MALAM NUHU RIBADU NA GAB DA SUBUCEWA APC
* APC na matsa lamba ga Ribadu kada ya fita.
* PDP ta tabbatarwa da Ribadu takarar Gwamna
* Fadar Shugaban kasa tayi alkawarin bashi goyon baya

Jaridar The Nation Newspaper
ta ruwaito cewar, shugabancin jam'iyyar Hamayya ta APC na yin dukkan
mai yuwuwa wajen ganin tsohon dantakarar Shugaban kasa a rusashshiyar
jam'iyyar ACN, kuma jigo a cikin jam'iyyar APC, tsohon shugaban hukumar
yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati Malam Nuhu Ribadu bai sauya sheka zuwa PDP ba.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewar tuni Malam Nuhu Ribadu ya gama dukkan shirye-shiryen tsallakawa PDP daga APC, wasu masharhanta na cewar daman can zaman doya da manja ake yi tsakanin Ribadu da shugabancin jam'iyyar APC.
Haka kuma, akwai alamun da suke nuna cewa daga yau Alhamis zuwa gobe juma'a ake sa ran Malam Nuhu Ribadu zai bayyana sauya shekarsa daga APC zuwa PDP inda ake sa ran zai yi takarar Gwamna a zaben da za'ai na cike gurbin Murtala Nyako a Oktoban nan mai zuwa.
Bayan wannan sanarwa ne kuma ake sa ran Malam Nuhu Ribadu da tawagar yakin neman zabensa da masu yi masa fatan alheri zasu gudanar da wani kwarya-kwaryar gangami a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Sannan kuma, a nasu bangaren shugabannin jam'iyyar APC sunyi wani zama na gaggawa da shi Malama Nuhu Ribadu domin rarrashinsa akan ya yiwa Allah ya ajiye batun komawa PDP da yake shirin yi acewarsu hakan wani komabaya ne ga jam'iyar.
Wata majiyar kuma ta tabbatarwa da The Nation cewar shugabancin jam'iyyar PDP reshen jihar Adamawa ya nuna cikakken goyon bayansa ga takarar Malam Nuhu Ribadu a PDP din duk kuwa da wasu rahotanni da ke nuna cewa masu hankoron yin takarar a PDP na kokarin yiwa Malam Nuhu Ribadu fancale a yunkurinsa na shigowa PDP din, a yayin da Manyan masu ruwa da tsaki karkashin jagorancin tsohon Gwamna Boni Haruna suka nuna amincewa da Ridabu a matsayin sabon dan PDP kuma dantakarar Gwamna.
Itama a nata bangaren fadar shugaban kasa tuni ta nuna farinciki da amsa kiraye-kirayen da aka yiwa Malam Nuhu Ribadu na yin takarar karkashin PDP, sun kuma nuna baiwa Ribadu dukkan goyon bayan da ya dace wajen ganin ya samu nasarar zama Gwamnan Adamawa a zaben da za'a yi nan gaba.
Yasir Ramadan Gwale
14-08-2014

No comments:
Post a Comment