Friday, February 14, 2014

Me Kae Yi A Afurka Ta Tsakiya Idan Ba ta'addanci Ba!


ME AKE YI A AFURKA TA TSAKIYA IDAN BA TA'ADDANCI BA!

Hakika irin abin da na gani ana nunawa na ta'addanci ban taba ganin irinsa ba a kasar Afurka ta tsakiya. A lokacin da na kalli wani Bidiyo na wani da ake kira MAD DOG yana cin naman mutum hankalina ya yi matukar tashi, abinda nake ji ana cewa wasu na cin naman mutum; sai gashi na gani. Abin ya bani tsoro sosai, babu shakka irin abinda ke faruwa a kasar ya zarce dukkan nau'in ta'addanci. Abin kuma yana faruwa akan idanun jami'an tsaron da aka jijjibge a kasar dan kawo zaman lafiya. Saboda kawai Musulmi ne ake kashewa, ana wawashe gidajensu, ana kone gidjensu tare da rugurguza masallatansu.

Abin mamaki lokacin da Kungiyar Saleka mai rinjayen Musulmi take fatattakar shugaba Bozizi mafi yawancin 'yan kasar sunyi murna da farinciki, duk kuwa da sanin cewar galibin 'yan kungiyar Musulmi ne. Bayan darewarsa shugabancin riko Michal Djotodia, su, 'yan kasar wai ba su dauka Musulmi bane, ana ganin yaje Masallacin juma'a shi kenan hankalin jama'a ya tashi, sai kuma 'yan Anti-balaka dake da makamai suka farwa Musulmi; sai tashin hankali; sai kashe-kashe; sai kone-kone da sace-sace.

A kasar Tchadi kasashen yankin suka tursasawa Shugaba Djotodia sauka daga shugabancin da samun zaman lafiya, da yake shima ba mai son tashin hankali bane ya bi ra'ayin 'yan kasar ya sauka, dan samar da zaman lafiya. 

Faransa ta bayar da soji 1600 tarayyar Afurka ta bada soji 4000 tarayyar Turai tayi alkawarin soji 1000 amma duk suna gani 'yan Jarida suna yada irin yadda ake kashe Musulmi sai dai kawai surutun da su Ban-ki Moon suke yi. Ina Amerika ko duriyarta baka ji tunda ta yi alkawarin taimakawa da kudi. 

Amma a Kwango da Sudan ta Kudu saboda kiristoci ke kashe junansu nan da nan ana lura da abinda ke zuwa yana komowa. Ana ta kokarin yadda za'a sasanta. Babu shakka Allah shi ne gatan Musulmi a duk inda suke, duk wasu masu ihu da ikirarin 'yancin dan adam makaryata ne, tunda gashi nan ba wai danne hakkin Musulmi aka yi ba, namansu danye ake ci duniya tana gani. Amma Allah baya gyangyadi bare bacci, daman kuma ya fada a cikin Sura ta 29 aya ta 2 cewa tsammaninku dan kunyi imani ba zamu jarrabeku ba! Hakika an jarrabi Musulmin Afurka ta tsakiya. Muna rokon Allah ya kai musu mafita da Dauki ta inda basu zata ba.

YASIR RAMADAN GWALE 
14-02-2014

Thursday, February 13, 2014

GENERAL MURTALA MOHAMMED: Najeriya Ta Yi rashin Shugaba


GENERAL MURTALA MUHAMMAD: NAJERIYA TA YI RASHIN SHUGABA

Yau Laraba 13 ga watan fabrairu, tayi dai dai da ranar da marigayi General Murtala Ramat Muhammad ya cika shekaru 38 da rasuwa, kwatankwacin Shekarunsa na rayuwar duniya, Ya rayuwa a duniya Shekaru 38, yanzu ya shafe tsawon wadannan shekaru kwance a Kabarinsa, a irin wannan ranace akayiwa wannan dan tahaliki kisan gilla, awani yunkuri na juyin mulki wanda baici nasaraba. Da ace Gen. Murtala yana raye har wannan shekarar, da ya cika shekaru 76 a wannan duniyar, an haifeshi a shekarar 1938 a tsakiyar birnin kano, Gen. Murtala ya rasu yana matashi domin bai cika shekaru 40 a duniya ba, an kasheshi a lokacin da yake da shekaru 38 da haihuwa, ya rasu yana begen ganin wannan kasar ta sami ingataccen shugabanci, da cigaba mai dorewa, sai dai har yanzu wannan buri da ya rayu kuma ya rasu tare da shi bai cika ba.

