Sunday, January 25, 2015

SA'UDIYYA: Najeriya Ta Mika Ta'aziyar Rasuwar Sarki Abdullah


SA'UDIYYA: Najeriya Ta Mika Ta'aziyar Rasuwar Sarki Abdullah

Mataimakin Shugaban Kasa Alh. Muhammad Namadi(na) Sombo jiya a Riyadh a lokacin da yake wakiltar 'yan Nigeria wajen mika ta'aziyar rasuwar Sarki Abdullah Marigayi. Shugabanni kasashen duniya na cigaba da yin turuwa zuwa Sa'udiyya dan yin Ta'aziya da kuma taya sabon Sarki Salman murnar.

Yasir Ramadan Gwale
25-01-2015

"Malam Yasir Wallahi Zan Zabi Malam Takai Saboda Kai"



"MALAM YASIR WALLAHI ZAN ZABI TAKAI SABODA KAI"

Jiya wani dan uwa aboki kuma amini ya shaida min cewa wallahi shi zai zabi Malam Saluhu Sagir Takai ne saboda ni. Ya shaida min cewa shi baya PDP amma albarkacina zai zabi Malam Salihu Takai. Ba shakka wannan magana ta faranta min Rai na kuma ji dadinta matuka. Wannan dan uwa ya nuna min kauna kuma yayi min kara, Allah ya saka masa da alheri ya barzumunci da kauna.

Ya Allah muna rokonka da sunayanka tsarkaka madaukaka. Ya Allah ka baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan Kano. Allah ka sa mulkin ya zamar masa sila ta budewar kofofin alheri a jihar Kano baki daya. Ya Allah mun kyautata zato a gareka, kai mai ji ne mai kuma amsawa ne. Allah kaine kace mu rokeka zaka amsa mana Ya Allah ka baiwa Malam Salihu Sagir Takai Gwamnan kano.

Ya Allah ka sani muna kaunar Takai sakamakon kyawawan halayensa da dabi'unsa na zahiri da suka bayyana a garemu. Allah ka tabbatar da duga dugansa wajen yi maka da'a da biyayya. Allah ka bashi ikon tsare gaskiya da mutuncin al'ummar Jihar Kano.

25-01-2015

Friday, January 23, 2015

SAUDIYYA: Sabon Sarki Salman Ya Karbi Mubayi'ah


SAUDIYYA: SABON SARKI SALMAN YA KARBI MUBAYI'AH

Khadimul Haramain Ash-Sherifain Sarki Salman Bin Abdulaziz Alsaud yayi jawabin karbar mubayi'ah. Sarki Salman ya taya al'ummar Musulmi da al'ummar Sa'udiyya ta'aziyar rasuwar King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud, ya yabawa magabancinsa tare da yi masa adduar samun Rahama, ya kuma ci alwashin dorawa daga inda Abdullah ya tsaya. 

Sarkin Ya kuma bayyana Yarima Mukrim Bin Abdulaziz Alsaud a matsayin sabon Yarima Mai Jiran gado (crown Prince) da kuma Muhammad Bin Nayef Bin Abdulaziz amatsayin mataimakin Yarima Mai Jiran gado, Sarkin ya kuma bada sanarwar nada Yarima Muhammad Bin Salman a matsayin ministan tsoro. 

Allah ya yi masa jagoranci ya bashi ikon hidimtawa addini fiye da magabatansa. Allah ya jikan Marigayi Sarki Abdullah ya gafarta masa, ya lullube shi da RahamarSa, Allah ya kyauta namu zuwan ya sa Aljannah ce makomarmu baki daya.

Yasir Ramadan Gwale
23-01-2015

Thursday, January 22, 2015

Sarkin Saudiyya Na Shida (6) Abdullah Ya Kwanta Dama



SARKIN SAUDIYYA NA 6: ABDALLAH YA KWANTA DAMA

Yau juma’a daya daga cikin manyan ranaku a Musulunci, Allah ya karbi rayuwar Sarki Abdullah Ibn AbdulAzizi Al-Saoud na Saudiyya. Allah yayi Sarki Abdullah rasuwa bayan ya sha fama da jinya ba mai tsanani ba, kamar yadda rahotanni suka nuna Sarki Abddullah ya jima yana fama da cutar Numoniya har zuwa lokacin da hukumomi a Riyad suka bayar da labarin kwantar da shi a wani asibii dake Riyar a makwannin da suka wuce. Abdullah Ibn AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya, ya rasu yabar ‘ya ‘ya da jikoki masu yawa, haka kuma, Sarki Abdullah shi ne Sarki na Shida (6) tun bayan kafa daular Saudiyya a Shekarar 1930.

