APC/BUHARI-ATIKU-KWANKWASO DA ZABEN 2015: HANYA DAYA TAK DA TA RAGEWA ‘YAN ADAWA DAGA AREWA
* wannan rubutu yana da tsawo, ina fatan duk wanda zai yi ta'aliki ya kasance ya karanta har karshe.
Dukkan
dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki,
tsira da amincinsa su kara tabbata ga shugaban Manzanni cikamakin
Annabawa Muhammadu Dan Abdullahi; Allah yayi dadin tsira a gareshi da
Alayansa da Sahabbansa da wadan da suka biyo bayansu da kyautatawa har
ya zuwa ranar sakamako. Ina rokon Allah ya sa wannan abun da zan fada ya
amfanemu baki daya, Allah kayi min jagoranci wajen fadin gaskiya.
Da
farko yana da kyau mu mutanan Arewa Musulmi mu sani cewar dama ce muke
da ita mukai sakaci ta kubuce mana, a dan haka ‘bari mukayi, masu magana
kuma sun ce “ba’a yin ‘bari a kwashe duka”, ina fatan mai karatu zai
kiyaye wannan magana da kyau! Idan muka duba Najeriya tun farkon
kafuwarta har kawo yanzu, mu mutanan Arewa mun dad’e ana cin moriyar
hakurinmu da kuma sakaci da sadaukarwarmu ba dan komai ba sai dan san
zaman lafiya da zaman tare.
A baya anyi mana wawar Asarar Sa
Abubakar Tafawa Balewa da su Sa Ahmadu Bello da sauransu wadanda ba dan
komai aka kashe su ba sai dan Najeriya watakila kuma dan kasancearsu
Musulmi daga Arewa. Mu ne mutanan Arewa saboda Alkawari da san zaman
tare muka sadaukar da Shugabancin tarayya dake hannunmu muka dauka
sukutum muka mikashi ga Obasanjo! Anyi hakan da kyakkyawar niyya ko
akasin haka Allah shi ne mafi sani.
Tun bayan waccan dama da ta
subuce mana, inda Obasanjo da aka bashi amana ya dinga gasa mana aya a
hannu, har ta kai mun kai wani mataki da muke ta magagin yadda waccan
dama da muka dauka da hannumu muka bayar muke fatan dawowarta hannunmu.
Tun a shekarar 2003 da 2007 da kuma 2011 ake ta wannan fafutuka ta ganin
cewar ikon tarayya ya koma hannunmu, domin da yawan mutanan Arewa munyi
Imani cewar babu wani dan kudu da zai yi mana Adalci face idan har namu
ya samu, shi yasa muka makance muke nema ido rufe.
A dan haka,
kamar yadda na fada a baya cewar “ba’a yin bari a kwashe duka” inji ‘yan
magana, to lallai ya kamata mu fahimci wannan magana da kyan gaske, mu
kuma yi nazarin halin da muke ciki, mu kuma samarwa kanmu makoma ta
gaskiya.
A dalilin neman waccan makoma, muka makance muka kasa
tunanin meye abinda yafi kamata a garemu tunda mun kasance masu hamayya.
Wannan ta sanya muke kiran “lallai mulki ya dawo Arewa” wanda wannan
magana kuskure ce, da abinda yafi kamata shi ne mu ce lallai muna
bukatar Musulmi ya zama Shugaban kasa na gaba, tunda yanzu wanda yake
kai ba Musulmi ba ne.
Haka kuma, ba zai yuwu ba mu mika kukanmu
ga Allah mahaliccinmu muna masu neman agaji da taimakonsa, sannan kuma
mu sanya masa sharadi ba! Sharadin shi ne na cewar lallai sai dan Arewa
(Buhari) ya zama Shugaban kasa! Tur kashi… ina fatan mai karatu yana
biye da ni sosai kuma zai fahimci me nake nufi. Zanyi bayanin hakikanin
abinda nake nufi nan gaba.
GEN. MUHAMMADU BUHARI: kamar yadda na
fada a rubutun da na yi da yayi ishara zuwa ga wannan rubutun kuma nai
alkawarin bayar da dalilai na. Anan yana da kyau mu mutanan Arewa
Musulmi mu sani cewar ba wai Buhari ake ki ba, shi yasa aka ki bashi
zabe a baya ba, a’a mu din ‘Yan Arewa Musulmi mu ne ake ki, mu ne ba’a
so a zaman tarayya. Dan haka duk wanda yake zaton cewar a cire Buhari a
kawo Gwamna Rabiu Kwankwaso ko Atiku Abubakar a matsayin dan takara shi
ne ko ita ce mafita to bai fahimci al’amarin ba. Daman kuma masu magan
sun ce "da dan gari akanci gari"
Ko an tsayar da Atiku ko
Kwankwaso a wannan zaben da yake tafe, to abinda ya faru a baya shi ne
dai zai sake faruwa, babu wani zani da zata canza, kamar yadda na fada
mu dinne dai ba’a so. A dan haka ne duk wanda ya tsaya takara daga
cikinmu yake shan mamaki.