Zaiyi kyau a ce gwamnati ta sauya darussan Social Studies domin karantar da yara manyan gobe irin gudunmawa da nagartar mutane irinsu Gen. Murtala Muhammad. Hakika gwarzo ne abin koyi da tarihin kasarnan bazai cika ba idan babu tarihin irin gudunmawar da ya baiwa cigaba da wanzuwar wannan kasa da kuma wannan nahiya tamu ta Afrika, abin kaico, shi ne yara da dama kawai suna ganin hotonsa ne ajikin takardar kudi ta Naira 20 ba tare da sun san hakikanin waye shi ba. Ka kamanta dukkan wani shugaba mai kishin al’umma da son cigabansu da kaunar kasarsa da irin so da kaunar da wannan dan tahaliki ya nunawa wannan kasa, shin ko Asibitin Murtala dake birnin kano da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad da ke Legas da titunan Murtala Muhammad dake galibin jihohin kasarnan sun isa su biya abinda wannan bawan Allah ya yi wa kasarnan a kwanaki 199?

Gen. Murtala kusan ya shafe kwanaki 199 a kan kujerar shugabancin kasar nan a matsayin Head of state, ya hau mulki daga 29 ga watan yuli 1975, zuwa 13 ga watan fabrairun 1976. Murtala shi ne mutum na biyar a jerin shugabannin kasar nan goma sha biyar, a iya tsawon kwanakin da ya shafe yana shugabanci bai kama ko kadangare ya daureba da sunan tuhumarsa da cin amanar kasa, kusan tarihi ya nuna cewa shi ne shugaban da bai taba daure kowaba a mulkin wannan kasar, haka kuma shi ne mutumin da ya fara assasa cewa mulki zai koma hannun farar hula, wanda mataimakinsa da ya dora daga inda ya tsaya Gen. Olushegun Obasanjo ya cika wannan alkawari a shekarar 1977, inda Shehu Aliyu Usman Shagari ya zama zababben shugaban kasa, haka kuma, shi ne ya kirkiro jihohi da dama da kuma inganta al’amarin kananan hukumomi, haka nan kuma shi ne mutumin da ya kafa harsashin maida cibiyar mulki daga Legas zuwa tsakiyar Najeriya inda ake kira Abuja, yanzu mutumin da ya yi wadan nan muhimman ayyukan ya dace tarihi ya mance da shi? Ko shakka babu amsar zata zama a’a, don haka ya zama dole gwamnati ta yi wani tsari domin koyar da yara halayyar mutanan kirki irinsa.

Ance kusan shi ne mutumin da ya fara daidaitawa ma’aikatan gwamnati sahu musamman ta wajen zuwa aiki akan lokaci da hukunta dukkan wanda ya karya doka. A wani littafi da fitaccen marubucin nan Mista Chinua Achebe ya rubuta mai suna The Trouble with Nigeria, ya yi bayanin kwanakin Murtala na farko-farko a mulkin wannan kasa, yace ko wane ma’aikaci na dari-dari da aikinsa da kuma tsoron karya doka musamman a birnin Legas inda nanne fadar gwamnati a wancan lokaci ta ke. Yace sau da yawa Gen. Murtala ya kanyi bazata ya fito kan titi da safe ya tsallaka ba tare da danja ta bashi hannun ba domin ganin matakin da ‘yan sanda zasu dauka, ance wata rana ya tuka mota danja ta tsaidashi amma ya wuce abinsa, da yalo fifa ya kamashi yace sai sunje caji ofis, ya nemi ya bashi dan na goro amma dansandan nan yace atafau, domin laifine akama ka kuma ka bada kudi domin fansa, suna zuwa ofishin ‘yan sanda kawai sai ya ware nadin da ke fuskarsa nan da nan DPO ya gane shugaban kasa ne inda ta ke ya sara masa, yalo fifa kuma yace kafa me naci ban baki ba domin yana tunanin ya gamu da gamonsa. Haka dai Achabe ya cigaba da bayyana Gen. Murtala wajen nuna kwazonsa da jajircewarsa, akan wannan kasa.

Gen. Murtala wadan da suka sanshi, sunce mutumne mai kwarjini da babu alamun wasa a tattare da shi, ance da zarar ya kalleka da ido idan baka da gaskiya sai kaga mutum ya hau tsuma yana kyarma, haka kuma Murtala mutumne da yake son yin abu da gaggawa ba tare da bata lokaci ko jin kiri ba, don haka ne akoda yaushe yake yawan maimaita kalmar "DA GAGGAWA" , Allahu akbar irin mutanan da Arewa ta fitar a wancan loakcin kenan, Bahaushe mutumin kano a birnin ikko ikon Allah. Ance lokacin da yake Head of state gidansa da yake aciki a lokacin da yake rike da mukamin Director of army signal corps kafin zamansa shugaba bai fita daga ciki ba domin haka kullum yake fita daga shi sai direba zuwa Dodan Barrack a Legas, shi mutumne da bai cika son wasa ba, don haka ko jerin gwanon motoci baya yi, haka kuma, baya kunna jiniya a lokacin da yake fita ko dawowa, shi kadai, daga shi sai direbansa suke zuwa kano tun daga Legas a motarsa ba ta gwamnati ba, tafiyar sama da kilomita dubu 1000.

