Tuesday, November 26, 2013

Cuwa-Cuwar Da Hukumar Zabe Ta Tafka A Zaben Anambra


CUWA-CUWAR DA HUKUMAR ZABE TA YI A ZABEN ANAMBRA

Otumba Dino Melaye ya bankado wannan cuwa-cuwa da hukumar Zabe ta kasa ta yi a zaben Ranar 16 ga watan Nuwamba da aka gudanar a jihar Anambra.

Hukumar Zabe ta tabbatar sahihancin zaben da ya zo hannu kamar haka:

  • Kuri’un Da Aka Tantance 451,826.

  • Kuri’un Da Aka Soke 16,544.

  • Ida ka kwashe Kuri’ar da aka soke guda 16,544 a cikin kuri’un da aka tantance, ya zama akwai halastacciyar kuri’a 435,282.

  • Kur’ar da aka yi zabe da ita bayan an tantance ita ce 429,549. Wato hakan ya nuna cewar akwai mutum 5,733 da aka tantance su amma basu yi zabe ba.

  • Kuri’un da aka bata a yayin da aka gudanar da zabe ita ce 113,113. Wato idan ka dauki kuri’un da aka yi zabe da su 429,549 ka kwashe kuri’un da aka lalata 113,113, kana da sauran halattacciyar Kuri’a 316,436 da aka yi zabe da ita.

Haka kuma, sakamakon da yake a hannu yanzu wanda aka bayyana adadin kur’ar da kowacce jam’iyya ta samu ya nuna cewar:

  • AFGA- ta samu 174,710.

  • PDP- ta samu 94,956.

  • APC- ta samu 92,300

  • LP- ta samu 37,440

Wannan ya nuna idan ka lissafa kur’un da AFGA da PDP da APC da LP suka samu zai baka adadin kuri’u 399,406.

To anan tahuma zata taso, idan ka duba lissafin baya hukumar zabe tace adadin halastattun kuri’un da aka yi zabe da su sune 316,436, to ya aka yi da aka tashi rabawa abinda ko wacce jam’iyya ta samu adadin ya zarta ainihin kuri’un da aka fada. Domin idan ka hada lissafin abinda dukkan jam’iyyu suka samu zai baka kuri’a 399,406. Wannan zai tabbatar maka an samu Karin kur’a 82,970 akan ainihin kuri’a 316,549 da aka yi zabe da ita.

TAMBAYA: Shin ya akayi aka samu Karin 82,970? Kuma ina kuri’un da aka samu kari 82,970 suka shiga, AFGA ko PDP? Kuri’ar wacce Jam’iyya aka kwashe a cikin wadannan jam’iyyu aka karawa wata? Wannan tambaya ce da hukumar zabe zata bayar da amsarta.
Yasir Ramadan Gwale

26-11-2013

Sunday, November 24, 2013

Jaimhuriyar Musulunci Ko Jamhuriyar Shedanu!!!


JAMHURIYAR MUSULUNCI KO JAMHURIYAR SHEDANU!!!

Ba shakka, da ace wata kasa ce da ta ke ta Musulmi ce tsantsa kuma ta ayyana kanta a matsayin Jamhuriyar Musulunci, tabbaci hakika da ba zata kai labari ba, domin za’a dauki karan tsanar duniyarnan a dora mata, a saka mata takunkumai da turaku bila-adadun domin karyata. Amma da yake su kansu Kasashen Yamma sun san da cewar kasar IRAN karya suke, sunyi hannun riga da Addinin Musulunci, basu da alaka da shi ko ta kusa ko ta nesa, sai kaji Tuarawa na kururuwar Jamhuriyar Islama akan kasar Majusawa da Safawiyyawa da Rafidawa masu bautar wuta ta Farisa.

Abinda zai tabbatar maka da haka, shi ne yadda suke yin kutu-kutu, suke rusa duk wata Jam’iyyar Siyasa da ta bayyana kanta a matsayin Jam’iyyar Musulunci dan hanata kaiwa ga kafa Gwamnatin Musulunci. Duk wata jam’iyya da aka alamtata da sunan Musulunci, sai kaga an sa mata ido har a kawo karshenta, ko kuma a gurgunta ta a hanata aiwatar da ayyukan da su ne aka kafa ta akai. Ko kuma su lankaya mata kalamr “Ta’addanci” kamar yadda suka a Ghazza wa kungiyar kuma Jam’iyyar Hamas.

A dan haka, duk wani Musulmi na Hakika baya taba samun rudani idan yaji an kira kasar Farisa da sunan Jamhuriyar Musulunci, dan yasan Shifcin gizo ce, kuma, fankam fayo ce a bangaren addini domin fanko ce. Basu san komai ba sai barna da ta’adi da ashararanci da badala, da shantakewa da sheke aya.

Allah ya rusa masu yiwa Addinin Musulunci shigar shantun kadangare, masu yiwa addini zagon kasa. ‘Yan Damfarar addini. Allah ka baiwa Musulmi kariya daga Sharrinsu a ko da wane lokaci. Allah ka warware dukkan wani kulli da kitififi da suka shirya dan halakar da Musulmi, Allah ka afkar musu da dukkan sharrinsu akansu. Allah ka tabbatar da mu akan hanyar gaskiya komai wuya komai tsanani.

Yasir Ramadan Gwale

25-11-2013

Gwamnatin Angola Ta Haramta Addinin Musulunci


GWAMNATIN KASAR ANGOLA TA HARAMTA ADDININ MUSULUNCI 

Kusan yanzu za'a iya cewa kasar Angola ita ce kasa ta farko a duniya da ta fito a hukumance ta soke Addinin Musulunci a kasar, ta kuma bayar da umarnin rurrusa dukkan wasu Masallatai da suke a kasar. A cewar Ministan Al'adu da yawan bude Ido na kasar Rosa Cruz e Silva, Ma'aikatar Shar'ah da 'yancin walwala ta kasar bata bayar da izni ko damar aiwatar da Addinin Musulunci ba a kasar, a dan haka suka haramta Musulunci baki daya a kasar, Silva ta kara da cewa kasar Angola bata maraba da Musulmi ko daga ina yake a duniya.

