Tuesday, September 9, 2014

Munir Muhammad Usman


Munir Muhammad Usman: Kani na ne, kuma abokina mun tashi tun muna yara, kwanakin baya ya gamu da jarabawar rayuwa, yayi hadari a bisa abin hawa, har ta kai kuma yau dinnan za'a yi masa aikin tiyata, muna yi masa addu'ar fatan alheri da fatan samun lafiya, Allah ya sa abinda ya sameshi ya zama kaffara a gareshi, Allah kuma ya sa a yi masa fida cikin Nasara. Allah ya baka lafiya Muniru, muna rokon 'yan uwa da su sanya shi a cikin addu'o'insu da bakunansu masu albarka.

YASIR RAMADAN GWALE
09-09-2014

Saturday, September 6, 2014

Makarantar Malam Bambadiya


MAKARANTAR MALAM BAMBADIYA: Ustaz Lawal Adam Gangara kenan yake karbar kyauta daga hannun Farfesa Malumfashi Ibrahim a madadin Yasir Ramadan Gwale dazu a Kaduna, wajen bayar da kyautukan gasar kagaggun Labarai da Makarantar ta shirya. Ina godiya da farin ciki da wannan kyauta, ina kuma fatan alheri ga sauran abokan takara da 'yan makaranta.

YASIR RAMADAN GWALE
06-08-2014

Boko Haram


Manzon Allah SAW yace, a karshen duniya kisa zai yawaita, wanda yake kisa da wanda ake kashewa babu wanda ya san dalilin kisan. Da yawan mutanan da 'yan Boko Haram suke kashewa basu san me suka yi musu ba aka kashe su, watkila idan da za'a tambayi wani dan Boko Haram din sai yace shima bai san dalilin kisan da yayi ba domin shima sashi aka yi (ba-mamaki). Duk wanda yake zaton duniya zata zauna lami-lafiya to ya sauya tunani, domin acikin al'umma akwai waliyyan Allah mutanan kirki wadan da suke umarni da kyakkyawa kuma su yi hani ga mummuna, kuma akwai waliyyan Shaidan, shi Iblis a koda yaushe waliyyansa yana yi musu mummunar huduba ne, yana kawata musu mummunan aiki har su dinga jin babu komai idan sunyi ko da kuwa sun san cewa abinda suka aikata haramun ne, wannan matakin shi ne na kekashewar zuciya Allah ya karemu. Shi yasa da yawa wasu suna yin zina da luwadi da sata, sun san laifi ne, amma suna ganin kamar ba komai, sun gafala cewa direban da yake jan su Iblis ne. Allah kuma labari ya bamu cewa, yana nan yana jiran kowannemu. Allah ka shiryemu shiriya ta gaskiya.

Yasir Ramadan Gwale
06-08-2014

Masu Jihadin Karya


Kungiyoyin Musulunci na 'yan Ta'adda suna fakewa da Musulunci wajen aikata Ta'addanci da cin zarafin Musulmi. Kasashen Yamma na fakewa da kungiyoyin 'yan Ta'adda dan yaki da Musulunci. Shi yasa duk abinda Israela ta ke yi a Ghazza sunansa kare kai a wajensu, Israela kuma na cewa 'yan Hamas ta ke yaka, a yayin da take jefa boma-bamai kan gidajen jama'a. Musulmi da dama an rude su da kafafen yada-labarai na kasashen Turai, da dama suna zaton duk abinda suka ji gaskiya ne.

Yasir Ramadan Gwale
06-08-2014

Tuesday, September 2, 2014

Idan An Bi Ta Barawo . . .


IDAN AN BI TA BARAWO . . .

Jiya an ruwaito cewar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ya manta inda garin Gwoza ya ke, a Borno ne ko a Adamawa abin ya shige masa duhu. Da naji wannan magana sai nace alamu na nuna cewar masu baiwa Shugaban kasa bayanan harkar tsaro a Arewa Maso Gabas basa gaya masa gaskiyar abinda ke faruwa kenan. Ina Gwamnan Borno Kashem Shettima, Ina Sambo Dasuki mai baiwa Shugaban kasa shawara a harkar tsaron kasa, ina Alhaji Aliyu Gusau Ministan tsaron Kasa, ina sabon sufeton 'yan sanda na kasa? Suna ina har Shugaban kasa ya manta inda Gwoza ta ke?