Wani marubuci, Aliyu Ammani ya bayyana Murtala a zaman wani gwarzo a lokacinsa wanda aiki kawai ya sanya a gaba, mutum mai saukin kai kuma maras girman kai. Yace wani tsohon Lauya kuma tsohon malamin jama’ar Legas mai suna Dr. Obarogie Ohanbamu ya rubuta a Mujallarsa mai suna African Spark cewa Gen. Murtala ya azurta kansa kafin ya zama shugaban kasa da mallakar dimbin dukiya da gidaje, amma duk da haka Gen. Murtala baiyi amfani da ikon da yake da shi ba wajen ci masa mutunci ko sanyawa a kameshi tare da gana masa gwale-gwale kamar yadda aka san sojoji da yi a Najeriya, kawai sai ya kai shi kara zuwa Igbosere magistrate Court a Legas domin ayi musa shari’a da mutumin da ya bata masa suna a cikin jarida, ance kotu ta zauna ta saurari wannan kara, kuma ta dage zaman zuwa 17 ga watan maris 1976, Allah mai yadda yaso Gen. Murtala bai riski wannan lokacin ba Allah ya cika masa ajalinsa, sai dai a wata hira da abokin Gen. Murtala na kusa ya yi da jaridar The Punch ta ranar 4 ga watan mayu 1982, marigayi Cif MKO Abiola ya ce Gen. Murtala ya rasu ya bar Naira bakwai da kwabo ashirn da biyu(N7.22) a cikin asusunsa na ajiya, tabdi jan! kaji fa shugaban kasa kenan! Allahu Akbar! Haka kuma ya bar duniya bashida gida ko katuwar gona ko gandun daji da gandun dabbobi.

Ammani, ya cigaba da cewa a ranar 11 ga watan Janairun 1976, Gen. Murtala ya kada hantar kasashen yamma da wata kasida da ya gabatar a taron kasashen Afrika na OAU da akayi a birnin Adis Ababa na kasar Eithiopia akan ‘yancin kasar Angola mai taken Africa has come of age. Gen. Murtala ya yi jawabi kamar haka, ya ce “ ya mai girma shugaba, idan ina tuna irin yadda fararen fata suka bautar tare da nuna wariya ga bakaken fata a kasar Afurka ta kudu, zuciyata tana tafarfasa tana kara bugawa ne, wannan al’amari yana dugunzuma tunani na matuka kamar yadda dukkan wani mai kishi yake jin ciwo idan ya tuna wani abu irin wannan” haka Gen. Murtala ya ci gaba da jawabi yana cewa “ yanzu fa kasar Afurka ta kawo karfi, babu wata kasa da zata cigaba da bamu umarni muna bi, kowacece kuma duk karfinta, dole mu hada karfi da karfe wajen yakar wannan cin-kashi da aikin bauta a cikin 'yanci da akeyi mana domin kwatowa ‘yan uwanmu ‘yanci ko da kuwa hakan zai kai ga salwantar rayuwarmu” Allahu akbar haka ikon Allah yake Gen. Murtala yana wannan jawabi ne a lokacin da tuni Allah ya rubuta cewa kwanaki 34 ne kacal suka rage masa a duniya, haka dai ya cigaba da jawabi mai cike da armashi da kwarin guiwa da nuna rashin tsoro ko gazawa.

Haka Gen. Murtala yake da karfin hali da rashin nuna tsoro ga kuma kwarjini. Kamar yadda marigayi Sunday Awoniyi yace shi mutumne da ko da yake a makaranta a Barewa College Zariya baya fada da sa’anninsa sau da dama zaka samu yana fada da na gaba da shi akan anzalinci na kasa. Kamar yadda masana sukayi bayani ana son shugaba jarumi mai kwarjini maras tsoro da kuma karfin hali, hakika Gen. Murtala ya cika dukkan wadannan abubuwa da suka sanya zai iya zama kowane irin shugaba.