Haka kuma, Silva ta kara bayanin cewar Haramcin ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke kokarin  dakile dukkan wani abu da ya yi kama da nuna kishin Addini daga cikin addinan da hukuma ta amince da su aiwatar da ibadarsu. Dan haka dukkan wasu Masallatai zasu cigaba da kasancewa a rufe kafin rurrusa su. 

A nasa bangaren shima, shugaban kasar ta ANGOLA José Eduardo dos Santos ya ce wannan shi ne ya kawo karshen Musulmi da Addinin Musulunci a kasar ta Angola. Haka shima Gwamnan Babban birnin kasar Luanda Mista Bento Bento yace babu wata rana da gwamnatin zata Halatta Addinin Musulunci a kasar.

A cewar wasu bayanai na hukumar leken asirin kasar Amurka CIA kasar Angola na da adadin yawan Musulmi kimanin kashi 15 cikin dari ne. Jaridar Gwamnatin kasar Jornal de Angola ita ce ta ruwaito wannan labari.

Idan sunyi haka ne dan su samu Aminci da yarda a Turai da Amerika, basu san cewa akwai Masallaci a cikin fadar gwamnatin AMerika ba ne? Ba su san cewa akwai daruruwan Masallatai a kasashen Turai bane? Hakika ALLAH sai ya cika hasken Addininsa ko da kafurai da Mushurukai sunki. Manyan Kafurai irinsu Utba Ibn Rabi'ah da Abu Lahab da Shaiba Ibn Rabi'ah babu abinda ba su yi ba, su da addinin aka saukar da shi akan idonsu. Hakan nan Allah ya darkakesu, haka kuma zai darkake na kasar ANgola. ALLAHUMMA ALAIKA BIHIM. Musulmin Kasar Allah ka kai musu dauki.

Yasir Ramadan Gwale 
24-11-2013

Shugaban Kasa Na Sheke Ayarsa Tare Da Wasu Ministocinsa Mata


SHUGABAN KASA NA SHEKE AYARSA TARE DA MINISTOCINSA MATA.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewar a lokacin bikin cikar shugaban kasa Shekara 56 a Landan bayan dab-dala da Da-dimar da aka kwana ana yi, Shugaban kuma ya gwangwaje tare da Ministar Albarkatun Manfetur Dieziani Allison Maduekwe a birnin Na Landan. Sahara Reporters sun ruwaito cewar bayan shan-gara da akayi a yayin wannan biki, ita ministar ta dauki Shugaban kasa inda suka fita su kadai ba tare da wani dan rakiya ya bisu ba a birnin Na Landan, Daga bayan sun dawo ne daga yawan da suka fita su kadai cikin Shugaban kasar ya murde, rahotanni sun tabbatarwa da Sahara  cewar ita ce mutum na karshe da ya gana da Shugaban kasa kafin daga bisani aka ji labarin ciwon da ya kwantar da shugaban a asibiti cikin gaggawa; a yayinda wasu rahotanni kuma suka ce Shugaban kasa yayi Mankas ne abinsa da Ruwan Kain-Kain me sanya jiri da hajijiya.

A kwanakin baya ma, sai da mijin ministar Sufuri Stella Oduah ya yi korafin cewar yana ganin sakonnin Tes na soyayya da Batsa da Shugabaan kasa yake aikowa da iyalin nasa akai-akai. Ance sai da mijin na Odua ya yiwa Shugaban kwamitin Amintattun PDP Cif Tony Anineh korafi akan cin-amanar da yake zargin Shugaban kasa yana yi masa, ina Mista Anineh din ya baiwa mutumin hakuri tare da alkawarin cewa zai yi kokarin takawa Shugaban Birki akan hakan.

Daman dai Tuni ake Zargin SHugaban kasa Goodluck Jonathan da aikata masha'a tare da wasu mata guda uku zuwa hudu, da akewa lakabi da Murhun Shugaban Kasa.

Yasir Ramadan Gwale 
24-11-2013

Thursday, November 21, 2013

Al-Amarin Kare Na Daga Cikin Abubuwan Ban Mamaki


AL-AMARIN KARE NA DAGA CIKIN ABUBUWAN BAN MAMAKI

Kare yana daga cikin dabbobin da Allah ya haramtawa Musulmi cin namansa. Ba shakka kare wata dabba ce da ba wata mai kima ko daraja ba ce a wajen mutane da dama, musamman Musulmi. Cikin ikonSa Subhanau Wata'ala, ya sanya fahimtar juna tsakanin Kare da Bil-Adama, babu shakka dukkan dabbobin da Allah ya hiltta babu wata dabba da ta kai kare sabo da Mutane, wannan ta sanya a kasashen Turai da Amerika ake lissafa kare a zaman daya daga cikin Iyalin gida, ko ahalin gida, kare yana samun kulawa ta musamman a wajensu. Sukan bashi wata irin daraja da ta shallake irin wadda wasu mutane suke samu a wasu sassa na duniyar nan! Allah buwayi gagara misali, shi ya sa da ya tashi bayar da labarin ASHABUL-KAHFI a cikin al-qur'ani mai tsarki, sai ya bayar da labarin har da karen da yake tare da su, wato kare ya lizimci mutanan kirki! 

Shin waye kare? Wani bincike ya nuna cewar, kare ya rayu a cikin wannan duniyar kusan fiye da shekaru 100,000 da suka shude, sannan  asalinsa, tsatso ne na dangin "wolf" wata dabba da ake samu a Arewacin Amerika da Turai da Kuma Asia, ita wannan dabba ta yi kama da Kare ta fuska, amma ta sauran sassan jiki sun sha bamban da kare, kuma amfi samun sa a waje mai sanyi da dusar kankara. Haka kuma, wani binciken ya nunar da cewr akwai sama da karnuka Miliyan 400 da suke watangaririya a duniya. Allah masani! Amma dai mun san cewa Allah ya halicci dukkan "DABBATIL ARD" bisa kaddarawarSa subhanahu wata'ala, shi ne ya halicci Mutum, da Aljani da kwado da gafiya da Barewa da Kunkuru da Matsaatstsaku da Rakumi da dukkan sauran ababen Halitta bisa Kaddarawarsa Alkhaliqu, tsarki ya tabbata a gareshi.

