Sunday, February 8, 2015

ZABEN 2015: Ido Ba Mudu Ba . . .


NAJERIYA DA ZABEN 2015: IDO BA MUDU BA . . .

Mutane da yawa na ruduwa da yawan Jama'a a wajen kamfe su dauka wanda yafi tara Jama'a shi zai ci zabe. Amma ba nan gizo yake sakar ba a zance na gaskiya, domin a zaben 2011 a yankin Arewa Maso Yamma da yafi kowane yanki yawan masu dauke da katin zabe, akwai sama da mutum miliyan tara da basu yi zaben Shugaban kasa ba, kuma sun karbi katin zabe. Sannan wasu dubbai sunyi zaben amma sun lalata kuri'unsu da su da wanda bai yi zabe ba duk daya. Tambayar ita ce shin ina wadannan mutane suka shiga? Ba irinsu bane suke zuwa su cika wajen taro a lokacin kamfe, amma idan zabe yazo su lafke a gida ba? Wane shiri muke da shi wajen ganin duk wanda yake da katin zabe yayi zabe? 

Muna da yakinin wadancan Miliyan taran ba zasu kuma kwantawa suki fitowa zabe ba? Dubban mutanan da suke lalata kuri'u a lokacin zabe wane shiri muke  da shi wajen ganin cewa a bana basuyi asarar zabe ba? Jihar Katsina a zaben da ya wuce itace tafi kowacce jiha yawan kuri'un da aka lalata (invalid) Wadannan dama wasu na daga cikin batutuwan da ya kamata mu kalla kafin zabe. Misali a zaben da ya gabata sai da na tabbatar Zainab tayi zabe sannan na tura mata katin waya nace tai ta bugawa kawayanta waya tana gaya musu muhimmancin su fito suyi zabe. To bana ma haka zanyi.

Yasir Ramadan Gwale 
08-02-2015

No comments:

Post a Comment