Sunday, February 8, 2015

ZABEN 2015: Duniya Ta Sanyawa Najeriya Ido


ZABEN 2015: DUNIYA TA SAWA NAJERIYA IDO

A safiyar yau Sakataren harkokin wajen Amerika Sen. John Kerry​ ya fitar da wata sanarwa da take nuna rashin amincewar Washington akan dage babban zaben kasa da hukumar zabe karkashin jagorancin Attahiru Jega tayi. Sanarwar tayi Allah-wadai da wannan yanayi da ya bayar da damar tura wannan zabe zuwa wani lokaci na gaba. Da farko dai, muna Allah-wadai da tsoma bakin Amerika a cikin harkokin cikin gida da suka shafi Najeriya. Najeriya kasa mai 'yanci da bata karkashin mulkin kowacce kasa a duniya. Bai kamata Amerika ta dinga yin katsa-landan a harkokin cikin gidan Najeriya da basu shafeta ba.

Dan gane da batun dage zabe kuwa, ba shakka ina daya daga cikin mutanan da suke ta fatan ganin wannan zaben yazo ya wuce dan mu san wace irin makoma ke garemu, hakika wannan zabe yana cikin zukatan duk wani dan najeriya a ko ina yake, wannan ta sanya yanzu 'yan najeriya ba suda wata hira da ta wuce batun zabe. Cikin kaddarawarsa, Subhanahu Wata'ala, rade-radin da ya kunno kai cewa za'a dage wannan zabe daga ainihin lokacin da aka tsara zuwa wani lokacin na daban ya tabbata.

Shugaban hukumar zabe ya bayar da sanarwar dage Zabe zuwa wani sabon lokaci a watan maris mai zuwa. Ba shakka, kuma nayi Imani da cewa Attahiru Jega mutumin kirki ne da ba za'a hada kai da shi a cuci al'ummah ba, na kyautata masa wannan zaton. Dan haka wannan dage zabe ba zai zama wani abin tashin hankali ko fusata ba, tunda Jega ya tabbatarwa da duniya cewar kamar yadda kundin tsarin Mulki ya tanada 29 ga watan mayu dole a samu sauyin Gwamnati.

Wannan sauyi da yazo mana afujajan mun karbeshi cikin kaddararawar Allah. Manzon Allah yace, Madallah da al'amarin mumini, idan abinda yake so ya samu sai yayiwa Allah godiya, tare da haka sai Allah ya sanyawa abin alkhairi a gareshi, idan kuma akasinsa aka samu sai ya maida komai zuwa ga Allah yayi hakuri, sai Allah ya sanya masa alkhairi kuma ya bashi ladan hakuri.

Muna fatan Allah ya sa wannan abin da ya faru ya kasance alkhairi ne, kuma adduaata ita ce, Allah yasa ayi zabe lafiya a gama lafiya. Domin yanzu haka duniya ta sanyawa Najeriya ido wajen ganin anyi zabe mai tsabta. Jega kuma muna yi masa adduar fatan alheri Allah ya bashi ikon gudanar da wannan zabe cikin Nasara, Allah kayi masa jagoranci wajen tabbatar da gaskiya da aiki da ita a wannan zaben.

YASIR RAMADAN GWALE​ 
08-02-2015

No comments:

Post a Comment