Kare shi ne kadai yake da dogon tarihin sabo da yiwa 'yan Adam hidima tun kusan fiye da shekaru 33,000 da suka shude a cewar wasu masana, musamman ta fannin da ya shafi kiwo, farauta, jan-kaya a cikin dusarkankara, da kuma taimkawa jami'an tsaro wajen gano wasu baoyayyun abubuwa da suka gagri dan-adam ganowa. Kare yana da rikon amana ainun, duk irin bala'i da masifa ta kura, da kuma irin yadda Allah ya sanyawa kare tsoron Kura, yakan mutu wajen kare dabbobin da yake rakiya a duk lokacin da kyarkyeci ya kawo musu farmaki ko barazana. Kare ne kadai dabbar da ake iya bashi kiwon wata dabba 'yar uwata! Subhanallah, kaji al'amarin ubangiji. Allah cikin hukuntawarsa ya sanyawa kare fahimta mai yawa da kuma lura da ganewa.

Allah ya halicci kare daban da sauran dabbobi. Domin yadda kare yake kallon duniya ba haka sauran dabbobi suke ganinta ba, sinadaran da suke cikin Idon kare suna ganin fari ne da baki kawai, a tarihin rayuwarsa bai taba ganin wani launi sabanin fari da baki ba, a bisa yadda Allah ya yi masa halittarsa. Kare yana daga cikin dabbar da bai damu da duniya ba, babu ruwansa, shi yasa a koda yaushe yafi son zama waje mai sanyi mai danshi mai ni'ima, watakila kamar yadda muka fada a baya tsatsonsa danginsu wolf suna rayuwa ne a waje mai sanyi watakila wannan ta sanya kare ke son sanyi da danshi.

Kamar yadda kare ya dauki tsahon lokaci tare da mutane, wannan ta sanya yake samun cigaba gwargwadon yadda mutane ke samun cigaba. Domin yanzu bincike ya nuna kare yana iya yin tarayya da mutane wajen yin wasu ayyuka da dama. Misali ba sau daya ba, ba sau biyu ba ansha cewa kare ya kubutar da wani yaro ko yarinya daga halaka, ko kare ya halaka garin kokarin kubutar da dan-adam daga halaka. Bayan ayyuka na tsaro da bincike da Kare yake taya dan-adam, kare na iya yin wasu ayyuakn da dama kamar bude kofa da rufewa, kunna hasken lantarki da kashewa, kallon talabijin, sannan kuma, kwanakin baya muka ji cewar an fara koyawa kare tukin mota a Amerika. Ba shakka a kasashen turai har aiken kare suke yi, kuma idan bai gane ba ya yi tambaya a yi masa kwatance. Kare baya magana amma yana jin magana kuma yana fahimta, gwargwadon tarbiyyar da ya samu da kuma irin yanayin da ya taso a cikinsa.

Idan muka dauki batun "SABO" byanai sun tabbatar da cewar Kare ya samu shakuwa da dan-adam sosai, ta yadda baya iya rabuwa da mutanan da ya saba da su. Wata rana a cikin shirin taba kidi na BBCHausa suka fadi cewar wani kare da ubangidansa ya rasu, sai da karen yazo ya tare a gindin kabarin da aka binne ubangidan nasa na wasu tsahon lokuta, yaje ya yi farautar abinda zaici sannan ya dawo wajen ya kwanta. Akwai nau'ka na kare sama da kala 400 a cewar wani bincike. Hakika akwai abubuwan ban mamaki a tattare da rayuwar kare. 

Yasir Ramadan Gwale 
21-11-2013

Wednesday, November 20, 2013

Daga Birnin Washington GUndumar Kwalambiya



DAGA BIRNIN WASHINGTON GUNDUMAR KWALAMBIYA

A ranar 22 ga watan Nuwamban shekarar 1964 shugaban kasar Amurka na wancan lokacin John F Kennedy ya shirya tsaf inda ya kama hanyar garin DALLAS babban birnin jihar TEXAS dan gudanar da kasaitaccen gangamin yakin neman zabensa a karo na biyu. A daidai lokacin da Shugaban Kennedy ya fito cikin fara'a da annashuwa dan wannan gagarumin gangami da aka jima ana yiwa tanadi, wasu harsasai guda uku suka kawo karshen rayuwarsa a duniya, a yammacin wannan rana. Ya abin ya faru ne?

Clint Hill ta ce, ina tsaye a daidai lokacin da budaddiyar motar da aka yiwa Shugaba Kennedy tanadi dan ya shiga ya zaga a tsakiyar Dandalin Dealey Plaza dake birnin Dallas. Muna tsaye muna jira, Can sai na hango zungurareriyar motar da take dauke da shugaban ta dumfaro filin da aka tanadar masa budaddiyar motar da zai hau, karasowarsa ke da wuya, kusa da inda nake tsaye, babu zato babu tsammani sai naji wata karar fashewa mai karfin gaske, na firgita matuka a daidai wannan lokacin, ban san me yake faruwa ba, ga hayaki ya turnuke, babu abinda kake iya ji sai ihun da jama'a suke dan gudun neman tsira da rayukansu. Da na hanga kusa da budaddiyar motar nan, sai na hangi Shugaba Kennedy kwance ya yana jan jiki ta bangaren gefen jikinsa na hagu, makogaronsa na furzar da jini, hankalina ya kara tashi da abin da na gani, ban yi wata-wata ba, na yunkura da sauri dan na matsa kusa da inda shugaba yake domin na kai masa dauki, sai naji wata kara fau-fau sau biyu, na sake kwantawa, can banyi kasa a guiwa ba, na kuma jan jiki dan na matsa kusa da inda yake na kai masa agaji sai na kara jin wata kara FAU! Ai ko da na kalli inda Shugaba Kennedy yake sai naga kwakwalwarsa a bude jini na ta kwarara, ina matsawa inda yake sai na sake jin wata mummunar kara da fashewa a dab da budaddiyar motar da ke kusa da mu. Inji Clint Hill tsohuwar jami'ar leken asiri take shaidawa masu bincike abin da ta gani a wannan rana.

Shugaba Kennedy mutum ne mai saukin kai, ba shida girman kai. A duk sanda ya fito yakan shiga cikin mutane ba tare da shayin wani abu ba yana mika musu hannu ana sowwa da murna. Haka kuma, a sau da dama Shugaba Kennedy mutum ne da baya yarda jami'an tsaronsa su dinga sanya masa labule da jama'a a duk sanda ya fito bainar jama'a.