Haka dai mutanan kirki suke cigaba da gushewa a wannan rayuwa, a dai-dai lokacin da ake bukatar juriyarsu da jajircewarsu. Hakika Najeriya ta yi rashin gwarzo abin koyi, daya tamkar da dubu, muna addu’ar Allah ya jikan Gen. Murtala ya kai rahama kabarinsa ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi, Ya Allah ka arzurta wannan al’umma da mutane masu karfin hali da kwazo irin nasa koma wadan da suka fishi. Allah ya jikan General Murtala Ramat Muhammad . . . Yallabai kamar yadda ka nuna kishi da kauna garemu da kuma kasarmu muma muna yimaka addu’ar fatan alheri, duk da nasan bakajina a halin yanzu, amma inada yakinin insha Allah addu’ata zata riskeka. Allah ya hadamu a darussalam da alheri. Bahaushe yana cewa kada Allah ya kawo ranar yabo! Amma nikam ina fatar Allah ya cigaba da nunamin ranar da zan yabi mutanan kwarai irinka. 

Yasir Ramadan Gwale 
13-02-2014

Wednesday, February 12, 2014

Wani Shaidanin Malami A Najeriya



WANI SHAIDANIN MALAMI A NAJERIYA

A Lokacin da Quraishawa suka fito domin Yakar Manzon Allah SAW da Sahabbansa Allah ya yarda da su, a yakin Badar, duk da Sahabban basu da yawa, basu da Makamai, basu Kware a wajen Yaki, amma saida Shaidan yayiwa Mushrukai ta ke yace dasu:

"لاغالب لكم اليوم من الناس واني جار لكم".

"YAU FA BABU WANDA ZAIYI RINJAYE AKANKU,TABBAS KUMA NI INA TARE DAKU".

Amma bayan Shaidan yaga Malaiku suna sauka daga sama da Makamansu, suna kawowa Mumunai da Manzon Allah SAW taimako, sai ya zura a guje, kuma ya kara cewa dasu: "اني برىء منكم اني ارى مالا ترون اني اخاف الله،والله شديد العقاب".

"LALLAI KAM NI BANA TARE DAKU, DON NI INA GANIN ABINDA BAKWA GANI, NI KAM INA JIN TSORON ALLAH, DON ALLAH MAI TSANANIN UQUBA NE".

Hakika Malaman tafsiri sunce Shaidan yazowa Quraishawa ne a cikin Siffar Mutane, ya yi musharaka da su a cikin Shawarwari da kuma farkon Yakin. In Mutane suka lura duk sanda shaidan zaiyi abu tare da Mutane, to cikin Surar shaidan din yake zuwan musu, domin a Lokacin yafi Sharri da kuma tunzurasu. A yanzu ma muna tare da Shaidan a matsayinsa na Mutum, kuma yana nufin ya zuga Mumunai ya hadasu FADA ko kuma yaga suna Kashe Junansu ko ana Kashe su.

Kowa yasan Ahlussunnah wajen bin koyarwar Manzon Allah SAW a lokacin da wata fitina ko Balai ya taso musu, basa daukar doka a hannuwansu, basa afkawa wani domin zargi ko kuma zato. Wannan yana kara sanyawa Jama'a suna kara Fahimtar Sunnah da kuma mabiyanta, da aikinsu a sarari da fili; ba boye boye.

Lokacinda aka Kashe Sheikh Ja'afar Mahmud Adam Rahimahullah, duk duniya an dauka Mumunai zasu fito da rikici da kuma kone kone da sallawantar da dukiyar Jama'a da kisan wadan da basu san hawa ba basu san hausa ba, sai gashi ko ja'ba babu wanda ya Kashe, balle kuma Dan Adam, tunda ba a san Makasan ba. Yanzu ma an Kashe sheikh Auwal Adam Albani Zaria Rahimahullah ,shima ana zaton za ayi tunzuri a kara kashe Jama'a a zaria, amma dai wannan dai koyarwar ta Manzon Allah SAW bata sanya Jama'a sun dauki doka a hannunsu ba.

Kwatsan aka Kawo Sojoji cikin Zaria don kawai suna zaton Mumunai zasuyi Rikici, shima basu sami sa'ar yin hakan ba. Ganin haka ne ya sanya wani Shaidani cikin bakar Alkhabba da rawani, Makaryaci kuma Matsoraci ya fito har yana tutiyar wai Salafawa sun san wanda ya kashe Albani, tsoro ne kawai suke ji suka ki fadan makasan. Burin wannan Sahi dani, shi ne, Mutane su tunzura su fito rikici karnukan Gwamnati su kara hallakasu, sai kuma ya fake da cewa wai shi yasan ko suwaye, kuma zasu fito su fadesu.

1-Abin Tambaya ta yaya ya san haka din?

2-Ko don haka mukaga duk sanda Za'a kama Makamai an shigo dasu Najeriya sai aga 'Yan Shi'a ne, kuma ba ayi musu Komai ba?

