ko ba haka bane Zainab?), sai dai kawai ayi motsi dan karin samun tabbata akan manufa. Akwatu ce zata raba gardama tsakanin masu ra'ayin Sak da kuma cancanta.

Ina ganin idan har dan takara ya san cewa ya cancanta ba zai ji tsoron kalmar Cancanta ba, a ganina masu san bin inna rududu sune ke fatan gamayya. Amma ina ganin babu laifi ga wanda yace zai bi cancanta ko wanda yace Sak ko wanda yace daga sama har kasa, Demokaradiyya ta baiwa kowa damar bin son ra'ayinsa dan samar da Shugabanci karkashin tsarin zabe, dan siyasa dake da katin Jam'iyya idan ya zabi 'yan takarar jam'iyyarsa baiyi laifi ba (a dimokaradiyyance kenan fa), wanda baya jam'iyya yayi wake da shinkafa (ma'ana ya zabi cancanta) shima yana da 'yanci.

Amma ni abinda nayi Imani da shi, shi ne, Allah zai yi kowa tambaya akan yadda ya gudanar da rayuwarsa tudaga kuruciya har tsufa, dan haka zab'e yana daga cikin abinda muka aiwatar a rayuwarmu, kowannemu zai bada bayani akan abinda ya zab'a, wanda duk yayi Sak yana da hujja, wanda yayi daga sama har kasa shima yana da hujja, haka nan wad'an da suke cewa Cancanta zasu zab'a, kowannemu zai bada bayani, ranar da kudi da dangi da sanayya ba zasu amfani kowa ba (Bello Yabo yace, ranar da babu Ricky Tarfa ba Joel Kyari Gadzama), sai abinda kowa yaje da shi, Ya Allah kada ka kama mu akan abinda muka yi bisa jahilci da rashin sani.

Fatanmu Allah ya kaimu ranar zabe lafiya, kowa yasan makomarsa. Lokacin da muna firamare a Gwale, Malam Tahir yake ce mana, ranar Lahira za'a jima a tsaye, hankalin kowa ya tashi, kowa ya k'gauta, buri kawai yake ayi Hisabi yasan makomarsa, wani idan anyi wuta zashi bai sani ba, amma ya k'agu ayi Hisabi inji Malam Tahir a lokacin da yake bamu labarin tashin alkiyama shekaru 21 da suka shude a lokacin muna 'yan firamare a Gwale.

Wata rana aka tambayi Dakta Sani fatawa, shin b'arawon jarabawa me yake ci, Malam yace yaci Haram, tun daga lokacin na tsorata kwarai da gaske, idan barawon jarabawa yaci Haram, barawon zabe kuma me yake ci kenan? Ya Allah ka kare tsokar jikinmu daga bubbuga da Haram, Manzo yace duk tsokar naman da ta ginu da Haram wuta ce tafi cancanta ta babbake ta, Malamai Suka ce da Sayyadinu Umar Allah ya Yarda da shi yaji wannan magana, da yaci wani tsokar nama da bai amintu da halaccinsa ba, sai da ya sa hannu a mak'oshi ya dawo da naman, dan kar wannan yayi sanadiyar teba a jikinsa kuma ya kasance Haram ne.

Ni kam gaskiya kullam ina tsoron gamuwa da Allah, sai dai idan na tuna cewa Allah mai Rahama ne kuma mai jin kai, sai na kyautata masa zato cewa cikin kaddarawarSa da jin kansa zamu samu babban Rabo. Ya Allah kada ka sanya siyasar Demokaradiyya tayi silar halakarmu. Allah ka bamu Shugabanni masu jinkai da tausayi da hakuri da juriya. Fatan Alheri Ga NIGERIA!

Yasir Ramadan Gwale​
25-03-205

No comments:

Post a Comment