Monday, March 31, 2014

Abinda Ya Faru A Funtua, Ya Taba Faruwa A Kano


ABINDA YA FARU A FUNTUA

Kamar yadda na ji labari tun jiya, cewa wata makaranta mai suna IDEAL an samu wani Malami ya yi wasu tambayoyinJarabawa da suka hargitsa daliban makarantar, har yau litinin muka ji cewa hautsuni ya tashi a garin funtuwar sakamakon wadancan tambayoyin jarabawa da aka ce wani KWAFA dan hidimar kasa wanda Kabila ne ya yi su. Ga dai tambayoyin kamar haka:

"Mohammed is mentally unbalanced, So you should be ___________ of his behaviour. (a) tolerant (b) unintelligible (c) indefinite (d) illegible

13. Aminatu was ________ and it was not clear to me what she meant. (a) unknown (b) unintelligible (c) indefinite (d) illegible."

Wadannan su ne tambayoyin da aka ce sun fitowa yara a cikin jarabawa. Ina ganin akan wannan tambaya, akwai abu na farko da ya kamata a ce anyi. Ya akamata ace kwamatin tsara Jarabawa (Exams Committee) Na makarantar ya duba tambayoyin kafin sakinsu, domin gudun kar su haifar da rashin fahimta.

Sannan abinda ya kamata ayi a wannan lamari shi ne, bincike ba daukar doka a hannu ba. Yana da kyau a samu shi malamin da ya yi tambayoyin aji me yake nufi. Wanne Muhammad yake nufi? Kuma Wace Amina yake nufi, idan yana Nufin MUHAMMAD NAMADI SAMBO ne da AMINA NAMADI to wannan wani al'amari ne daban, idan kuma kai tsaye ya nuna MUHAMMADU Manzon ALLAH SAW yake nufi, to kai tsaye za'a yanka shi ba sai an jira zuwan jami'an tsaro ba.

Ya 'yan shari'ar Musulunci bata bar mutane haka sakaka ba. Saboda hikimar tace ba'a tabbatar da hukuncin ZINA har sai shaidu duka sunga turmi da tabarya, idan biyu suka gani biyu suka saba ganin biyun farko na to za aiwa biyun farko bulalar Qazafi ko da kuwa abinda suka gani din ZINANCE a zahirinta, amma saboda rashin cikar shaidu sai hukunta su.

Irin wannan ta taba faruwa a Makarantar ACE ACADEMY a Kofar Gadon Kaya ina zaton a wajen 2005 inda wata Malama Kwafa itama ta yi makamantan irin wadannan tambayoyi a Jarabawa. Cikin Ikon Allah Malam Jafar Allah ya jikansa ya kwantar da hankulan mutane akan cewa za ayi bincike dan tabbatar da gaskiyar abinda ya faru.

Haka kuma, a garin Bichi irin makamancin haka ta taba faruwa, inda wani Inyamiri ya shiga kasuwa yana talla ance Inyamurin yana son ya Fadi cewa; NA ANNABI YA ZO KASUWA kasancewar bai iya Hausa sosai ba Sai Ya Dinga Cewa GA ANNABI YA ZO KASUWA, babu bincike matasa suka far masa da duka. Wanda sanadiyar haka aka yi kone-kone da yamutsi.

Haka nan, idan akayi tarzoma kamar yadda kuka sani  a cikinmu ana samun masu fasadi, suje suyi ta'addanci, suyi sata suyi zina har gidan giya suna shiga suna fadin wai an zagi annabi su sha giyar suyi intiqami akan wanda bai jiba bai gani ba. A kone dukiyar wadan da basu san hawa ba, basu san sauka ba. Hakan ba shakka yana aukuwa ne saboda bude damar tarzoma da rashin bincike.

YASIR RAMADAN GWALE
31-03-2-14

Monday, March 17, 2014

NAJERIYA: Abu Biyu Ne Zai Iya Faruwa Bayan Zaben 2015!

