ADALCIN DA BUHARI YA YIWA MR JONATHAN
A cikin tattaunawa da aka yi da dan takarar Shugaban kasa karkashin jam'iyyar Adawa ta APC. An tambayi Muhammadu Buhari ko yana zargin Gwamnatin Najeriya karkashin Mr. Jonathan da daurewa Boko Haram Gindi. GMB ya bada amsa da cewar, baya zargin Gwamnatin Najeriya da hannu wajen balahirar Boko Haram domin babu wasu shaidu da suka tabbatar masa da hannun gwamnati a ciki, yace sai dai yana zargin gwamnati da gazawa da sakaci na wajibin da yake kanta. GMB ya kara da cewar da ana yin abinda ya kamata da ba'a kawo har yanzu wannan rikici na cigaba da wanzuwa ba.
Tambayar da na yiwa kaina ita ce, shin yanzu idan da GMB ne Shugaban kasa wannan balahira ke faruwa karkashn gwamnatinsa, idan AlJAZEERA suka tambayi Femi Fani-Kayode ko Dr. Doyin Okupe cewar shin suna zargin da Hannun Gwamnatin Muhammadu Buhari ko babu! Watakila Amsar da zasu bayar ta bada mamaki.
Adalci shi ne sanya komai a Muhallinsa. Addinin Musulunci ya hori Musulmi da yin Adalci ko da kuwa akan abokan gabarsu ne. Shi yasa ma Bahaushe ke cewa gaskiya ko ta karece a bashi kayarsa. Da Adalci ne ake samun dorewar rayuwa cikin aminci. Rashin Adalci da bashi muhimmanci shi yakai Najeriya halin da take ciki. Mutanan kudu basa yiwa Na Arewa Adalci, Na Arewa basa yiwa na udu Adalci kirista basa yiwa Musulmi Adalci. Kowa kokarin kore kasawa da gazawa yake daga kansa ya maida ita zuwa ga abokin zaman tarayya.
Bamu ce a dauki hakkin wani a bamu ba, ko abinda yake hakkin wani ne a hanashi. Kullum kiranmu shi ne ayi Adalci a zaman tarayya, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa. Mai gaskiya a bashi gaskiyarsa ko da ba'a sansa, Mara gaskiya a bashi rashin gaskiyarsa sannan ayi masa nasiha.
Ina da yakinin Adalci zai zaunar da al'ummar Musulmi da Kirista Bahaushe da bayerabe da Inyamuri lafiya, cikin aminci ba tare da fargabar yankan baya, kyashi, hassada, kiyayya, gaba ko danne hakki ba. Idan kowa ya samu Nutsuwar cewar za'ayi masa adalci a zaman tarayya ba Shakka za'a zauna lafiya.
Amma a cikin irin halin da muke ciki, an raba tsakanin al'ummar Najeriya, ta yadda kowa yana jin nasa ne kadai zai iya yi masa adalci, indai ba nasa bane, to ba shida cikakkiyar nutsuwar cewa za'a biya masa bukatunsa na wajibi. Fatana Allah ya azurta wannan kasa tamu da Shugabanni masu Adalci da tsoron Allah.
YASIR RAMADAN GWALE
09-02-2015
No comments:
Post a Comment