ADAMAWA: TAKARAR NUHU RIBADU NA KARA SAMUN TAGOMASHI
A jiya asabar ne a Yola babban birnin jihar Adamawa aka busa kusumburwar yakin neman zaben Malam Nuhu Ribadu
a matsayin dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar PDP mai alamar
lema. Tun da sanyi safiyar asabar din ne dubun-dubatar matasa suka yi
fitar farin dango zuwa tashar jirgin saman jihar Adamawa domin marabtar
bakon da ake tsumai. Bayan da matasa suka sarraha aka yi wokokin tsuma
zukata da nuna biyayya da goyon bayan takarar Malam Nuhu Ribadu ne, can bayan zawali bakon ya sauka.
Gurin ya barke da sowwa da murna yayin da matasa suka yi adabo da Malam
Nuhu Ribadu. Ribadu ya fito daga cikin jirgi sanye da fararen kaya,
dinkin babbar riga da jamfa da hula zanna mai launin fari da ruwan omo
da ratsin ja da baki. Cikin farin ciki da annashuwa Malam Nuhu Ribadu ya
kasa rufe bakinsa dan nuna gamsuwa da abinda ya gani na soyayya da
kauna da dubban mutane suka nuna masa, nan ya dinga daga hannu yana
gaishesu yana musu addu'ar Allah ya muku albarka, tare da maimaita
Alhamdulillah, yana mai cike da sakankancewa da al'amarin ubangiji.
Daga nan ne tawagar Malam Nuhu Ribadu tayi jerin gwano zuwa wajen da aka shirya shi musamman dan zuwan Bakon Alkhairi, kuma Gwamna Mai Jiran Gado ISA. Bayan isar tawagar ne kuma shi mai gayya mai aiki Malam Nuhu Ribadu ya jagoranci bude katafariyar sakatariyar yakin neman zabensa da aka samar.
Malam Nuhu Ribadu yayi kalamai masu ratsa zukata da mika lamuransa ga Allah a yayin wannan taro, ya kuma yi kira ga al'ummar jiharsa da ya jima yana nuna musu kauna da cewa su kasance masu da'a da biyayya da kuma sanya Allah a cikin dukkan al'amuransu, ya kuma yi addu'ar Allah ya dafawa wannan takara da al'umma suka nuna sha'awarsu akai.
Yasir Ramadan Gwale
24-08-2014

No comments:
Post a Comment