Friday, October 11, 2013

SHEIKH (Dr.) MANSUR IBRAHIM SOKOTO: Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

 
SHEIKH (Dr.) MANSUR IBRAHIM SOKOTO: Zararren Takobin Sunnah Akan 'Yan Shiah!!!

Idan akwai wani Malamin Sunnah wanda kai tsaye zaka ce 'yan Shiah suna kwana da tararrabin bankado irin abinda miyagun litattafansu suka kunsa dan ankarar da al'ummar Musulmi illa da mugunya da ke tattare da wannan ADDINI na Shiah to kai tsaye zaka iya cewa shi ne Dr. Mansur Sokoto. Hakika, Malam Mansur Sokoto ya yiwa Addinin Allah hidima wajen bankado irin miyagun aqidun 'yan Shiah dan Ilmantar da al'umma da nuna musu irin mugun hadarin da yake tattare da 'yan Shiah da kuma shi'anci, Malam ya kutsa cikin tafka-tafkan litattafan 'yan Shiah da suke dauke da guba mai karya garkuwa da lalata tsiga da lakar jikin Imani na hakika, Imani na kadaita ALLAH da Bauta da cikakken Tauhidi.

Manya manyan litattafan Shiah, musamman littafinsu mafi tsarki da girma, wato AL-KAFI wanda daya daga cikin miyagun Malamansu wanda akayi a tsakanin karni na 3 zuwa na 4 wato KULAINI, wannan littafi shi ne mafi girman littafi a wajen 'yan Shia na da da na yanzu, sababbinsu da tsofaffinsu; kuma Shi ne mafi girman wani littafi da ya kunshi sharri da kararirayi da makirci da kutunguila da tufka da warwar akan Sahabban Manzon Allah tsarki ya tabbata a garesu, Malam Mansur ya kutsa cikinsa, inda ya tsiraita kusan kafatanin hujjojin da suke rakitowa daga cikin wannan littafi suke takama da dagawa da su.

Malam Mansur Sokoto ya shahara wajen bayyanawa al'ummar Manzon ALLAH SAW cewa duk inda kaga 'yan Shiah a duniya sun siffanta da wasu suffofi guda uku, wadannan suffofi sune JAHILCI, MAKARYATA NE sannan kuma MASU CANZA GASKIYA NE, wadannan su ne manyan siffofin da zaka iya gane duk inda dan Shiah yake. Dan Shiah duk girman rawaninsa da girman Alkyabbarsa sai ka same shi da irin wadannan siffofi manyansu da kananansu, na farkonsu da na karshensu. Alhamdulillah, da daman al'umma sun fahimci 'yan Shiah yanzu, domin kullum wadannan siffofi kara bayyana suke yi a garesu.

Tarihi bai gushe ba yana tabbatar da duk wasu maganganu da aka fada akan 'yan Shiah, domin tarihi ya shaide su da yin karya, da batar da sawun gaskiya, da canza hakikanin gaskiyar lamura zuwa wasu abubuwan daban, kuma su din mutane ne masu kambama wani abu da bai kai ya kawo ba, dan rudar da al'ummar Musulmi,Kuma tarihi ya shaidesu wajen dakushe gaskiya, da nuna rashin kimarta da rashin bata muhimmanci. Duk wannan abubuwa ne da suke a zahiri wanda tarihi ya shaidi 'yan Shiah da su.