ABU BIYU NE ZAI FARU BAYAN ZABEN 2015

Mai kwarmin ido da wuri yake fara yin kuka inji 'yan magana. Yana da kyau mu kalli zaben 2015 da ke tafe mu kuma fadawa kanmu gaskiya. Ga duk wanda ya kalli yadda siyasar 2015 ta ke tafiya ya san cewa babu wani abu da zai iya hanawa shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan cin zaben nan sai KADDARAR ALLAH, domin alamu sun tabbatar da cewa muddin an zuba zabe sai ya koma shugabanci a karo na biyu, ko da kur'ar Halal ko da ta Haram. Wannan wani abu ne sananne, wanda ba a boye yake ba.

Yanzu alamu sun nuna cewa Shugaban kasa, yafi 'yan Hamayya kwarin guiwar cin zabe mai zuwa, domin abinda ake kira "Body Language" dinsa ya nuna haka, a yayin da a gefe guda, masu ikirarin hamayya basa nuna wani kwarin guiwa akan zaben, idan banda hayaniya a kafafen jaridu da Internet. To mai zai faru idan Shugaban kasa ya kuma cin zabe? Wannan wata muhimmiyar tambaya ce da mutane da dama zasu iya bayar da amsarta, idan aka dubi abinda ya biyo bayan sakamakon zaben 2011.

Abu guda biyu ne zai iya faruwa idan Shugaban kasa ya wuce a karo na biyu. Abu na farko, shi ne, irin Misalin abinda ya faru a kasar THAILAND, inda masu adawa da Shugaban Kasar Yunlak Shinwatra suka fito kan tituna suna bore tare da kona tayoyi da yin tofin Alla-tsine ga shugabar. Sai da ta kai, masu zanga-zanga sun dangana har zuwa fadar Shugaban kasar, inda suka yanke wutar lantarkin da ta shiga fadar, suka sanya siminti suka tottoshe kokfofin shiga fadar, suka farfasa tagogi da gilasai da daddaye tile din da aka shimfida akan tituna, suka yi zaman dirshan, ba shiga ba fita an baiwa mahaukaci gadin kofa, har dai, daga karshe suka saduda suka koma gidajensu ba tare da bukatarsu ta Tunbuke  shugabar ta biya ba.

Abu na biyu da zai iya faruwa, shi ne, abinda ya faru a kasar UKRAINE, inda masu zanga-zanga suka fito cikin tsananin sanyin dusar kankara suna kiran, shugaba Victor Yunokovich ya sauka. Wanda daman sun taba yin haka a 2004 inda suka kori Shuagabn lokacin Yushechenko. Sun kona tayoyi tare da bankawa gine-ginen gwamnati wuta. Har dai shugaban yaga babu sarki sai Allah, ya arzce ya kama gabansa. Masu zanga-zanga suka ci nasarar fatattakar shugaban kasa. Wanda hakan ya yi sanadiyar ballewar wani yanke da ake kira CRIMEA, inda kasar RUSSIA da ke san dawo da karfin tsohuwar rusashshiyar SOVIET ta mamaye yankin. Duk da cewa yankin ba shi da wani muhimmanci ta fuskar Tattalin arziki, ba zai nakasta Ukraine ba ko da kuwa ya koma karkashin Russia.

Daya daga cikin biyun nan na iya faruwa a Najeriya bayan zaben 2015. Ko dai masu zanga-zanga su ci nasarar korar Shugaban Kasa kamar yadda ya faru a Ukraine, wanda abu ne mai kamar wuya wai gurguwa da auren Nesa. Ko kuma, irin abinda ya faru a kasar Thailand ya faru a Najeriya, masu zanga-zanga bayan sun gama bore a titunan biranen Kano da Kaduna da Bauchi da Sokoto da Katsina su koma gida bayan sun gama artabu da jami'an tsaro, wadan da zasu mutu sun mutu, wadan da zasu karye sun karye a zubawa Sarautar Allah ido, a kuma yi tunanin tarawa a 2019 ga mai yawan RAI.

