Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi: Akramakalahu yanzu na fara Nazarin Nasihar ka.
Ba shakka Dan danon magani ba shida dadi ko kadan a wajen mara lafiya
da ake kokarin ceto rayuwarsa, amma tabbas shi ne abinda yafi bukata.
Sau da dama mara lafiya har danne shi ake yi a dura masa magani, amma
yana shure-shure yana kukan kura yana nuna baya so, amma haka nan ake
dura masa maganin yana baya so, baya so. Karshe kuma maganin da ya dinga
fatali da shi a baya sai ya zama silar samun
warakarsa. Ai ko likata ma yasan Allah ka bada lafiya ba garin magani
ba. Amma kuma haka sunnar Allah take, idan anyi rashin l;afiya aka sha
magani sai kaga an samu sauki garas. Dan haka magani komai dacinsa a
danne mara lafiya a bashi ya sha ko yana so ko baya so, a gaba shi zai
fi kowa murna da maganin da aka bashi.
SAI DAI KUMA: Shi fa magani yana da lokuta kayyadaddu kuma
kididdigaggu, idan akai sa'a aka sha akan lokaci, cikin dace sai a samu
waraka. Kai akwai yana yin da idan ma aka baiwa mara lafiya magani
tamkar kara masa ciwo ake yi. Dan haka kiyaye ka'idar shan magani ita
kanta na taimakawa mara lafiya. Haka nan shima mai bada magani.
HAKA KUMA, wasu suna ganin ita gaskiya dandanonta yayi kama da na magani mai daci. To dan haka idan har mun gamsu cewa ita gaskiya daci gareta, to meye na tada jijiyar wuya? Allah ya baiwa mara-laiya lafiya, ya karawa mai lafiya lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
13-11-2014
HAKA KUMA, wasu suna ganin ita gaskiya dandanonta yayi kama da na magani mai daci. To dan haka idan har mun gamsu cewa ita gaskiya daci gareta, to meye na tada jijiyar wuya? Allah ya baiwa mara-laiya lafiya, ya karawa mai lafiya lafiya.
Yasir Ramadan Gwale
13-11-2014
No comments:
Post a Comment