Marigayi Sarki AbdulAziz Ibn Abdulrahman Ibn Muhammad AlSaud wanda ake yiwa lakabi da Abu-Turki Akhu-Noura, shi ne ya jagoranci Jihadin kafa Daular Sa’udiyya a yankin Hijaz. Bayan rasuwar Sarki AbdulAziz Alsaud a shekarar 1953, yarima mai jiran gado wanda shi ne babban dansa Sa'ud Ibn AbdulAziz ya gajeshi a matsayin Sabon Sarki na biyu bayan kafa Mamlakatul Araabiyat Ass-Sa’udiyya.

Sarki Saud Ibn AbdulAziz ya karbi Sarauta daga mahaifinsa har zuwa shekarar 1964 lokacin da Allah yayi masa rasuwa. Kafin rasuwarsa Saud Ibn AbdulAziz shi ne wanda ya fara samar da majalisar ministoci a masarautar da suka hada da Ilimi, lafiya da kuma kasuwanci. Haka kuma, Sarki Sau’d ya zabi Gwamnan Riyad na lokacin wanda shi ne kaninsa Faisal Ibn AbdulAziz a matsayin Yarima mai jiran gado, inda bayan rasuwarsa Yarima Faisal Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki na uku.

Sarki Faisal shi ne mutumin da ake ganin har yanzu Sa’udiyya bata yi shugaba kamarsa ba, ana ruwaito Sarki Faisal a matsayin wani mutum mai ra’ayin bin addini sau da kafa, mutum ne mai san yin abu da gaggawa, bai cika wasaba, an bayyana shi a matsayin mutumin da bai cika yin dariya a bainar jama’a ba. Kullum maganarsa itace yadda za’a ciyar da addinin Musulunci gaba da kasashen.
A lokacin Sarki Faisal ne Masarautar Sa’udiyya ta fara samar da kamfanoni da kulla alaka da kasashen Gulf dan habaka tattalin arzikin yankin. Sarki Faisal ne ya jagoranci kafa kungiyaar kasashen Musulmi ta OIC, haka kuma, shi ne Sarkin da ya kafa garin Jeddah a matsayin cibiya ta kasuwanci. Sarki Faisal ya damu da harkokin addini ainun a zamanin Mulkinsa.

Sarki Faisal ya rasu a shekarar 1975, inda bayan rasuwarsa ne Yarima na lokacin kuma Gwamnan Riyadh, Khalid Ibn AbdulAziz ya zama sabon Sarki na hudu. Sarki Khalid shi ne Sarki na Farko da ya fara tsallaka Hijaz zuwa kasar Amurka domin yin ziyara da kuma bude ido. Sarki Khalid yayi kokari wajen kulla alakar kasuwanci tsakanin kasashen yankin Gulf inda ya samar da kungiyar GCC da ta hada Qatar, Kuwait, Bahrain, Oman, Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Saudiyya.
Bayan da Allah ya yiwa Sarki Khalid Rasuwa a shekarar 1982 ne Fahad Ibn AbdulAziz ya zama sabon sarki. Sarki Fahad shi ne Sarki mafi dade a kan karagar Mulkin Saudiyya domin ya shafe Shekaru 23 a matsayin Sarki. Sannan kuma, shi ne mutum na farko da aka fara yiwa lakabi da Khadimul Haramain Ash-Sherifain (Custodian of the two holy mosques), Sarki fahad ya kawo sauye sauye masu yawa a kasar Saudiyya ta fuskar lafiya da ilimi da gina kasa da habaka tattalin arziki.

Haka kuma, Sarki Fahad shi ne mutumin da ya tsaya kai da fata wajen ganin an samu ‘yantacciyar kasar Palasdinu, da kuma tsayawa wajen warware mamayar da Iraqi ta yiwa Kuwaiti, haka kuma ya tsaya kai da fata wajen ganin an warware rikicin kasashen Bosnia-Herzegovina, Kosovo, Checniya, Afghanistan, Somaliya da kuma yankin Kahsmir. Bayan haka, a lokacin Sarki Fahad ya maida hankali wajen taimakawa kasashen Musulmi matalauta da suka hada da Somaliya da Bosniya da Afghanistan da sauransu. Allah ya yiwa Sarki Fahad rasuwa a shekarar 2005, inda Yarima mai jiran gado Marigayi Abdullah ya gajeshi, Abdullah shi ne mutumin da yafi kowa daukan lokaci a matsayin Yarima mai jiran gado.

