PDP DA APC
Ina fatan duk wanda zai yi magana akan wannan rubutu to ya tabbata ya
kai karshensa. Ina farawa da sunan Allah mai kowa mai komai. Kamar yadda
na bude da harafan PDP da APC to zanyi batuna ne kacokam akansu da kuma
halayenmu. Kasancewar yanzu siyasar Najeriya na tafiya ne tsakanin APC
da PDP, haka kuma al'ummar Najeriya sun kasu gida biyu ko dai masu nuna
goyon baya ga PDP ko kuma APC.
Ya 'yan uwa yana da kyau mu fahimci cewa ita Jam'iyyar siyasa wani
dandamali ne da ake takawa a hau dan kaiwa ga dare madafun iko, dan
shugabantar al'umma. A bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, babu
wani mutum da zai iya zama shugaba a kowanne mataki na wakilci ko
zartarwa sai ya biyo ta kwararon jam'iyya PDP ce ko APC ko wata daban.
Sau da dama ni da kai da sauran al'umma mukan yi kuskuren fahimtar
ma'anar siysar jam'iyya, da kuma kuskurewa fahimtar ma'anar ita kanta
siyasa. Da dama sukan dauka tilas ne siyasa ta zama gaba tsakanin mutnan
da suke jam'iyyu mabanbanta. Watakila yau da Buhari zai gayyaci
Shugaban kasa su ci abincin rana tare su biyu, sai dukansu su zama abin
zargi a wajen magoya bayansu.
Ya isa abin misali a ce maka
Atiku Abubakar wanda jigo ne a APC, kuma yake taimaka mata ta kowanne
fanni dan samun nasararta amma ace dansa na cikinsa yana auren diyar
Ahmed Adamu Mu'azu wanda shi ne Shugaban jam'iyyar PDP na kasa baki
daya! Jam'iyya ta bambanta su amma kuma su din sirikan juna ne, Shin
wannan ba zai zama darasi na kurkusa da zamu dauka ba?
Gwamnan
Bauchi Isa Yuguda yana ANPP ya auri diyar shugaban kasa marigayi Malam
Umaru Musa YarAdua. Shin idan siyasar jam'iyya gaba ce Shugaban Kasa zai
aurawa dan ANPP 'yarsa ta cikinsa? Haka fa Tsohon Gwamnan Zamfara
Mahmuda Aliyu Shinkafi yana ANPP ya auri diyar tsohon Shugaban kasa
Ibrahim Badamasi Babangida wanda jigo ne, kai kusan shi ne babban Fulogi
a PDP suka zama surikan juna.
Ka koma baya kaga yadda AVM
Mukhtar Mohammed yana ANPP kuma dan-gani kashenin General Buhari amma
kuma matarsa da yake Aure tana PDP tana takarar Sanata, wannan kuma bai
kawo komai a cikin auratayyarsu ba sai karuwar dankon zumunci da soyayya
da kaunar juna. A kwara yanzu Bukola Saraki na APC kanwarsa uwa daya
uba daya ita kuma tana PDP, hakan kuma bai haifar da komai a alakar
dangantaka tsakaninsu ba, sai zumunci da kaunar juna.
Amma sai
mu da muke na can kasa, da muka fi su iya fahimtar siyasa muke zaton
cewar dolenmu mu zama abokan gabar juma matukar jam'iyyunmu sun
bambanta, mu dinga jifan juna da miyagun kalmomi da munana kalamai? Ya
kamata mu nutsu muyi hankali musan inda yake mana ciwo. Da PDP da APC
dukkan su jam'iyyu ne da babu wadda aka gina manufofinta dan fita
wa'azin maguzawa, babu wacce aka gina dan kare Addinin Musulunci ko kare
muradun Musulmi.
