Tuesday, October 28, 2014

ATIKU ABUBAKAR: Kadangaren Bakin Tulu


ATIKU ABUBAKAR: KADANGAREN BAKIN TULU

Kasancewar Turakin Adamawa Atiku Abubakar daya daga cikin 'yan takarar Shugaban kasa a jam'iyyar hamayya ta APC ta sa ya zamo kadangaren bakin tulu a cikin jam'iyyar; ance kadangaren bakin tulu idan an jefeshi za'a fasa tulu, idan an kyale shi kuma dole ayi hakuri asha ruwan a haka.

Fitowar Atiku Abubakar takara tare da Gen. Buhari yana yiwa magoya bayan Janar din barazana. Domin duk wani yunkuri na samar da wanda zai yiwa jam'iyyar takara ta hanyar sasantawa ko kwansansus, Atiku ba zai yarda da shi, abinda yake nuna dole sai anyi zaben fitar da gwani wanda daliget ake sa ran zasu yi.

Zaben fitar da Gwani kusan shi ake kallo a matsayin wata dama da shi Atikun ya makalewa. Domin wannan zabe na fid da gwani shi ne zai bada damar amfani da kudi wajen sayan masu zabe. Abinda ake ganin tuni Atiku ya tanadi jakar kudi dan wannan zabe. Ba shakka masharhanta na ganin cewar kudi zasu taka muhimmiyar rawa a wannan zabe. Kuma zasu taimakawa Atiku wajen iya samun nasarar zama dantakara.

Haka kuma, alamu na nuna cewar duk wani yunkuri dan kaiwa zuwa ga wannan zabe tamkar shatale takarar Buahri ne da ke zaman wanda yafi sauran 'yan takarar jam'iyar yawan magoya baya. Daga gefe guda kuma tsohon Shugaban kasa Olushegun Obasanjo na gargadin Apc da kada su sake su sanya Atiku a matsayin dantakararsu, abinda ke kara bayyana jikakkiyar da ke tsakani Atikun da tsohon mai gidansa Obasanjo.

Koma dai ya abin zai kasance. Lokaci ne zai tabbatar da waye zai fuskanci Shugaban Kasa Dr. Goodluck Jonathan a zaben 2015 da ke tafe.

Yasir Ramadan Gwale
27-10-2015

1 comment: