DAN
SANDA: Wata rana wani mutum ya kirani a waya yace akwai kaninsa an tsare
shi a caji ofis na 'yan sanda, naje na sa hannu a bada belinsa. Banyi
musu ba na tafi caji ofis din da ya yi min kwatance, naje na sami kanin
nasa a gaban 'yan sanda, na tambayi abinda ya faru. Sai ya shaidamin
cewa ya samu kwangila ne a wata karamar hukuma a Jigawa, dan haka ya
karbi kayan wani Inyamuri na Miliyan 3, gashi
har yanzu kudinsa basu fito ba, shi ne, shi kuma Inyamuri ya kawo kara
wajen 'yan sanda, amma mun yi yarjejeniya zan kawo kudin wajen 'yan
sanda nan da sati 2, dan haka yanzu kawai hannu zaka sa su bada belina.
Aka nuna min takarda na rattaba hannu, mutumin ya dauko ni a motarsa
muka rankaya wajen wansa da ya turani kar bar beli. Bayan kamar kwana 10
mutumin ya kirani a waya, cewa ya samu wani abu, dan haka zai zo ya
daukeni mu kaiwa 'yan sanda, ya zo muka rankaya, kafin mu shiga caji
ofis ya kawo wani dunkuli yace ga wannan a sayawa su Zainab burodi, nace
haba har da nima, na karba na soke. Muna shiga wajen 'yan sanda aka
dauko fayil ya zaro kudi dubu dari biyar ya mikawa DPO yace ga abinda ya
samu, ya nemi a kara masa sati biyu nan gaba dan ya biya sauran, ya
kawo wani abu ya sinnawa DPO. Abin mamaki a gabanmu kafin mu tafi aka
rabe dubu dari biyar din Inyamuri. Mukai Sallama muka tafi! A mota nace
masa to shi Inyamuri idan yazo karbar kudinsa fa? Sai yace, Uban Wa Ya
Sa Shi Ya Zo Wajen 'Yan Sanda?
Yasir Ramadan Gwale
08-03-2014
No comments:
Post a Comment