Yana da kyau mu fahimci cewar mu da muke
nunawa juna Adawa maras kyau mara kan gado saboda bambancin jam'iyya sai
mu zama abin dariya a wajen wadan da muke gani su ne shugabanni idan
mun gansu tare da juna a wajen taruka suna taya juna murna. Sau nawa
muke ganin hotunan Buhari da Obasanjo a taruka suna musabiha suna yiwa
juna dariya? Bayan kuma dukkanmu mun san cewar anyi takara tsakanin Obj
da Buhari a 2003 da 2007 har aka je kotu dan kwatar hakki? Shin Obasanjo
da Buhari basa kishinmu ne suke musabiha da juna a gaban kyamara?
A zaben 2011 da akayi takara tsakanin Goodluck Jonathan da Muhammadu
Buhari, babu wani abu na nau'in rashin jin dadi da bai faru ba, anyiwa
mutane da dama ta'adi da sunan goyon bayan wadannan mutane. Amma a bikin
cikar Najeriya shekaru 100 aka nuna Shugaban kasa Jonathan yana
ratayawa Buhari lambar girma a wuya dukkansu suna yiwa juna dariya,
karshe kuma suka yi musabiha.
Dukkan wadannan abubuwa da suka
faruwa kuma suke cigaba da faruwa ba zasu zamar mana darasi ba, sai mun
dauki layin raba tsakanin junanmu? Duk wata baragada da hayagaga da
mutum zai yi dan nuna goyon baya ko Adawa da sunan jam'iyya mutanan
cikin jam'iyyar kuma abokan juna ne, sai yaya?!
Meye Kwankwaso
bai yiwa Buhari ba a lokacin zaben 2003? Amma yau da Buhari da Kwankwaso
suna cikin jam'iyya daya. Wane irin abu ne bai faru ba tsakanin
Bafarawa da Wamako ba, amma sai da suka hada jam'iyya daya, kuma suka yi
magana da juna. Duk wadannan jagororin siyasar muna jin mu da muke
mabiya mun fisu fahimtar siyasa ne?
Yau ina Najatu Mohammed ina
Buhari? Wace irin magana ce Najatu bata gayawa mutane akan Buhari ba,
amma yau sun raba gari da Buhari jam'iyyarta daban jam'iyyar Buhari
daban, ya kamata mu fahimci maganar da ake cewa Siyasa ba tada
tabbataccen masoyi kuma bata da tabbataccen makiyi.
Ya kamata
mu sani cewa idan hankali ya bata, to, hankali ne yake nemo shi.
Dukkanmu fatan Allah ya bamu Shugabanni nagari muke yi, kuma kowa yasan
ba Mala'iku za'a turo mana ba, kuma ba wani mutum za'a sauko mana da shi
daga sama ba ya zama shugabanmu, daga cikinmu Shugaban zai fito. Tayaya
muke fatan samun kyautatuwar rayuwa alhali mu bamu mutunta kanmu ba
kuma bamu mutunta wadan da muke fatan nan gaba su zama Shugabanni ba?
Ya zama dole mu fahimci tsantsar gaskiya dangane da siyasar Najeriya da
kuma siyasar Jam'iyyar PDP da APC. Babu wata jam'iyya da aka bude
kundinta da Bisimillah. Babu kuma wata jam'iyya da ake aiwatar da
manufofinta a duk jihar da take Mulki. Da gwamnatin Akwa Ibom da
Gwamnatin Yobe ba suda wani bambanci wajen tafiyar da jagoranci, duk
abinda Gwamna yake so shi ake aiwatarwa ko ya dace da jam'iyya ko bai
dace ba, haka abin yake a ko ina a Najeriya.
Dan haka, mune
zamu cigaba da kasancewa a wahale wasu na can a kwance suna amfanuwa da
jahilcinmu gidadancinmu na kin fahimtar ma'anar ita kanta rayuwarmu da
kuma siyasa da hamayyar siyasa.
Zamu zama Azzalumai na gaske
idan jam'iyyar Siyasa ta zama ita ce ma'aunin mutanan kirki da na banza a
wajenmu. Mutum yayi duk abinda yaga dama a PDP amma daga randa ya shiga
APC sai a yi masa kallon shi tsarkakakke ne. Shi kenan mun zama
gidadawa na karfi da yaji?
