Tuesday, August 5, 2014

GHAZZA: Abin Boye Yana Fitowa Fili A Burtaniya

Lady Warsi tare da David Cameron

GHAZZA: ABIN BOYE YANA FITOWA FILI A BURTANIYA

Babbar Ma'aikaciya a ofishin da ke kula da harkokin wajen kasar Burtaniya Malama Lady Warsi ta ajiye mukaminta na Minista a sakamakon yadda taga Gwamnatin da Praminista David Cameron ke jagoranta na nuna goyon bayanta ga irin zalincin da Israela ta ke yi a Ghazza. Lady Warsi wadda ita ce Musulma kwaya daya tal da take aiki tare da Piraminista Cameron a gwamnatin, ta rubuta a shafinta na Twitter kamar yadda BBC suka ruwaito tana cewa, "cikin matukar Nadama a wannan safiya nake bayyanawa Shugaba Cameron tare da gabatar masa da takardar barin aiki da na yi, ba zan taba goyon bayan duk wani tsari na zalinci ba akan Ghazza" a cewar Lady Warsi.

A nasa bangaren Piraminista David Cameron ya yabawa Lady Warsi a iya tsawon lokacin da ta yi aiki da shi, ya kuma yi mata godiya. Sai dai Cameron din yayi wasu kalamai da suke nuna borin kunya, inda yace "Ina bukatar ganin an tsagaita wuta a Ghazza ba tare da gindaya wasu sharudda ba". Wannan murabus na Lady Warsi ya samu goyon bayan jam'iyyar Adawa ta Labour tare da yaba mata bisa yadda ta nuna kishi da jajircewa.

A wani labarin mai kama da wannan itama BBC ta kori Ma'aikacinta Mai dauko mata Rahoto daga yankin na Zirin Ghazza Mista Jeremy Bowen a sakamakon rahoton da ya aiko cewa shi baiga ta inda 'yan Hamas suke amfani da fararen hula dan samun mafaka da su ba, zargin da Israela ta jima tana yi. Sai dai ita Israela ta nuna rashin jin dadinta a wadannan kalamai na Jeremy Bowen inda ta bukaci BBC da ta dauke Mista Bowen daga Ghazza nan take kuma BBc suka cika wannan umarni na Israela. Allah yana tare da mai gaskiya.

YASIR RAMADAN GWALE
05-08-2014

No comments:

Post a Comment