Bayan zamansa Sarki na shida ne Abdullah Bin AbdulAziz ya zabi kaninsa Nayef a matsayin Yarima mai jiran gado, sai dai cikin kaddararSa Subhanahu Wata’ala, Yarima Nayef ya riga Sarki Abdullah rasuwa, inda aka maye gurbinsa da Yarima Salman a matsayin sabon yarima mai jiran gado. Sarki Abdullah za’a jima ba’a manta da shi ba, domin ya cigaba da amsa sunan Khadimul Haramain Ash-Sherifain inda ya kawo sauye sauye masu yawa a Masallacin Makkah da Madina da ba’a taba gani ba a tarihin Saudiyyah. Yayi aiki tukuru wajen ganin ya hidimtawa Masallatan Allah masu alfarma. Ya taimaki addinin Allah gwargwadan iko.

Sarki Abdullah ya samar da manya-manyan jami’o’in kimiyya da fasaha da kere-kere guda biyu da suka hada da Jami’ar King AbdulAzizi da kuma Jami’ai Noura ‘yar uwar mahainsu. Kafin zamansa Sarki Abdullah ya rike mukamai da yawa na Minista inda ya rike ministan tsaro da kasuwanci da cikingida sannan ya zama Gwamnan Riyadh. Sarki Abdullah Bin AbdulAzizi ya rasu yana da Shekaru 90 a duniya a lokacin da Saudiyya ta cika Shekaru 84 da kafuwa. Za a jima ana tunawa da Sarki King Abdullah bin Abdulaziz Al Saud wajen tsayawarsa kai da fata akan kasar Bahrain wajen ganin bata fada hannun 'yan Shiah ba.

Yanzu dai Yarima Salman Ibn AbdulAziz dan shekara 79 shi ne zai zama sabon Sarki na bakwai (7), inda shima ya zabi wani matsahi Yarima Mukrim a matsayin mai jiran gado, kuma shi ne ake zaton mutum na karshe daga ‘ya ‘yan AbdulAziz da zai rike Sarautar Mahaifinsu. Yau in sha Allah bayan kamala Sallar Juma’ah za ayi jana’izar Sarki Abdullah. Muna yi masa adduar Allah ya jikansa ya gafarta masa ya sa Aljannah ce makomarsa, Allah ya biyashi ladan hidimar da yayi dakunanSa masu alfarma a Makkah da Madina, Allah ka yafe masa kurakuransa. Allah ya kyauta bayansa. Allah ka jikan Musulmi.

Yasir Ramadan Gwale
22-01-2015

Sunday, January 18, 2015

Kuskuren Wasu Musulmi Akan Jaridar Kasar Faransa


KUSKUREN WASU MUSULMI AKAN JARIDAR FARANSA

Nakan ga mutane da yawa na yada wasu hotuna na wadan da ba Musulmi ba, da suka yi maganganu na yabawa tare da jinjina ga fiyayyan Halitta Manzon Allah SAW. Ai a matsayinmu na Musulmi tuni Allah ya bamu labarin waye Manzon Allah a cikin alQuraani, yanzu mu da Allah ya bamu labarin ManonSa Sallallahu Alaihi Wasallam, har akwai wani arne da zamu dinga yada maganarsa dan ya yabi Manzon Allah? Duk abin da wani mushuriki daga Mushirikan wannan zamin zai fada na yabawa Manzon Allah, ba zai amfaneshi da komai ba idan bai yi Imani da shi ba, haka kuma, duk wani abu da zai fada bai kai ABU-TALIB ba. Dan haka, idan zamu yada kyawawan Maganganu da aka fada akan Manzon Allah SAW, mu koma cikin al-qurani muji me Allah yace akan ManzonSa Sallallahu AlaihiWasallam.

Haka kuma, yana da kyau mu sani, da yawa masu yada hotunan wannan jarida suna taimakawa gidan jaridar ne wajen yada hotunan. Ba daidai bane, dan mutum zai yada bayanan wannan Jarida sai ya sanya zanen batancin da sukayi akan fiyayyan halitta dan nuna munin aikin da suka yi. Lallai mutane su kaucewa yada hotunan wannan La'anniyar Jarida kuma a yi ta La'antar jaridar.