Masu mulki sai su handame, su tara,
su kuntata ga son kai da wawura. Sai ma kaga wata tsana ko kiyayya ta
shiga tsakanin su da al'umma. Ba tausayi ba hange ba tuna makoma ba
waiwaye da daukan izina daga darassin rayuwar su ta baya ko rayuwar wani
da suka sani.
Ta kowanne fanni ka dubamu babu gaskiya a
lamuranmu! Kalli yadda malamai suke a yanzu, tarbiyyar su, kalmomin su,
alakar su da juna. Mu dubi yadda kowa yake neman ya shahara ko a san
shi, duba tsakanin su da mahukumta da masu dukiya.
Ga karanci
ibada, ana wa'azi ba ikhlasi. Kowa na tsoron fadin gaskiya a zarge shi,
mabiya sun zama sai abinda suke so shi Malamin zai fada, shi kuma ba zai
taba fadin abinda zai saba musu ba dan kar su watse masa. Wannan ita ce
ta jawo akai shiru akan matsalar Boko Haram har ta zamo ala kakai,
shi'a ke ta yaduwa, ana tsoron bayyana ra'ayin siyasa don mabiya! Ila
aina tazahabun?
Yan bokon mu sukayi watsi da ilimin Allah, suka
kasa ciyar mana kasa gaba da nasu ilimin, suka kawo dabarun son duniya,
ga annobar cin rashawa ga dukkan nau'i na cin bulus ana karya hula ana
dogon turanci na gaza gani da yawan suka da iya kalubale a rubuce da
kuma baki amma ba kere kere ko wani ci gaban zamani daga masanan mu.
Suka jawo mana tasirin jita jita ta hanyar radio da jaridu, suka koyawa
mutane zama cima zaune duk akayi watsi da sana'oin gado, kowa ya nade
hannu yana san cin na banza.
Sarakuna suka manta gadon iyayen
su, suka ki karatun addini, suka fi damuwa da masha'a da kade kade da
bushe bushe da nadin sarautu, ana ta hawa dawakai ana bushasha, har ta
kai kusan kullum Kimar su raguwa ta ke yi. Duk sarkin daya mutu na
bayansa zai zo ya gazashi karbuwa, ba kwarjini, ba wani girma na darajar
mulki.
Al'umma kuma ta zabi zaman kara zube da gadi da son kai
da kan-jiki. Maula da kwadayi da tumasanci ya zama babba da yaro, roko
ya zamo maza da mata ba sai wadanda suka gada ba. Rashin ilimi ya jawo
ana addini da rayuwa da ka. Kowa yana da ta cewa a addini, wanda ya san
addini da wanda bai sani ba.
Gamu da rashin bin doka da sabawa
ka'ida ta addini da ta hukuma. Rashin tarbiyyar addini tasa kowa ba
wanda yake rusunawa sai mai bashi. Rayuwa ta koma kowa a fusace kamar
ana filin daga, bamu dana gaba don malunta ko mulki wadda keda tasirin
yasa ko ya hana mu. Aka daina yiwa juna zaton alheri, kowa sai ka bi
nasa ya gode maka. Wallahi duk wannan jahilncin addini ne ya samu ciki.
Dubi yadda ake sanar da ganin wata dubbai suyi tawaye amma ji yadda aka
yada labarin wanka da gishiri don maganin ebola gida kadan ne ba suyi
ba.
Duk wadannan abubuwa da ke faruwa ba zasu zama izna a
garemu ba? Sai mu koma jifan juna da miyagun kalmomi da kazafi da
karairayi kawai saboda bambancin ra'ayin siyasar jam'iyya! Wace irin
al'umma ce mu? Allah ka nuna mana gaskiya mu fahimci gaskiya ce ka bamu
ikon binta ka nuna mana karya mu fahimceta ka bamu ikon kauce mata.
YASIR RAMADAN GWALE
25-08-2014