Kisan da aka yiwa Shugaba Kennedy, hakika ya girgiza Amurkawa, hankalin mutane da dama ya tashi. A halin yanzu motar da aka budewa Shugaba Kennedy wuta tana gidan adana kayan tarihi na Henry Ford museum dake birnin Dearborn a jihar Michigan.

Wasu muhimman tambayoyi su ne: Wanene ya kashe shi?
Kuma menene dalilin kisan nasa? Me ya biyo bayan kisan ta fuskar hukunci?

20-11-2013

Monday, November 18, 2013

Shin Jega Ne Matsalar Zaben Najeriya?

SHIN JEGA NE MATSALAR ZABEN NAJERIYA?

Zaben gwamnan jihar Anambra da aka gudanar ranar 16 ga watan nuwamba, kusan shi ne ya bankada asirin hukumar zabe ta kasa karkashin jagorancin kwararren malamin jami’ah masanin kuma mutafannini a harkar siyasa Farfesa Attahiru Muhammad Jega, dan gane da kurari da karajin da ya dinga yi a baya cewa ya nazarci dukkan kurakuran da suka fuskanta a zaben 2011 da ya gabata, ya kuma sha cin alwashin cewar sai ya tsaya kai da fata wajen ganin an aiwatar da sahihi kuma tsarkakken zabe daga dukkan nau’in magudi a babban zaben kasa na 2015 da ake ta tsumayin lokacin. Sai dai Hausawa sunce “juma’ar da zatai kyau akan fara gane ta ne tun daga asubahin ranar laraba” sai gashi abin mamaki da ta’ajibi laraba ta yi har rana ta fadi ana shirin wayar gari Al-hamis babu wasu alamu da suke nuna cewar juma’ar da zata zo gaba kyakykyawa ce da jama’a zasui murna da farin ciki da ita.

Wannan zaben na Anambra da aka gudanar mai cike da kace-na-ce da tababa, shi ne zaben da ‘yan Najeriya suka sanyawa ido a matsayin wani ma’auni ko zakaran gwajin dafi akan zaben da zai gudana na kasa a shekarar 2015. Sai gashi duniya ta shaida tsiraicin hukumar zaben da Jega ya dinga shan alwashi akan zasu aiwatar da sahihin zabe. Almundahanar da aka tafka a wannan zaben ba wai ta tsaya akan al’adar nan ta ‘yan siyasa ta sayan kuri’u da rarraba kayan masarufi ga masu yin zabe ba, abin har da jami’an hukumar zabe aka samu da hannu dumu-dumu wajen yin kaci-baka-ci-ba baka-ci-ba-kaci, aka raunana zaben, aka hana wasu yin zabe, aka sossoke wasu kuri’u. Na san da cewa da daman ‘yan Najeriya abin da ya faru a Anambra dangane da ‘yan siyasa bai basu mamaki ba, dan dama mai hali baya fasa halinsa, illa kawai abin mamaki shi ne, ashe hukumar zabe shararata ta dinga yi dangane da wannan zabe.

Ba shakka, ya zuwa yanzu mutane da dama sun sallama da samun sahihin zaben da aka tsammata a 2015 wanda Jegan ya sha alwashin aiwatarwa. Dukkan wani kyautatawa hukumar zabe zato da aka yi akan zaben 2015 a yanzu dai hukumar zaben ta zubewa ‘yan Najeriya kasa warwas idan banda ‘yan Fidifi bangaren shugaban kasa. Babu wani kwarin guiwa da muke da shi akan hukumar zabe dangane da samun sahihin zabe da zamu iya aminta da sakamakonsa. Abinda ya faru a baya watakila a zaben 2015 ya ninka ninkim-ba-ninkim na almundahana da cuwa-cuwa da satar akwati da hadin baki tsakanin jami’an tsaro da ma’aikatan hukumar zabe da baragurbin ‘yan siyasa masu san cin zabe ta kowace irin hanya.

To amma abin tambaya anan shi ne, shin Farfesa Attahiru Jega shi ne matsalar zaben Najeriya? Ba shakka Jega shi ne shugaban hukumar zabe ta kasa, shi ne yake da dukkan wani alhaki na ganin ya tsaya kai da fata wajen ganin anyi gaskiya, anyi adalci a matsayinsa na shugaban hukumar zabe. Sauran jama’a masu zabe su kuma a nasu bangaren su tabbata sunyi zaben gaskiya wanda bai sabawa doka da ka’ida ba.

Tuni har wasu sun fara yin kira akan Farfesa Attahiru Jega ya kama gabansa ya san nayi. A ganina yin murabus din Jega ba shi ne mafita ba dangane da samun sahihin zabe, ba shakka Shugaban hukumar zabe yana da dama mai girman gaske wajen ganin anyi zaben gaskiya, amma yana da kyau idan anbugi jaki a bugi taiki, domin su kansu jama’a da dama ba gaskiya suke da itaba, dole mu hada karfi da karfe wajen ganin ansamu zaben gaskiya. Yana da kyau mu sani ko Jega ya sauka, Shugaban kasa Me-Malafa shi ne dai zai sake nada sabon shugaban hukumar zabe, kuma ba shakka, shugaban rashin gaskiyarsa da rashin tsoron Allahnsa sun bayyana karara kamar wata darn goma sha hudu, dan haka ba zai taba nada wani mutum mai gaskiya da zai jagoranci hukumar zabe dan ya aiwatar da sahihin zabe ba.

A ganina gara Jega ya cigaba da zama a matsayin shugaban hukumar zabe har zuwa karshen wa’adinsa, tunda mun riga mun sanshi, munga irin kamun ludayinsa. Muna kuma da yakinin cewar yayi Imani da Allah, ya yi Imani da Wutar Jahannama ya yi imani da Al-Jannah, ya kuma san cewa Marasa gaskiya maciya amana masu jefa rayuwar al’umma cikin mummuna hali da garari ba zasu hada hanya da al-jannah ba. Wallahi Jega idan yayi gaskiya yasan makomarsa kyakykyawa ce a ranar gobe kiyama, idan kuma yayi rashin gaskiyar da muke zarginsa ba shakka yasan makoma ta munana ga mutanan da suka aikata aiki irin na marasa gaskiya makiya gaskiya, makiya cigaban kasa.