Sannana kuma, duk wanda zai La'anci wannan Jaridar lallai ne ya halarto da 'yan SHIAH a cikin la'antar tasa. Domin 'yan SHIA sune suka fara zana hoton Manzon Allah suka nuna shi ya daga hannun Sayyadun Aliyu Ibn Abi-talib a matsayin Khalifa. Mabiya Addinin SHIAH sune suka fara yiwa Musulunci zagon kasa kafin wasu arna suyi. Dan haka babban kuskure ne, mutane su dinga La'antar Jaridar kasar Faransa ba tare da sun La'anci 'yan SHIAH masu zana hotan Manzon Allah SAW da Iayalan gidansa ba.

Muna yin Bakarariyar adduar akan duk wanda ya zana hoto yace Manzon Allah ne, ko waye shi Ya Allah ka tsine masa albarka, Allah ka wulakantashi ka La'anceshi, ka kumbura cikinsa, kasa yayi mutuwar wulakanci. Allah ka wargaza shirinsu da sha'aninsu. Allah kar ka basu zaman lafiya da nutsuwa da kwanciyar hankali. Wannan Adduah zamu cigaba da yinta akan wannan La'ananniyar Jarida da kuma 'yan SHIAH masu zana hoton Manzon Allah da iyalan gidansa.

Haka kuma, wannan ba shi ne dalilin da zai sa a farwa wadan da ba Musulmi ba, da basu san hawa ba basu san sauka ba. Arna irinsu Devid David Cameron da suke daurewa wannan cin fuskar addinin gindi suma mu dinga halarto su muna tsine musu. Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai.

Yasir Ramadan Gwale
18-01-2015

Tuesday, January 13, 2015

NIGER: Ya Zama Dole Shugaba Mouhammadou Isoufou Ya La'anci Jaridar Kasar Faransa


NIJAR: SHUGABA MOUHAMMADOU ISOUFAOU MUNA JIRAN KA KA NUNA FUSHI AKAN BATANCIN DA JARIDAR FARANSA TAI AKAN MANZON ALLAH SAW

Shugaban Jimhouriyar Nijar Mouhammadou Isoufou na daya daga cikin Shugabannin kasashen duniya 50 da suka hadu a birnin Paris a kwanaki biyu da suka wuce, inda suka nuna alhini tare da nuna cikakken goyan baya ga uwargijiyarsu Faransa akan abinda suka kira da "Harin Ta'addanci" da aka kaiwa Jaridar Charlie Hebdo, wacce ta yi batanci ga Manzon Allah, Annabi Muhammadu (SAW). 

Shugaban NIjar Mouhammadou Isoufou ba shi kadai ne shugaban kasar Musulmi da ya halarci wannan gangami ba, akwai shugaban kasar Mali IBK da shugaban Palasdinawa Muhamud Abbas Abu Mazine da Sarkin Jordan. Dukkansu sunyi Allah wadai da abinda akaiwa wannan la'annaniyar Jarida sun kuma tausayawa kasar Faransa da iyalan wadan da aka hallaka. Sai gashi a jiya wannan jarida La'ananniya ta kuma yin zanen batanci ga cikamakin Annabawa Manzon Allah SAW.

Ba shakka, wannan ya zama wajibi ga Shugaba Isoufou da ke zaman kwabci a garemu, muyi kira a gareshi da kakkarfar Murya akan ya fito fili yayi Allah wadai da wannan aikin ta'addanci da wannan Jarida tayi, ko kuma mu lissafashi sahun makiya musulunci, masu yiwa addinin Allah zagon kasa. Wadan da suka fifita martabar Duniya kan ta lahira. Martabar Manzon Allah tafi Martabar kasar Faransa da tarayyar Turai a idan al'ummar Musulmin Kasar NIjar baki daya. Dan haka muna kira ga Shugaba Isoufou da ya fito fili balo-balo yayi Allah wadai da wannan jarida kamar yadda yayi Allah-wadai ga maharan da suka kashe ma'aikatan ta.

Allah ya taimaki Musulunci da Musulmi ya kaskantar da kafirci da kafirai. Allah ka rusa wannan Jarida ka hada su da dukkan dangin bala'in duniya da lahira. Allah ka lalatasu ka wargaza sha'aninsu gaba daya.

