IDAN AN BI TA BARAWO . . .
Jiya an ruwaito cewar Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan ya manta inda garin Gwoza ya ke, a Borno ne ko a Adamawa abin ya shige masa duhu. Da naji wannan magana sai nace alamu na nuna cewar masu baiwa Shugaban kasa bayanan harkar tsaro a Arewa Maso Gabas basa gaya masa gaskiyar abinda ke faruwa kenan. Ina Gwamnan Borno Kashem Shettima, Ina Sambo Dasuki mai baiwa Shugaban kasa shawara a harkar tsaron kasa, ina Alhaji Aliyu Gusau Ministan tsaron Kasa, ina sabon sufeton 'yan sanda na kasa? Suna ina har Shugaban kasa ya manta inda Gwoza ta ke?

Lallai dole Gwamnati da hukumomin tsaro su tashi tsaye tare da matsa
kaimi wajen yaki da 'yan ta'adda. Abin akwai tashin hankali ace mutane
na guduwa suna barin garuruwansu a Bama da Gwoza saboda ceton rayukansu,
tilas ne masu mulki su kiyaye amanar da ke hannunsu.
Ya Allah ka fitar da jihar Borno daga cikin wannan kangi da tashin hankali da ta ke fama da shi. Allah ka dawo da zaman lafiya dawwamamme a wannan yanki na Arewa maso gabas. Yana da kyau mu yawaita addu'o'in samun zaman lafiya a Najeriya mu kuma yi riko da sabubban karbar addu'ah mu kyautata tsakaninmu da Allah. Allahumma Sallim Sallim!!!
Yasir Ramadan Gwale
02-09-2014

No comments:
Post a Comment