Lallai dole Gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye tare da matsa kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda. Abin akwai tashin hankali ace mutane na guduwa suna barin garuruwansu a Bama da Gwoza saboda ceton rayukansu, tilas ne masu mulki su kiyaye amanar da ke hannunsu.

Ya Allah ka fitar da jihar Borno daga cikin wannan kangi da tashin hankali da ta ke fama da shi. Allah ka dawo da zaman lafiya dawwamamme a wannan yanki na Arewa maso gabas. Yana da kyau mu yawaita addu'o'in samun zaman lafiya a Najeriya mu kuma yi riko da sabubban karbar addu'ah mu kyautata tsakaninmu da Allah. Allahumma Sallim Sallim!!!

Yasir Ramadan Gwale
02-09-2014

Monday, September 1, 2014

Ta'aziya Ga Shahrazad Bibi Farouk


TA'AZIYA GA SHAHRAZAD BIBI FAROUK

Dazu muka samu labarin Allah ya yiwa mahaifin 'yar uwa Shahrazad Ibrahim Faruq rasuwa, Alhaji Farouk Bibi Farouk wanda tsohon mataimakin Gwamnan Kano ne a jamhuriya ta biyu. A madadina ni da Zainab muna mika sakon ta'aziyarmu ga Malama Shahrazad da Rihab bisa rasuwar mahaifinsu. Allah ya jikansa ya gafarta masa, ya sa Al-jannah ce makomarsa. Allah ya basu hakurin jure wannan rashi.

Wa'azi A Kano


WA'AZI A KANO: A 'yan kwanakinnan naga mutane na ta yin rubutu cewar Gwamnantin Kano zata takaita mana yin wa'azi a Kano. Ni kam ban fahimci wannan magana ba, ban kuma ji sahihancin maganar ba. Da farko dai tambaya ta ita ce, shin da gaske ne akwai wannan yunkuri? Sannan ya abin zai kasance (ma'ana hanawar, shin harda shafuka irinsu Facebook, ko kuwa wa'azozi na cikin unguwanni?) Shin wane irin Wa'azi ake nufi, karatuttukan Tafseer da na Hadisai da ake gabatarwa a Masallatai da Majalisai daban-daban a fadin Kano ake nufi, ko kuwa Muhadarori (Lacca) da akan shirya dan zaburar da al'umma idan hali ya samu? Irin Wa'azin Kasa da kungiyar Izala ta ke Shiryawa da Maukibin Qadiriyya da Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara ke jagoranta da kuma taron Adduah da ake yi a fadar Maimartaba Sarkin Kano wanda Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu yake jagoranta duk suma suna cikin abubuwan da za'a hana? Ina matsayin mutanan nan masu yin maci dauke da tutoci sanye da bakaken kaya suna tottoshe hanyoyi suna damun mutane da mugun wari da zarni, suna bata gari da tarin shara duk suma suna cikin wannan doka? Ban sani ba ko Kiristoci suma suna yin Wa'azin kasa da sai na tambaya har da kiristoci wannan abin zai shafa? Sannan wannan doka ce da gwamnati ke son Majalisar Dokoki ta jihar Kano tayi, ko kuwa wani kundin Daftari ne ya baiwa Gwamnati damar sanya wannan doka? Ko kuwa Dikiri (Decree) ne irin na soja mazan fama, dan nasan gwamnan Kano ya taba zama mininstan tsaro ban sani ba ko tsohuwar allura ce ta motsa? Ko ma dai meye Ini da ire-irena muna neman karin bayani akan wannan batu. Duk da na karanta mabanbantan ra'ayoyin abokaina irinsu Danladi Haruna da El-Ameen Daurawa da sauransu da dama da naga sun yi magana akai. Allah ya sa mu samu cikakken bayani.