ATIKU ABUBAKAR: Masu magana suka ce
dama kwaya daya ce tal take zuwarwa wasu a rayuwa, idan sun yi azama
sukanci amfaninta lokaci mai tsawo. Atiku Abubakar yana daga cikin wadan
da suka samu dama mai kyau bayan zaben 1999, inda ya samu goyon bayan
mafiya yawan gwamnonin Arewa na lokacin dan ayi wancakali da Obasanjo ya
maye gurbinsa, amma Atiku ya barar da wannan damar.
Atiku ne fa
saboda dadin Mulki ya dinga cinnawa gidansa (Arewa) wuta ya manta cewar
idan sun gama Mulki zai baro Abuja ya dawo Arewa. Haka kuma, a baya ai
Atiku Abubakar yayi takara a 2007 kuma anyi abinda akai, me ya iya yi?
Don haka ko an sake tsayar da shi abinda akai masa a 2007 shi za a kuma
yi masa, babu kuma abinda zai faru sai hanayi da hargowwa da ba zata iya
canza komai ba.
GWAMNA RABIU KWANKWASO: Kwankwaso na daga cikin
manyan na hannun damar Obasanjo a lokacin da Obj din yake sharafinsa.
Ance har yanzu Gwamna Kwankwaso suna d'asawa da Obasanjo.
Gwamna
Kwankwaso na daga cikin sabbin zubin da ake masa fatan tsayawa takarar
Shugaban Kasa, da fatan zai yi abinda magabatansa suka kasa. Tauraruwar
Kwankwaso ta fara haskawa ne tun lokacin da ta bayyana cewar akwai
baraka tsakaninsa da Shugaban kasa, wanda wannan ta janyo masa farin
jini da karbuwa a wajen mutane da yawa. Kamar Buhari da Atiku shima
Kwankwaso babu wani abu da zai sauya idan ya zama dan takarar hamayya.
Dan haka maganin kar ayi kar a fara.
Kamar yadda na fadi cewar
Buhari zai fi zamarwa PDP karkatacciyar kuka mai dadin hawa idan ya zama
dan takara, domin an san shi an kuma san logar kayar da shi zabe. Kuma
PDP zasu fi kowa murnar kasancewarsa dan takara a wannan zaben, dan suna
da lissafinsu a hannu. Haka kuma, yana da kyau mu sani cewar matsalar
cin zabenmu mu ‘yan Arewa Musulmi a zaben tarayya a kudancin Najeriya
take.
Yana da kyau mu sani cewar PDP tana da girkakkiyar kuri’a a
kudu, kuma tana da hanyoyin cin zabe sama da dubu na halal da na haram a
kudancin Najeriya, a cikin jihohi goma sha bakwai (17) babu wata jiha
da PDP ba zata samu sama da kashi 50 ba fiye da yadda hukumar zabe take
bukatar kowane dan takara ya samu. Haka kuma, akwai jihohin da PDP tana
cin zabe 100 bisa 100 ko mutum daya baya mutuwa kafin zabe. A Arewa kuwa
babu wani dan takara dan Arewa da zai iya cin zabe a wata jiha 100 bisa
100!
Jam’iyyar PDP tana da tabbacin samun waccan kuri’ar ta
kudancin Najeriya, zata sameta ta hanyar halal da haram. Wanda
dan-takarar Arewa idan ya iya samun kashi ashirinda biyar a zabe na
tsakani da Allah to shi ne ya iya samun jiha daya tak a kudu, itama sai
anyi kamar ana yi.
A zaben daya gabata akwai jihar da Buhari
kwata-kwata bai je yakin neman zabe ba. Sannan kuma, a bangaren PDP suna
da masaniyar cewar Buhari na da karfi a Arewa, dan haka basu tayar da
hankalin sai sun ci jihohin Arewa kamar yadda suka yiwa na kudu cin-dare
daya, cin dari-bisa-dari ba, dan haka zasu dage ne wajen samun kashi
25, a lokacin da Buhari ko dan takarar Arewa yake murnar samun dubban
kuri’u a Arewa, itama PDP ta baza komarta inda ta yakuto kashi 25 din da
na Arewa ya kasa samu a kudu.
