Saturday, November 29, 2014

Malam Idi Mai Nika


MALAM IDI MAI NIKA

Tun ina yaro akan tura ni kai nika injin Malam Idi, kaf unguwarmu ba wani me injin nika sai Malam Idi, tun kafin Ganganci ta fara sayar da abinci muna kiran layin da sunan lungun malam Idi, sai bayan da ganganci ta fara sayar da abinci ne, kuma mutane suka rage cin tuwan gari, aka daina bukatar nika sosai sannan sunan Malam Idi ya bata, aka fi sanin layin da sunan layin ganganci kamar yadda ake kiransa a yanzu.

Dazu nake samun labarin cewa Malam Idi Mai Nika na daya daga cikin mutanan da harin Bom ya rutsa da su jiya a Masallacin Gidan Sarki. Ina yi masa adduar fatan Alheri da fatan samun rahama da daukaka, yayi dace ya rasu a ranar Juma'a, ranar da Manzon Allah SAW yace idin Musulmi ce da take kewayowa duk mako. Kuma kashe shi akayi a yayin da ya amsa kiran Ladan na Hayya AlaS-Salah. Sallar Juma'a. Hani'Allahka Ya Malam Idi Mai Nika.

Amadadin kaina Yasir Gwale da Zainab Gwale muna yiwa Malam Idi adduar fatan samun Shahada. Allah ya sa mutuwa hutu ce a garesu. Iyalansa su Malam Musa da abokina Isa ina mika ta'aziyata a garesu. Allah ya basu hakurin jure wannan rashi. Allah ya kyauta namu zuwan.

YASIR RAMADAN GWALE
29-11-2014

Hattara Jama'a: Idan Hankali Ya Bata Hankali Ke Nemoshi


Allah madaukakin Sarki, yana gaya mana a cikin littafinsa mai tsarki AlQurani sura ta 29 aya ta 2: Cewar "Shin tsammaninku dan kunyi Imani ba zamu jarrabeku ba?" Lallai ku sani al'ummar da ta gabace ku an jarrabesu da fitina da tsoro, da firgici da tsanani da tashin hankali. Allah Subhanahu Wata'ala yana da hikima a dukkan abubuwan da ya saukarwa bayinSa na alkhairi ko sharri, shi yasa ma yace daya daga cikin rukunan Imani shi ne yadda da KADDARA mai kyau da marar kyau.

Ba shakka wasu al'amuran kan faru dan jarraba masu Imani na hakika wadan da suke maida gazawa a garesu tare da kyautatawa Allah zato. Da yawa daga cikin Annabawa, wadan da sune zababbun zababbunSa Subhanahu Wata'ala, an kashesu, kisa na wuulakanci, Allah da ya fi kowa sansu da kaunarsu, yana kallo, amma saboda ya tanadar musu da wata daukaka ta sanadiyar hanyar mutuwarsu, ya sanya mutuwarsu ta kasance a irin halin da ta zo musu.

Allah buwayi ne gagara misali, da babu wani mahaluki da ya isa tambayar dalilin da yasa abubuwansa suke faruwa bisa ikonSa. Allah masani ne ga abinda duk yake boye a garemu ne, babu wani abu da yake fakuwa gareshi Subhanahu Wata'ala.

Mun kyautata zato ga Allah madaukakin Sarki, cewa yana gani kuma yana ji, yasan masu shirya dukkan kaidi da makida akan bayinSa masu kadaita shi da Ibada. Watakila Allah ya yi nufin daukaka darajar wadan da aka kashe a irin wannan yanayi na tashin hankali a ranar gobe alkiyama.

Ya 'yan uwa masu girma. kada mu taba yanke tsammani daga samun rahama da taimakon mahaliccinmu. Shi Allah Assami'u ne kuma Albasiru ne. Babu wani abu da yake kaucewa ganinsa.

Manzon Allah SAW ya fada mana cewa karshen Duniya kisa zai yawaita, tashin hankali zai yawaita, har ta kai matsayin da wanda yake kisa bai san dalilin kisan ba, shima wanda ake kashewa bai san me ya aikata ba aka kashe shi. Munji munyi Da'a a gareka Ya Rasulullah.

Ba shakka a halin da ake ciki a yanzu. kashe kashe sun yawaita a gurare da dama. Wannan kuma duk yana faruwa ne bisa kaddarawar Ubangiji Subhanahu Wata'ala.

Dan haka, yana da kyau a lokacin da mutane ke cikin tsananin firgici da damuwa su kame harsunansu daga furta kalaman da zasu zamar musu nadama a ranar alkiyama da bazata amfanesu ba. Muyi hakuri mu maida lamuranmu ga Allah, muyi gaskiya, muji tsoron Allah gwargwadan Iko, kar muyi shirka kar mu zargi Allah akan abubuwan da suke faruwa a garemu. Mu sani cewar Allah mai ji ne kuma mai gani ne.