Babban abin tsoron, shi ne barkewar rikicin kabilanci da na Addini a musamman jihohin Arewacin Najeriya. Wanda za'a shiga gaba kura ne . . . , dan ga hare-haren da ake cewa ba'a san ko su waye suke kaiwa ba, kuma ga al'amuran bayan zabe. Allah ya kiyaye ya kare asarar dukiya da ta rayuka.

YASIR RAMADAN GWALE
17-03-2014

Thursday, March 13, 2014

Dan Sanda . . .


DAN SANDA III: Wata rana muna office wajen aiki da daddare, sai muka samu labarin cewa akwai wasu 'yan fashi sun tare hanya, suna harbin mutane, nan da nan na hada wani squad muka fita farautar 'yan fashin nan a daren. Muna zuwa wajen da aka yi fashin, sai muka tarar cewa, 'yan fashin sun gudu, amma, a kasa ga gawarwakin mutane nan yashe a kasa. Abin da na gani shi ne, wasu daga cikin 'yan sandan da muka zo da su, sun fara lalube aljuhun gawarwakin nan suna kwashe dan abinda yake ciki, sannan wasu kuma suna cire agogunan a hannun gawarwakin. Ban taba nadamar shiga aikin dan sanda ba, sai a wannan ranar. Daga lokacin naji duk aikin ya fita daga raina, har na yanke shawarar barin aikin. Amma cikin kaddarawar Allah wani dan uwa ya yi mun nasiha ya nuna min muhimmancin zama na a aikin ya fi ficewata, domin ko babu komai zan iya kawo gyara idan lokacina ya yi. Wannan magana Malam Nuhu Ribadu ya taba fada a wata tattaunawa da aka yi da shi a kwanakin baya. Dan Sanda abokin Kowa.

YASIR RAMADAN GWALE 
13-03-2014

Tuesday, March 11, 2014

Dan Sanda II . . .


DAN SANDA II: Muna zaune wani Dan Sanda yake baiwa wani abokina labari cewa shi fa barin aikin zai yi, duk da cewa sabon dauka ne yana Murnar shiga aikin. Aka ce da shi lafiya? Sai ya ce, wata rana wani mutum ya aiki yaronsa ya kai masa Mota wani kango inda yake ajiye mota, wajen kusa da caji Ofis ne, yaran ya je aje motar da daddare, bayan da ya fito ne sai 'yan Sanda suka kama shi, suka ce barawa ne, ya yi musu bayanin cewar ai suna gani ya shiga da motar ajewa ya yi ba dauka ya zo yi ba. Suka tsare shi, shiru-shiru Oga mai mota yana jiran yaro ya kai masa mukullinsa, bai dawo ba, kuma ga dare yana tsalawa sawu yana daukewa, can dai ya biyo baya, da yaga babu alamunsa sai ya je wajen 'yan sanda yake basu bayanin cewar ya aiki yaransa da mota ya ajiye amma bai dawo ba. Ogan 'yan sandan ya tambayi wani dan sanda a kusa da shi, ya ce, ko shi ne wanda muka kama da MAKAMAI? Sai ya ce fito da shi, ana fito da Yaran, mutumin ya ganshi, sai Ogan 'yan Sanda ya tambayi sabon Dan Sandan da yake baiwa abokina labari, cewa ba shi kuka kama da Makami ba? Sai ya ce, gaskiya ba mu kama shi da komai ba, nan take Ogan 'yan sanda ya ce Oh Sorry! Ashe ba shi bane, yana gayawa mai motar. Aka sallameshi ya tafi. Suna fita, Ogan 'yan sanda ya Kwarfi kafafun wannan dan sanda da ya karyata shi, ya zazzage shi, ya ce idan ka kuma karyata DAN SANDA sai ka yabawa aya zakinta. Aka ce dole a yi masa hukuncin karyatawa da ya yi.

Dan Sandan, ya ce shi fa aikin ya fita daga ransa, yana ganin barin aikin zai yi gaba daya. Dan Sanda!