Zabe kuma ba zai taba cuwuwa a
kudu ko Arewa kadai ba. Dole dan takara yana bukatar samun Nasara a
jihohi 23 kafin ya samu Nasara, a yayin da mu a Arewa jiha 19 muke da
ita muna bukatar jiha hudu kenan daga kudu. A hakanma da sauran rina a
kaba! Domin a Arewa kana da jihar Plateau da Benue wanda ko ana ha-maza
ana ha-mata dan takarar Arewa ba zai iya cin Plateau ba, har gwara Benue
dan kiyayyarsu bata kai ta Berom ba.
A dan haka, duk wani
yunkuri na tsayar da Buhari ko Atiku ko Kwankwaso takara a zabe mai zuwa
tabbas karfafawa PDP guiwar cin nasarar wannan zabe ne. Watakila aji
wannan magana bambarakwai, ba mamaki wani yayi fart da garaje yace karya
ne… Amma dai abin da na sani shi ne lokaci ne kadai zai iya karyata
wannan magana tawa ko da kuwa duk an taru an karyatani, dan haka indai
da gaske muke kuma mun nufi Allah a wannan al’amari to dole Buhari da
Kwankwaso da Atiku su hakura da duk wani batu ko yunkuri na yin takara a
2015 indai da gaske dan al’umma suke! Watakila mai karatu yace sam ba
zata sabu ba, domin waye zai yi takarar kenan, ina nan dauke da amsar
tambayarka mai karatu, kai dai biyoni kaji inda zan sauka.
KALMAR
“IDAN” TAKWARA CE GA “DA”: Sau da dama in maganar wannan zaben ta taso,
mu mutanan Arewa mukance “IDAN” har Yarabawa suka zabi dan takararmu to
munci zabe! Wannan kalma ta “idan” tana nuna cewar bamu da wani tabbas
kenan akan Yarabawa dangane da wannan zabe, duk kuwa da cewa tsakanin mu
da su ‘yan Uba muke. Shi yasa idan abinda ya saba faruwa ya faru sai
muyi amfani da kalmar “DA” ma’ana da anyi kaza da kaza ya faru.
Ina
fatan mai karatu yana biye da ni, domin yanzu ne zamu yi bayanin
mafitar wannan halin da muke ciki na tsahin Bamabami da kaskanci da
karyewar tattalin arziki da koma baya ta fuskar ilimi da noma da kiwo da
harkar lafiya da wutar lantarki da sauransu. Ga mafita nan tafe.
MECECE
MAFITA A GAREMU? Wannan tambaya muhimmiya ce, da kowa zai so jin
amsarta, ba shakka amsar wannan tambaya tana da sauki, kuma ita ce zata
nuna makomarmu a wannan zabe da yake tafe. Watakila Allaah ne ya karbi
adduarmu abinda ya faru na hadaka ya faru tsakanin ‘yan siyasa a Arewa
da yankin Yarabawa suka hada kai dan samun mafita guda daya. Bari na
sake tuna mana abinda na fada dazu a baya, amaganar da na ce “ba’a yin
bari a kwashe duka” to lallai mu sani mu mutanan Arewa munyi bari dan
haka ba dole ba ne mu kwashe duka, sai dai wanda zai kwasu wanda ba zamu
iya kwashewa ba kuma mu barwa Allah.
Abinda nake nufi anan shi
ne duk ‘yan Arewa dake san yin takarar Shugaban kasa a APC su hakura a
dauko dan kudu Beyerabe Musulmi wanda ba Bola Tinuba ba, kuma ba Gwamna
Fashola ba. Yana da kyau mu sani cewar a halin da muke ciki a yanzu mu
‘yan Arewa muna bukatar wanda zai yi mana Adalci ne a zaman tarayya,
wanda ba zai zalince mu ba, wanda zai bamu hakkokinmu a matsayinmu na
‘yan Arewa Musulmi, kuma mutum wanda mu ‘yan Arewa ba zamu ji shakka
akansa ba.
A dan haka mutumin da nake ganin zaifi karbuwa a
wajenu fiye da duk wani Beyerabe shi ne Gwamnan jihar OSUN Abddul-Rauf
Aregbesola! Eh tabbas shi nake nufi, gwamna Aregbesola a ganina shi ne
mutumin da ‘yan Arewa ba zasu ji shakkar mara masa baya ba, kuma mutane
da yawa zamu nutsu cewar zai yi mana Adalci idan ya zama Shugaban kasa.
Dalili
akan haka shi ne, kamar yadda na fada a baya, matsalar cin zaben dan
Arewa a kudu take, na tabbata kuma nayi Imani idan ka kawo gwamna
Aregbesola daga yankin Yarabawa kana da tabbacin samun kuri’ar yankin
Kudu-maso-yamma gaba dayanta. Dan haka idan muka yi hakuri da damarmu
muka barwa ‘dan kudu Bayerabe Musulmi to ba shakka Shugaban Kasa
Goodluck Jonathan babu inda zashi, domin bayan ka rikita masa lissafi,
to ka kassara shi duniya da lahira. Mu kuma tuan cewar a baya mun
sadaukar da su Tafawa Balewa da Ahamadu Bello munyi hakuri da rashinsu,
balle kuma hakuri da tsayawa zabe!
