Wednesday, November 12, 2014

Tashin Hankalin Da Ya Faru A Potiskum

TASHIN HANKALI: Ba shakka abinda ya faru a Potiskum a wannan makon na tayar da Bom a cikin dalibai abin tashin hankali ne matuka da gaske. Duk wadan da sukai wannan aika aikar sun cika cikakkun Azzalumai makiya Allah makiya san zaman lafiya. 

Wadannan yara ne da basu yi wani laifin da suka cancanci mutuwa ta irin wannan hanya ba. An zalinci yara an kawo karshen rayuwarsu a daidai lokacin da yaran da iyayansu ke fatan samun kyakykyawar rayuwa a gaba, ashe basu sani ba ajali na nan gaba garesu ba tare da cikar burinsu na samun karatu mai zurfi ba.

Ya Allah ka sani wadannan yara an zalincesu ba tare da hakkinsu ba. Allah kai mai ji ne kuma mai gani ne. Ya Allah ka sakawa wadannan yara akan ta'addancin da akai musu. Wadannan masu aikata ta'addanci Ya Allah ba zasu taba bacewa ganinka ba Ya Allah ka nuna kudurarka ikonka akansu. Ya Allah kaine kafi sanin abinda ya cancanci wadan da sukai aiki itin nasu, Allah ka sakawa wanda aka zalinta. Iyayan wadannan yara Allah ka basu hakuri da dangana.

Allah ka baiwa hukumomin tsaro da duk wanda abin ya shafa ikon cin lagon 'yan ta'adda. Allah ba dan halinmu ba, ba dan abinfa gabbanmu suke aikatawa ba, Ya Allah albarkacin raunana daga cikinmu Allah ka Amintar da mu a garuruwanmu.

Ina mai amfani da wannan dama a madadin Ni Yasir Gwale da Zainab Gwale muke mika sakon ta'aziya ga iyayan wadannan yara, da gwamnatin jihar Yobe. Allah ka yaye mana abinda ya damemu.

Yasir Ramadan Gwale
12-11-2014

No comments:

Post a Comment