Malam Mansur Sokoto hakika, mutum ne mai saukin kai da taqawa da kamun kai, ga kula da zumunci, duk wanda ya san Malam Mansur Sokoto ya sanshi da zumunci da kaunar 'yan uwa Ahlussunnah. Malam Mansur Sokoto ya yi hidima ainun wajen bayyana miyagun Aqidun Shiah ya kuma rubutu kasidu da litattafai da dama akan haka, Kasidun da ya rubutu a cikin turancin Ingilishi da Hausa ba za su lissafu ba. Haka kuma, ya rubuta litattafai da dama dan bayyanawa al'umma su waye 'yan Shiah, kadan daga cikin muhimman ayyukan da Dr. Mansur ya yi akwai fassara katafaren littafin nan na Ibn Taymiyya na Min-Hajis-Sunnah zuwa Harshen Hausa wanda ya zuwa yanzu babu wani Littafin Hausa da aka taba bugawa da yakai girmansa duk fadin kasarnan, akwai da dama daga cikin litattafan Malam da suka dade a hannun al'umma suna karantawa kamar KUBUTACCEN KARBALA, KADDARA TA RIGA FATA, SU WAYE MASOYAN AHLULBAITI da sauransu da dama, wadan da ba'a kai ga bugawa ba.

Hakika a wannan zaminin da muke ciki musamman a Najeriya ta Arewa idan akwai wani Zararren Takobi da yake yawon a saman kan 'yan Shiah suka firgita suka dimauce suka rasa ina gabas take to la-shakka shi ne Malam Mansur Sokoto. Allah ya taimaki Malam, ya sanyawa rayuwarsa Albarka, ya tsawaita rayuwarsa dan amfanar Addinin Musulunci. Allah ya sanya masa Albarka a cikin zurriyarsa da dukkan lamuransa baki daya. Na tabbata wannan ban fadi komai akan Malam Mansur Sokoto ba, da dama idan sun samu dama zasu yiwa al'umma cikakken bayani sama da wanda na rubuta akan irin hidimar da wannan Bawan Allah ya yiwa Sunnah.

YASIR RAMADAN GWALE
11-10-13

Thursday, October 10, 2013


MUNA KIRA GA GWAMNATIN KANO TA GAGGAUTA KORAR ALI BABA FAGGE

Kalaman da aka ruwaito Hon Ali Baba Agama Lafiya Fagge yana yi akan Malaman Addini cin fuska ne ba wai ga Malaman Addini ba har da Gwamnatin Kano. Hakika damuwa ta kai damuwa, a ce daya daga cikin Mashawartan Gwamna wanda ya kamata yafi kowa taka tsan-tsan da kokarin bin Addini sau da kafa shi ne yake furta irin wadannan munana kalamai masu zubar da kima da mutunci da haiba, wannan abin kaico ne, abin assha ne, abin Alla-wadai ne. Bayanai sun nuna cewar ba wannan ba ne karon farko da shi wannan mutum ya taba yin irin wannan gagarumar katobara ba, a baya ma ya taba yin maganganu masu kama da haka, rahotanni sun same mu cewar Hukumar Hisbah karkashin Jagorancin Mal.Aminu Ibrahim Daurawa ta ja hankalin wannan mutum akan abinda ya fada kuma har ya nuna damuwarsa akan kuskuren da ya yi, da nuna cewa a gafarce shi sharrin shaidan ne.

Abin mamaki sai gashi a jiya ya sake maimaita irin kalaman da ya yi, har ma yana kama sunan kwamandan Hisbar a matsayin daya daga cikin wadan da yake kira da su dinga sayan fina-finan Hausa dan karin samun gogewa wajen yada da'awa. Wannan cikakken rashin mutunci ne da nuna kaiwa maqura wajen nuna dan isakanci da tsageranci da jahilci da gidadanci da kidahumanci da toshewar kwakwalwa. Haka kuma, wadannan kalamai tamkar ya kwancewa gidansu da danginsu zani ne a kasuwa cewar basu bashi wata tarbiyya ta Islama da duk d'a nagari yake samu daga Iyayansa ba.

Lallai muna kira ga Mai girma Gwamna Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ba tare da wata-wata ba ya fito ya nesanta kansa da wadannan munana kalamai na mai bashi shawara ta fuskar Addini, kuma ya gaggauta sallamarsa daga wannan mukami. Dan mutum irin wannan da yake maganganu da suka yi kama da na mai tabin hankali bai kamata a ce shi ne zai baiwa Gwamnati shawara a Addinance ba. Muna nuna bakin cikinmu da damuwarmu da kaiconmu akn wadannan miyagun kalamai da wannan mutumin ya yi. Allah ya raba wannan Gwamnati da mutane irinsu Ali Baba miyagu fandararru masu kafurcewa gaskiya.