Yasir Ramadan Gwale
11-03-2014

Dan Sanda . . .


DAN SANDA: Wata rana wani mutum ya kirani a waya yace akwai kaninsa an tsare shi a caji ofis na 'yan sanda, naje na sa hannu a bada belinsa. Banyi musu ba na tafi caji ofis din da ya yi min kwatance, naje na sami kanin nasa a gaban 'yan sanda, na tambayi abinda ya faru. Sai ya shaidamin cewa ya samu kwangila ne a wata karamar hukuma a Jigawa, dan haka ya karbi kayan wani Inyamuri na Miliyan 3, gashi har yanzu kudinsa basu fito ba, shi ne, shi kuma Inyamuri ya kawo kara wajen 'yan sanda, amma mun yi yarjejeniya zan kawo kudin wajen 'yan sanda nan da sati 2, dan haka yanzu kawai hannu zaka sa su bada belina. Aka nuna min takarda na rattaba hannu, mutumin ya dauko ni a motarsa muka rankaya wajen wansa da ya turani kar bar beli. Bayan kamar kwana 10 mutumin ya kirani a waya, cewa ya samu wani abu, dan haka zai zo ya daukeni mu kaiwa 'yan sanda, ya zo muka rankaya, kafin mu shiga caji ofis ya kawo wani dunkuli yace ga wannan a sayawa su Zainab burodi, nace haba har da nima, na karba na soke. Muna shiga wajen 'yan sanda aka dauko fayil ya zaro kudi dubu dari biyar ya mikawa DPO yace ga abinda ya samu, ya nemi a kara masa sati biyu nan gaba dan ya biya sauran, ya kawo wani abu ya sinnawa DPO. Abin mamaki a gabanmu kafin mu tafi aka rabe dubu dari biyar din Inyamuri. Mukai Sallama muka tafi! A mota nace masa to shi Inyamuri idan yazo karbar kudinsa fa? Sai yace, Uban Wa Ya Sa Shi Ya Zo Wajen 'Yan Sanda? 

Yasir Ramadan Gwale
08-03-2014

Thursday, March 6, 2014

RE: Boko Haram


RE: BOKO HARAM: 


Assalamu Alaikum Warahmatullah, Hakika Malam Yasir, naji dadin maganarka akan Boko Haram. Kaga mu da muke Borno da wad'an da matsalar Boko Haram ta ke yankinsu ba muda shakka ko kiris akan cewa Boko Haram ne suke ta'addancin nan, wallahi babu hannun gomnati ko Kungiyar CAN, domin mu muka sansu, ka ganni nan nayi MUQABALA da Shugabansu na yanzu wato SHEKAU a garinmu, kuma na kureshi domin da bakinsa ya furta cewa ilimin BOKO ya halatta ako ina, duk da lokacin naje har Maiduguri ne muyi mukabalar da Muhammad Yusuf amma sai ya kauce ya turo Shekau ya wakilceshi, bayan na kureshi na nemi Muhammad Yusuf akan zan zo muyi da shi sai yace sun gama wa'azi sauran yaki ya rage musu, nan take suka cire list namu da malaman Sunnah kusan 150 sukace sai sun kashemu ciki kuwa, har da Sheikh Ja'afar da Albany da abokina Sheikh Fantami, hakika sun sami daman kashe malamai da dama, hatta nima sun sha bani wa'adin kwana uku uku na kisa, ko tada bom don hallakani; bayan target da suka sha shiryawa akaina Allah yana tsare ni, hatta a wannan Ramadan din da ya wuce sunyi target nawa awurin tafsirina da hanya ta ta zuwa tafsirin sama da sau 5, kumafa su da kansu suna fada, Malam hatta wanda yayi commanding kisan Malam Ja'afar dan Borno ne kuma dan Boko Haram ne, wanda yabar aikin ganduroba ya shiga Boko Haram, daf da fadan 2009 bom yatashi dashi a Maiduguri, don barazanarsu saida aka mayar dani barikin soja da zama amma a wancan lokacin ma har gidana na barikin sun gwada zuwa.