Idan akayi haka, mutane daga
kudu irinsu Femi Fani-Kayode hankalinsu zai yi matukar tashi domin zasu
yi ta yin ihun Muslim-Muslmin Tiket, wanda ihunsu da maganganunsu babu
abinda zai karawa wannan tafiya sai karfi da kara samun yakini, domin
Yarabawa zasu jajirce wajen ganin sun zabi Rauf tunda Yarbawa Musulmi su
ne suke da rinjaye a yankin kudu maso yamma, tunda dan uwansu aka kawo.
Daman tun asali ai su Awolowo ne suke nuna cewar Yarabawa ba ruwansu da
addini dan kawai su danne yarabawa, amma wannan Magana ko kusa ba
gaskiya bace, domin duk wanda yasan yarabawa ya san mutane ne masu san
addini da san Musulunci. Mu kuma dole mu dawo daga rakiyar tuninmu na
cewar Beyerabe ba musulmin kwarai ba ne, yana fifita Yare akan addini,
wannan zato ne wanda shima kirkirarsa akai dan nesanta Musulmin Arewa da
Musulmin Yarbawa.
A dan haka, anan Arewa mu kuma zamu hadu gaba
daya mu zurarawa Rauf Aregbesola kuri’ah kan kace kwabo an fara lissafin
Rauf a matsan shugaban kasa na gaba. Ina fatan ya zuwa yanzu mai karatu
ya samu nutsuwa akan wannan batu, dan haka sai a samu mutum daga yankin
Arewa-maso-yamma a bashi mukamin mataimakin shugaban kasa ko dai Gwamna
Kwankwaso ko kuma wani zakakuri wanda zai iya tsolewa mutanan
kudu-maso-kudu da kudu-maso-gabas ido.
A ganina wannan ita ce
kadai hanyar da mulkin Najeriya zai dawo hannun dan Arewa a shekarar
2024, kaga daga nan sai muyi ta yi har illa masha Allah, inyamurai da
mutanan kudu-maso-kudu sai dai suga ana yi. Kuma wannan ita ce mafitarmu
a wannan zaben, tunda mufa mutanan Arewa bari muka yi, kuma ba zai taba
yuwuwa ba ace sai mun kwashe duka, waton hannun karba hannun mayarwa.
Dole ko mun so ko munki mulki ba zai dawo hannun dan Arewa ba sai da
‘yan dabaru.
Haka kuma, akwai wani kuskure da mu mutanan Arewa
muke tafkawa amma ko a jikinmu, domin a 2011 a yankin Arewa maso yamma
kadai akwai mutane kusan miliyan tara (9m) da suka yanki katin jefa
kur’ah amma basu yi zabe ba, shin ina suka shiga? Mutuwa sukai ko me?
Wannan kuri’ar fa tafi ta yankin Inyamurai baki daya, dan haka dole sai
munyi abinda ake kira da turanci Mobilization na kuri’un jama’a har
daren da za’a kada kuri’ah a samu wasu jajirtattun matasa su dinga bin
mutane gida-gida suna jaddada musu cewar lallai asubar fari ta yiwa
mutane a layin zabe, abi kauye-kauye, gari-gar, unguwa-unguwa, ina
tabbatar maka mai karatu 2015 sai Musulmi ya zama shugaban kasa indai
anyi haka da gaske kuma da kyakkyawar niyya.
Dan haka kamar yadda
na fada wannan ita ce kadai hanyar da nake ganin zamu iya samun zabe a
2015, kauce mata kuwa ko mun yarda ko bamu yarda ba karawa PDP kwarin
guiwar cin zaben Shugaban kasa ne. Buhari, Atiku, Kwankwaso kuwa sai mu
yi musu addua tare da nuna godiya amma su yi hakuri da takara dama ce
kuma ta wuce su. Yarabawa kuwa tuni ka sayesu ka biya kudin, domin
muddin muka basu wannan damar dole su tsaya kai da fata wajen ganin
dan-takara daga yankinsu yaci zabe. Ina fatan Allah ya nuna mana zaben
2015 rai da lafiya, ni da ku zamu zo nan facebook muna baiwa juna wannan
labarin ko akasinsa.
Wanda zai karyata yana da iko, wanda zai
gasgata shima yana da iko, amma ni dai nasan lokaci shi ne alkali, shi
zai gasgatani ko ya karyatani. Dan haka mai hankali yi tunani.
Yasir Ramadan Gwale
11-10-2014