SHEKAU MAI RAYUKA DA YAWA
Shugabannin hukumomin tsaro a
Najeriya sunyi ikirarin kashe Shekau a wannan karon, bayan a baya ansha
cewa an kashe shi amma a bada labarin ya sake b'ulla. A yadda naga
Olukolade na bada sanarwa da kwarin guiwar cewar sunfa kashe Shekau, ina
zaton da gasken ne, idan har haka ne batun munyi murna, muna kuma fatan
Allah ya sa ba za ayi baya babu zani ba, muna kuma yabawa sojojin da
suka sadaukar da rayuwarsu dan kare kasarmu Najeriya daga hare-haren miyagun 'yan ta'adda.
Amma ni abinda ya tsaya min a rai game da wannan batu shi ne, me yasa
sai yanzu da aka bayar da rahoton kama jirgin shugaban CAN da yunkurin
safarar makamai, akai irin wannan maza-maza haka? Bana shakkar cewar
anyi kokari wajen aika Shekau Barzahu, nayi murna da hakan.
Ina fatan Allah ya sa wannan karan anyiwa Shekau din kisan karshe, daga nan muji THE END akan al'amarin Boko Haram. Suma wadan da aka ce sunyi saranda sun mika kansu ga hukuma, ina fatan Allah ya sa sunyi tuba taubatan-Nasuha. Amma duk da haka ina tambayar ina makomar rayukan mutanan da wadannan sarandaddu suka kashe ba bisa hakki ba? Shin sunci banza kenan? Duk wata kungiya da taga dama ta dauki makamai da sunan ko ma meye su kashe wadan da suka ga dama, Alabashshi daga baya bayan anci galabarsu su ce sunyi saranda, hakan ya dace?
Lallai wadan da aka kashe ba bisa hakki ba, suna da hakkin a bi kadun jininsu. Masu kulle-kulle daga nesa ko daga kusa Allah ya sansu ya san duk abinda suke aikatawa, kuma yasan duk inda suke, Allah ya tona musu asiri. Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya mai dorewa. Allah ka sa wannan shi ne karshe Boko Haram.
Yasir Ramadan Gwale
25-09-2014