Muna yi masa addu'ar Allah ya shirye shi. Amma tabbas wadan nan kalamai zasu jima suna yi mana ciwo a duk sadda muka tuna su.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

Wanne Ne Maganin Musulunci Wanne Na Kafurci?

WANNE NE MAGANIN MUSLUNCI WANNE NA KAFURCI?

Allah SWA bai halicci wata cuta ba face sai da ya halicci maganinta kamar yadda Malamai suka gaya mana. Manzon Allah SWA da kansa ya yi bayanin wasu cututtuka kuma ya yi bayanin maganinsu, haka kuma, Manzon Allah ya bayar da wasu addu'o'i a matsayin garkuwa ta musamman ga wasu cututtuka. Cuta ma'anarta tana da fadi, rashin lafiyar jiki cutane, rashin lafiyar Imani ma cutane, shafar aljanu da dangoginsa duk cutane, dan haka duk wadannan cututtuka babu wata cuta da aka ce ta Musulunci ce ko ta kafurci, kamar yadda Musulmi zai iya kamuwa da kowacce irin cuta haka ma wanda ba Musulmi ba zai iya kamuwa da kowacce irin cuta. Sai dai fa irin garkuwar da manzon Allah SAW ya baiwa Musulmi kamar Azkar na safe da yamma, da Hailala da Salati da karatun al-qur'ani, da sauransu wannan garkuwa ne ga Musulmi.

A saboda haka, babu wani maganin wata cuta da mutum zai ware ya alakanta shi da Musulunci ya nuna duk wanda ba shi ba na kafurci ne, ko da kuwa idan ansha za'a samu sauki. Shaidan ya yi magana manzon Allah SWA ya ce abinda ya fada gaskiya ne, amma shi din makaryaci ne, dan haka ko kafiri ya yi magani sai ka dauki maganin ka barshi da kafurcinsa. Malamai sunyi bayanin cewar duk wani magani da binciken Likitoci ya tabbatar da cewar yana maganin cuta kaza to Wannan maganin ya halatta Musulmi ya yi amfani da shi, matukar ba ayi amfani da wasu sinadarai da suka sabawa Musulunci ba, kamar Alhanzir da sauransu.

Yana da kyau al'umma su fadaka, kada wasu masu tallar magani su dinga yaudararsu da cewa magani kaza na MUSULUNCI ne, sabaninsa kuma na kafurci ne. Da yawan masu tallar irin wadannan magunguna akan samu marasa tsoron Allah su dinga fadawa Mutane zuma da man zaitun da habbatus Sauda da dangoginsu sune maganin Musulunci sabaninsu kuma maganin Nasara ne, eh Musulunci bai hana yin amfani da maganin Nasara ba. Duk wanda ya fada maka haka ya yaudareka, kamar yadda zuma take magani haka bincike na likita ya tabbatar da cewa Kafenol da dangogin Maganin Bature suna yin magani.

Babban kuskure ne mutane su dauka akwai wani kantin saida Magani ISLAMIC CHEMIST, duk wani dakin sayar da magani matukar an gwada maganinsu an samu sauki to shima Islamic chemist ne, ko da kuwa wanda ba musulmi bane ya yi maganin. Kamar yadda na fada a baya, cuta bata da alaka da addini haka shima magani. Kirista zai iya amfani da Man-zaitun ya sha ya samu sauki, kamar yadda Musulmi zai iya amfani da Paracetamol ya sha dan ya samu sauki, babu inda aka ce ya sabawa addini dan ya sha maganin bature.

