Friday, October 3, 2014

Godiya Ta Musamman



GODIYA TA MUSAMMAN: Kusan tun kwana uku kafin jiya Malamina a CAS Alasan Sule ya rubuta sakon fatan alheri akan Timeline dina yake tuna min ranar da aka haifeni. Tun daga lokacin kuma na fara samun sakon taya murna da fatan alheri.

Hakika nayi murna da farin ciki a jiya yadda mutane suka dinga lekowa turakata suna barin sakonnin fatan alheri da addu'o'i a gareni, kuma fatan alherin bai tsaya gareni ba ni kadai har Zainab jama'a da dama sunyi mata addu'ah da fatan alheri a dalilin wannan rana. Ba shakka naji dad'in wannan al'amari, da ni da Zainab muka kasance cikin adduoinku a jiya.

Muna matu'kar godiya a gareku baki daya. Da so samu ne nabi dukkan wadan da duka aiko da sako nai musu godiya a jikin sakon, amma kasancewar abin da yawa ban samu dama ba, amma duk wanda ya aiko da sakon na gani kuma naji dadi.

Ba shakka hakan na nufin ina kara kusa ga ajalina ne, na shirya ko ban shirya. A shekarun da aka diba min naci wani adadi daga ciki. Ina rokon Allah ya amsa dukkan adduoinku na alkhairi da kuka yi mana. Ina kuma fatan hakan ya zama tuni a gareni cewar ako da yaushe ina iya riskar ajali. Allah ya sa yadda muka zo muna masu Imani da Allah mu koma muna masu Imani a gareshi Subhanahu wata'ala.

Nima zan d'an koma baya na tunawa kaina baya dan na fahimci yadda rayuwa ta sauya a gareni. Wannan hoto da kuke gani an dauke shi a shekarar 1988. Wannan yaron da kuke gani ni ne. Yau gashi gabbai sunyi tsawo gashi ya baibaye fuska. Akwana a tashi ance jariri ango ne.

Amadadina da Zainab da dukkan 'yan uwa d danginmu muna muku godiya da fatan alheri. Allah ya saka da alheri ya bar zumunci.

Yasir Ramadan Gwale
03-10-2014

No comments:

Post a Comment