YASIR RAMADAN GWALE
13-01-2015

Monday, January 12, 2015

Me Zai Hana A Gano 'Yan Matan Chibok?


IDAN HAR ZA'A IYA GANO JIRGIN AIR ASIA, ME ZAI HANA A GANO 'YAN MATAN CHIBOK?

Hukumomi a Jakarta-Indonesia sun bayar da sanarwa tsamo baraguzan jigin saman kamfanin Air Asia da ya lume a ruwa da kusan mutane 170. Bayan an tsamo gawarwakinsu an kuma tsamo dagargazazzun baraguzan jirgin daga cikin teku, sannan abu mafi muhimmanci, shi ne, an gano jakar da ake kira Bakin Akwatu, dan samun bayanan yadda jirgin ya fadi.

Shi dai wannan Jirgi na Air Asia, an daina jin duriyarsa ne gaba daya bayan da rahotanni suka ce ya tashi daga Surabayo a kasar Indonesia zuwa Singapore. Jirgin ya bace bat, kamar yadda hakan ta faru a makwabciyar Indonesia wato Malaysia a Shekarar da ta gabata. Tun daga nan, aka shiga laluben inda jirgin ya shiga, inda aka bazama nema ta sama ta kasa da ta cikin ruwa. Da taimakon Allah masu linkaya suka fara gano alamun cewa jirgin ya lume ne a ruwa.

Hukumomi a Jakarta sun dukufa haikan, wajen tsananta bincike a ruwa, har Allah yasa aka kai daidai inda jirgin ya fadi kuma aka tsamo garwakin mutane da yawa, sannan dirka-dirkan baraguzan jirgin da suka tarwatse a ruwa suka lume duk aka lalubo kuma aka dauko su zuwa gabar teku. Wannan wata muhimmiyar Nasara ce da Hukumomi suka ci a Jakarta-Indonesia wajen gano wannan jirgi.

A Najeriya shekarar da ta gabata aka bada labarin sace 'yan mata sama da 200 a makarantar Sakandiren Chibok, wanda kafin sace na Chibok sai da aka sace 10,20,30,40 a garuruwan Miri, Mafa, Konguga da sauransu. Sace 'yan matan Chibok ya daurewa mutane kai da dama a duniya, ta yadda d dama suna mamaki yadda  za'a ce an saci wadannan 'yan mata. Kusan da yawa sun karyata labarin faruwar hakan in banda su Boko Haram sun saki wani faifan Video da ya nuna wani sashe na 'yan matan.

Satar wadannan 'yan Mata ta dauki hankalin duniya sosai. Inda har hakan yayi sanadiyar samar da kungiyar #BringBackOurGils wannan ya karade kusan ko ina a duniya, inda aka dinga ganin manyan mutane da Hash Tag na kiran a dawo da 'yan Matan Chibok da suka hada da Matar Obama, McCain da Piraministan Burtaniya Cameron. Na tabbata wannan al'amari da a wata kasa ne ba Najeriya ba ko Afeika da tuni wani batun ake daban.

Lallai inda gaske ne kasashen duniya su taimakawa Najeriya wajen ganin an ceto wadannan mata na Chibok. Ya kamata kamar yadda muka ga an taru a Paris dan taya faransa Makokin mutane 12, to akalla Shugabannin Afurka gaba daya su taru a garin Chibok dan jajantawa iyayan wadannan 'yan mata, tare da matsawa Gwamnatin Najeriya tayi duk abinda ya kamata wajen ganin an kubutar da 'yan matan Chibok.

Gaskiya a shekarar 2014, batun sace 'yan Matan Chibok shi ne abinda yafi bani mamaki matuka da gaske, abin kamar wasan-kwaikwayo amma kuma gaskiya ne, ace an sace Mata sama da 200 kamar Tumaki. Satar wadannan Mata ba ita ce abu mafi ban mamaki ba, illah yadda akayi aka sace su din, domin a Najeriya wannan ba abin mamaki bane sace mutum, dan an taba sace Gwamna Chris Ngige yana matsayin gwamna aka ce an sace shi. Amma yadda aka sace din shi ne zai fi zama abin mamaki.

Watakila nan da wani lokaci Najeriya ta zama kasa mafi abubuwan al'ajabi a duniya, indai ba al'amura ne suka sauya. Domin abinda ake jin ba zai taba faruwa ba a wata kasar to  Najeriya yana faruwa. Allah ya kyauta.

Yasir Ramadan Gwale
12-01-2015