Yana da kyau mutane su yi tattalin lafiyarsu. Duk mara lafiya kamata ya yi a kaishi asibiti likitoci su gwada shi su san ciwon da yake damunsa, da kuma irin maganin da ya dace da shi, amma wasu kanyi kuskure kawai daga ciwo ya kama su sai su samu irin wadannan masu magungunan su yi ta dafka musu wasu abubuwa da ka iya tsananta ciwon da yake damunsu a matsayin magani, tunda babu wasu gwaje-gwaje na kimiyya da suka yi wajen gane cutar da kuma maganin da ya dace da ita. Haka kuma, mafi yawan irin wadannan magungunan dace ne kawai, domin wani yana iya shan hulba da Habbatus Sauda su yi masa magani wani kuma su tsananta cuta a gareshi. Wasu marasa tsoron Allah sai su fake da yiwa mutane wa'azi da fadin Allah ya ce Annabi yace, daga karshe kuma su b'uge da tallar magani da tallata hajojinsu.

Duk maganin da binciken kimiyyar likitoci ya gano cewa yana magani ya halatta a yi amfani da shi, matukar ba zai cutar ba, ko kuma baya dauke da wani abu da Musulunci ya haramta kamar giya, dan haka, kada kawai dan kana fama da ciwon "sugar" wani ya ce kaje ka yi ta shan Hulba da zaitun da sauransu ba tare da ya gudanar da kwakwaran bincike na kimiyya akanka ba. Eh gaskiya ne Hulba da sauransu duk suna maganin cututtuka, amma ba daidai bane wasu su dinga Yaudarar mutane da sunan cewa Magani kaza shi ne na Musulunci koma bayansa kuma na kafurci ne. Da maganin Bature da sauran zuma da Hulda da na 'yar me ganya duk sunansu magani, duk wanda bincike ya nuna cewa yana magani to shima ISLAMIC MEDICINE ne idan akwai wani magni da aka kebance da Musulunci. Allah ya sa mu gane.

Yasir Ramadan Gwale
10-10-13

Wednesday, October 9, 2013

Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?


Yau She Za'a Ceto Miliyoyin Tumatir Din Da Suke Halaka A Arewa?

Najeriya ita ce kasa ta biyu a duk fadin nahiyar Afurka da ta yi fice wajen samar da irin tumatur mai kyau. Allah ya bamu albarkar kasar noma da tana iya dacewa da yanayin kowanne irin abin shukawa tun daga 'ya 'yan itace da dangin hatsi da kayan lambu da sauransu. A baya can Najeriya na samar da tumatur wajen tan miliyan 1.14 duk da cewa binciken masana ya nuna cewa Najeriya zata iya samar da fiye da tan Miliyan biyar na tumatur a kowacce shekara, wanda zai iya wadatar da Afurka da wasu kasashen gabas ta tsakiya. Amma kusan yanzu kullum harkar noman tumatur armashin ta raguwa yake yi, kasantuwar babu wasu masana'antu a Arewa da suke sarrafa danyan tumatur dan a zuba shi a cikin gwangwanaye da lodoji da saurin mazubai dan amfanin yau da kullum na harkar girke-girke. Kasantuwar duk kasarnan a Arewa ne aka fi yin amfani da tumatur a sha'anin girke-girke.

Da yawan manoman tumatur da masu kasuwancinsa na yin harkar ne cikin tararrabi da fargabar samun riba ko faduwa kasa warwas. A lokacin da ake tsaka da kakar tumatur a jihohin Arewa zaka ga yadda manoma ke yin roronsa kwando-kwando kai ka ce gaba daya Arewa Tumatur kadai ake nomawa, amma mafiya yawancin Manoman tumatur sun dogara ga kudancin Najeriya ne domin yin kasuwancinsa, mota-mota ake yi  ana daukar tumatur daga Arewa zuwa kudancin Najeriya. Wani abin mamaki shi ne, akwai lokacin da a Arewa zaka nemi jan tumatur sama da kasa ka rasa, gaba ki daya babu shi, kodai sabo bai karaso ba, wanda aka noma a baya kuma tuni aka yi kasashen kudu da shi.