Don haka, mu kam, mun sani su suke wannan barnar tunda ni kaina sun taba mini waya kuma na sansu akan zasu kashe Shugaban Majalisar Malaman garinmu mai suna Sheikh Ibrahim Ndatti kuma haka suka kashe shi din. Kuma, akwai wani Malami ana kiransa Sheikh Ibrahin Gomari Basakkwace ne yana Maiduguri da zama wanda yanzu haka ni nake gudanar da tafsirinsa na Ramadan, tare sukayi kaset na KARSHEN ALEWA KASA da Sheikh Albany Zaria, shima sun kasheshi bayan Sallar Magriba kafin ya shiga gida, wasu suka yita yada jita jitar cewa gomnatine, WALLAHI MALAM YASIR da kunnena nake jin wani dan Boko Haram mai suna USMAN OPIPI amfi saninsa da WAL-JIHAD yake fada a waya wa wata 'yar uwarsa wacce matatace yake gaya mata dashi akaje aka kashe shi Sheikh Gomarin yake cewa sunje da bakar JEEF, kuma bayan dan lokaci kadan sojoji sun kai sumame awani gida a Damaturu da aka tsegunta musu cewa Shekau yana gidan, wallahi ansami bakar Jeef din da bindigogi acikin gidan bayan arcewan shekau din. Shi, wannan, WAL-JIHAD din yataba zaman yari a Bauchi sakamakon boren da sukayi na Boko Haram daga baya suka kai farmaki zuwa gidan yarin suka tsere, daga baya kuma aka sake kamashi yayinda suka kai wata sumame yanzu haka yana gidan yari a Abuja.


Gaskiya duk wanda yake kare Boko Haram cewa ba su bane suke kai wannan hare-haren to bai san ainihin lamarin ba, mutanan nan fa a gabanmu suka fara wannan tayar da hankalin, kuma hatta boma boman da aka tayar a Kano a baya wad'an da sukayi kunar bakin waken 'yan garinmu ne, kuma na san wasu daga cikinsu, domin, kafin suyi kunar bakin waken sai sunyi waya, sun nemi gafarar iyayensu akan za su yi kunar bakin wake ranan kaza, amma ba zasu fadi wurinba sai ya faru aji. Gaskiya idan zamu tsaya muna ta zargin wasu wadanda ba su ba kuma muka barrantar da su 'yan Boko Haram din, wallahi zamu wahala, mu kam tuntuni mun sani. Ya rage namu, wanda zai yarda ya yarda, wanda zai ki yarda yaki, kuma wahala a yi ta shanta. Allah ya kare.


NA SAMU WANNAN SAKON DAGA WANI BAWAN ALLAH A JIYA.

Wa'azi . . .!


WA'AZI: Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam yana zaune, sai ga wani matashi yazo wajensa, yace da shi Ya Manzon Allah Kayi Min Izni Na Yi ZINA! Sai Manzan Allah SAW ya kauda kai, ya kuma maimaitawa, Manzan Allah Ya Kuma Kauda kai, har sau uku. Daga bisani Manzan Allah SAW ya juyo gareshi, Ya tambaye shi, shin zaka yarda wani ya yi Zina da Kanwarka ko Yarka ko Mahaifiyark ko Matarka? yace a'a, Manzan Allah SAW yace da shi to saboda me kake san yin zina alhali baka san ayi da naka! Hakika Allah SWT ya aiko Manzon Allah dan ya kasance Rahama da Shiriya ga Talikai Sallallahu Allaihi Wasallam. Ba shakka wannan wa'azi ne mai girma. Duk wanda zai aikata zina, ba zai so ayi da nasa ba, kuma wadanda zai yi da su din kannen wasu ne ko yayye koma Mahaifiyar wani ce. Allah ka karemu ka kare zuriyyarmu.

Yasir Ramadan Gwale
06-03-2014

Wednesday, March 5, 2014

A Baya . . .