3-Yana so yace dama yasan za'ayi Kisan kawai fadane yaki yi, ko kuma sai bayan Kisan aka sanar dashi ko su waye suka yi?

4-Su waye Jami'an Tsaron farin Kayan da suke bashi labari kamar yadda yake cewa???

5-Hakika a fili yake a SOKOTO munga 'Yan Shi'a sunyi kisan kai, kuma Hukumomin Nigeria sun fito dasu wai da tutiyar rashin cikakkiyar shaida (Beyond Reasonable Doubt), amma kuma har yanzu Jama'a basu manta da wannan ba. Dan haka, Ahir Hukumomi suka maida wasu Mutane 'Yan Mowa, wasu kuma 'Yan Bora, domin Hukomomi su bada Tsaro ga wasu, da kuma suka ga abin ya bada Mamaki,s ai kuma suka fito suna neman Wawantar da Mutane. Idonmu a bude yake,muna Karatu ko da wasali ko ba wasali, don haka muna fadake muna ankare muna kuma fadakarwa.

Hattara muke so Hukuma da Sauran Jama'a suyi akan wannan rikici da Wannan Shaidanin Malamin yake Kokarin kawowa a Kasar nan. Allah yasa masu hakkin daukar mataki sun ji,kuma suna gani.

Yasir Ramadan Gwale
12-02-2014

Tuesday, February 11, 2014

Matsalar Shi'ah Ta Su Wa Ye?


MATSALAR SHI'AH TA SU WAYE?

Kusan da dama daga cikin mutane ba su fahimci meye gaskiyar al'amari game da Shi'ah ba. Wa su da dama suna kallon mun cika matsawa da muke yawan magana akan 'Yan Shi'ah, kuma sau da dama, sukan kalli cewar Matsalar Shi'ah ta 'Yan Ahlussunnah ce su ya su! Da daman mutane wadan da basu san komai game da Shi'ah ba haka suke kallo, a saboda haka ne, suke ganin matsantawa ne, zafin Addini ne ya sanya muka cika yin magana akan Shi'anci, dan haka, duk wani Malami ko mai isar da sako da yin Da'awa da zai yi magana akan Shi'ah sai a dinga yi masa kallon ya cika zafin kishi addini, sau da yawa sukan kafa hujja cewa, ai 'yan Shi'ah Musulmi ne, dan haka abar kowa ya yi abinda yaga dama ko ya fahimta a matsayin addini. Masu irin wannan fahimtar a cikinmu suna da yawa, sai dai sau da yawa nakan yi musu Uzurin rashin sanin meye Shi'anci yake dauke da shi.

Matsalar 'Yan Shi'ah ba ta 'yan Salafiyyah/Wahabiyawa/Izala da duk sunan da aka kiramu ba ce, Al'amarin Shi'ah  batu ne da ya shafi Musulunci gaba daya. Domin dukkan Musulmi na hakika sunyi Imani da cewar garin Makkah nan ne ALKIBLAR Musulmin Duniya gaba daya, kuma Makkah nan ne, inda duk Musulmin Duniya suke haduwa dan yin daya daga cikin Ibadu mafi girma a cikin rukunan Musulunci, wanda a bayyane take cewar a tsarin Shi'ah  babu wani abu da ya yi kama da cewa Makkah ko Ka'abah ita ce alkiblarsu, suna ganin Karbala, nan ne birnin mafi tsarki duk duniya, kuma nan ya kamata Musulmi su maida hankali don ya zama Alkibla. Wannan bayyanannen al'amari ne, domin duk wanda ya ji abinda Shugaban Iraki Nuri Maliki ya fadi a yayin bukukuwan Arba'in da Ashura zai gasgata hakan, ko da bai bibiyi ainihin meye Shi'anci ba. Wannan fa, da kansu suke fada, cewa biranen KARBALA da NAJAF sune birane mafiya tsarki duk duniya, suna ganin MAKKAH da MADINA birane ne da suke dauke da Najasa da datti. Wal'iydhu Billah!

Dukkan Musulmi na hakika da ya Yarda da manzancin Annabi Muhammada Sallalahu Alaihi Wasallam, ya sabawa 'Yan Shiah, ya san karya ce kafirci ne, ba Musulunci bane. Irin wadan nan da suke jingina kansu cewa Musulunci suke yi, su ne wasu ke kiran wai an cika matsanta musu. Bayan a bayyane take cewar mutane ne masu dauke da datti da mugunyar Aqidah da ta ke gurbata addinin Musulunci.