Wadan da harkar tumatur ta yi musu kyau su ne wadan da suka yi sa'ar kai shi kudancin Najeriya ba tare da ya lalace ba. Domin duk mutumin da ya yi rashin sa'ar yin lodin tumatur a dai-dai lokacin da aka samu budewar rana kwal, to sai dai wani ba shi ba, domin kafin a isa ga inda aka nufata tumaturin ya narke ya tsiyaye, da yawan manoman tumatur sun sha tafka asara ta irin wannan hanya, wasu manoman da dama sun zautu wasu ma sun haukace saboda asarar da suka yi ta irin wannan hanyar. Haka kuma, ansha samun sabani ga direbobin daukar tumatur din da manomansa musamman wadan da suka yi rashin sa'a, wasu su loda tumatur din ganin asarar da suka yi su gudu su bar direba da jogoguwa, shi kudinsa bai fito ba, ga kuma dole sai ya nemi inda zai zubar da ragowar rubagen a can kudancin Najeriya.

A baya a Arewa muna da kamfanonin tumatur a IKARA da KURA da kuma DADIN-KOWA amma yanzu duk sun zama kangwaye. Masana'antun sun mutu murus, dan haka dole manoma su nemawa tumatur din da suke nomawa kasuwa a yankin kudancin kasarnan, abin mamaki kasar kudu da basa iya samar da ko da koren tumatur, sune yanzu haka suke da kamfanonuwan tumatur din da galibi ake yin girki da shi a Arewa, Jihohin Legas da Ibadan sune kadai inda suke da kamfanonin sarrafa tumatur, suma basu dogara da kasuwancin da suke daga Arewa ba, domin bayanai sun nuna cewar Najeriya na shigo da markadadden Tumatur din da ba'a sarrafa ba daga Chana na kimanin Naira Biliyan 12 a kowacce shekara. Wanda masana harkar lafiya suka tabbatar da cewa babu wani sahihanci na ingancin nikakken tumatur din da ake shigo da shi Najeriya a cikin dururrukan da suka jima suna galudaya akan ruwa.

Yanzu da masu kudinmu da gwamnatocinmu zasu taimakawa Manoman tumatur da tayar da kamfanonin Kura da Ikara da suka mutu da alal akalla, za'a samarwa da dubban matasa aikin yi. Duk da cewar rahotanni sun tabbatar da cewar Alhaji Aliko Dangote yana yunkurin samar da katafaren kamfanin sarrafa Tumatur a garin Kura, wannn yunkuri idan har yaci nasara hakika babban cigaba ne, kuma wannan zai sanya da yawan manoman tumatur da suka watsar da harkar su koma mata, da kuma samar da karin sabbin manoman tumatur.

Amma saboda rashin kamfanonin da suke sarrafa tumatur din a Arewa, haka nan miliyoyin tumatur suke halaka bayan ankai wasu kudancin kasarnan anyi kasuwancinsu cikin kasada, wasu kuma haka nan manoman kan yayyanka su suke shanyawa akan tituna da rufin gidaje. Allah ya nuna mana lokacin da za'a samar da sabbin kamfanonin sarrafa tumatur da kuma tayar da komadar wadan da suka kwanta dama.

Yasir Ramadan Gwale
09-10-2013

Tuesday, October 8, 2013

Dan Giya


DAN GIYA: Ina zaune naji wasu mutane suna labarin cewar duk dan giya ya fi kowa dacewa da samun matar aure ta kirki. Suka ce zaka samu mafiya yawancin 'yan giya, idan sun sha sun bugu su yi ta yiwa matansu amai suna zazzaginsu amma matan na hakuri, kuma suna nuna soyayya a garesu. Wannan maganar ta shiga kunnena sosai.