Allah da kansa yace kuyi Bushara ga masu hakuri da juriya a lokacin tsanani. Ba shakka abinda yake faruwa a garemu ya wuce duk yadda muke kaddarashi, mu kyautata zato ga Allah, muji tsoron Allah a maganganunmu da ayyukanmu.

Allah da kansa ya korewa kansa zalinci, yace kuma sai ya sakawa duk wanda aka zalunta ko da kuwa wanda aka zalunta baice Allah ya saka masa ba. Ya dan uwa ka sani ko daidai da magana idan ka zalinci wani Allah ba zai yafe ba matukar ba wanda aka zalinta din bane ya yafe. Muji tsoron Allah, mu kiyaye harsunanmu wajen furta kalaman da zasu zama nadama a garemu ranar da nadamar ba zata amfanawa bawa da komai ba.

A madadin Ni Yasir Gwale da Zainab Gwale muna taya al'ummar da wannan ibtila'i ya rutsa da su alhinin wannan al'amari. Wadan da suka rasu Allah ya jikansu ya gafarta musu. Allah ka sa mu cika da Imani.

YASIR RAMADAN GWALE
29-11-2014

Friday, November 28, 2014

SHAIDU: Yadda Harin Boko Haram Yai Ta'adi Ga Masu Ibada A Kano

SHAIDU: Yadda Harin Boko Haram Yai Ta'adi Ga Masu Ibada A Kano

Naman mutane ya warwatsu a harabar Masallacin Juma'a na kofar gidan Mai Martaba Sarkin Kano Muhammad Sunusi II. Wani mutum ne da yayi jigida da bamabamai ne yai yunkurin kutsa kai cikin Masallacin a lokacin da Liman yake jagorantar Sallar Juma'a a yau dinnan. 

Gawarwakin mutane sun warwatsu a farfajiyar masallacin, ko dai wadan da harin bom din ya kashe kai tsaye ko kuma wadan da suka mutu ta sanadiyar harbin binduga ko kuma wadan da suka rasu sakamakon turmutstutsu. 

Sai dai wata majiya daga fadar Kano tace Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi yana kasar Faransa a lokacin da wannan bala'i ya auku, majiyar tayi karin bayanin cewar Sarkin ya tafi Faransa ne domin binciken lafiyarsa, haka kuma, manyan 'yan majalisar Sarki sun halarci wannan Sallah tare da Liman a cikin masallaci.

Bom na farko ya tarwatse ne a daidai lokacin da liman ya fara Sallah. Wani dan kunar bakin wake ne da ya makare wata karamar Toyota da bamabamai ne ya yo kan masallata a daidai lokacin da liman ya kabbara Sallah, inda ba tare da wata wata ba Bom din ya tarwatse. Bom na biyu kuma ya tarwatse ne a kusa da sahun da mutane sukai dan bin Sallah, haka kuma, Bom na uku ya fashe ne a cikin harabar Masallacin.

Sannan kuma, wani da abin ya faru akan idansa yace yaga wasu matasa suna harbin kan mai uwa da wabi a tsakanin masallata, abinda ya haifar da guje-guje da turmutstutsu. Mutumin ya kara da cewar naga mutum biyu dauke da bindigogi sun nufi cikin masallacin suna harbin kan mai tsautsayi, daya daga cikinsu ma naga yana dura harsasai a cikin kwansan bindigar, a cewar Umar Farouk wani matashi da abin ya faru a gabansa.

Wani ganau kuma ya kara da cewar bayaga gawarwaki da suke yashe a kasa, yaga yadda guntattakin naman mutane da jini yadda suka dinga makalewa a jikin kofofi da tagogin shiga Masallacin. Mutumin yace, duk da tsawo da ginin masallacin yake da shi, yaga naman mutane makalkale a saman masallacin ga jini face-face ko ina yana diga.

Ya Allah muna tawassuli da kyawawan ayyukanmu wadan da ka karba daga garemu Ya Allah ka dube ba dan halinmu ba ba dan mun kasa ba. Allah ka dubi raunana daga cikinmu, da kananan yara da marayu Ya Allah ka kawo mana karshen wannan masifa da bala'i. Allah ka jikan wadan da suka rigamu gidan gaskiya a wannan hari. Na ruwaito daga shafin Jaafar Jaafar.