Baya ga wannan, ga aibata da zagin Sahabban Manzon Allah SAW wadan da su ne mafiya daraja a cikin al'ummar Manzon Allah bayansa, suna kafitasu da jifansu da munanan kalmomi, ga zagin Matan Manzon Allah SAW iyayan Muminai. Duk wanda ya tashi a cikin Shiah to akan haka aka tarbiyyantar da shi. 

Dan haka kullum Shi'ah ba su da wani aiki sai rabewa jikin Musulmi domin gurbata musu tunani da sahihiyar Aqidah ta Musulunci. Tayaya zamu bari a dauki yaranmu a kaisu Iran domin yin karatu ko wane iri ne? Wasu na kafa hujja da cewar, mutanan da suka tafi ENGLAND da AMERIKA da FARANSA da CANADA da sauran kasashe shin su me ya sa ba'a ce zasu juye zuwa Kiristanci ba, wanda duk wanda ya yi wannan magana, yana da rarraunan tunani game da sanin meye Shi'ah, ai sauyawa Mutum Aqidah abu ne mai sauki ainun akan sauyawa Mutum addini. A iyakar sanina babu wani mutum da ya je Iran Karatu face sai da ya juye zuwa Shi'anci.

Dan haka, dole muyi Allah wadai da duk wani yunkuri na daukar yaranmu dan kaisu Iran neman karatu ko wanne iri ne, komai tsananin bukatarmu gareshi.

Yasir Ramadan Gwale 
11-02-2014

Sunday, February 9, 2014

RE: Ko Shugaban Kasa Bai Isa Ya Gina Coci A Jami'ar Bayero Ba - Galadiman Kano


RE: KO SHUGABAN KASA BAI ISA YA GINA COCI A JAMI'AR BAYERO BA- Galadiman Kano

Jiya na tuntubi makusantan Masarautar Kano dan tabbatar da gaskiyar wannan labari, kuma Alhamdulillah, an tabbatar da cewa wannan al'amari na shari'ar da kungiyar CAN ta kai karar fadar Ma Martaba Sarki akan rushe ginin cocin da aka fara a cikin jami'ar Bayero gaskiya ne, sai dai a yadda aka bada labarin akwai karin gishiri akansa.

Abu na farko dai Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya kai ziyarar gani da ido a wajen da ake gina wannan coci a cikin BUK, amma bayan barinsa wajen babu jimawa wasu suka sauke ginin Cocin amma ba Galadima ne ya basu umarnin yin hakan ba. Daga baya labari ya je wajen Galadima cewar ya sanya an rushe ginin cocin, Mai Girma Galadima ya fusata yace, yaga uban da zai gina cocin a BUK ko za'a gina sau goma sai ya sa an rushe sau goma tunda abin rashin kunya ne. Ya kuma kalubalanci duk wanda yake shakka akan haka, ya kuma ce a fara baiwa Musulmi damar gina Masallaci a jami'ar Fatakwal da Nsukka da sauran jami'o'in kudu kafin su bayar da dama a Kano.

Dan gane da batun Shari'ar kuma, kotu ta zauna har karo biyu ba tare da bayyana wakilan Mai Martaba Sarki ba, kamar yadda su CAN suke karar Mai Martaba Sarki akan Zargin Masarauta ta sanya a rusa ginin cocin, inda suke ganin taya za'a ce ana karar wasu amma sunki bayyana a gaban kotu kuma sun ki turo wakilansu. Wanda tun farko da aka nemi mai Martaba Sarki akan ya bayar da Iznin gina cocin, ya shaida musu cewar ba shi da hurumin a cikin jami'ar Bayero da ya shafi wannan aiki.

Sannan kuma, batun cewa Sakataren Gwamnatin Tarayya ya wakilci Sarki a kotu nan ma ba gaskiya bane, hasalima shi Dr. Anyim su ne suke daurewa CAN gindin samar da cocin. Haka kuma, batun cewar dukkan alkalan kotun da Babbar Mai Shari'ah ta kasa Maryam Aloma Mukhtar su gurfana a gaban Mai Martaba Sarki, wannan ma akwai zukale, fadar Mai Martaba Sarki ta bukaci ganin Justice Maryam Aloma Mukhtar zuwa fada a matsayinta na 'yar Kano. Tun cikin Shari'ah ita Kotu ta bukaci a warware wannan al'amari a wajen Kotu.

Yasir Ramadan Gwale
09-02-2014

Ko Shugaban Kasa Bai Isa Ya Gina Coci A Jami'ar Bayero Ba- Galadiman Kano



KO SHUGABAN KASA BAI ISA YA GINA COCI A JAMI'AR BAYERO BA- Galadiman Kano

Zaman babbar kotun Shariah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta kasa CAN ta kai Masarautar Kano saboda Mai-martaba Sarkin kano Alh Dr Ado Bayero yasa an rushe wata coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero kano (BUK). A zaman koton da akayi a ranar litinin din da ta gabata, kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed, da wakilin kungiyar kiristoci ta kasa, da kuma Mai Martaba Sarkin kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga prof Rasheed da mataimakin shugaban CAN sun mike tare da lauyoyinsu amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba.