Wannan ya tuna min da wata waka da wani mawaki ya raira mai suna ZAMA NA AURE, inda yake cewa "Zama na aure yana da dadi yana da daci . . ." Mawakin ya bayar da wasu labarai guda hudu a cikin wakar tasa, a labari na uku daya bayar ya yi kama da abin da naji wadannan mutanan suna tattaunawa akan dan giya. Ga abinda wakar ta ke cewa:

Zama na Aure Yana da dadi yana da daci maĆ”urata ashe soyayya da dadi…

Shi ko Gambo kunga dan giya ne

Sai can dare zai dawo gida nai

Da rangaji zai shigo gida nai

Ta kasa barci matarsa zaune

Bugu na kofarsa ma dabanne

Ta je ta bude ya yi shigowa

Da ya shigo zai fara hararwa

Ruwa ta debo tai tsabtacewa

Yana ta zaginta da dadawa

Ita ko kwalla take zubarwa

Kullum nasiha take gare shi

Dan ilimi gunta kwai yawan shi

Dan ilimin addini akwai shi

Sannu a sannu a kwan-a-tashi

Ya nutstsu tsaf-tsaf idan ka ganshi

Ya daina shaye ya canza halinshi

Gambo ai soyayya da dadi…..

Wannan labarin shakka babu ya yi kama da abinda naji wadannan mutane suna tattaunawa. Haka kuma, akwai wani mutum da na sani shi da kansa ya bani labari cewar a lokacin da yake shan giya, matarsa har wanka take yi masa, ya zageta ya fasa mata kaya amma bata damuwa, tana nuna masa soyayya tana masa Wa'azi da Nasiha. AMMA ME YA SA 'YAN GIYA SUKE DACEWA DA MATAN KIRKI?

Sunday, October 6, 2013

Wani Sabon Salon Tayar Da Tarzoma Da Su Zazzaky Suka Bullo Da Shi

WANI SABON SALON TAYAR DA TARZOMA DA SU ZAZZAKY SUKA BULLO DA SHI

Shugaban 'yan harka El-Zakzaky da mabiyansa, sun bullo da wani sabon salo na tayar da rikici a kasarnan. A yau da yawan shafukan 'yan Shia mabiyan zazzaky sun dunga bayar da sanarwar tayar da fitina, inda suke bayyana cewar 'yan shia za su shiga garin Sokoto a yau, dan haka ana kira ga duk wasu Ahlussunnah da su fito dan kare unguwanninsu, dan su hana 'yan Shia wucewa. Wannan sanarwa 'yan Shi'ah suka dinga bayarwa, dan jan hankalin wasu mutane daga cikin Ahlussunnah marasa kangado dan su fusata su fito dan hana 'yan shi'ar wucewa, inda zasu dinga takalarsu da fada, daman haka suke jira sai su yi amfani da wannan damar wajen tayar da tarzoma, kafafan watsa labari masu kishirwar labarin tashin hankali su yi ta bazawa dan kasar ta hargitse, Allah ya kiyaye.

Zakzaky bai damu da duk wani rikici da zai janyo sanadiyar halakar 'yan shi'ah ba ko su nawa zasu mutu. Domin yasan 'ya 'yansa suna can a kawwame, ya kaisu Amerika suna can suna rawa da su Lady Gaga, a kashe dan uban kowa bai damu ba, dan babu nasa. Idan ka duba yadda Zakzaky ya kira mabiyansa da sunan tattaki a kafa daga nisan duniya su zo inda yake, zaka san dagaske wannan mutumin ba kaunar mutanansa yake ba, a garin tafiya wasu suka dinga mutuwa a hanya, wasu motoci suka dinga markadesu, amma babu abin da ya dameshi saboda babu 'ya 'yansa a ciki.

