DAN
SANDA II: Muna zaune wani Dan Sanda yake baiwa wani abokina labari cewa
shi fa barin aikin zai yi, duk da cewa sabon dauka ne yana Murnar shiga
aikin. Aka ce da shi lafiya? Sai ya ce, wata rana wani mutum ya aiki
yaronsa ya kai masa Mota wani kango inda yake ajiye mota, wajen kusa da
caji Ofis ne, yaran ya je aje motar da daddare, bayan da ya fito ne sai
'yan Sanda suka kama shi, suka ce barawa
ne, ya yi musu bayanin cewar ai suna gani ya shiga da motar ajewa ya yi
ba dauka ya zo yi ba. Suka tsare shi, shiru-shiru Oga mai mota yana
jiran yaro ya kai masa mukullinsa, bai dawo ba, kuma ga dare yana
tsalawa sawu yana daukewa, can dai ya biyo baya, da yaga babu alamunsa
sai ya je wajen 'yan sanda yake basu bayanin cewar ya aiki yaransa da
mota ya ajiye amma bai dawo ba. Ogan 'yan sandan ya tambayi wani dan
sanda a kusa da shi, ya ce, ko shi ne wanda muka kama da MAKAMAI? Sai ya
ce fito da shi, ana fito da Yaran, mutumin ya ganshi, sai Ogan 'yan
Sanda ya tambayi sabon Dan Sandan da yake baiwa abokina labari, cewa ba
shi kuka kama da Makami ba? Sai ya ce, gaskiya ba mu kama shi da komai
ba, nan take Ogan 'yan sanda ya ce Oh Sorry! Ashe ba shi bane, yana
gayawa mai motar. Aka sallameshi ya tafi. Suna fita, Ogan 'yan sanda ya
Kwarfi kafafun wannan dan sanda da ya karyata shi, ya zazzage shi, ya ce
idan ka kuma karyata DAN SANDA sai ka yabawa aya zakinta. Aka ce dole a
yi masa hukuncin karyatawa da ya yi.
Dan Sandan, ya ce shi fa aikin ya fita daga ransa, yana ganin barin aikin zai yi gaba daya. Dan Sanda!
Dan Sandan, ya ce shi fa aikin ya fita daga ransa, yana ganin barin aikin zai yi gaba daya. Dan Sanda!
Yasir Ramadan Gwale
11-03-2014
No comments:
Post a Comment