Daga nan sai jagoran alkalan kotum Justice Alakola Nweri yace dayake muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kafin wadannan mintoci. Daga nan sai Justice ya dubi prof Rasheed yace a baya Kotu ta baku umarnin Gina coci a jami'ar ko kunbi umarnin kotu? Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi umarnin kotu, dan sai da ginin Cocin ya kai linta sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh Tijjani Hashim ya jagoranci Rushe ginin gaba daya. Justice yace, kuna nufin kenan kunyi watsi da umarnin kotu kunbi na sarki? Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda Sarki Ubanmu ne kuma shi ne Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan sarkin Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi masa biyayya ba.

Daga nan sai Justice ya ya Umarci Farfesa Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa? Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya ne hukumar Makarantar Jami'ar Bayero ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda haka muke rokon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya zauna. sannan kotu ta nemi Sarkin daya bayyana a gabanta, ana haka sai ga Sakataren Gwamnatin Tarayya Dr Anyim Payios Anyim ya bayyana a gaban kotun, anga alkalan kotun sun mike tsaye domin girmamawa ga Dr Anyim, daga nan Dr. Anyim yace ya mai shari'ah ni ne wakilin Mai martaba Sarkin kano Alh. Dr. Ado Bayero, ya umarceni dana wakilceshi a wannan koto domin amsa kira.

Justice yace, kana nufin kana tsaye anan a matsayin Maimartaba Sarki kenan? Dr. Anyim yace kwarai kuwa, kuma duk abinda zan fada ba ni na fada ba His Royal Highness ne ya fada. Justice yace, muna jinka, Dr. Anyim yace, sarki yace na sanar da wannan Kotu shiya sa a rushe Cocin, badan komai ba sai dan basa bukatar ganin cocin a Jami'ar, Sannan yace na gayawa wannan kotu mai daraja cewar, idan za'a gina Coci sau 10 a Jami'ar to kuwa zai sa a rusheta sau 10! Sannan Galadiman kano Alh Tijjani Hasheem yace na gayawa wannan Kotu ko Shugaban kasa Goodluck Jonathan bai isa ya gina Coci ba a harabar Jami'ar Bayero ba tare da yardar Mai Martaba Sarki ba, Dr Anyim ya cigaba da cewa, wannan shi ne sakon da Mai martaba sarkin kano da Mai Girma Galadiman Kano suka turo ni domin na sanarwa da wannan kotu na gode.

Daga nan, anga alkalan kotun suna tattaunawa a tsakaninsu, kafin daga bisani akaga Babbansu ya daga waya yana magana, daga nan sai Alkalin yace to duk munji baya nan ku, dan haka, wannan kotu tana kira ga Shugaban kasa daya duba wannan Lamari idan yaga da yiwuwar gina Cocin to ya bada umarnin ginin, idan kuma yaga ba sai an gina ba to shikenan. Daga karshe kotu ta Sallami wannan Kara kuma tana yiwa Mai Martaba Sarkin Kano fatan alkhairi da fatan Allah ya kara masa lfy da adalci. Wannan shi ne hakikanin abinda ya gudana a wannan Shari'ah da akai.

Sai dai bayan gama wannan Shari'ah, Mai Girma Galadiman Kano, ya bayar da sanarwar cewa Babbar Mai Shari'ah ta kasa Justice Maryam Aloma Mukhtar da Alkalan kotun da suka jagoranci Shar'ar da su gurfana a fadar mai martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero LLD JP.

ME YE GASKIYAR WANNAN LABARIN DA NA GANI A WALL DIN Abba Muhammad Lawan?

Sunday, February 2, 2014

Sheikh Auwal Adam Albani Zaria: Kullu Man Alaiha Faan!

SHEIKH AUWAL ADAM ALBANI: KULLU MAN ALAIHA FAAN

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Daga gareshi muke, kuma gareshi zamu koma Subhanahu Wata'ala. 'Dazu da safenna dan uwa Malam Aminu Sani Musa ya kirani a waya yake yi min ta'aziya. Yasir ya hakuri? Ya tambayeni, hakika gaba na ya fadi, duk da na amsa masa da godiya tare da jiran bayanin dalilin ta'aziyar. Ya sanar da ni cewar wasu 'yan binduga 'yan ta'adda miyagu azzalumai fajirai fasikai zindikai tambadaddu sun kashe Malaminmu Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria! Hakika na ji kaduwa ainun da wannan bakin labari. Na yi masa addu'ar fatan samun rahama a wajen ubangiji.

