A
BAYA: Lokacin da aka kashe mana Malam Jaafar a Masallacin Juma'a na Dorayi a Kano, ba
jimawa wasu mutane suka bulla a kusa da kauyen Galinja dake bayan garin
Panshekara suka dinga ta'addanci, suna kisa baji ba gani, wani ya
shaidamin cewa yaga gawarwakin sojojin Najeriya da aka dinga lodawa a
akorikura ana ficewa da su daga Panshekara, haka aka wayi gari mutanan
nan sun sulale ba'a san ta inda suka fice ba su da
makamansu.
Amma dai rashin gaskiyar Gwamnatin Najeriya ya sanya bama
saurin gasgata duk abinda ta fada. Ni na fahimci jami'an tsaron Najeriya
har yanzu basu fahimci cewa duniya ba a tsaye take ba, shi yasa ko
Makamin Nukiliya ka dauko a motarka indai ba acikin but ka saka shi ba,
to zaka iya sada shi da duk inda kake so, ba tare da fargaba ba. Na kuma
fahimci al'amarin Boko Haram ba zai iya karewa nan kusa ba, domin ana
yiwa lamarin kallo ta madubin siyasa, ana kuma bugun jaki ana barin
taiki ana kallo kulba na barna ana cewa jaba ce. Amma dai nayi Imani
babu abinda ya gagari Allah.
Yasir Ramadan Gwale
05-03-2014
No comments:
Post a Comment