Ahlussunnah mutane ne masu son zaman lafiya. Baya daga cikin aqidar Sunnah daukar doka a hannu, duk kuwa yadda lamura suka kai ga tabarbarewa matukar akwai hukumomi. Hakkin hukuma ne karewa tare da tsare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa. Tunda 'yan shiah suke yawace-yawacensu a kasarnan, Ahlussunnah basu taba tare musu hanya ba, balle su neme su da tashin hankali wannan ya sabawa manhajin Sunnah, hakki ne na hukumomi su bayar da dama ko su hana ga duk wanda ya fito yana ragaita akan titi da sunan ko ma meye.

An kashe mana Malamin da muke so muke kauna bamu tayar da hankali ba, sai wasu kananan kwari zamu tarewa hanya! Idan da mu masu tashin hankali ne, da jikin uban kowa ya gaya masa lokacin da aka yi mana ta'addanci a ranar 13 ga watan Afrilun 2007 a unguwar dorayi a Kano. Amma saboda mu al'ummah ce mai tsari da bin dokoki, da biyayya ga hukumomi babu wanda muka dungurewa kai, ko kaza bamu buge da sunan daukar fansa ba.

Dan haka duk wasu wadan da suke kiran Ahlussunnah da cewa su fito dan hana 'yan Shiah ragaitarsu su sani wannan sanarwa bata da alaka da Sunnah. Bama daukar doka a hannu mu sanya wani ko mu hana wani yin wani abu, sai dai fa idan abinda yake yi barnace ko fasadi da hukumomi suka ki daukar mataki.

Ko zazzaky ya sani ko bai sani ba, ballantana ma yana sane cewa ana amfani da shi wajen tayar da husuma a kasarnan. Suna son duk yadda za su yi su haifar da yamutsi a kasarnan da za'a yi amfani da shi a kama na kamawa ko a kashe na kashewa, ko ma kasar ta tarwatse. Muna tuna musu fadin Allah ta'ala cewa "WAMAKARU WA MAKRULLAH WALLAHU KHAIRUL MAKIREEN" In Sha Allah duk wani mai burin kawo hayaniya da tashin hankali aniyarsa zata bishi, kuma In Sha Allah sai yaji kunya. Allahumma Alaika Bihim . . . Allah ka kare bayinka na gari a duk inda suke. Allah ka bamu lafiya da zaman lafiya a kasarmu.

Yasir Ramadan Gwale
06-10-2013

Shiekh (Dr.) Bashir Aliyu Umar: Kwararren Malamin Sunnah!!!

SHEIKH (Dr.) BASHIR ALIYU UMAR: KWARARREN MALAMIN SUNNAH!!!

Yana daga cikin baiwar da ALLAH yake yiwa bayinsa kebantattu, shi ne ya hore musu bai ta ilimi. Hakika, Allah ya yiwa Dr. Bashir Aliyyu Umar baiwa ta ilimi a fannoni da dama, bayan kasancewarsa Injiniya ne, kuma kwararren Malamin kimiyyar Hadisi ne. Malam ya karanta Ilimin Hadisi da kimiyyarsa a Jami'ar Musulunci ta Islamic University of Madinah tun daga matakin Degree na farko har zuwa Degree na uku inda Malam ya yi Kimiyyar Hadisi wato (PhD, Hadith Sciences).Allah ya yiwa Malam Bashir hikima da kaifin kwakwalwa, da sanin hukunce-hukuncen da suka shafi Ilimin Fiqhu, Allah ya bashi hazaka, da iya warware mas'aloli cikin hikima da ilimi.