Babu shakka, Sheikh Adam Albani ya rasu a tafarkin da muke fatan Allah ya dauki rayuwarmu akai. Wannan tafarki da muke kai, hakika an kashe Annabawa da Siddikai da salihan bayi, ba dan sun aikata wani laifi ba, sai dan sun bi tafarkin da Manzon Allah ya zo da shi. Wadan da suke yin wannan kisa, dangi da tsatso ne na wadan can miyagu azzalumai na farko da suke kashe mutanan kirki akan hanyar Allah. Wadan da suke yin wannan kisan, su sani cewa, barazanar kisa da tsoratarwa ba zai bata dusashe sautin gaskiya ba, sautin gaskiya sai ya daga yayi sama yana madaukaki, ko da kafurai da munafukai sun ki.

Ya 'yan uwa, yana da kyau mu tuna cewa, An kashe Sayyadina Umar Bin Khattab an kashe Usman Bin Affan an kashe Aliyu Abul Hasnain, an kashe manyan bayin Allah duk akan wannan tafarki. Irin  Wannan kisa da ake yiwa manyan bayin Allah wanda ya gangaro har kan Malamanmu na wannan zamanin, wani alkhairi ne wanda sai zababbu daga cikin bayin Allah suke tafiya ta wannan hanya. Kisan da aka yiwa Malam Adam Albani a daren jiya babu shakka ya tuna mana mutuwar Marigayi Sheikh Jaafar Adam, duk sun rasu akan wannan tafarki. Wadannan masu kisan ba zasu taba dainawa ba, domin mabiyan shaidan ne, dan Manzon Allah yayi ishara da hakan, a karshen zamani fadace-fadace da kisan babu gaira babu dalilai zai yawaita. Amma, su sani da sannu ajali zai riski kowannenmu ko mai daren dadewa, babu ko shakka akan cewa mutuwarmu ita ke yi mana gadin rayukanmu, lokacin da wa'adi ya yi, wayo da dabara ba zasu taba zama abin dogaro ba.

A saboda haka, yana da kyau mu sani, wannan kuma ba zai taba zama dalili na cewar mu zauna kara zube ana yi mana irin wannan kisan gillah ba. Ya zama dole mu tashi mu kawo karshen wannan al'amari, mu ne zamu baiwa Malamanmu kariya da garuruwanmu da dukiyoyinmu tare da taimakon Allah. Lallai ne dukkan hukumomin tsaron da abin ya shafa su tashi haikan wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma, wajibin gwamnati ne ta Tarayya da ta Jiha su kare martaba da jinin al'ummar da suke shugabanta.

Muna tunawa, miyagu Azzalumai cewar, tunda Manzon Allah Salallahu Alaihi Wasallam ya bar duniya, babu wani mahaluki da zai yi saura a raye. Kowacce rai sai ta dandani zafin mutuwa kamar yadda Sheikh Albani tuni ya dandana nasa, babu wanda zai rage face mai riska ta riske shi. Manyan 'yan Ta'adda na da can da na wannan zamanin sun dandana zafin mutuwa kuma suna ganin sakamakon abinda suka aikata. Ina suke da dama da suka kashe mutanan da basu san hawa ba basu san sauka ba? A ranar Badar da aka kashe Manyan kafurai sai da Manzon Allah SAW ya tsaya a bakin rijiyar da aka zuba gawarwakin Mushrikai ya tambayesu Ya Utbah Ibn Rabi'ah! Ya Shaiba Ibn Rabi'ah shin kun sami alkawarin Allah gaskiya ne! Haka nan suma wadan da suka biyo tafarkinsu zasu samu alkawarin Allah gaskiya ne.

Ina mai amfani da wannan dama wajen taya 'yan uwana dubban jama'a dake ciki da wajen Najeriya ta'aziya da Alhinin wannan gagarumin rashi da mukai, wanda irinsa ne karo na biyu da ya faru garemu ta irin wannan hanya a wannan lokacin. Allah ya jikan Sheikh Adam Albani Zariya da Iyalinsa da Dansa, Allah ka karbesu a matsayin Shahidai, Allah ka daukaka darajarsu. Allah ka jikan Musulmi da duk inda suke. Babu shakka duk inda aka samu babban rashi irin na Malamai dole zukata su kadu hankula su dugunzuma idanu su raurawa, amma mu tuna idan akwai wani rashi da zai dugunzumar da mu shin akwai rashin da ya kai na Manzon Allah SAW? Ya Allah ka kashemu akan wannan tafarki.

Yasir Ramadan Gwale 
02-02-2014