YASIR RAMADAN GWALE
28-11-2014

Kwankwaso Ya Shammacemu

KWANKWASO YA SHAMMACE MU

Yanzu dai dukkan kwannafi ya kwanta dangane da wanda Gwamna Kwankwaso zai zaba wanda zai yi takarar Gwamna a APC. Wannan dai zabi ne na mai girma Gwamna ba zaben fidda Gwani bane, kamar yadda aka ce a zaben da ya gabata Malam Ibrahim Shekarau ya zabi Malam Salihu Sagir Takai ba tare da anyi zabe ba. Daman ance Tarihi hakanan yake maimaita Kansa.

Sai dai wannan zabe da akaiwa Ganduje ba shakka ya shammaceni, dan banyi tsammanin haka. Amma kuma nayi Imani da Allah cewa Malam Umar Abdullahi Ganduje mutumin kirki ne mai kamala da sanin yakamata.

Duk a cikin masu neman takara a APC alal hakika nafi samun nutsuwa da Ganduje dan na san ba zai cuci al'ummah ba. Ina taya shi murnar wannan zabi da akai masa.

Ina kuma adduah tare da rokon Allah ya sa ya zamar mana karkatacciyar kuka mai dadin hawa a zabe, Malam Salihu Sagir Takai ya kada shi cikin sauki. Ina da kwarin guiwar cewa Dan Takararmu Malam Salihu Sagir Takai zai baiwa Ganduje ruwa a wannan zabe mai zuwa da tazara mai yawa.

Na kuma tabbatar cewa Malam Salihu Sagit Takai yafi Ganduje cancantar zama Gwamnan Kano a zaben 2015. Ina kuma da yakinin cewar zamu shammaci Kwankwaso a wannan zabe. KANO TAKAI MUKE FATA. ALLAH YA AMINCE MAKA MALAM SALIHU TAKAI.

Yasir Ramadan Gwale
28-11-2014

Sunday, November 23, 2014

Malam Nuhu Ribadu 54


MALAM NUHU RIBADU 54

Allah ya sanya Albarka a cikin wadannan shekaru masu cike da alfanu. A madadina Yasir Gwale da Zainab Gwale muna yiwa Malam Nuhu Ribadu da iyalansa adduar Allah ya sanya masa albarka a sauran rayuwarsa ya amfanar da al'umma da dumbin baiwa da falaloli da ya baiwa Malam Nuhu Ribadu. Allah ya kara maka wasu shekaru masu yawa cike da koshin lafiya, Allah ya cika maka burinka na alkhairi. Najeriya na nan na jiranka a 2019. Allah ya amince maka.

Yasir Ramadan Gwale
22-11-2014

Zancen Zuci


Har kullum tambayar da take raina ita ce, Shin yanzu idan aka samu 'yan ta'adda da suka labe cikin al'umma a London da Warshington da Tel Aviv shin wadannan kasashen zasu bada Umarnin a yi amfani da jirgi mara matuki yayi ruwan bamabamai daga sama a rurrusa makarantu da asibitoci da kantuna da gidajen jama'a sauransu duk da sunan yakar 'yan ta'adda? Mu kalli yadda Netanyahu ya ragargaza Ghazza da sunan yakar 'Yan Hamas; Ga kuma yadda ake rushe gidajen jama'a a Iraqi da Suriya duk da sunan yakar ISIS. An hada karya da gaskiya ta hanyar amfani Khawarij sun sani ko basu sani ba ana cutar da Musulunci da Musulmai.

Wadannan fituntunu ba zasu taba karewa ba sai dai ma sabbi su sake bullowa. Domin Manzon Allah yayi ishara da faruwar kashe kashe a karshen duniya da bayyana tsiraici da aikata alfasha a bainar jama'a da fashi da sata da kwace. Babu wani abu da baya faruwa a yanzu duk wani nau'i na aikin sabo ana yinsa a cikin al'ummar Musulmi. Mace ta kashe mijinta, Miji ya kashe matarsa; d'a ya kashe iyayansa, uba yayi zina da matar dansa, uwa tayi zina da mijin 'yarta. Dan Adam yayi zina da dabba, ayi zina tsakanin mace da mace, namiji da namiji. Duk wannan ba sai anje da nisa ba laifuka ne da sukai katutu a tsakanin al'ummarmu.

Wasu sukan dauka cewa Wai Musulmi ba zai iya kashe Musulmi ba. Duk wanda suke da wannan tunani yana da kyau su je su karancin tarihin Khawarij. Wanda ya kashe Sayyaduna Usman RA Musulmi ne, haka wadan da suka kashe Aliyu dan Abi Talib da Dalha da Zubair duk masu ikirarin Musulunci sukai wannan aika aika.


'Yan shiah masu kiran kansu Musulmi suka fille kan jikan Manzon Allah SAW. Ya dan uwa ka kyautata tsakaninka da Allah, kaji tsoran Allah a cikin lamuranka, ka bautawa Allah gwargwadan ikonka, kar kaci hakkin wani, kar kayi shirka In Sha Allah zaka samu mahaliccinka mai tsanani Rahama ne da Jin Kai. Allah ka yafe mana laifukanmu wadan da muka sani da wadan da bamu sani ba.