A BAYA: Lokacin da aka kashe mana Malam Jaafar a Masallacin Juma'a na Dorayi a Kano, ba jimawa wasu mutane suka bulla a kusa da kauyen Galinja dake bayan garin Panshekara suka dinga ta'addanci, suna kisa baji ba gani, wani ya shaidamin cewa yaga gawarwakin sojojin Najeriya da aka dinga lodawa a akorikura ana ficewa da su daga Panshekara, haka aka wayi gari mutanan nan sun sulale ba'a san ta inda suka fice ba su da makamansu. 
 
Amma dai rashin gaskiyar Gwamnatin Najeriya ya sanya bama saurin gasgata duk abinda ta fada. Ni na fahimci jami'an tsaron Najeriya har yanzu basu fahimci cewa duniya ba a tsaye take ba, shi yasa ko Makamin Nukiliya ka dauko a motarka indai ba acikin but ka saka shi ba, to zaka iya sada shi da duk inda kake so, ba tare da fargaba ba. Na kuma fahimci al'amarin Boko Haram ba zai iya karewa nan kusa ba, domin ana yiwa lamarin kallo ta madubin siyasa, ana kuma bugun jaki ana barin taiki ana kallo kulba na barna ana cewa jaba ce. Amma dai nayi Imani babu abinda ya gagari Allah.
 
Yasir Ramadan Gwale
05-03-2014

Boko Haram

BOKO HARAM: Daga lokacin da 'yan Arewa suka yarda cewar Masu kai wadannan hare-hare 'yan Boko Haram ne, ba CAN ko Gwamnatin Tarayya da ake zargi bane, sannan ne aka fara gano bakin zaren warware matsalar. Amma, Muddin muka cigaba da kawar da kai daga masu laifi, muna dorawa wasu na nesa laifin, to, lashakka, cewar har furfura ta riskemu zamu cigaba da fama da wannan tashin hankali Allah ya kiyaye. Dole a fadi magana ta gaskiya akan abubuwan da suke faruwa a Arewa Maso gabas, da dama wadan da ba a Maiduguri ko Yobe suke ba, ko kuma ba su da alaka da yankin sukan yi tutsun cewar SAM wannan abin ba 'yan Boko Haram bane, wasu suce CAN ne; wasu su ce Shugaban Kasa ne da sauran zantuttuka irin wadannan.

Na tabbata, babu yadda CAN ko Shugaban kasa zasu shirya mana irin wannan makarkashiya a ce mun kasa ganewa, duk da muke zargin Shugabanninmu da gazawa wajen kare muradunmu, Tabbas CAN ko Shugaban kasa ba zasu shirya mana haka ba su yi shiru su zuba ido, ai lalacewarmu bata kai haka ba, gidadancinmu bai iso wajen ba.

Idan zamu ga laifin Gwamnati akan wannan batu bai wuce na rashin bin sahihan hanyoyin magance matsalar ba. Domin ita gwamnati tana daukar mataki ne bisa la'akari da rahotannin masu yin Sharhi akan al'amuran tsaro, wadan da galibinsu a Abuja ko Legas suke, suna kwance suke fadin abinda basu fahimci hakikaninsa ba.

Sannan wasu, musamman 'yan siyasa daga Arewa, suka ki fahimtar gaskiyar lamarin da gangan saboda siyasa. Lallai ya kamata mu fahimci cewar, shifa Shugaban Kasa wannan al'amari gobarar titi ne a gareshi, domin idan akwai abinda yake akan rikicin bai wuce "taking advantage" ba, muna cigaba da yiwa batun tutsun fahimta, muna kara basu damar zaftare makudan kudaden da ake warewa akan tsaro.

Ya rage namu, ko dai mu tsaya mu fahimci wannan ala'amari a zahirin yadda yake, dan tunanin mafitarsa, ko kuma, mu cigaba da yiwa abun gurguwar fahimta, muna kara kwana da tashi cikin tashin hankali da zullumi. Allah ya kiyaye.

YASIR RAMADAN GWALE
05-03-2014