Ko shakka babu, bamu yanke tsammani daga wajen Allah ba dan samun Shugabanni na gari masu gaskiya da tsoron Allah wadan da zasu ji-kanmu su fitar da mu daga cikin halin fatara da talauci da kuncin rayuwa, da samar mana da dukkanin abubuwan bukata, da kare mana martabarmu da rayukanmu da dukiyoyinmu. Allah muke roko Al-Azizu ya wargaza dukkan wani shiri da nufi na Azzalumai ko su waye, Ya Allah kasansu ka san abinda suke kullawa, Allah ka yi mana maganinsu. Ya Allah! Bad an halinmu ba, ka arzutamu da samun shugabanni na gari Adalai.

Yasir Ramadan Gwale

18-11-2013

ZABEN 2015: ANYA ZA'A IYA KAYAR DA GOODLOCK KUWA?


ZABEN 2015: ANYA ZA'A IYA KAYAR DA GOODLOCK KUWA?

Abinda ya faru jiya a jihar Anambra ya kara tabbatar mana da cewar tun daga zaben 2011 har zuwa yau babu wani abu da ya canza dangane da harkar zabe a Najeriya. Zaben Anambra duk da ba'a fadi sakamako ba, amma irin almundahanar da ta wakana ta nuna cewa hukumar zabe babu wani kwarin guiwa akanta, dangane da aiwatar da sahihin zabe. Tambayar da na yiwa kaina, anya hukumar zabe karkashin Attahiru Jega zata iya shirya tsarkakkaken zaben da zamu iya yarda da sakamakonsa ko da kuwa ba wanda muke so ba ne ya yi Nasara? Allah ya kiyaye.

A kasar Kenya, babu abinda ya damu Moi Kibaki da duk mutanan da suka rasa rayukansu domin duk talakawa ne suka kashe talakawa. Ya murda zabe yayi abinda yaga dama, ya kammala wa'adinsa, kuma ya kama gabansa babu ko kara da aka daga masa da sunan dukkan irin balahirar da aka tafka a zaben da ya mayar da Kebaki kan kujerar Mulkin wa'adinsa na biyu. Sai abin ma ya zama wasan kwaikwayo, wasu daban ake zargi da tashin hankalin da ya faru! Kura ta sha kashi shi kuwa gardi ya cika lalitarsa.

A kasar Senegal mun gani duk da irin dan banzan taurin kai da san dawwama a Mulki na shugaba Abdullahi Wade, amma da aka yi zabe ya sha kaye ya hakura da kayen da ya sha, kuma ya mika mulki ga zabin jama'a, ba tare da anyi asarar rayukan talakawa ba, kamar yadda aka yi a Kenya. Watakila saboda yana da hasken Imani na Musulunci a zuciyarsa ne. Allah masani.

A babban zaben kasa na 2015, ko dai shugaba Goodluck Jonathan yabi irin hanyar da Kebaki yabi a Kenya ya kashe kunnensa, ayi ta kashe-kashe da kone-kone tundaga Gonin-Gora har Jibiya, tundaga Sokoto har Maiduri babu abinda zai sha masa kai. Ko kuma ya nuna dattako irin na shugaba Wade idan ya sha kaye ya hakura ya mika mulki ga zabin jama'a Alabashshi tarihi ya rubuta karfin hali da juriyar da ya nuna na karbar kaddara. Wanda ba shakka abu ne mai kamar wuya haka siddan wannan bakin arnen ya yarda ya sha kaye, balle da wuya har akai ga fagen shan kayen.

Babban abin tambaya ta shi ne, shin me ye zai biyo bayan sakamakon zaben kasa na 2015? Anya kuwa jam'iyyar APC da muka saka a gaba ta shirya da gaske dan kwace goriba a hannun-kuturu? Ba shakka talakawa suna cikin garari kwarai da gaske. Ina ji a jikina cewa PDP na iya samun halattaciyar kuri'ah a kafatanin jihohin Najeriya, tunda suna da kudin sayan kuri'u, ba shakka kuma za'a sayar musu. Amma dai al'amarin akwai ban tsoro kwarai da gaske.

Wata muhimmiyar tambaya da nake yiwa kaina, ita ce, meye makomar Musulmi a cikin gwamnatin Jonathan idan aka ce shi ne ya ci zabe? nayi Imani shugaban kasa Goodluck mutumne mara tsoron Allah. Meye makomar tashin hankalin da muke fama da shi a Arewa musamman a jihar Borno da Yobe? Nasan da cewa, duk tsiyar shugaban kasa da takadarancinsa ba zai haura shekara ta 2019 ba, to amma me zai faru da mu kafin wannan lokacin? Allah shi ne masani.

Yasir Ramadan Gwale 
      17-11-2013

AREWA: A GANI NA . . .

AREWA: A GANI NA . . .

Batun halin da Arewa ta ke ciki na zubewar mutunci da kima da haiba da kamala da koma baya ta fannin tattalin arziki da sukurkucewar Ilimi da lalacewar makarantu da kiwon lafiyar da asibitai suka zama tamkar makabartu da al’amuran tsaro da suka jagwalgwale suka hana kowa walwala da jin dadi, kusa wadannan da ma wasu sun damu duk wani dan AREWA mai kishi babba ne ko karami, mace ce ko Namiji. Yau a Arewa babu wani wanda zaka titsiye ka tambayeshi halin da ake ciki ya yi maka hamdala da godiya da wannan hali da muke ciki, sai dai fa idan tantagaryar makiyin Arewa ne makiyin Najeriya wanda baya son cigaban Arewa da Najeriya. Halin da muke cikin ya wuce duk yadda ake zato, domin wani abin ma idan mutum yaji sai yaji kamar ba gaskiya bane, ba wai kawai lalacewa Arewa ta yi ba, a’a komawa baya ta ke a sukwane, Kamar Misalin motace ka baiwa dan koyo kuma ya sanya giyar reverse yana gudun tsiya, shakka babu dole ya yi barna, ba wai motar kadai zai mammokada ya lallauya tayoyin ba har da duk abinda ya samu akan hanya sai ya bangajeshi mai gyaruwa ya gyaru wanda ya mutu ya mutu kenan; to kamar misalin irin haka Arewa take a yanzu, a halin da muke ciki.

Matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ta addabi samarinmu maza da mata, Ilimin makarantun hukuma ya tabarbare makarantun gwamnati sun zama garken jahilai, malaman babu ilimi, daliban babu ilimi gwamnatocin kananan hukumomi da na jihohi da sauran al’umma da ake kira “community” kowa ya kame hannunsa daga lalacewar ilimi anyi ko in’kula, kowa ya gwammace idan zai iya ya dauki dansa ya kaishi makarantar kudi, wanda kuma bashi da karfi alal-larurati ‘ya ‘yansa suke karatu a makarantun gwamnati ba dan ransa yana so ba, sai dan bashi da yadda zai yi. Irin wannan mawuyacin halin hannu baka hannu kwarya, ya sanya da dama dagacikinmu suka fara yanke tsammani daga Ubangiji, wasu suka bazama neman yaki halal yaki haram, Mutane burinsu su tara dukiya babu ruwansu da tsarkinta.

Yanzu a Arewa yaro da babba, mace da Namiji, almajiri da wanda ba al’majiri ba, mai gata da mara gata, mai mulki da wanda ake mulka; Kusan kowa neman damar dan uwansa yake, ta ina zai samu dama ya kwashe kafufuwan duk wanda Allah ya dorawa kaddarar fitar rabo. Cuta da cutarwa ta zama ruwan dare gama duniya, babu malamai babu jahili, masu hankali da marasa hankali kowa neman hanyar cuta yake, yan kasuwa da masu sari, leburori da iyayan gidansu; daman ma’aikatan gwamnati ya zamar musu tamkar halaliya yin almundahana da kayan hukuma, a sace duk abinda zai iya satuwa, tundaga masu gadi har oga kwata-kwata duk wanda ya samu abin dauka indai na hukuma ne, to gaban kansa yake ya dauka, tamkar wanda ubansa ya mutu ya bar masa gado shi kadai, a sace man jannareto, a sace fanka a saci tabarma da darduma, wani abinma bai kai a sace shi ba, amma saboda tsabar mutuwar zuciya, sai ma’aikata su dinga satar abinda ko kadan ba zai amfanesu ba, illa kawai wani tunani da ya dade da yin tsiro a zukatan al’umma na cewa “raba arne da makami ibada ne” dan haka ake ganin kayan hukuma kamar ganima.

Wannan yanayin shi ne wani irin mawuyacin lokaci da Arewa bata taba mafarkin samun kanta a cikin irinsa ba. Magabatan shugabanninmu sun barmana kyakkyawan abin gado, sun gina harsashin samun ingantacciyar rayuwar wadan da zasu zo baya, sun samar mana da Gidan jaridar NNN da gidan Radio Najeriya Kaduna, da kamfanonin murza auduga na Arewa da Babban Bankin Arewa da makarantun tundaga kwalejoji da jami’o’I da makarantun koyon sana’a, da makarantun horas da malamai da sauransu da dama, amma basu yi sa’ar samun hannu na gari da zai iya alkinta su ba, wannan duk wanda ya san Arewa ya san halin da ta ke ciki zai iya bayar da shaida akan haka. To amma hakikanin gaskiya tafiya tayi tafiya, tura ta kai bango, lokaci ya yi da za’a zauna zama na gaskiya a kalli halin da muke ciki dan dawo da martabarmu da aka yi mana shaida da ita tun a baya.

Haka kuma, lokaci ya yi da zamu ja layi akan dukkan wasu laifuka da muke ta zargin kawukanmu da aikatawa, tunda halin da muke ciki ya shafi kowa da kowa, babu wanda yake walwal cikin jin dadi da kwanciyar hankali, kusakurai an riga anyisu manya da kanana, dan haka, abinda ya kamata mu maida hnaklai shi ne kokarin nemo mafita da bakin zaren halin da muke ciki. Shugabannin baya da kuma wadan da suka nannada kansu Shugabancin Arewa a yanzu duk sunyi abinda zasu iya, wadan da suka tafka ta’adi da wadan da suka yi abin kirki duk sunyi, kuma anga abin da kowa ya yi, Allah ya sakawa kowa da gwargwadon abin day a aikata, idan khairan khairn, idan sharran sharran.

Wata rana Shehu Jaha ya aiki diyarsa ta debo masa ruwa a tulu, sai ya yi mata kashedin kada ta sake ta fasa masa tulu, idan kuwa ta fasa to zasu gauraya, har ta kama hanya ta tafi sai Shehu ya kirata ya tsinko tsumagiya ya shashshauda mata, wani abokinsa ya ce haba Shehu yaya ka gargadeta kar ta fasa, bayan kuma bata fasa ba ka doketa. Sai Sheshu ya kada baki yace, babu amfanin na doketa a lokacin da ta riga ta fasa tulu, domin dukan ba zai sanya tulu ya dawo ba. Kamar misalin haka ne na irin halin da muke ciki, yawan zargin junanmu da laifin halin da muke ciki babu abinda zai kara, illa kara wagegen gibi a tsakaninmu, tunda matsaloli dai ana cikinsu tsamo-tsamo, batun ko laifin su wane ne ko ba laifin su wane bane, duk ya kamata mu wuce wajen, batun da ya kamata mu maida hankali shi ne ta yaya zamu fito daga cikin wannan halin da muke ciki shi ne abinda dukkanmu ya kamata mu maida hankali akai.

Dukkanmu dole mu ji tsoron Allah a cikin al’amuranmu, mu sanya gaskiya da amana a cikin mu’amalolinmu, shugabanni su zama adalai a ajiye komai a inda ya dace, a baiwa kowanne mai hakki hakkinsa, babu wasu mutane daga Ingila ko Faransa ko Amerika da za su zo su fitar dam u daga cikin halin da muke ciki, mune muka san kanmu, muka san halin da muke ciki, muka san irin azaba da radadin da muka shiga ciki, ya zama tilar mu hada karfi da karfe wajen fito da sahihan hanyoyi da zasu amfani ‘yan bayanmu masu zuwa nan gaba. Mu shata layi kamar yadda na fada, ko da bamu yafe irin satar da ‘yan uwanmu suka dibga ba, to mu dakatar da abin haka, kudin hukuma ba na uban kowa bane, na dukkanmu ne, idan mun alkinta dukiyarmu kanmu muka alknta, idan mun barnatar kanmu da jikokinmu muka yiwa illa.