Yasir Ramadan Gwale
19-11-2014

Thursday, November 13, 2014

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi

Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi: Akramakalahu yanzu na fara Nazarin Nasihar ka.

Ba shakka Dan danon magani ba shida dadi ko kadan a wajen mara lafiya da ake kokarin ceto rayuwarsa, amma tabbas shi ne abinda yafi bukata. Sau da dama mara lafiya har danne shi ake yi a dura masa magani, amma yana shure-shure yana kukan kura yana nuna baya so, amma haka nan ake dura masa maganin yana baya so, baya so. Karshe kuma maganin da ya dinga fatali da shi a baya sai ya zama silar samun warakarsa. Ai ko likata ma yasan Allah ka bada lafiya ba garin magani ba. Amma kuma haka sunnar Allah take, idan anyi rashin l;afiya aka sha magani sai kaga an samu sauki garas. Dan haka magani komai dacinsa a danne mara lafiya a bashi ya sha ko yana so ko baya so, a gaba shi zai fi kowa murna da maganin da aka bashi.

SAI DAI KUMA: Shi fa magani yana da lokuta kayyadaddu kuma kididdigaggu, idan akai sa'a aka sha akan lokaci, cikin dace sai a samu waraka. Kai akwai yana yin da idan ma aka baiwa mara lafiya magani tamkar kara masa ciwo ake yi. Dan haka kiyaye ka'idar shan magani ita kanta na taimakawa mara lafiya. Haka nan shima mai bada magani.

HAKA KUMA, wasu suna ganin ita gaskiya dandanonta yayi kama da na magani mai daci. To dan haka idan har mun gamsu cewa ita gaskiya daci gareta, to meye na tada jijiyar wuya? Allah ya baiwa mara-laiya lafiya, ya karawa mai lafiya lafiya.

Yasir Ramadan Gwale
13-11-2014

Wednesday, November 12, 2014

Tashin Hankalin Da Ya Faru A Potiskum

TASHIN HANKALI: Ba shakka abinda ya faru a Potiskum a wannan makon na tayar da Bom a cikin dalibai abin tashin hankali ne matuka da gaske. Duk wadan da sukai wannan aika aikar sun cika cikakkun Azzalumai makiya Allah makiya san zaman lafiya. 

Wadannan yara ne da basu yi wani laifin da suka cancanci mutuwa ta irin wannan hanya ba. An zalinci yara an kawo karshen rayuwarsu a daidai lokacin da yaran da iyayansu ke fatan samun kyakykyawar rayuwa a gaba, ashe basu sani ba ajali na nan gaba garesu ba tare da cikar burinsu na samun karatu mai zurfi ba.

Ya Allah ka sani wadannan yara an zalincesu ba tare da hakkinsu ba. Allah kai mai ji ne kuma mai gani ne. Ya Allah ka sakawa wadannan yara akan ta'addancin da akai musu. Wadannan masu aikata ta'addanci Ya Allah ba zasu taba bacewa ganinka ba Ya Allah ka nuna kudurarka ikonka akansu. Ya Allah kaine kafi sanin abinda ya cancanci wadan da sukai aiki itin nasu, Allah ka sakawa wanda aka zalinta. Iyayan wadannan yara Allah ka basu hakuri da dangana.

Allah ka baiwa hukumomin tsaro da duk wanda abin ya shafa ikon cin lagon 'yan ta'adda. Allah ba dan halinmu ba, ba dan abinfa gabbanmu suke aikatawa ba, Ya Allah albarkacin raunana daga cikinmu Allah ka Amintar da mu a garuruwanmu.

Ina mai amfani da wannan dama a madadin Ni Yasir Gwale da Zainab Gwale muke mika sakon ta'aziya ga iyayan wadannan yara, da gwamnatin jihar Yobe. Allah ka yaye mana abinda ya damemu.

Yasir Ramadan Gwale
12-11-2014

Saturday, November 1, 2014

Takai 2015


KANO 2015: Malam Salihu Sagir Takai salihin mutum managarci. Allah ya sani kyakkyawar shaida da aka bayar akansa da halayansa na gari da suka bayyana zahiri a garemu ya sa muke tare da shi, kuma zamu cigaba da kasancewa da shi.

Muna fatan alheri ga wannan adalin mutum salihi managarci amanar Sardaunan Kano Munistan Ilimi Malam Dr. Ibrahim Shekarau CON. ALLAH ka amince Takai 2015. Kowa ya samu dama yace Kano Sai Takai 2015.

Yasir Ramadan Gwale
30-10-2014