Bayan kasancewar Dr. Bashir kwararren Malamin Sunnah, Malam Marubuci ne na Hausa da Turanci, domin ya rubuta litattafai da dama wasu anbuga su tuntuni wasu kuma ba'a kai ga buga su ba. Malam ya rubuta litattafai da daman gaske kamar The Methodology of Imam Ahmad regarding the inconspicuous weaknesses of hadith narrations, Garkuwar Musulmi ta Addu'o'i daga Alkur'ani da Sunnah; Hausa translation of Hisnul Muslim Min Adhkaaril Kitaab was Sunnah, Na Dr. Sa'eed bin Wahf Al Qahtani, Useful Ways of Leading A Happy Life, Fadakarwa Kan Hukunce-Hukunce da suka kebanci Mata Muminai. Wadannan su ne kadan daga cikin irin dumbin litattafan da Malam Bashir ya rubuta a cikin Ingilishi da Hausa, bayan haka kuma, akwai wasu litattafai da Malam ya rubuta wadan da ba'a kai ga buga su ba kamar: Between the Companions and Members of the Household of the Prophet, may Allah bless him and grant him peace, 55 rules regarding the inconspicouos weaknesses of hadith narrations and their applications among the scholars of hadith (an original work), Takhreej Nusoos 'aml ahlil Madinah fil Muwatta wal Mudawwanah da sauransu da dama.

Malam Bashir kwararre ne wajen sanin Ilimin Aqeedah, ya yi fice sosai a wannan fage, haka kuma masani ne a sauran fannoni Ilimai da dama, kuma masanin siyasar duniya, kuma Masanin Tattalin Arziki Bisa koyarwar Shar'ah, uwa uba kuma Malam Bashir Mahaddacin AlQur'ani ne, Ya Salam! Malam Bashir Mutum ne mai kan-kan da kai ga tawalu'u, yana girmama ilimi yana kuma girmama malamai masu Ilimi. Watarana, wasu al'amura guda biyu sun faru akan idona, Na farko wani ya zowa da Malam Bashir da wata fatawa, amma sai ya tambayi meye ra'ayin abokinsa Dr. Muhd Umar akan wannan fatawa. Abu na biyu kuma, wani ya tambayi ra'ayinsa dangane da kalaman da Barack Obama ya yi a lokacin da ya kai ziyara kasar Masar ga Musulmin duniya, a lokacin Dr. yace mu saurara muji ra'ayinsu Sheikh Dr. Yusuf Qardawi tukuna. Wannan ya kara nunamin irin yadda Malam Bashir yake taka-tsantsan da Ilimi da kuma girmama maganganun Manyan Malamai.

Malam Bashir mutum ne wanda duk mutumin da Mu'amala ta hadasu da shi, sai ya fadi alkhairinsa da kirkinsa, da kaunarsa da jama'a. Mutum ne salihi, Allah ya bashi baiwar iya rike sunayan mutane, Yau zaku yi Mu'amala da Malam, Insha Allah bayan shekara guda idan ka dawo zai ambaci sunanka, bai cika manta suna mutanan da ya yi mu'amala da su ba. Allah ya bashi wannan baiwar.

Sannan kuma, Malam Bashir kusan yana daga cikin mutanen sahun gaba wadan da suka yi uwa suka yi makarbiya wajen ganin tabbatar Bankin Musulunci a Najeriya. Da shawarwarinsu da maganganunsu da hangen nesansu wannan alkhairi ya tabbata da dumbin al'ummah ke cin mariya a yanzu. Hakika Malam Bashir yana daga cikin kalilan din mutane da Allah ya yiwa tarin baiwa mai yawa da dumbin hikimomi. Na tabbata idan da za'a tara mutum goma da suka san Malam Bashir zasu yi rubuce-rubuce mabambanta wajen bayanin waye Malam Bashir. Tabbas Dr. Bashir Aliyu Umar kwararren Malamin Sunnah ne a wannan zaminin a Najeriya ta Arewa. Sautinsa bai tsaya iyakar Arewacin Najeriya ba, wajen kira zuwa ga Allah da Tauhidi, sautinsa ya karade kasarnan da sauran kasashen Afurka da Asiya da Gabas ta Tsakiya. Allah ya sakawa Malam Bashir da alheri, ya sanya albarka a cikin rayuwarsa da iliminsa da zurriyarsa. Allah ya yawaita mana irinsu.

Yasir Ramadan Gwale
06-10-2013