Ya zama dole da Masu mulkinmu na Siyasa wadan da hakkin jagorancinmu yake a hannunsu, da shugabanni masu rike da sarautu, da malamai da kungiyoyi mu samar da wata Hadaka da zata fitar da mu daga cikin halin da muke ciki. Kamar yadda aka samu hadewar jam’iyyu dan kawai ga gaci da samun nasara, muma dole sai mun hade kanmu mun hade kungiyoyinmu, sannan mu samu nasarar fita daga cikin wannan mawuyacin halin da muke ciki. Akasin haka, babu abinda zai yi mana illa kara jefa mu cikin bakin ciki da damuwa da ba za su iya yi mana maganin halin da muke ciki ba, idan banda kara nesanta mud a juna. Dole mu dawo da ‘yan uwantaka tsakaninmu da kaunar juna, da taimakekeniya, mu cire kyashi, mu daina hassada, mu yiwa kanmu tarbiyyar hakuri da halin ‘yan uwanmu, mu kuma yi hakuri da halin talauci da kuma baiwa mawadatanmu uzuri. Ya Allah ka karkato da hankulanmu gaba daya mu fahimci juna dan ciyar da Arewa da Addininmu gaba, Allah ka taimakemu ba dan halinmu ba, ba dan munanan ayyukan da wasu daga cikinmu suka aikata ba. Allah ka taimakemu ka sa wannan shi ne lokacin da zamu yi ban-kwana da dukkan irin sarkakiyar da muke ciki da wahalar rayuwa. Allah ya taimaki Arewa da Najeriya baki daya.

Yasir Ramadan Gwale 26-10-2-13

Ojukwu Da Rawar Da Ya Taka A Juyin Mulkin Janairun 1966


OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN MULKIN 1966!!! (4)

A shekarun baya irin wancan ra’ayi na bayar da kariya ga Ojukwu da mutane irin sa na fitowa ne daga kudu. Ko a 1987 a wani littafi nasa mai suna “Nzeogwu” Chif Obasanjo ya bayyana Nzeogwu da mutumin kirki, mai saukin kai, mai hangen nesa da tausayi. To a yau gashi ‘yan Arewa sun fara, Sai muce Allah ya sauwaka. Don haka dalilan da zasu sa wani koyi da marigayi Ojukwu, koda kuwa ibo ne, marasa tushe ne. Balle kuma ace dan Arewa da yakai matsayin gwamnan jiha kuma jagoran wamnonin jihohi 19 da a baya suke karkashin kulawar Sardauna.

A dan haka, a bias bayanan da suka gabata a baya, zamu fahimci cewar Ojukwu wani irin mugun mutum ne maketaci mai son tashin hankali da rashin san zaman lafiya, kuma Ojukwu zaka iya kwatantashi da wani irin mugun makiyin Arewa na bugawa a Jarida, duk da irin waccan mugunta da kiyayya da keta ta Ojukwu da bata bar ‘yan kabilar Ibo ba, to wai har wani mutimin Arewa da yake takama da cewa shi ne magajin Sardauna a yanzu domin shi ne yake jagorancin Gwamnonin Arewar su Sardauna. Anya kuwa wannan mutumin ba Inyamuri bane da rigar Hausawa? Ko kuma irin inyamuran nan ne da aka Haifa a Arewa kamar yadda shi kansa Ojukwu din a jihar Neja inda Babangida Aliyu yake Gwamna aka haifar, Lallai ina mai cike da shakkun cewar da kyar idan Babban Hadimin jihar Neja kamar yadda ya kira kansa shi ma ba Inyamuri bane haihuwar Arewa. Amma dai komai daren dadewa tarihi baya karya.

Akwai da yawa daga cikin Inyamurai da suke da waccan muguwar Aqidah ta kakkabe mutanan Arewa daga harkar Gwamnati kamar yadda Ironsi da Ojukwu suka nuna aiwatarwa, domin sojojin da suka kasha su Balewa da Sardauna da Zakariya Maimalari das u Akintola ai duk said a Ironsi ya yi musu Karin girma, sannan ya zabge sojojin Musulmi ‘yan Arewa da kuma Musulmi daga bangaren Yamma na Yarabawa, sannan ya yi Karin girma ga mutum 25 kamar yadda muka bayyana a baya amma mutum 3 ne kcal Musulmi ‘yan Arewa a yayin da mutum 1 ne kacal daga yankin Yamma na Yarbawa.

To tarihi fa shi yake maimaita kansa. Yanzu irin waccan muguwar Aqida ta su Ojukwu da Ironsi ita shugaban sojojin Najeriya na yanzu Laftanar Kanar Ihejirika yake aiwatarwa a kaikaice. Inda idan bamu manta ba, a kwanakin baya ya zabge manya-manya sojojin kasarnan Musulmi gaba dayansu Hausawa da Yarabawa kuma, yam aye gurbinsu da Ibo Inyamurai gabaki daya babu kunya babu tsoron Allah, Shugaban kasa kuma yana ji yana gani ya kasha kunnensa domin dadawa Inyamurai kamar yadda a kullum yake nuna cewar shi fan a sune.

Haka kuma, a irin yadda ake kwashewa ‘yan Arewa Musulmi kafafu a dibar sopjoji a makarantar horon soji ta NDA dake Kaduna zaka kara fuskantar akwai wasu boyayyun lamura a harkar tafiyar da al’amarin soja a kasarnan, domin a mafiya yawancin jihohin da suke da Kiristoci sai da aka fifita su akan Musulmi a wajen daukar adadi,\. Duk wannan fa yana faruwa bayan irin yadda ake yi mana kisan Mummuke da sunan farautar ‘yan Ta’adda a yankin Arewa maso gabas, wanda rahotanni sun nuna cewar galibin sojojin da aka jibge a wannan yanki Inyamurai ne ‘yan kabilar Ibo, suke ta karkashe mana mutane babu ji babu gani da sunan ta’addanci, wanda ko a baya-bayannan sai asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya bayar da sanarwar cewar sojojin rundunar JTF sun kawo gawarwakin mutane sama da 3000 asibitin a cikin kasa da shekara daya! Lallai akwai lauje a cikin kunshin rundunar sojojin Najeriya.

