Monday, September 1, 2014

Wa'azi A Kano


WA'AZI A KANO: A 'yan kwanakinnan naga mutane na ta yin rubutu cewar Gwamnantin Kano zata takaita mana yin wa'azi a Kano. Ni kam ban fahimci wannan magana ba, ban kuma ji sahihancin maganar ba. Da farko dai tambaya ta ita ce, shin da gaske ne akwai wannan yunkuri? Sannan ya abin zai kasance (ma'ana hanawar, shin harda shafuka irinsu Facebook, ko kuwa wa'azozi na cikin unguwanni?) Shin wane irin Wa'azi ake nufi, karatuttukan Tafseer da na Hadisai da ake gabatarwa a Masallatai da Majalisai daban-daban a fadin Kano ake nufi, ko kuwa Muhadarori (Lacca) da akan shirya dan zaburar da al'umma idan hali ya samu? Irin Wa'azin Kasa da kungiyar Izala ta ke Shiryawa da Maukibin Qadiriyya da Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara ke jagoranta da kuma taron Adduah da ake yi a fadar Maimartaba Sarkin Kano wanda Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu yake jagoranta duk suma suna cikin abubuwan da za'a hana? Ina matsayin mutanan nan masu yin maci dauke da tutoci sanye da bakaken kaya suna tottoshe hanyoyi suna damun mutane da mugun wari da zarni, suna bata gari da tarin shara duk suma suna cikin wannan doka? Ban sani ba ko Kiristoci suma suna yin Wa'azin kasa da sai na tambaya har da kiristoci wannan abin zai shafa? Sannan wannan doka ce da gwamnati ke son Majalisar Dokoki ta jihar Kano tayi, ko kuwa wani kundin Daftari ne ya baiwa Gwamnati damar sanya wannan doka? Ko kuwa Dikiri (Decree) ne irin na soja mazan fama, dan nasan gwamnan Kano ya taba zama mininstan tsaro ban sani ba ko tsohuwar allura ce ta motsa? Ko ma dai meye Ini da ire-irena muna neman karin bayani akan wannan batu. Duk da na karanta mabanbantan ra'ayoyin abokaina irinsu Danladi Haruna da El-Ameen Daurawa da sauransu da dama da naga sun yi magana akai. Allah ya sa mu samu cikakken bayani.

No comments:

Post a Comment