Lallai ya zama dole Mu ‘yan Arewa mu yi karatun baya mu tuna abubuwan da suka faru a baya, sannan mu kalli abubuwan da suke faruwa a yanzu da wadanda zasu iya faruwa a nan gaba, dan tunanin Makomarmu, idan kuwa bah aka ba, muna ji muna gani Ojukwu zai dawo da wata rigar daban ya kashe kashewa iya san ransa, wadan da suka yi saura kuma ya tarwatsa zuwa kasashen Nijar da Chadi da Kamaru kamar yadda a bayyane take cewar da yawan ‘yan Jihar Borno suna samun mafaka a wadannan makotan kasashe.

Idan mun ki ji shakka babu ba zamu ki gani ba.

Yasir Ramadan Gwale da Mustapha Ibrahim suka yi hidimar kawo wannan tarihi.

Ojukwu Da Rawar Da Ya Taka A Juyin Mulkin Janairun 1966



OJUKWU DA RAWAR DA YA TAKA A JUYIN MULKIN 1966!!! (3)


Ga ‘yan Najeriya da basu san Ojukwu ba har suke zaton bashi da hannu a aika aikar janairun 1966 su sani :rahoto ya inganta cewa Ojukwu ya fita kasashen waje ba da sanin ofishin sa ba a 9 zuwa 13 ga janairu. Wani jami’ain soja dake aiki a kano ya tabbabar da haka. Domin a jirgi daya suka fita daga kasar tare das hi Ojukwu. A 14 ga wata kuma Ojukwu ya shiga garin Kaduna- yamma zuwa farkon dare tare da wata mata da ya ajiye a Hamdala Hotel ya gana da wasu mutane. Wanda ya fitar da maganar yasan matar. Ya tambayeta bayan nan kuma ta tabbatar masa da hakan. Awoyin farko na 15 ga wata ya mamaye filin jirgi da Gidan radio a kano bisa tunanin manyan Arewa zasu sulalo don gudun hijira… duba littafin Let Truth be Told na David Muffett.

Chif Christian Onoh, shima, tsohon gwamnan Anambara, amini kuma suruki ga Ojukwu cewa yake “tun Disambar 1964 zuwa Janairun 1965 Ojukwu yaso yin juyin mulki. Da hakan bata samu ba sai ya yaudari wasu yara 5 masu mukamin Manjor don cimma burin sa a 1966. Bayan matasan sun kwace kasar sai wasu manyan soja bisa jagorancin Ironsi Mai-kada suka murkushe su (juyin mulki cikin juyin mulki). Ganin haka sai Ojukwu ya juya wa wadancan kananan sojoji baya da yin biyayya ga Ironsi. Bai’ar da yayi tasa Ironsi nada shi gwamnan jihar gabas. Samun wannan matsayi ta sashi wulakanta Azikiwe da yake ganin yazame masa kadangaren bakin tulu ga kasancewar sa shugaban kasa. (C.C Onoh yaci gaba da cewa) ta kai ga Azikiwe rubuta takardar koke ga Ironsi don ya tsawata wa Ojukwu. Wannan Fada ya faro ne daga lokacin da Ojukwu ya roki Azikiwe daya bashi hadin kai don kawar da Tafawa Balewa a 1964, shi kuma wancan tintirin jahili (kamar yadda yake kwatanta Ironsi) watau Birgediya Ironsi suyi masa ritaya. Da yin haka sai Azikiwe ya zama shugaban wucin gadi ko Piraminista shi kuma ya zama shugaban sojoji. A cewar sa hakan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa. A matsayin Azikiwe na wanda ya yarda da dimokaradiyya, yaki yarda. Daga nan basu kara zama inuwa daya da Ojukwu ba.

Hadin kan da Zik bai bayar ba yasa Ojukwu yaudarar wadancan tsageru. Ya tsara yadda zasu kawar da Ironsi a matsayin Shugaban Hafsan-hafsoshin sojojin Najeriya da Tafawa Balewa Prime-Minister a Lagos da yadda zasu kame Gidan radiyo da bayyana shi a shugaban gwamnati kuma jagoran sojojin Najeriya gaba daya.

(C.C Onoh ya kara da cewa) kashe Ironsi dai bai samu ba, karshe ma ya amshe ragamar gaba daya. Dole Ojukwu ya mika wuya, shi kuma ya saka masa da gwamnan yankin gabas… Wannan bayani yana nan cikin wani karamin littafi da Farfesa Tom Forsyth yarubuta mai suna The Heroes Of Change.

Ga mai neman sanin abin da ya faru a janairun 1966 lallai dole ya shiga duhu ya kuma shiga haske. A Arewa Magana daya ce, saboda hadamar mulki aka zabi madaukakan ta aka kashe da gangan. Hasken kenan. Amma a inda duhun yake shi ne a kudu musamman yankin gabas inda makasan suka fito. kowa so yake ace shi gwani ne. shi ne mafifici cikin inyamurai. Tahsabuhum jami’a, wakulubuhumut-shaattah, sun hada baki amma zuciyar su a rarrabe. Ojukwu ya kitsa juyi don zama shugaban kasa, akayi juyi shugabanci bai samu ba. Ironsi ya zama shugaban kasa ba da son Ojukwu ba. shi kuma Ojukwu daya kafa Biafra, Nzeogwu bai so ba. Dalili kenan ma ya ra’ba ya har’be shi a wani artabu kusa da garin Nsukka. Bayan nan ya hallaka Ifeajuna wai suna shirin yi masa juyin mulki a kasar Biafra. A dunkule Ojukwu da mutanen sa sun so danne yan Arewa ne, Allah bai basu dama ba.

A shekarun baya irin wancan ra’ayi na bayar da kariya ga Ojukwu da mutane irin sa na fitowa ne daga kudu. Ko a 1987 a wani littafi nasa mai suna “Nzeogwu” Chif Obasanjo ya bayyana Nzeogwu da mutumin kirki, mai saukin kai, mai hangen nesa da tausayi. To a yau gashi ‘yan Arewa sun fara. Sai muce Allah ya sauwaka. Don haka dalilan da zasu sa wani koyi da marigayi Ojukwu, koda kuwa ibo ne, marasa tushe ne. Balle kuma ace dan Arewa da yakai matsayin gwamnan jiha kuma jagoran gwamnonin jihohi 19 da a baya suke karkashin kulawar Sardauna.